Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 04/09/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 04/09/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Haruna Kakangi da Aisha Aliyu Ja'afar

  1. Rufewa

    Masu bin shafin namu nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnim.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Amma kafin nan muke cewa mu kwana lafiya.

  2. Amurka ta sanar da bai wa Ecuador tallafin tsaro na dala miliyan 20

    Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya sanar da tallafin tsaro na kusan dala miliyan 20 ga ƙasar Ecuador domin daƙile ƙaruwar laifuka a ƙasar.

    Bayan ganawarsa da shugaban ƙasar, Daniel Noboa, a birnin Quito, Mista Rubio ya tabbatar wa taron manema labarai cewa, Amurka na fuskantar matsalar laifuka da fataucin miyagun ƙwayoyi daga Ecuador fiye da yadda ta saba gani a baya.

    Ya kuma sanar da cewa Amurka ta ayyana ƙungiyoyin wasu ‘yan daba biyu na Ecuador a matsayin ƙungiyoyin ta’addanci.

    Gwamnatin Trump ta fara tattaunawa da Ecuador, wadda ta ƙara ba da haɗin kai wajen daƙile kwararar baƙin haure ba bisa ƙa’ida ba zuwa Amurka, inda za'a dinga tisa ƙeyarsu zuwa Ecuadon.

  3. Sojojin Najeriya sun kashe ƴanbindiga 13 a Binuwai da Filato

    wasu yanbidiga riƙe da makamai

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Najeriya sun ce sun kashe mutum 13 da ake kyautata zaton ƴanbindiga ne masu garkuwa da mutane ciki har da jagororinsu a lokacin wani samame a jihohin Binuwai da Filato.

    Darakta yaɗa labaran ayyukan soji na shalkwatar tsaron ƙasar, Manjo Janar Markus Kangye ne ya bayyana haka a lokacin taron manema labarai ranar Alhamis a Abuja.

    Janar Kangye ya ce baya ga kashe ƴanta'addan, dakarun ƙasar sun kuma wargaza wani yunƙuri na satar ɗanyen mai da kudinsa ya kai naira miliyan 28, da wasu haramtatun rijiyoyin mai 17 a yankin Neja Delta.

    ''Haka kuma dakarunmu na rundunar Hadin Kai sun nuna turjiya wajen fuskantar ,ayaƙan Boko Haram, tare da kashe 13 daga ciki a wani kwanton ɓauna da mayaƙan na Boko Haram suka da bai yi nasara ba a yankin Kareto, da ke jihar Borno'', in ji Janar Kangye.

    Lamarin ya faru ne a ranar Laraba lokacin da dakarun ke yi wa tawagar kayan agaji rakiya a kan hanyar Gubio zuwa damasak.

  4. Fitaccen mai tallata tufafi na duniya Giorgio Armani ya rasu

    Giorgio Armani sanye da kwat da farar riga a ciki

    Asalin hoton, Getty Images

    Fiutaccen mai tsara tufafin sawa ɗan asalin Italiya, attajiri, Giorgio Armani, ya rasu yana da shekaru 91.

    Fitaccen mai tsara tufafin ya yi aiki tuƙuri wajen hidimta wa kamfanin a tsawon rayuwarsa.

    Bayan ɗan lokaci da ya yi a soji, Amani ya fara aiki na ɗan lokaci a matsayin mai shirya kaya a shago, kafin daga bisani ya fara tsara tufafi ga shahararrun mutane a duniya.

    Mista Armani ya kafa kamfaninsa mai ɗauke da sunansa a shekarar 1975, wanda daga baya ya zama ɗaya daga cikin manyan gidajen tallata kayayyakin sawa na duniya, da kuma shaguna kusan 2,000 a sassa daban-daban na duniya.

    Manyan mutane a faɗin duniya na ci gaba da aika wa da saƙonnin ta'aziyyar rasuwar marigayin.

    Firaministan Italiya, Giorgia Meloni, ta ce ta hanyar kwalliyarsa da sauƙin kansa da ƙirƙirarsa, ya haskaka harkar tallata kayayyakin sawa a Italiya tare da zaburar da duniya baki ɗaya.

    Ita ma fitacciyar mai tsara kayayyakin sawa Donatella Versa-ce, ta bayyana shi a matsayin gwarzo kuma abin tarihi da za'a dinga tunawa da shi har abada.

