Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 04/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 04/01/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen shafin a yau, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    Amma kafin nan Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Yadda zamani ya sa ɗan'adam ya rage yawan aure

    Hannayen wasu ma'aurata

    Asalin hoton, Getty Images

    Yayin da ake ci gaba da samun manhajojin da ke haɗa ma'aurata marasa adadi, ake kuma samun bunƙasar soyayya tsakanin masoya, tambayar ko me ya sa ɗan'adam a ɗabi'arsa ba ya son haɗa aure da wani na ci gaba da kasancewa mai muhimmanci.

    Alina, ƴar asalin Romania mazauniyar London, ta riƙa mamakin kanta bayan da ta samu kanta da kishi a auren mutumin da ke da aure, 'polyamory' - yanayin da ake samun mutum fiye da ɗaya suna soyayya da mutum guda, kuma kowa na sane da hakan.

    "Ban jima da haɗuwa da mutumin da ke da aure da yawa ba, kuma shi kullum a haka yake,'' kamar yadda ta yi bayani.

    ''Ina son sanin: Me ya sa muka taƙaita da aure da mutum guda a al'ummarmu''?

    Hanya ɗaya ta fahimtar hanyar juyin halittar mu ita ce ta nazarin makusantan danginmu na farko da kuma dabarun haihuwarsu.

  3. 'An kashe jami'an da ke gadin Shugaba Maduro lokacin harin Amurka'

    Ministan tsaron Venezuela Janar Vladimir Padrino ya ce an kashe da dama cikin jami'an tsaron da ke gadin shugaban ƙasar Nicolas Maduro, lokacin harin da Amurka ta kai birnin Caracas.

    Sai dai bai bayyana yawan mutanen da aka kashe a yayin harin ba.

    Janar Padrino - wanda bayyana a tsakiyar sojoji ya buƙaci a gaggauta sakin Mista Maduro da matarsa, waɗanda ya ce an yi garkuwa da su.

    ''Wannan barazana ce ga duniya baki ɗaya, idan yau kan Venezuela aka faɗa, gobe ana iya afka wa wata ƙasar'', in ji shi.

    Ya kuma bayyana goyon bayansa da zaman Delcy Rodriguez a matsayin shugabar ƙasa ta riƙon ƙwarya.

  4. Tinubu ya umarci hukumomin tsaro sun kamo maharan Neja

    Tinubu

    Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umarci ministan tsaron ƙasar da babban hafsan tsaron ƙasar da manyan hafsashin sojin ƙasar da babban sifeton ƴansanda da daraktan hukumar tsaro ta farin kaya su farauto tare da kama maharan Kasuwan Daji da ke jihar Neja, domin su fuskanci hukunci.

    A ranar Asabar da maraice ne dai wasu mahara suka far wa ƙauyen Kasuwan Daji a jihar Neja inda suka kashe fiye da mutum 30 tare da sace wasu mata da ƙananan yara da ba a san adadinsu ba da kuma ƙona kasuwar da sace kayan abinci.

    Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Tinubu ya umarci jami'an tsaron ƙasar su kuɓutar da mutanen da maharan suka sace.

    Sanarwar ta ce ana zargin maharan sun taso ne daga jihohin Sokoto da Zamfara domin guje wa hare-haren da Amurka ta kai musu a jajiberin Kirsimeti.

    Haka kuma Tinubu ya aike da saƙon ta'aziyya ga iyalan mutanen da harin ya rutsa da su.

  5. 'Za mu yi aiki da sabuwar gwamnatin Venezuela idan ta yi abin da ya dace'

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya ce a shiye ƙasarsa take wajen yin aiki da sauran shugabannin Venezuela idan sun yi abin da ya kira ''ɗaukar matakan da suka dace''.

    Mista Rubio ya kuma ce Amurka za ta ci gaba da kama jiragen ruwa tare da ƙwace rijiyoyin mai, idan har ba a magance matsalar ƴancirani da masu safarar miyagun ƙwayoyi ba.

