Mu zama lafiya
Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafin na ranar Alhamis.
Mu haɗu da ku gobe da safe domin samun wasu labaran.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 07/11/2024
Usman Minjibir, Abdullahi Bello da Isiyaku Muhammed
Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafin na ranar Alhamis.
Mu haɗu da ku gobe da safe domin samun wasu labaran.

Asalin hoton, Reuters
Firaministan Hungary Viktor Orban ya ce shugabannin kasashen Turai 42 da ke taro a Budapest sun amince cewa dole su tashi tsaye wajen kare kansu, su kuma daina dogaro da Amurka.
Mista Orban, daya daga cikin shugabannin Turai kalilan masu kusanci da Donald Trump, ya ce shugabanni sun amince a tabbatar da zaman lafiya a Turai.Sai dai ba a fahimci abin da yake nufi ba ƙarara.
Shi ma shugaban Ukraine da ke halartar wannan taron, Volodymr Zelensky, ya ce akwai rashin adalci idan har aka bai wa Rasha zabi kan ta janye mamayarta a ƙasarsa.
Shugaban majalisar Turai, Charles Michel ya yi nuni da cewa "lokaci fa ya yi da ya kamata kasashen Turai su nema wa kansu mafita ta hanyar rike akalar makomarsu".
Akwai matukar damuwa cewa Mista Trump zai rage goyon bayan da Ukraine ke samu daga Amurka, abin da ya sa shugabannin Turai ke ta gargadin cewa bai kamata a bar Rasha ta yi nasara kan gwamnatin Ukraine ba.

Asalin hoton, EPA
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce ba shi da wata masaniya game da shirin Donald Trump na kawo ƙarshen yaƙin ƙasarsa da kuma Rasha cikin gaggawa.
Da yake magana yayin wani taron ƙasashen Turai a birnin Budapest, Zelensky ya ce bai tattauna batun da zaɓaɓɓen shugaban na Amurka ba.
Ya ƙara da cewa ya yi imanin Trump zai so ya kawo ƙarshen yaƙin cikin gaggawa amma ba lallai ne hakan ya yiwu ba, a cewar rahoton kamfanin labarai na Rueters.
Donald Trump ya daɗe yana cewa zai kawo ƙarshen yaƙin da zarar ya sake cin zaɓe "cikin kwana ɗaya".

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar lafiya a Najeriya ta ƙaddamar da wani shiri na yi wa mata masu ciki tiyata kyauta a faɗin ƙasar.
Shirin da aka yi wa take da Maternal Motality Reduction Innovation Initiative Mamii), an ƙaddamar da shi yayin wani taron bita na shekara-shekara a Abuja.
Ministan Lafiya Muhammad Ali Pate ya bayyana shirin da zimmar rage mutuwar mata yayin haihuwa a faɗin Najeriya.
"Babbar manufar wannan shiri ita ce yi wwa mata marasa ƙarfi tiyatar haihuwa kyauta, amma waɗanda suka cika ƙa'ida a asibitocin gwamnati da na kuɗi," a cewar ministan.
"Ta hanyar cire matsalolin kuɗi, muna ganin babu wata mace da ya kamata a bari ba tare da an kula da ita ba ko da ba ta da kuɗi."
Ya ƙara da cewa mutuwa yayin haihuwa na ci gaba da zama barazana, inda ƙananan hukumomi 172 ke haifar da kashi 50 cikin 100 na dukkan mace-macen da ake samu wajen haihuwa a faɗin ƙasar.

Asalin hoton, Citi Newsroom
Shugaban Ƙasar Ghana mai barin gado Nana Akufo-Addo na shan suka a shafukan zumunta bayan ya ƙaddamar da mutum-mutuminsa da kansa a yankin Yammacin ƙasar.
An ƙirƙiri makwafin domin girmama ayyukan da shugaban ya yi lokacin da yake kan mulki, a cewar ministan yankin Kwabena Okyere Darko-Mensah.
Sai dai 'yan Ghana da dama na ta tsokanar mutum-mutumin, wanda aka girke a wajen wani asibiti da ke birnin Sekondi, sua cewa "yabon kai ne".
"Mazauna yankin Yamma sun fi ƙarfin wannan yabon kan," a cewar wani ɗanmajlisar adawa Emmanuel Armah Kofi-Bash cikin wani saƙon X.
Addo wanda zai sauka daga mulki a watan Janairu bayan wa'adi biyu, ya yi kurin cewa ya cika kashi 80 cikin 100 na alƙawurran da ya ɗaukar wa 'yan Ghana.
Birtaniya ta ƙaƙaba takunkumi kan wasu kungiyoyin mayaka uku da ke samun taimako daga Rasha masu gudanar da ayyuka a kasashen Afirka, da kuma wasu kamfanoni da ta ce na taimaka wa sojojin Rasha.
Rundunar tsaron Rasha da ake kira "Africa Corps", wadda ta maye gurbin ɓangaren soji na Wagner, ofishin da ke sa ido kan harkokin katare na Birtaniya, ya ce sun kasance barazana ga tsaron kasashen Afirka da dama.
Wata sanarwa da suka fitar na cewa rundunar tsaron da wasu na sa-kai biyu na aikata laifukan keta hakki da cin zarafi, sannan Rasha na amfani da wannan dama wajen karfafa kanta da tasiri a yankunan Afrika.

