Ƙananan hukumomi 9 ne ke fama da matsalar tsaro - Gwamnan Kano

Asalin hoton, Abba Kabir/Facebook
Gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatin sa ta mayar da hankali wajen tunkarar ƙaruwar matsalolin tsaro a jihar, kamar ayyukan ta'addanci da satar mutane da kuma satar shanu a wasu ƙananan hukumomi.
Da ya ke magana a taron majalisar zartarwa karo na 34 a fadar gwamnatin jihar, gwamna Kabir ya ce gwamnati na aiki tare da hukumomin tsaro domin magance matsalar da ke tasowa da dawo da zaman lafiya.
Ya ce ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Kunchi da Tsanyawa da Gwarzo da Kabo da Sumaila da Shanono da TudunWada da Doguwa da Rogo, inda ya bayar da tabbacin cewa ana ayyukan haɗin gwiwa domin toshe hanyoyin da ɓata garin ke amfani wajen shigowa.
A farkon makon nan ne dai wasu ƴan bindiga suka sace mutum 18 a wasu ƙayuka uku da ke yankin ƙaramar hukumar Tsanyawa a jihar.

























