Adadin mutanen da suka mutu a ambaliyar Texas ya haura 80
'Abin da ya sa Kwankwanso bai shiga haɗakar ADC ba'
Rahoto kai-tsaye
Usman Minjibir da Abdullahi Bello Diginza
Rufewa
To jama'a masu bin wannan shafi na BBC Hausa na kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a yau Litinin 7 ga watan Yuli, 2025.
Sai kuma gobe Talata idan Allah Ya kai mu.
Mu kwana lafiya
An ɗaure mataimakin shugaban rundunar sojin Rasha saboda rashawa
Asalin hoton, Getty Images
An aike da tsohon mataimakin shugaban rundunar sojin Rasha gidan yari bisa zargin cin hanci da rashawa, a cewar kamfanin dillancin labarai na gwamnatin ƙasar TASS.
Kamfanin ya ce an sami Khalil Ars-lanav da laifin satar kuɗaɗen gwamnati da suka haura dala miliyan goma sha biyu, da kuma karɓar na goro da ya kai fiye da dala dubu ɗari da hamsin daga wani kamfanin sadarwa na soji.
An kuma yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 17 a gidan yari, yayin da wasu manyan hafsoshin soja biyu da ke ƙarƙashinsa su ma aka yanke musu hukuncin ɗaurin shekara shida da bakwai kowannensu.
Ba ruwan Najeriya da gwajin makamin nukiliya - Shettima
Asalin hoton, OTHERS
Mataimakin shugaba Najeriya Kashim Shettima ya ce ƙasar na nan daram - kai da fata a kan haramcin gwajin makaman nukiliya.
Shettima ya bayyana hakan ne a lokacin ganawa da tawagar hukumar yarjejeniyar hana gwajin makaman nukiliya ƙarƙashin jagorancin sakataren zartarwarta, Dr Robert Floyd, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce Najeriya kamar sauran ƙasashen Afirka da dama na fama da tarin matsaloli na zamantakewa da tattalin arziƙi da suka haɗa da fatara da talauci da sauyin yanayi.
Ya ce yanzu babban abin da ke gaban Afirka shi ne ta ga ta shawo kan matsalolin da ke barazana ga wanzuwarta - na fatara da kuma tasirin sauyin yanayi, amma ba batun mallakar makaman nukiliya ba.
A nashi ɓangaren jagoran tawagar hukumar, Dr Robert Floyd, ya yaba da ƙoƙarin Najeriya wajen cimma muradun hukumarsa.
Sannan kuma ya yaba da shugabancin Najeriya ƙarƙashin Bola Tinubu wajen bayar da gudummawar rage gwaje-gwajen makaman nukiliya a duniya, kamar yadda ya ce.
Tinubu na kitsa yadda zai gurgunta haɗakar 'yanhamayya - ADC
Asalin hoton, Facebook/Bola Ahmed Tinubu
Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC, wadda wasu manyan 'yanhamayya a Najeriya suka haɗu a ƙarƙashinta domin ƙalubalantar Shugaba Tinubu a zaɓen 2027 ta yi zargin cewa akwai wasu daga cikin gwamnatin Tinubun da ke neman tarwatsa shirin 'yanhamayyar.
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na riko kuma kakakinta Mallam Bolaji Abdullahi ya fitar a yau Litinin, jam'iyyar ta ADC ta bayyana cewa an gayyaci tsofaffin shugabannin jam'iyyar na jihohi da manyan ƙusoshin kwamitin zartarwarta na jihohin arewa maso gabas da arewa maso yamma wata ganawa ta sirri da manyan jami'an gwamnatin tarayya.
Sanarwar ta ce, ''muna da sahihan bayanan sirri cewa manufar wannan taron ba wai don tsaron ƙasa ba ne ko kuma samar da zaman lafiya.
Shiri ne na nufin harzuka su da tilasta musu idan ma ta kama a shigar da waɗannan mutane cikin wani ƙirƙirarren shiri na kawo cikas ga haɗakar hamayyyar.
''Wannan ba siyasa ba ce. Wannan zagon-ƙasa ne,'' in ji sanarwar.
Jam'iyyar ta ADC ta ƙara da cewa manufar shirin a bayyane take - ita ce haddasa ruɗani a cikin jam'iyyar, da haramta sabon shugabancin jam'iyyar tare da durƙusar da ita daga hanyar da ta kama ta bunƙasa a matsayin sabuwar fuskar 'yanhamayya.
