Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku irin wainar da ake toyawa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi a kan Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya na ranar 24/04/2026

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR

  1. Ba ma zumuɗin ƙulla alaƙar zaman lafiya da Iran - Pete Hegseth

    Sakataren tsaron Amurka, Pete Heg-seth, ya ce Washington ba ta zumuɗi wajen kulla yarjejeniya zaman lafiya da Iran.

    Yayin da yake magana a wani taron manema labarai, ya yi gargadin cewa toshe mashigar Hormuz na ƙara tsananta, kuma lamarin na shafar duniya baki ɗaya. Ya ce makomar kawo ƙarshen taƙaddamar na hannun Iran.

    Wannan furuci na nuna yadda ake samun maganganu masu karo da juna daga Amurka, bayan da Shugaban ta Donald Trump ya ce ya tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar, ba tare da wani wa'adi ba a farkon makon nan.

    Kafafen watsa labaran gwamnatin Iran sun ce ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Aragh-chi, na kan hanyarsa ta zuwa Pakistan, wadda ke shirin karɓar baƙuncin zagaye na biyu na tattaunawar zaman lafiya.

  2. Sojojin Isra'ila na shirin kai wa Hezbollah hare-hare

    Sojojin Isra’ila sun fitar da gargadin gaggawa ga mazauna garin Deir-A-mes da ke kudancin Lebanon, inda suka ce suna shirin kai hare-hare kan mayakan Hezbollah da ake zargi suna a yankin.

    Garin Deir-A-mes na arewacin yankin mai tsaro da Isra’ila ta ayyana, inda dakarunta ke ci gaba da aiyukan su, duk da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta ta makonni uku da aka amince da ita awanni kaɗan da suka gabata.

    Wakiliyar BBC ta ce Lebanon ta ce tana son fara tura dakarunta zuwa kudancin ƙasar domin ci gaba da kula da Iyakar yankin nan ta ke.

    Ministan yaɗa labaran ƙasar, Paul Mor-cos, ya ce babban sharadin Beruit shi ne janyewar sojojin Isra’ila daga yankin.

    Sai dai Isra’ila na cewa dole ne ta ci gaba da kasancewa a yankin, domin hana ƙungiyar Hezbollah da Iran ke marawa baya harba makaman roka zuwa cikin ƙasarta.

  3. Peter Obi na neman ƙulla ƙawancen siyasa da arewa maso gabas

    Ɗantakarar neman kujerar shugabancin ƙasa a jam'iyyar LP a 2023, Peter Obi ya jagoranci wata bababr tawaga ta ƴan siyasar kudu maso Gabas domin ƙulla ƙawance da arewa maso gabas da sauran sassan Najeriya da manufar ciyar da ƙasar gaba.

    Mista Obi ya faɗi hakan ne a ranar Alhamis a Bauchi bayan wata ganawa ta sirri da ya yi da gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad da masu ruwa da tsaki dangane da ƙulla ƙawancen siyasa.

    Peter Obi dai yana ta zagaye a faɗin ƙasar domin ƙulla ƙawance yayin da kakar zaɓe ke ƙara ƙaratowa.

    A makon da ya gabata ne dai magoya bayan Peter Obi da Rabi'u Musa Kwankwaso suka kafa wata ƙungiya mai suna OK movement da ke son goyon baya ga takarar Obi da Kwankwaso a matsayin shugaba da mataimaki a jam'iyyar ADC.

  4. Sarki Sanusi ya soki yawan cin bashi da gwamnatin Najeriya ke yi

    Sarki Muhammadu Sanusi na biyu ya nuna damuwarsa dangane da yadda gwamnatin tarayya ke ci gaba da dogaro ga ciyo bashi duk da cire tallafin man fetur da ƙasar ta yi.

    Da yake magana yayin wata hira da gidan talbijin na News Central TV ranar Juma'a, Muhammadu Sanusi ya yi gargaɗin cewa rashin alkilta kuɗi ka iya zagwanye cigaban da ake tunani za a samu sakamakon sauye-sauyen tattalin arziƙin da Najeriya ta yi.