  5. Ayyukan mazaɓu na ƴanmajalisa tamkar fashi ne da rana tsaka - Obasanjo

    Obasanjo sanye da koriyar hula

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana ayyukan mazaɓu da ƴanmajalisar dokoki na ƙasa da na jihohi a matsayin tamkar fashi da rana tsaka.

    Obasanjo ya bayayan hakan ne cikin sabon littafinsa da ya wallafa mai suna ''Nigeria Past and Future: Contemplations on Nigeria’s History and Vision For Tomorrow''.

    Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana ƴanmajalisar wannan jamhuriya a matsayi mafiya muni fiye da na jamhuriya ta farko da ta biyu.

    Mai shekara 88 ya ce yana tuna wasu lokuta biyu da ya bata da ƴanmajalisar dokokin ƙasar a lokacin yana shugaban ƙasar.

    Mista Obasanjo - wanda ya mulki Najeriya sau biyu, lokacin soja da farar hula - ya ce ƙudirin kafa hukumar EFCC mai yaƙi da rashawa ya shafe fiye da shekara guda da gaban majalisar kafin ta amince da shi.

    Ba wannan ne karon farko da tsohon shugaban kasar ke zargin yanmajalisar dokokin ƙasar da wawure kudin ƙasar ba.

    A shekarar 2021 ma ya bayyanasu da ''marasa gaskiya kuma ƴan fashi'' a wani taro da aka gudanar a Legas.

  6. Sakataren lafiyar Amurka ya kare aikinsa a majalisar dokokin ƙasar

    Sakataren Lafiya na Amurka, Robert F Kennedy Jr, ya kare aikinsa na tsawon wata shida a gaban kwamitin majalisar dokokin ƙasar, wanda ya haɗa da yanjam'iyyar Democrats da kuma abokan hamayyarsu na Republican.

    Bayyanarsa a majalisar na zuwa ne mako guda da sallamar shugaban Cibiyar Kula da Cututtuka ta Amurka.

    Haka kuma ya kori manyan ƙwararru kan allurar riga-kafi tare da dakatar da bincike kan wasu alluran riga-kafin da ke ceton rayuka, matakin da ya janyo cece-kuce.

    Mista Kennedy ya ce dole ne a yi sauye-sauye a cibiyar saboda yadda ta gudanar da aiki a lokacin annobar COVID-19.

    A yayin musayar zafafan kalamai, ‘yan Democrats sun buƙaci ya yi murabus ko kuma a tsige shi.

  7. Hukumomin Nijar sun kama tsohon shugaban hukumar kwastam ta ƙasar

    Kanal Oubandawaki

    Asalin hoton, Medias Niger

    Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun kama tsohon shugaban hukumar hana fassa -ƙwabri ta ƙasar, Kanal Abou Oubandawaki, tare da tsare shi a gidan yar.

    Rahotonni sun ce jami'amn na Nijar na zargin Kanal Oubandawaki da hannu cikin wata badaƙallar wasu muƙudan kuɗi na taba sigari da aka shigar cikin ƙasar.

    Bayanai sun ce shugaban mulkin sojin ƙasar, Janar Abdourahamne Tiani ne ya bayar umurnin kama tsohon shugaban hukumar ta hana-fassa kwabri ko kuma Douane ta ƙasar.

    Ana tuhumar Kanal Abou Oubandawaki - wanda shi ma mamba ne a majalasar mulkin sojij ƙasar - ana tuhumarsa da hannau a badaƙalar tare da wasu laifuka da ake zargin ya aikata a lokacin da yake bakin aiki.

    Bayanai sun ce jami'an hukumar tattara bayanan sirri ta ƙasar ne suka kama Kanal Oubandawaki.

    A makon da ya gabata ne wata jarida mai zaman kanta a ƙasar ta sanar da binciko badakallar biliyoyin saifa a ma’aikatar hana fassa kwabri ta ƙasar.

    A ranar 11 ga watan Agusta ne aka naɗa Kanal Abou Oubandawaki a matsayin babban daraktan ma'aikatar hana fassa ƙwabri ta kasa a taron majalasar ministocin ƙasar, kafin a sauke shi a ranar 31 ga watan Maris ɗin da ya gabata.