    Kalaman na babban jami'in diplomasiyyar na Amurka na zuwa ne kwana guda bayan dakarun Amurka sun kama Shugaba Maduro tare da tafiya da shi birnin New York don fuskantar tuhumar safarar miyagun ƙwayoyi.

  6. ‘Sun yanka mutane kamar kaji’:Yadda aka kashe fiye da mutum 30 a Neja

    Kasuwar

    Asalin hoton, Zakari Kontagora

    Al’ummar ƙauyen Kasuwan Daji da ke jihar Neja sun zama na baya-bayan nan da suka fuskanci cin zarafin ƴanbindiga, waɗanda suka kwashe kimanin shekara 10 suna kai farmaki a ƙauyuƙan arewa maso yamma da kuma arewa ta tsakiyar Najeriya.

    Wani ɗanjarida a jihar Neja ya shaida wa BBC cewa "Ƴanbindigar sun shiga garin a kan babura ɗauke da makamai, inda suka tattara mutane kuma daga baya suka riƙa bi suna masu yankar rago, wasu kuma suka harbe su. Wanda kawo yanzu an tattara gawarwaki aƙalla 42.''

    Wannan na zuwa ne ƙasa da wata biyu da wasu ƴanbindiga suka sace ɗalibai da malamai sama da 200 a ƙauyen Papiri da ke jihar ta Neja, lamarin da ya tayar da hankulan al’umma.

    Karanta cikakken labarin a nan

  7. Maduro ba halastaccen shugaban Venezuela ba ne - Rubio

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya ce Nicolas Maduro ''ba halastaccen shugaban Venezueala ba ne'', in da ya bayyana shi da ''mutumin da Amurka ba za ta yi aikin da shi ba''.

    Yayin wata hira da kafofin yaɗa labaran ƙasar, Mista Rubio ya ce yana ''fatan'' samun wasu mutanen da za su iya samar wa ƙasar sauyin da take buƙata, don ''inganta'' ta.

    "Babban muradinmu shi ne Amurka'', kamar yadda ya yi ƙarin haske, yana mai cewa dole a kawar da harkar miyagun ƙwayoyi da dabanci.

  8. Makusantan Maduro sun ce su ke da iko da Venezuela

    Delcy Rodriguez

    Asalin hoton, YUAN BARATTO AFP Via Getty Images

    Abokai da makusantan Shugaban Venezuela da Amurka ta kama, sun dage cewa su ke da iko da ƙasar.

    Shugar riƙo ta ƙasar, Delcy Rodriguez, ta yi kiran sakin shugaban ƙasar tare da shan alwashin ''kare'' ƙasar.

    Mista Trump ya ce Ms Rodriguez na son aiki da Amurka, yayin da ya ce jagorar adawar ƙasar, Maria Corina, ba ta samu cikakken goyon baya ba.

    Tun da farko shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ƙasarsa ce za ta ja ragamar ƙasar har zuwa lokacin kafa sabuwar gwamnati.

    Mazauna Caracas, babban birnin ƙasar, sun ce babu wadatattun jami'an tsaro a kan titunan birnin, duk kuwa da barazanar Trump na sake ƙaddamar da hare-hare.

  9. Fafaroma ya nuna damuwa da kama shugaban Venezuela

    Fafaroma

    Asalin hoton, Getty Images

    Fafaroma Leo ya ce dole ne a tabbatar da martabar Venezuela tare da walwalar ƴan ƙasar fiye da komai.

    Jagoran ɗariƙar Katolikan na duniya - wanda ya yi aiki na kusan shekara 20 a kudancin Amurka - ya ce yana biye da abubuwan da ke faruwa a Venezuela.

    Tun da farko China ta yi kiran a gaggauta sakin Shugaba Maduro, tana mai cewa Amurka ta keta dokokin duniya.

    Ana sa ran Mista Maduro zai gurfana a gaban kotu ranar Litinin domin fuskantar tuhume-tuhume kan safarar miyagun ƙwayoyi da makamai, zarge-zargen da a baya ya sha musantawa.