    Sarki Sanusi wanda a baya ya yi kakkausar suka ga cire tallafin mai ya nanata cewa ba abu ne mai dorewa ba sannan ya soki yadda Najeriyar ta dogara kacokan a kan matatun mai na ƙasashen waje.

  5. Amurka na son ɗaukar matakin korar wasu ƙasashe daga NATO kan yaƙin Iran

    Rahotanni sun ce ma’aikatar tsaron Amurka, wato Pentagon, na nazarin wasu matakai na ladabtar da ƙasashen ƙungiyar tsaron na NATO, saboda rashin goyon bayansu ga yaƙin Amurka da Iran.

    Wani jami’in Amurka ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, wani saƙon imel ya nuna takaicin da take ji kan yadda wasu ƙawayenta ke ƙin bayar da damar amfani da sansanoninsu, da kuma izinin zirga-zirgar jiragen sama a sararin samaniyarsu.

    Daga cikin matakan har da yunƙurin dakatar da Spain daga NATO, da kuma duba yiwuwar sake nazarin amincewa da ikon Birtaniya kan tsibirin Foklands.

    A cewar wakilin BBC, wani jami’in NATO ya ce kundin yarjejeniyar ƙungiyar tsaron ta NATO bai tanadi dakatarwa ko korar mamba ba.

    A martaninta, Fadar Downing Street ta ce ikon mallakar tsibirin Foklands na hannun Birtaniya.

  6. Tarayyar Turai ta nemi a shigar da ƙwararru kan nukiliya a batun Iran

    Jami'ar tsare-tsaren ƙasashen waje na Tarayyar Turai, Kaja Kallas ta ce haɗarin Iran ka iya ƙaruwa idan ƙwararru kan nukiliya ba a shigar da su cikin tattaunawar da ake yi da Iran ba.

    Da take magana yayin wani taron shugabannin na Turai a Cyprus, Kaja Kallas ta ce duk wata yarjejeniya da za a cimma ka iya samun tasgaro fiye da yarjejeniyar baya ta 2015

    "Idan dai tattaunawar ta taƙaita ga shirin nukiliya kuma ba tare da ƙwararru a fannin nukiliya ba to yarjejeniyar ka iya lalacewa fiye da ta baya," in ji Kallas.

    "Sannan kuma idan ba a magance batutuwan makamai masu linzami ba da tallafa wa ƙungiyoyi bamsu riƙe da bindiga to tarayyar Turai za ta fuskanci barazana daga Iran" kamar yadda ta ƙara bayani.

  7. Iran da Pakistan na tattauna batutuwan da suka shafi tsagaita wuta

    Ministan harkoki ƙasar Iran ya ce sun tattauna batutuwan da suka shafi tsagaita wuta da manyan jami'an ƙasar Pakistan, a daidai lokacin da Pakistan ɗin take shirye-shiryen karɓar baƙuncin tattaunawar ta Iran da Amurka.

    Abbas Araghchi, a wata sanarwa a Telegram ya fadi cewa ya tattauna da Ishaq Dar, mataimakin firaiministan Pakistan tare da ministan harkokin Pakistan da kuma Field Marshall Asim Munir.

    Ya ƙara da cewa sun yi maganganu dangane da "ci gaban yakin gabas ta Tsakiya mai alaƙa da batun tsagaita wuta.

    Aragchi bai fayyace ko yana magana ne dangane da batun tsagaita wutar Iran da Amurka ko kuma ta Isra'ila da Lebanon ko kuma duka biyun.

  8. A Najeriya yan majalisar dattawa sun yi karin haske kan bukatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta neman su amince masa ya karbo rancen bashin dala miliyan 516 daga Babban Bankin Jamus domin gudanar da aikin gina babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry.

    Shugaban ya miƙa buƙatar ne ta hanyar wata wasiƙa da ya aike wa shugaban majalisar Dattijan Godswill Akpabio, wanda shi kuma ya karanta ta yayin zaman da aka yi a jiya Alhamis.