Sanarwar ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya san da wannan maƙarƙashiyar da ta ce wasu daga cikin jami'an gwamnatinsa na yi, ya dakatar da su.
ADC ta ƙara da cewa Tinubu na buƙatar ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa shi mai kishin dimukuraɗiyya ne.
Jam'iyyar ta ce ya kamata shugaban ya tunatar da mutanensa cewa idan da gwamnatin Goodluck Jonathan ba ta juri hamayya ba kamar yadda wannan gwamnatin ke kasa jurewa to da APC ba ta ci zaɓe ba.
Kuma shi kansa Tinubun da bai zama shugaban ƙasa ba.
An kashe masu zanga-zangar ƙin gwamnati 11 a Kenya
Asalin hoton, AFP via Getty Images
'Yansanda a Kenya sun ce an kashe mutum 11 a zanga-zangar ƙin jiningwamnati a faɗin ƙasar.
A wata sanarwa da suka fitar sun kuma ce gomman 'yansanda sun ji rauni a tarzomar.
Hukumar kare haƙƙin ɗan'Adam ta gwamnatin Kenya, wadda ke sukar gwamnati kan matakin da ta ɗauka a kan masu zanga-zangar, akwai 'yandaba da suka rufe kawunansu ɗauke da muggan makamai irin su adda da suke aiki tare da 'yansandan.
Kafin wannan sanarwa wani asibiti a Nairobi, babban birnin ƙasar ya ce ya karɓi gawawwakin mutum biyu waɗanda suka rasu sakamakon harbin bindiga bayan 'yansanda sun buɗe wuta a kan masu zanga-zangar ta ƙin gwamnati.
A watan da ya gabata an kashe mutum 19 a lokacin zanga-zangar neman kawo ƙarshen zaluncin da 'yansanda ke yi.
Mutuwar wani mutum a hannun 'yansanda wanda suka tsare bisa zargin cin mutuncin wani jami'in ɗansanda a shafin intanet ita ta rura zanga-zangar.
Ministan sufuri na Rasha ya kashe kansa bayan an cire shi daga muƙamin
Asalin hoton, EPA
Bayanan hoto, Jami'ai sun ce an ga raunin harbin bindiga a jikin Roman Starovoyt
An samu tsohon ministan sufuri na Rasha mace a cikin motarsa a wajen babban birnin ƙasar, Moscow, 'yan sa'o'i bayan an sanar da tuɓe shi daga muƙamin.
Jami'an Rasha sun ce an ga raunin harbin bindiga a jikin, Roman Starovoyt, abin da ke nuna alamun ya kashe kansa ne.
Tun da farko yayin sanar da tuɓe shi daga muƙamin kakakin fadar gwamnatin Rasha (Kremlin) ,Dmitry Peskov, ya ƙi bayar da cikakken bayani kan abin da ya sa aka cire shi da ga muƙamin.
An sauke shi daga ministan ne bayan matsaloli da aka samu a ƙarshen mako a filayen jirgin sama na Rasha, inda aka soke ko jinkirta tashin ɗaruruwan jiragen sama saboda hare-haren jirage marassa matuƙa na Ukraine.
Kafafen yaɗa labarai na Rasha na cewa ƙila ana gudanar da bincike ne a kan Mista Starovoyt, a kan rashawa, amma kuma ba wata sanarwa ta hukuma da ta tabbatar da hakan.
Shugaba Trump ya aika wa ƙasashe 12 takardar lafta musu haraji
Asalin hoton, OTHERS
Shugaba Trump ya aika wa ƙasashe sama da goma sha biyu wasiƙu kan ƙarin haraji a kan kayayyakin da suke siyar wa Amurka.
A wasiƙar ya gaya wa Japan da Koriya ta Kudu cewa su yi tsammanin ƙarin harajin kashi 25 cikin ɗari daga ranar ɗaya ga watan Agusta.
Sai dai ba ƙasar da za ta biya harajin idan kamfanoninta suka yi kayayyakinsu a cikin Amurka.
Da farko Mista Trump ya sanar da abin da ya kira 'harajin ranar 'yanci' a watan Afirilu domin matsa lamba a kan ƙasashe a kan abin da ya kira tsare-tsare da manufofi na kasuwanci marassa adalci.