  8. Ma'aikatan agaji a kan jakuna sun kai tallafi ƙauyen da aka samu zaftarewa laka

    Wasu mutane a kan jakuna

    Asalin hoton, Save the Children

    Ma'aikatan ƙungiyar agaji ta Save The Children haye a kan jakuna sun samu nasarar kai tallafin gaggawa na farko da ya ƙunshi abinci da magunguna da ruwan sha da tampol zuwa ƙauyen yammacin Sudan da ya fuskanci mummunar zarftarewar laka.

    Ƙungiyar agajin tare da haɗin gwiwar ofishin jin ƙai na Darfur da Majalisar Dinkin Duniya, ta aike da tawagar jami'an bayar da agajin gaggawa 11 a kan jakuna zuwa ƙauyen da ke cikin tsaunuka.

    Tafiyar ta ɗauke su fiye da sa'o'i shida sakamakon taɓo da ramuka a kan hanyar ƙauyen.

    Tawagar ta ƙunshi jami'an lafiya da ƙwararru wajen kare ƙananan yara da masu kula da lafiyar ƙwaƙwalwa,

    Tawagar za ta auna girman ɓarnar da mamakon ruwan sama ya haifar ranar Lahadi - domin duba yiwuwar buƙatr ƙarin agajin.

    Iftila'in - wanda ya yanke duka titunan da ke kai wa ga ƙuyane - ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutum 300 zuwa 1,000.

  9. Benjamin Hundeyin ya zama kakakin rundunar ƴansandan Najeriya

    CSPHundeyin zaune cikin kayan yansanda a ofishinsa

    Asalin hoton, Nigeria Police Force

    Babban Sifeton Ƴansandan Najeriya, Kayode egbetokun ya naɗa CSP Benjamin Hundeyin a matsayin sabon mai magana da yawun rundunar ƴansandan ƙasar (FPRO)

    Naɗin Hundeyin na ƙunshe cikin wata sanarwa da kakakin rundunar mai barin gado, Muyiwa Adejobi ya fitar.

    ‎”Babban Sifeton ƴansandan ya buƙace shi da aiki da ƙwarewarsa ta sadarwa wajen inganta aikin ɗansanda a Najeriya ta hanyar ƙarfafa hulda da jama'a,'' in ji sanarwar.

    Kafin sabon muƙamin, CSP Benjamin Hundeyin ya kasamnce kakain rundunar ƴansanda reshen jihar Legas, inda ya kwashe shekaru yana wannan aiki.

  10. Cutar Ebola ta sake ɓarkewa a DR Congo

    Wasu likitoci

    Asalin hoton, BBC World Service

    An samu rahoton sabuwar ɓarkewar cutar Ebola a Jamhuryar Dimokraɗiyyar Congo.

    Jami'an lafiya sun ce an samu mutum 28 da suka kamu sannan 15 suka mutu a lardin Kasai, ciki har da jami'an lafiya huɗu.

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce cutar - wadda aka fara ganowa a jikin wata mai juna biyu, wata biyu da suka gabata - ta bazu zuwa yankuna biyu na kudancin lardin.

    Gwaje-gwaje sun tabbatar da cewa cutar nau'in Zaire ce, da ba a fiye samu ba, amma kuma mai kisa.

    Wannan ne karo na 16 da ake samu ɓarkewar cutar a ƙasar tun bayan da aka fara ganota kusan shekara 40 da suka gabata.

  11. FCCPC ta ƙaddamar da dokokin kare jama’a daga tsangwamar manhajojin ba da bashi

    Hukumar kare masu siyan kaya ta Najeriya (FCCPC) ta ƙaddamar da sabbin dokoki domin daƙile tsangwama da satar bayanai, da sauran ɗabi’u marasa kyau daga masu ba da bashin kuɗi ta intanet a Najeriya.

    Hukumar ce ta sanar da hakan a cikin wata sanarwar da ta fitar a shafin sada zumuntarta na X.

    Shugaban hukumar, Tunji Bello ya ce ƴan Najeriya sun daɗe suna fuskantar tsangwama da satar bayanansu, da ɗabi’u marasa kyau daga masu ba da bashi ta intanet ko manhajoji da ba a tsara ba.

