Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC, wadda wasu manyan 'yanhamayya a Najeriya suka haɗu a ƙarƙashinta domin ƙalubalantar Shugaba Tinubu a zaɓen 2027 ta yi zargin cewa akwai wasu daga cikin gwamnatin Tinubun da ke neman tarwatsa shirin 'yanhamayyar.
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na riko kuma kakakinta Mallam Bolaji Abdullahi ya fitar a yau Litinin, jam'iyyar ta ADC ta bayyana cewa an gayyaci tsofaffin shugabannin jam'iyyar na jihohi da manyan ƙusoshin kwamitin zartarwarta na jihohin arewa maso gabas da arewa maso yamma wata ganawa ta sirri da manyan jami'an gwamnatin tarayya.
Sanarwar ta ce, ''muna da sahihan bayanan sirri cewa manufar wannan taron ba wai don tsaron ƙasa ba ne ko kuma samar da zaman lafiya.
Shiri ne na nufin harzuka su da tilasta musu idan ma ta kama a shigar da waɗannan mutane cikin wani ƙirƙirarren shiri na kawo cikas ga haɗakar hamayyyar.
''Wannan ba siyasa ba ce. Wannan zagon-ƙasa ne,'' in ji sanarwar.
Jam'iyyar ta ADC ta ƙara da cewa manufar shirin a bayyane take - ita ce haddasa ruɗani a cikin jam'iyyar, da haramta sabon shugabancin jam'iyyar tare da durƙusar da ita daga hanyar da ta kama ta bunƙasa a matsayin sabuwar fuskar 'yanhamayya.
Sanarwar ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya san da wannan maƙarƙashiyar da ta ce wasu daga cikin jami'an gwamnatinsa na yi, ya dakatar da su.
ADC ta ƙara da cewa Tinubu na buƙatar ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa shi mai kishin dimukuraɗiyya ne.
Jam'iyyar ta ce ya kamata shugaban ya tunatar da mutanensa cewa idan da gwamnatin Goodluck Jonathan ba ta juri hamayya ba kamar yadda wannan gwamnatin ke kasa jurewa to da APC ba ta ci zaɓe ba.
Kuma shi kansa Tinubun da bai zama shugaban ƙasa ba.