Rasha da Ukraine za su tattauna a mako mai zuwa

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce jami'an Ukraine za su tattauna da takwarorin aikinsu na Amurka a ƙasar Saudiyya a ranar Litinin mai zuwa, kuma wannan na zuwa ne bayan Rasha ta tabbatar cewa wakilanta za su tattauna da jami'an Amurka a ranar ta Litinin.
Jerin tattaunawar ta baya-bayan nan na zuwa ne yayin da Amurka ke ƙoƙarin samar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ƙasashen biyu bayan fiye da shekara uku ana gwabza yaƙi.
Shugaban Ukraine ya ce ya zama wajibi Rasha ta daina "gindaya sharuɗɗa marasa tushe waɗanda ke tsawaita yaƙin."
Shugaban Rasha Vladimir Putin na neman a yanke duk wani tallafin makamai da ƙasashe ke bai wa Ukraine.
Haka nan Zelensky ya yi gargaɗin cewa yin watsi da batun shigar Ukraine ƙungiyar NATO - wata buƙata da Rasha ta gabatar - tamkar "bai wa Rasha garaɓasa ne".

