    "Waɗannan dokoki sun bayyana iyaka sosai cewa ana maraba da ƙirƙire-kirkire, amma ba tare da takura hakki da darajar masu amfani ko tauye doka ba."

    "Dokokin sun fara aiki ne tun 21 ga Yuli, 2025, kuma duk masu ba da bashi ta intanet da kuma ta manhajoji dole su yi rijista da hukumar FCCPC cikin kwanaki 90.

    Masu karya dokokin za su iya fuskantar tara har na naira miliyan 100 ko kashi 1% na kudaden da ke shigar musu, har ma da hana su aiki har tsawon shekaru biyar, in ji sanarwar.

    Dokokin sun hana ba da bashi kai tsaye ba tare da izini ba da karbar bayanai ba bisa ƙa’ida ba.

    Hukumar ta kuma buƙaci jama’a da su kai ƙarar masu ba da bashi waɗanda ba suyi rijista ba ko ba bisa ƙa'ida ba.

  12. Rundunar yansandan Kano ta kama masu yi mata sojan gona

    Hannu a ɗaure

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama ƴansandan bogi uku da ake zargi da yin damfara ta hanyar shigar burtu a matsayin ƴansanda a jihar Kano, bayan sun damfari wani mutum naira miliyan ɗaya da dubu talatin.

    Mutanen da aka kama sun fito ne daga ƙaramar hukumar Daura ta jihar Katsina inda aka kama su a ranar 2 ga Satumba, 2025, a Danagundi Quarters.

    Rundunar ce ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da Jama’a na ƴansanda, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar.

    Sanarwar ta ce "Kamar yadda bincike ya nuna, an kama su ne bayan wanda suka damfara ya nemi ɗauki, inda ya yi bayanin yadda abin ya faru.

    "Binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargi sun yi shigar burtu a matsayin ƴansanda inda suka yi iƙirarin cewa suna da wasu ƙwarewa na musamman da za su taimaka wa wanda aka damfara kuma suka umurce shi ya kai kudin wani wuri," in ji sanarwar.

    Daga nan ne jami’an ‘yansanda suka gaggauta ɗaukar mataki tare da haɗin gwiwar jama’a, wanda ya haifar da kama wadanda ake zargin.

    Ana ci gaba da gudanar da bincike, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala binciken.

  13. Sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram da yawa a dajin Sambisa

    Nigerian Army soldiers stand at a base in Baga on August 2, 2019

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Sojojin Najeriya a Baga na jihar Borno cikin shekara ta 2019

    Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta kashe mayaƙa sama da 15 a wasu hare-haren da ta kai ta sama a maɓuyarsu da ke dajin Sambisa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar, ta ce an kai hare-haren ne a ranar Laraba, 3 ga watan Satumba, a kan mayaƙa da kuma kwamandojin da ake alaƙantawa da wasu hare-haren da aka kai a baya-bayan nan.

    Najeriya na fama da rikicin ƙungiyar Boko Haram da ISWAP a tsawon shekara 16, lamarin da ya haifar da asarar dubban rayuka da tarwatsa miliyoyin mutane, wani abu da ya haifar da matsalar jin-ƙai.

    A baya-bayan nan al'umma a wasu yankunan jihar Borno sun shiga fargaba sanadiyyar dawowar hare-haren mayaƙan, inda a makon da ya gabata aka ruwaito yadda mayakan suka kashe kimanin mutum takwas.

    Harin saman na sojojin Najeriya na zuwa ne bayan "bayanan sirri sun tabbatar da ayyukan mayakan a yankin," kamar yadda mai maganar ya bayyana.

    Ya kuma ƙara da cewa harin ya lalata kayan aikin mayakan Boko Haram da Iswap da dama.

  14. Tinubu zai yi hutun kwana 10

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, STATE HOUSE

    Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya fara wani hutun kwana 10 daga yau Alhamis, inda yake sa ran yin kwanaki a ƙasashen Turai irin su Faransa da Birtaniya.

    Hakan na ƙunshe ne a cikin wani bayani da mai magana da yawo shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar a yau Alhmais.

    Sanarwar ta ce "Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja yau, 4 ga watan Satumba domin fara hutu a Turai, a matsayin wani bangare na hutunsa na aiki na shekara ta 2025.

    "Hutun zai ɗauki tsawon kwana 10.