    A gobe ne kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani taro domin tattaunawa kan harin da Amurka ta kai wa Venezuela tare da kama shugaban ƙasar da mai ɗakinsa.

  10. 'Muna neman jam'iyyar haɗaka amma wadda za ta ba ni takara'

    Jagoran NNPP

    Asalin hoton, Rabi'u Kwnakwanso/X

    Jagoran Jam'iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana ɗaya aga cikin matakan da zai iya ɗauka don tunkarar zaɓen 2027.

    Yayin jawabinsa a wani taro na Kwankwasiyya, Sanata Kwankwaso ya ce "a matakin ƙasa muna neman jam'iyyar da za mu haɗa kai da ita, amma sai wadda za ta ba ni takarar shugaban ƙasa ko na mataimaki".

    Wannan na zuwa nea daidai lokacin da ake ci gaba da raɗe-raɗin shirin ficewar Gwamna Abba Kabir daga NNPP zuwa APC, lamarin da Kwankwaso ya bayyana ''tamkar mafarki''.

    Cikin jawabin nasa, jagoran na Kwankwasiyya ya kuma soki salon siyasar Shugaba Tinubu inda yake cewa tarin gwamnoni a jam'iyyar APC ba ya nufin tabbacin lashe zaɓe.

  11. Jirage marasa matuƙa sun yi ruwan bama-bamai a Sudan

    jerin gwanon jirage marasa matuƙa

    Asalin hoton, EPA

    Rahotonni daga Sudan na cewa hare-haren jirage marasa matuƙa sun faɗa jihar North Kordofan da ke tsakiyar ƙasar.

    Kamfanin samar da wutar lantarki na ƙasar ya ce ɗaya daga cikin hare-haren ya faɗa kan kamfanin a babban birnin jihar El-Obeid ranar Lahadi da safe, lamarin da ya haifar da katsewar lantarki a birnin, wanda sojoji ke iko da shi.

    Hukumomi sun ce sun kakkaɓo wani jirgin maras matuƙi da maraicen ranar Asabar a jihar.

    Yayin da rahotonni suka ce an kakkaɓo wasu da suka yi yunƙurin kai hari sansanin sojin sama da wani kamfani a kusa da jihar White Nile mai maƙwabtaka.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta damu da yawaitar amfani da jirage marasa matuƙa da duka ɓangarorin da ke yaƙi da juna a Sudan ke yi.

  12. Ƴanbindiga sun kashe fiye da mutum 30 a Neja

    Gwamnan Neja

    Asalin hoton, Mohammed Umaru Bago/X

    Bayanai daga jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Najeriya na cewa wasu ƴanbindiga sun kai hari jihar, inda suka kashe sama da mutum 30 tare da sace wasu da dama.

    Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun ya aike wa BBC ya ce ƴanbindigar waɗanda ake zargi sun fito daga dajin Kabe sun far wa Kasuwan-Daji da ke ƙauyen Demo da maraicen ranar Asabar, inda suka ƙona kasuwar tare da lalata shaguna da sace kayan abinci.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa da safiyar yau Lahadi ne haɗin gwiwar tawagar jami'an tsaro suka ziyarci yankin, kasancewar sun samu rahoton harin cikin dare.

    ''A lokacin ziyarar jami'an tsaron sun tarar da sama da mutum 30 da ƴanbindigar suka kashe, yayin da suka samu labarin sace wasu'', a cewar sanarwar.

    Jami'an tsaron sun tabbatar da cewa suna bakin ƙoƙarinsu don ganin sun kuɓutar da mutanen da ƴanbindigar suka sace.

    Jihar Neja na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da hare-haren ƴanbindiga.

    Ko a watan Nuwamban shekarar da ta gabata ma wasu mahara sun far wa makarantar sakandiren Papiri tare da sace ɗalibai fiye da 300, kodayake daga baya sun sako su.

  13. Mutum 25 sun mutu bayan kifewar kwale-kwale a Jigawa

    Danmodi

    Asalin hoton, Umar Namadi/X

    Bayanai daga jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya na cewa mutum 25 ne suka mutu bayan kifewar kwale-kwale a jihar.