Ya dakatar da matakin tsawon wata uku bayan da ya rikita kasuwannin duniya.
An kammala zagaye na biyu na tattaunawar zaman lafiya a Gaza ba tare da cimma matsaya ba
Asalin hoton, Getty Images
An kammala zagaye na biyu na tattaunawar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas ba tare da cimma wata matsaya ba.
Sai dai wakilin BBC a Gaza ya ce akwai alamun cewa za a ci gaba da tattaunawar nan gaba a yau a birnin Doha.
A gefe guda kuma Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na shirin ganawa da shugaban Amurka Donald Trump a Washington.
Can kuwa a Gaza rundunar tsaro da agaji ta Zirin ta ce sojojin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa goma sha biyu a yau kaɗai.
Faransa za ta mayar wa Ivory Coast gangar tarihi da ta sace a lokacin mulkin mallaka
Asalin hoton, Pierre Firtion / RFI
Faransa za ta mayar wa Ivory Coast wata ganga ta musamman da ta sace a lokacin mulkin mallaka sama da shekara ɗari da ta wuce.
Al'ummar Ivory Coast na girmama gangar wadda a wancan lokacin suke amfani da ita wajen yin wata sanarwa ta gargaɗi.
Gangar mai tarihi wadda ake kira Djidji Ayôkwé, ko "Ganga mai magana", ƙatuwa ce da ta kai tsawon ƙafa goma.
A duk lokacin da aka buga gangar duk ƙauyukan da ke nisan kilomita talatin suna jin hirty kilometres around villages.
Turawan mulkin mallaka na Faransa sun ƙwace ta ne a 1916, suka kai ta Paris inda aka ajiye ta a gidan adana kayan tarihi da ake zuwa kallo.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi alƙawarin mayar da dukkanin kayan tarihi da aka sace daga ƙasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka, amma kuma masu sharhi na cewa ana jinkiri sosai wajen cika alƙawarin.
Amurka ta gamsu da matakin Lebanon na ƙwace makaman Hezbollah
Asalin hoton, Getty Images
Jakadan Amurka, Thomas Barrack, ya ce ya gamsu da yadda gwamnatin Lebanon ta amsa shawarar da Amurka ta gabatar na a kwace makaman Hezbollah.
Ya ce shawarwarin sun haɗa da samar da tsarin da zai daƙile rikicin Lebanon, duk da cewa har yanzu akwai abubuwan da ba a kammala ba.
Hezbollah ta gamu da babban rauni daga hare-haren soji da Isra’ila ke ci gaba da kai wa cikin dare.
Sai dai a ranar Lahadin da ta gabata shugaban ƙungiyar, Naim Qassem, ya sake jaddada cewa ba za su miƙa wuya ko a kwace musu makamai ba.
Shawarar Amurka na cewa Hezbollah ta miƙa duk makamanta nan da wata huɗu.
Ita ma, Isra’ila za ta dakatar da hare-haren jiragen sama tare da janye dakarunta daga matsugunan da take da su a kudancin Lebanon.
'Jihohin Najeriya tara da za a iya samun ambaliya tara cikin watan Yuli'
Asalin hoton, AFP
Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya Nimet ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a wasu yankunan ƙasar.
Nimet ta kuma gargaɗi mazauna wasu yankunan jihohin arewacin ƙasar tara su zama cikin shirin ko-ta-kwana sakamakon yiwuwar samun ambaliya.
Jihohin da ake sa ran samun ambaliyar sun haɗa da Jigawa da Yobe da Gombe da Plateau da Bauchi da Nasarawa da Kaduna da Katsina da kuma Kano.
Hukumar ta buƙaci mazauna kwari da waɗanda ke zaune a kusa da koguna a waɗannan jihohi su ɗauki mataki tare da zama cikin shiri.
Mutum biyu sun mutu bayan ƴansanda sun buɗe wuta kan masu zanga-zanga a Kenya
Asalin hoton, AFP via Getty Images
Mutum biyu sun mutu sakamakon harbin da ƴansanda suka yi kan masu zanga-zanga a Kenya.
Ƴansandan sun buɗe wuta ne kan ayarin wasu masu zanga-zanga a babban birnin Nairobi, na ƙasar.