    "Shugaban kasar zai kwashe wani lokaci tsakanin Faransa da Birtaniya kafin ya koma ƙasar."

  15. Yara da mata da aka wa magani bayan fuskantar lalata a DR Congo sun ninka sau huɗu

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Ƙungiyar kare haƙƙin yara ta Save the Children ta bayyana cewa adadin yara da mata da aka wa magani bayan fuskantar cin zarafi ta hanyar lalata a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DRC) ya ninka sau huɗu a farkon rabin wannan shekara, daga 612 a bara zuwa 2,702.

    Ma’aikatar Lafiya ta DR Congo ta ruwaito cewa cin zarafi ta hanyar lalata ya ƙaru da kashi 16 zuwa kimanin 73,400, inda kusan kashi daya bisa uku ‘yan mata ne masu shekaru ƙasa da 16.

    Rikice-rikice a gabashin ƙasar da hare-haren kungiyoyin masu ɗauke da makamai sun ƙara yawan cin zarafi ta hanayr lalata da yunwa da gudun hijira.

    Ƙungiyar ta ce duk da bayar da taimakon gaggawa, rashin kayan aiki da wahalar isa wurare na hana wasu samun kulawa, wanda ke ƙara haɗarin kamuwa da cututtukan jima’i da sauran matsalolin lafiya.

  16. Tsare-tsaren mu sun daidaita tattalin arziƙin Najeriya — Shugaba Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu

    Asalin hoton, FADAR SHUGABAN NAJERIYA

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce muhimman tsare-tsaren gwamnatinsa sun soma samar da sakamakon da ake buƙata, inda ya ce tattalin arziƙin ƙasar ya daidaita har ya soma janyo hankalin masu zuba jari daga ƙasashen duniya.

    Tinubu ya faɗi hakan ne a fadar sa da ke Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, a lokacin da ya karbi baƙuncin Oba Ghandi Afolabi Oladunni Olaoye, Orumogege III na Ogbomoso da tawagarsa.

    A cewar shugaban, halin ko-in-kula da rashawa da fasa kauri da yaudara ne su ka hana Najeriya samun kuɗaɗen shiga da za a yi amfani da shi wajen samar da ci gaba.

    ''Tattalin arziƙinmu ya fuskanci barazana, wajibi ne mu ɗauki matakai ƙwarara. Amma tare da adduo'in ku da haƙuri da juriyarku, ina farin cikin shaida muku cewa a yanzu tattalin arziƙi ya dai-daita'' In ji shi.

  17. Mutum 32 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a jihar Neja

    ...

    Asalin hoton, NSEMA

    An kawo ƙarshe aikin ceton da aka gudanar domin ceto mutanen da suka nutse sakamakon hatsarin kwale-kwale da ya faru a yankin Borgu da ke jihar Neja a Najeriya.

    Lamarin da ya faru a ranar Talata ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 32.

    Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar, Abdullahi Baba Ara, ya bayyana wa BBC cewa kusan duk waɗanda ake tunanin suna cikin kwale-kwalen da ya yi hatsari an gama aikin ceto a wurin.

    Ya ce, “Har an yi jana’izar waɗanda suka mutu, kuma waɗanda suka jikkata an garzaya da su asibiti inda aka ba su kulawa, kuma yawanci dukansu an sallamesu.”

    Baba Ara ya ƙara da cewa, “Bayani na ƙarshe da aka tantance zuwa jiya da dare ya nuna cewa mutum aƙalla 32 ne suka rasa rayukansu, yayin da guda 50 aka ceto. Muna kyautata zaton cewa saura mutum takwas da ba a gansu ba, amma ba za muyi ƙasa a gwiwa ba wajen aikin ceto su.”

    Ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne saboda kwale-kwalen ya yi lodin wuce kima, wato ɗaukar kaya da mutane fiye da yadda ya kamata.

    Hakanan, yayin da jirgin ke tafiya cikin ruwa, ya bugi kututture na icce, wanda ya haifar da kifewar kwale-kwalen.

    Dangane da dokokin da ke tabbatar da cewa jiragen ruwa ba sa yin lodin wuce kima, Baba Ara ya ce, “Akwai doka, amma kasan al’amari na ɗan adam, yawanci wasu ba sa bin waɗannan dokokin.”