    Wasu yanmjalisar dattawan sun nuna goyon baya ga buƙatar yayin da kuma wasu ke cewa an daɗe ana neman amincewar majalisa kan irin wannan buƙatar ta aikin babbar hanyar ta Sokoto zuwa Badagry a jihar Legas

  9. Shugaban Kenya na shan suka saboda ya ce ƴan Najeriya ba su iya turanci ba

    Shugaban Kenya William Ruto na shan suka a shafukan sada zumunta bayan wasu kalamai da ya yi na shaguɓe kan yadda ƴan Najeriya ke turanci. Ya ce idan ƴan Najeriya na turanci sai mutum ya nemi tafinta kafin ya gane abin da suke cewa.

    Yayin da yake yi wa ƴan Kenya mazauna Italiya jawabi a ranar Litini, Ruto ya ce: "Idan kana sauraren yadda ƴan Najeriya ke magana, ba za ka gane me su ke cewa ba - sai ka nemi wanda zai fassara maka," inda ya bugi ƙirjin cewa ƴan Kenya na daga cikin mutanen da suka fi iya magana turanci a duniya.

    Kalaman nasa na shan suka daga ƴan Najeriya da wasu ƴan Afrika da suka zargi shugaban Kenyan da cin fuskar ƙasar da take a Afrika.

  10. Ƙasashen Afirka za su fuskanci matsalar bashi

    Wani kamfanin bincike da nazari kan al'amuran da suka shafi kuɗaɗe da kimanta ƙarfin tattalin arziƙi na ƙasashen duniya mai suna S&P Global Ratings, ya yi gargaɗi cewa yawan bashin da ake bin ƙasashen Afirka na iya ta'azzara, idan har yakin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran ya tsawaita.

    Kamfanin ya ce bashin da ƙasashen na Afirka za su buƙata zai ƙaru ne matuka, a sakamakon tasirin yakin.

  11. Ghana ta koka da nuna ƙyamar mutanensu da ake a Afirka ta Kudu

    Gwamnatin Ghana ta ce mahukuntan Afirka ta Kudu sun fara gudanar da bincike kan wasu hare-haren nuna kyama da ake kai wa ƴan ƙasar mazauna Afirka ta Kudu.

    Hotunan bidiyo da ke nuna ana cin zarafin 'yan Ghana a Afirka ta Kudu sun karaɗe shafukan sada zumunta na Intanet a ƴan kwanakin nan.

    Hare-haren ƙyamar baƙi wani lamari ne mai sarƙaƙiya, wanda matsalolin tattalin arziƙi da labaran ƙarya da rashin fahimtar tarihi ke haifarwa.

    Ana dai samun ƙaruwar zanga-zanga da tashin hankali kan nuna ƙyama ga waɗanda ba ƴan asalin Afrika ta Kudu ba musamman a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a ƙasar.

  12. Birtaniya ta ce ƴan China na sayar da bayanan sirrin jama'a

    Wani shirin tattara bayanai na lafiya na Birtaniya ya ɗora alhaki a kan masu bincike 'yan China marasa taka-tsantsan, kan yadda ake sayar da bayanan sirri na wajen mutum rabin miliyan da suka bayar da bayanansu bisa radin kansu.

    Ana dai sayar da bayanan ne a yanzu a wani shafin kasuwanci na intanet na China.

    Wata ƙungiyar agaji wadda ke gudanar da shirin tattara bayanan na Birtaniya ta gabatar da kanta ga hukumar da ke sa ido wajen kare bayanai ta Birtaniya.

    Shirin dai yana amfani da bayanan lafiya, na dubban mutane da na ƙwayoyin halittarsu na DNA, wajen inganta hanyoyin gano wasu cutuka masu tsanani da kuma magance su.

    Masu bincike a faɗin duniya na iya samun bayanan, amma bisa sharaɗi mai tsanani na tabbatar da kare sirri.

  13. Trump ya bayyana India da tambaɗaɗɗiyar ƙasa

    Gwamnatin India ta mayar da martani kan wasu kalamai da Shugaba Trump ya sake yaɗawa a shafin sada zumunta, kalaman da ke bayyana India a matsayin wata tambaɗaɗɗiyar ƙasa.

    Hukumomin Indiyar sun ce, kalaman ba su dace ba sam-sam kuma muzanci ne gare su.

    Ma'aikatar harkokin waje ta India ta ce kalaman ko alama ba su nuna irin ainahin alaƙar da ke tsakanin India da Amurka ba.