Asalin hoton, Reuters
Shugaban kwamitin harkokin tsaro a Rasha, Sergei Shoigu, ya ce kasashen yamma na cikin wani yanayi na tsaka mai wuya game da yaƙin Ukraine.
A cewarsa, ko dai ƙasashen su shiga tattaunawa da Moscow kan kawo karshen yakin ko kuma su ci gaba da ba da tallafi da "na ruguza al'ummar kasar".
Mista Shoigu, wanda ya riƙe muƙamin ministan tsaro na wadanan bayanai ne a taron manyan jami'an tsaro na tsofaffin kasashe mambobin Tarayyar Soviet.
Yayin da Rasha ke ci gaba da danna kai a yankuna da dama na gabashin Ukraine a watannin baya-bayanan, Mista Shoigu ya ce a bayyane yake karara cewa Rasha na samun nasara a yakin.
Kalamansa na zuwa ne bayan wata sanarwar ma'aikatar tsaron Rasha da ke cewa ta yi nasarar kwace wani gari da ke yankin Donetsk.

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Nato chief Mark Rutte ya bayyana cewa za su zauna da zaɓaɓɓan shugaban ƙasar Amurka domin fuskantar barazanar da haɗuwar Rasha da Koriya ta Arewa ke ɗauke da ita.
Rutte ya bayyana hakan ne a cikin jawaban da ya gabatar a daidai lokacin da ake shirye-shiryen gabatar da taron shugabannin tarayyar Turai da za a yi yau a Budapest.
Da yake magana kan shiga yaƙin Ukraine da Rasha da Koriya ta Arewa ta yi, Rutte ya ce, "yana fatan zai zauna da Donald Trump," domin tattaunawa barazanar.
Ya ƙara da cewa haɗin kai tsakanin Rasha da Koriya ta Arewa zai jawo "barazana babba ba ga ƙasashen ƙungiyar Nato kaɗai ba, har ma da Amurka."
A watan jiya ne Nato ta ce a karon farko ƙasar Koriya ta Arewa ta aika sojojinta zuwa Rasha.

Asalin hoton, Reuters
Ƴansanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa ɗaruruwan masu mas zanga-zanga, waɗanda suka taru babban birbin Maputo na ƙasar suna ci gaba da nuna rashin jin daɗinsu kan sakamakon zaɓen ƙasar.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam sun ce an kashe aƙalla mutum takwas daga farkon ɓarkewar zanga-zangar zuwa yanzu.
Jam'iyyun hamayya sun zargi jam'iyyar FRELIMO mai mulki da maguɗin zaɓe, wanda shi ne ya jawo zanga-zangar, wadda zuwa yanzu ta kai mako ɗaya.
Jam'iyyar Frelimo wadda ke mulkin ƙasar Mozambique tun shekarar 1975, ta yi ikirarin sake samun nasara a zaɓen da aka yi, duk da binciken ƙungiyoyin sa ido na ciki da wajen ƙasar sun bayyana cewa an takfa maguɗi a zaɓen.
Ko a zaɓukan baya an zargi jam'iyyar da yin maguɗin zaɓe, duk da cewa ta musanta aikata hakan.
Ƙungiyar lauyoyi ta Mozambique ta yi kira da shugaban ƙasar, Filipe Nyusi da ya, "kira tattaunawa," da dukkan waɗanda abun ya shafa, ciki har da ɗantakarar shugaban ƙasa Venâncio Mondlane domin samun maslaha.