    Hukumar ta ce za ta ci gaba da wayar da kan jama’a kan muhimmancin bin ka’idojin tsaron ruwa domin rage aukuwar irin wannan hatsari a nan gaba.

  18. Ma'aikatan ceto sun kasa isa yankin Darfur inda aka sami iftila'in zaftarewar ƙasa

    zaftarewar ƙasa

    Asalin hoton, AFP

    Yanayi da hanyoyi marasa kyau na ci gaba da kawo tsaiko ka ayyukan ceto da ake yi a yankin Darfur, inda ake fargabar zaftarewar ƙasa ta shafe wani ƙauye baki ɗaya.

    Shugaban bayar da agajin gaggawa na yankin Jebel da Tawila, Abdul Hafeez Ali, ya shaidawa BBC cewa sun gaza yin aiki yadda ya kamata saboda ƙarancin kayan aiki.

    Zaftarewar ƙasar, wadda ruwan sama mai ƙarfi ya janyo a ranar Lahadi, ya yi sanadiyyar rushewa ɓangaren wani tsauni.

    Yankin da abin ya faru ƙauye ne sosai, wanda ya sa ake samin mabanbantan rahotanni kan adadin waɗanda abin ya shafa.

    Mista Ali ya ce zuwa yanzu an gano gawarwaki 9, sai dai ƴan tawayen da ke iko da yankin sun ce alkaluman sun kai 270.

  19. Dattawan Arewacin Najeriya na son Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a yankin

    wasu yan bindiga ɗauke da makamai da alburusai a rataye a wuyansu

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar dattawan Arewacin Najeriya (NEF) ta buƙaci shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a yankin sakamakon matsalar tsaro da ke ci gaba da ta'azzara wanda ya lalata rayuka da tattalin arzikin ƙasar.

    A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyar, Farfesa Abubakar Jiddere ya fitar, ƙungiyar ta bayyana damuwarta kan hare-hare da garkuwa da mutane da kashe su ba ƙaƙautawa da ake ci gaba da yi a yankin.

    Ya yi gargaɗin cewa idan ba a magance matsalar ba, alummomi ka iya ɗaukar matakin kare kai wanda zai iya kai wa ga ƙazancewar rikicin da kuma kawo cikas ga dimokraɗiyyar ƙasar da zaman lafiyar yankin.

    "Muna kuma yi kira ga gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakai da dama ciki har da ayyana dokar ta-ɓaci domin ƙara duba girman lamarin, kuma ta aika jam'ian tsaro masu ƙwarewa tare da kayan aiki domin su kare fararen hula da tsare iyakoki." in ji ƙungiyar.

    Ƙungiyar ta kuma buƙaci "Gwamnati ta bayar da diyya da agaji ga waɗanda lammuran matsalar tsaro suka shafa ciki har da waɗanda suka rasa matsugunansu."

    Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnati ta ɗauki matakan da suka haɗa da ƙarfafa tsaron iyakoki, da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe makwafta cikin ƙungiyar ECOWAS da Tarayyar Afirka domin magance ayyukan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da ke ta'adi kan iyakoki, da kuma haɗa kai da ƙungiyoyin ƙasashen waje kamar Majalisar ɗinkin duniya domin samun tallafi.

  20. Amurka da Ecuador za su tattauna haɗin gwiwa kan harkokin tsaro

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya isa Ecuador, a wata ziyarar da ya kai da nufin haɗin gwiwa a fannin tsaro.

    Rubio zai gana da shugaban ƙasar Daniel Noboa wanda ya ba da fifiko kan magance tashe-tashen hankula a ƙasarsa.

    Kasar na jan hankalin ƙungiyoyin masu aikata laifuka daga ko ina a faɗin duniya saboda yadda ta zamo wata babbar hanyar safarar hodar iblis.

    Kusan kashi saba'in cikin ɗari na hodar iblis da ake amfani da ita a duniya na bi ta cikin kasar, da ke tsakanin kasashe biyu da aka fi samar da ita, wato Colombia da Peru.

    Ziyarar ta Mista Rubio na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Amurka ta kai hari kan wani jirgin ruwa da ake zargin yana safarar miyagun kwayoyi da ya taho daga Venezuela, lamarin da ya janyo mutuwar mutane goma sha ɗaya.