    Shugaban na Amurka ya yaɗa takardar bayanan wani shiri ne na siyasa wanda Micheal Savage ya gabatar, inda Savage din ya yi ƙorafi da cewa - duk jaririn da aka haifa a Amurka, nan take kai tsaye yake zama ɗan ƙasa, kuma wanda aka haifa ɗin nan sai ya shigo da gaba ɗayan 'yan uwansa daga China ko India ko kuma wata lalatacciyar ƙasa a duniya.

  14. BBC ta gano gidan da Jeffrey Epstein ke ajiye matan da yake lalata da su

    BBC ta bankado shedar da ke nuna cewa matan da Jeffrey Epstein, mutumin nan da aka kama da laifin lalata da ƙananan yara, ya riƙa ajiye su a gidaje daban-daban a birnin London, bayan da 'yansanda suka yanke shawara cewa ba za su bincike shi ba.

    Wakiliyar BBC ta ce, bincike a takardun da ma'aikatar sharia ta Amurka ta fitar, mun gano cewa yana biyan haya a aƙalla gidaje huɗu a London inda yake ajiye mata ɗaya daga cikin matan Virginia Giuffre.

    Ya kuma faɗa wa hukumar 'yansandan London a 2015 cewa - ta kasance wadda masu safarar mutane na ƙasa da ƙasa don lalata, wadda take da alaƙa da London, ta ci zarafi.

    A lokacin hukumar 'yansandan London din ba ta bude wani cikakken bincike ba kan lamarin, da cewa ba ita ce hukumar da ya kamata ta yi bincike ba.

    A yanzu ta ce, an shigar da ita tare da wasu hukumomin tsaron masu alaƙa ciki har da na Amurka, domin samun ƙarin bayanai don tabbatar da musayar bayanai a tsakaninsu.

  15. Amurka ta kama sojan da ya shiga cacar $400,000 kan cire Maduro

    Ma'aikatar sharia ta Amurka ta ce an kama wani sojin musamman na ƙasar wanda ake zargin ya samu sama da dala dubu 400, ta hanyar caca kan batun cire shugaban Venezuela Nicolas Maduro.

    Wakilin BBC ya ce maiakatar sharia ta gano sojan a matsayin Gannon Ken Van Dyke, wanda ta ce yana daga cikin wadanda suka tsara da aiwatar dakama Maduro a watan Janairu.

    'Yan sa'o'i kafin Shugaba Trump ya sanar da kama Nicolas Maduro, ana ganin sojan, Gannon Ken Van Dyke ya sanya caca - kan ko za a cire Maduro daga mulki, da kuma ko Amurka za ta mamayi Venezuela.

    Nan da nan wannan caca ta canke ta janyo aka fara bincike. Sojan na fuskantar tuhume-tuhume da dama, ciki har da satar jin bayanai, da samun kudin da hanyar da ba ta halal ba.

    Idan aka same shi da laifi zai iya fuskantar hukuncin daurin shekara har 50

  16. Trump ya tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar Lebanon

    Shugaba Trump ya ce za a tsawaita yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta ta Lebanon inda Isra'ila ke yaƙi da ƙungiyar Hezbolla da Iran ke mara wa baya da ƙarin mako uku.

    Wa'adin wadda ake kai yanzu zai ƙare ne a ranar lahadi.

    Trump ya sanar da ƙara wa'adin ne bayan wata ganawa ta biyu da manyan jami'an Lebanon da Isra'ila a Washington.

    Hezbollah ta yi suka ga tatattaunawar, yayin da Israila ta ci gaba da mamaye wasu sassan kudancin Lebanon.

  17. Buɗewa

    Masu bibiyarmu barkan ku da safiyar ranar Juma'a. Da fatan za mu samu albarkacin da ke cikin wannan rana. Allah ya sa hakan.

    Kamar kullum yau ma mun sake dawo muku da shafin BBC Hausa na kai tsaye inda muke kawo muku labarai da rahotanni dangane da irin wainar da ake toyawa a yaƙin Amurka da Isra'ila ke yi da Iran da kuma sauran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da mu.