    Sakataren ƙaramar hukumar Guri, inda lamarin ya faru Alhaji B Jaji Adiyani ya tabbatar wa BBC faruwa lamarin inda ya ce jirgin ya tashi daga garin Adiyani na yankin ƙaramar hukumar Guri zuwa garin Garbi da ke ƙaramar hukumar Nguru a jihar Yobe.

    Ya ƙara da cewa jirgin ya kife ne da misalin ƙarfe 8:00 na dare, sakamakon lodin wuce kima da aka yi masa.

    ''An loda wa jirgin fiye da mutum 40, wanda hakan ya saɓa wa ƙa'idar abin da ya kamata jirgin ya ɗauka, lamarin da ya tilasta masa kifewar'', in ji shi.

    Sakataren ƙaramar hukumar ta Guri ya ce zuwa yanzu an zaƙulo gawar mutum 25 daga cikin ruwan.

    ''Daga ciki mutum uku ƴan asalin Jigawa ne, sauran kuma ƴan Yobe ne kuma tuni aka wuce da su jiharsu domin yin jana'izarsu'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

    Ya ci gaba da cewa baya mutanen da suka mutum masu aikin ceto sun samu nasarar ceto wasu mutanen aƙalla 10 da rayukansu, waɗanda tuni aka garzaya da su babban asibitin Nguru.

    A lokuta da dama kifewar kwale-kwale kan haddasa asarar rayuka a Najeriya, wata matsala da masana ke alaƙanta da sakacin hukumomi.

  14. An tsare Maduro a gidan yarin New York

    Maduro

    Asalin hoton, @realDonaldTrump/Reuters

    Kafofin ya ɗa labaran Amurka sun bayar da rahoton cewa ana tsare da shugaban Venezueal, Nicolas Maduro da Amurka ta kama a gidan yarin New York.

    Gidan yarin ya yi fice wajen ajiye manyan fursunoni ciki har da Ghislaine Maxwell Ba'amurka ɗan asalin Birtaniya da aka samu da laifin safarar ƙananan ƴan mata domin karuwanci a 2021 da kuma Sean 'Diddy' Combs, fitaccen mawaƙin gambara na Amurka.

    Kawo yanzu dai ba a san inda matarsa tasa take ba.

    A ranar Asabar ne dai Amurka da kama shugaba Maduro da matarsa bayn ƙaddamar da manyan hare-hare a ƙasar.

    Inda daga baya aka gurfanar da shi a Amurka kan tuhumar zargin safarar miyagun ƙwayoyi da makamai.

    Tuni shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ƙasarsa za ta ci gaba da jagorantar Venezuela har zuwa lokacin kafa gwamnati.

  15. Kotun ƙolin Venezuela ta umarci mataimakiyar shugaban ƙasar ta karɓi mulki

    Delcy Rodriguez

    Asalin hoton, YUAN BARATTO AFP Via Getty Images

    Kotun Kolin Venezuela ta bayar da umarni ga mataimakiyar shugaban ƙasar, Delcy Rodriguez ta kama aikin shugaban ƙasar a matsayin mai riko, saboda abin da ta kira rashin kasancewar Mista Maduro - na tilas.

    A ranar Asabar ne Amurka ta kama shugaban ƙasar da mai ɗakinsa tare tafiya da su ƙasarta kan zargin hada-hadar miyagun ƙwayoyi da makamai- zargin da ya sha musantawa.

    Idan aka same shi da laifi za a iya yi masa ɗaurin rai da rai.

    Tun da farko Ms Rodriguez, ta yi wani jawabi kakkausa a ranar Asabar, inda ta zargi Amurka da sace Maduro, tana mai cewa Venezuela ba za ta taɓa zama wani yanki na mulkin Amurka ba.

    Ta bayyana hakan ne duk kuwa da kalaman Trump cewa ta bayyana aniyarta ta yin aiki tare da gwamnatin Amurka a wata tattaunawa da jami'ansa.

  16. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.