Jami'an ƴansandan sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye tare da toshe hanyoyi domin hana jama’a isa tsakiyar birnin.
An shirya gudanar da zanga-zangar ne a faɗin ƙasar domin tunawa da fara zanga-zangar neman mulkin dimukradiyya a 1990.
Yawanci garuruwa sun kame saboda tsoron tashin hankali.
Masu fafutikar kare haƙƙin bil’adama sun zargi gwamnati da tura wasu ƴandaba da ta ɗauka haya domin lalata zanga-zangar baya-bayan nan, zargin da hukumomin tsaron suka musanta.
An zargi ministan ƴansandan Afirka ta Kudu da katsalandan a binciken kashe-kashe
Wani babban jami'in ƴansanda a Afirka ta Kudu ya zargi ministan ƴansandan ƙasar da katsalandan a lokacin binciken da ake yi kan kashe-kashen siyasa da aka yi a lardin KwaZulu-Natal.
Yayain da yake jawabi ga taron manema labarai, Janar Nhlanhla Mkwanazi ya ce binciken da ake yi kan kashe-kashen ya fallasa wasu manyan mutane a ƙasar, ciki har da ƴansiyasa da jami'an ƴansanda da ƴankasuwa masu harƙallar ƙwayoyi.
Jami'in yansandan ya ce ministan harkokin ƴansandan ƙasar, Senzo Mchunu ya bayar da umarnin dakatar da tawagar da ke jagorantar binciken daga aikin binciken.
Mista Mchunu ya musanta zargin katsalandan a binciken, kuma ya ce zai ɗauki matakin wanke kansa.
Ƴansiyasa daga jam'iyyu daban-daban sun yi kira ga Shugaba Cyril Ramaphosa ya ɗauki mataki game da batun.
Jihohin Najeriya uku na cikin shiri kan fargabar ɓallewar madatsar ruwan Lagdo ta Kamaru
Jihohin sun haɗar da Benue da Edo da kuma jihar Bayelsa, waɗanda tuni suka fara shiri don kauce wa barazanar ambaliyar, kamar yadda Jaridar Punch a ƙasar ta ruwaito.
Kodayake ma'aikatar albarkatun ruwa ta Najeriya ta yi watsi da rahotonnin da ke cewa an buɗe madatsar ruwan, tuni jihohin suka fara shirya wa barazanar.
Gwamnatin jihar Benue ta ce ta fara aikin wayar da kan jama'a sakamakon ƙaruwar saukar ruwan sama da ake samu a ƴan kwanakin nan.
Jami'ar yaɗa labarai na hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar, Tema Ager ta ce gwanatin jihar na jiran umarni daga ma'aikatar albarkatun ruwa ta ƙasar.
An kammala aikin ceto a Pakistan bayan gano gawa 27 da gini ya danne
Ma'aikatan agaji a Pakistan sun kammala aikin ceto na kwana uku a wurin da wani gini ya faɗi a birnin Karachi, bayan gano gawarwaki 27.
Mazauna birnin sun bayar da rahoton jin ƙasar tsagewar ginin kafin ruftawarsa a ranar Juma'a da safe.
Shekara uku da suka wuce ne hukumomi suka bayyana ginin a matsayin wuri maras aminci, amma mazauna wurin sun ce ba a ba su sanarwar ficewa daga wurin ba.
Faɗuwar gine-gine ba baƙon al'amari ba ne a Pakistan, inda a lokuta da dama ba a bin ƙa'idojin gine-gine.
Shugaban Uganda mai shekara 80 zai sake tsayawa takara bayan kusan shekara 40 a mulki
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, A shekarar 1986 ne, Yoweri Museveni ya fara shugabancin Uganda
Jam'iyyar NRM mai mulki a Uganda ta ayyana shugaban ƙasar, Yoweri Museveni a matsayin wanda zai yi mata takara a zaɓe mai zuwa.
Matakin zai bai wa shugaban ƙasar - wanda ya fi kowa jimawa kan mulkin ƙasar - damar tsawaita kusan shekara 40 da ya shafe yana jagorantar ƙasar.
A jawabin amincewa da takarar da ya yi, Mista Museveni ya ce idan ya yi nasara a zaɓen zai samu damar cimma muradinsa na mayar da ƙasar ''cikin jerin ƙasashen masu masu tasowa''.
