Peter Obi na neman ƙulla ƙawancen siyasa da arewa maso gabas

Asalin hoton, Obi/Kwankwaso
Ɗantakarar neman kujerar shugabancin ƙasa a jam'iyyar LP a 2023, Peter Obi ya jagoranci wata bababr tawaga ta ƴan siyasar kudu maso Gabas domin ƙulla ƙawance da arewa maso gabas da sauran sassan Najeriya da manufar ciyar da ƙasar gaba.
Mista Obi ya faɗi hakan ne a ranar Alhamis a Bauchi bayan wata ganawa ta sirri da ya yi da gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad da masu ruwa da tsaki dangane da ƙulla ƙawancen siyasa.
Peter Obi dai yana ta zagaye a faɗin ƙasar domin ƙulla ƙawance yayin da kakar zaɓe ke ƙara ƙaratowa.
A makon da ya gabata ne dai magoya bayan Peter Obi da Rabi'u Musa Kwankwaso suka kafa wata ƙungiya mai suna OK movement da ke son goyon baya ga takarar Obi da Kwankwaso a matsayin shugaba da mataimaki a jam'iyyar ADC.