Masu sukar shugaban, sun zarge shi da mulkin kama karya tun bayan da ya ƙwace mulkin ƙasar a matsayin jagoran ƴantawaye a 1986.
Tun daga lokacin ne ya riƙa lashe duka zaɓukan ƙasar da aka gudanar, yayin da aka yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima har sau biyu, domin cire ka'idar shekaru da wa'adi domin ba shi damar ci gaba da zama a kan karagar mulki.
Ƴansanda sun kama ƴan Ghana 19 da aka yi safararsu don 'sama musu aiki' a Najeriya
Asalin hoton, Others
Rundunar ƴansandan Najeriya ta kuɓutar da wasu ƴan Ghana 19 da ake zargin an yi safararsu zuwa Najeriya.
Cikin wata sanarwa da rundunar ƴansandan jihar Oyo ta fitar, ta ce an kama mutanen ne a Ibadan, babban birnin jihar.
Ƴansandan sun ce sun kuɓutar da mutanen ne bayan samun bayanan sirri kan ayyukan waɗanda ake zargi da safarar mutane a wasu gine-ginen birnin.
Kakakin ƴansandan, Adewale Osifeso ya ce matasan da suka haɗa da maza 14, mata biyar, an yaudare su zuwa Najeriya da nufin samar musu ayyuka.
Rahotonni na cewa tuni aka miƙa matasan hannun hukumar shige da ficen ƙasar domin faɗaɗa bincike.
Ana kuma sa ran mayar da su Ghana da zarar an kammala binciken.
Peter Obi ba zai taɓa zama shugaban Najeriya ba - Wike
Asalin hoton, BBC/Peter Obi
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jamiyyar LP, Peter Obi ba zai taɓa zama shugaban Najeriya ba.
A ƙarshen mako ne Peter Obi ya bayayna aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaɓen 2027 ƙarƙashin sabuwar haɗakar ADC.
To sai dai yayın da yake jawabi a wajen bikin ƙaddamar da wasu ayyuka a Abuja, tsohon gwamnan na jihar Rivers, ya ce burin na Mista Obi ba zai taɓa cika ba.
E "Ana cewa Peter Obi zai zama shugaban ƙasa, amma wacce ƙasa? Ku ba ku san wasu mutanen ba, kawai suna faɗin duk abin da ya zo bakunansu ne", in ji Wike.
"Ta yaya ƴan Najeriya za su amince da kai, a shekarar 1999 kana wata jamiyya, a 2006 ka shiga wata, haka ma a 2014 kana wata daban, sannan a 2019 ka sake komawa wata, yanzu a 2025 ka ce ka shiga wata don ceto ƙasa, wa za ka ceto?, inj Ministan na Abuja
Olubadan na Ibadan ya rasu yana da shekara 90
Asalin hoton, OYSG
Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin ya rasu, yana da shekara 90 a duniya.
Kakakin iyalan basaraken ne ya tabbatar da mutuwarsa da safiyar yau Litinin cikin wani saƙo da ya aike wa manema labarai.
Kwanaki biyu da suka gabata ne basaraken ya gudanar da bikin cikarsa shekara 90 a duniya a wani ƙasaitaccen biki da aka gudanar a fadarsa.
A shekarar da ta gabata ne aka naɗa Sarki Olakulehin a matsayin Olubadan na Ibadan bayan rasuwar wanda ya gabace shi Sarki Alli Okunmade II.
'Abin da ya sa Kwankwanso bai shiga haɗakar ADC ba'
Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba ta shiga ƙawancen haɗakar ADC shi ne saboda gudun saki-rishe- kama ganye.
Sakataren kwamitin amintattu na jam'iyyar, Injiniya Buba Galadima ne ya bayyana haka a hirarsa da BBC.
''Su ba su zo suka shiga tamu jam'iyyar ba, sai kawai mu bar tamu mu shiga tasu a wane dalili?'', in ji shi.
Buba Galadima ya ƙalubalnci duka ƴansiyasar Najeriya da kowa ya je ya kafa tasa jam'iyyar ya ga idan zai yi tasiri kamar ubangidansa Sanata Rabi'u Kwankwaso.
Fitaccen ɗan siyasar ya ce duk da cewa kafa haɗakar zai ƙarfafa adawa a ƙasar amma ya ce haɗakar na da jan aiki a gabanta.