Asalin hoton, TCN
Baban layin lantarki na Najeriya, ya sake faɗuwa, lamarin da ya sake jefa wasu sassan ƙasar cikin rashin wutar lantarki.
Faɗuwa - wadda ta auku da misain karfe 11:28 na safiyar yau Alhamis - ita ce ta biyu cikin mako guda, sannan ta 10 a 2024.
Bincike da aka yi kan shafin 'Independent System Operator', wanda sashe ne na TCN ne mai kula da fannin rarraba wutar, ya nuna cewa babu wuta a duka tasoshin samar da wuta daga babban layin.
Kawo yanzu dai kamfanin rarraba wutar na TCN bai yi bayanin dalilin faɗuwar ta baya-bayan nan ba.
Faɗuwar babban layin na lantarki na neman zama wata matsala ta yau da kullum a Najeriya, wani abu da 'yan ƙasar da dama ke ɗora alhakinsa kan gwamnatin ƙasar.

Asalin hoton, Nigeria Police/X
Babban sufeto janar na ƴansandan Najeriya Kayode Egbetokun ya buƙaci ƴansandan Najeriya su ɗaura baƙin kambi a hannunsu na tsawon kwana bakwai domin nuna jimamin rasuwar babban hafsan sojin ƙasan Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.
Kayode Egbetokun ya yi wannan kiran ne a wata sanarwa da kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi ya fitar.
"Bayan rasuwar babban hafsan sojin ƙasan Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, babban sufeton ƴansandan Najeriya Kayode Egbetokun ya buƙaci ƴansandan su ɗaura baƙin kambi a hannu na tsawon kwana bakwai domin jimamin rasuwar babban hafsan".
“An bayar da umarnin ne domin alhini da girmamawa kan irin sadaukarwa da jajircewa da yaƙi da miyagun laifuka da ya yi. Shi ɗin babban jagora ne da ya dace da girmamawa ta ko'ina''.
Babban hafsan sojin ƙasan ya rasu ne a ranar Talata bayan fama da jinya.

Asalin hoton, Abba Kabir Yusuf/X
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci ƙungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa su dakatar barazanar yajin aikin da suka yi.
Cikin wani jawabi da ya yi wa haɗakar manema labarai a jihar ranar Laraba da daddare, gwamnan ya yi gargaɗin cewa hakan zai sanya rayukan al'ummar jihar fiye da miliyan 20 cikin hatsari.
Abba Kabir Yusuf ya tabbatar wa ƙungiyar likitocin cewa kwamitin bincike da ya kafa - kan zargin kwamishinar ayyukan jinƙai ta jihar da cin zarafin wata likita a asibitin Murtala - ya kammala tattara rahotonsa, kuma yanzu haka rahoton na kan teburinsa, kuma zai ɗauki mataki a kai.
Ƙungiyar likitocin dai ta bai wa gwamnan wa'adin sa'o'i 48 ya kori kwamishinar, ko ta tsunduma yajin aiki.
Gwamnan ya kuma bayyana damuwarsa kan matakin ƙungiyar kan abin da ya kira ''saɓani tsakanin mutum biyu'' bai kamata ya haifar da matsalar jinƙai ba.

Asalin hoton, Other
Kamfanonin dillancin wutar lantarki a Najeriya sun sanar da ƙarin farashin kuɗin mitar wutar lantarki ga waɗanda suke amfani da ita a Najeriya.
Kamar yadda kanfanin dillancin wutar na Discos ya wallafa a shafinsa na X, sabon farashin ya soma aiki nan take tun daga ranar Talata, 5 ga watan Nuwamba da muke ciki.
Wannan dai shi ne karo na biyu a cikin wata huɗu da aka yi irin wannan ƙarin na kuɗin mita.
Masu amfani da wutar lantarkin sun koka da ƙarin, inda suka kira lamarin a matsayin rashin tausayi.
Koriya ta Kudu ta ce kawo yanzu ba ta cimma matsaya kan ko za ta saida wa Ukraine makamai ba, bayan matakin da maƙwabciyarta Koriya ta Arewa ta ɗauka na tura dakarun da suke taimakawa na Rasha yaƙi a Ukraine.
Shugaba Yoon Suk Yeol, ya ce zai ci gaba da sa ido kan hannun Pyongyang a yaƙin, kuma cikin tsanaki Seoul za ta tallafawa Kyiv kan saida makaman.
Ya kara da cewa shigar Koriya ta Arewa yaƙin babbar barazana ce ga tsaron ƙasarsa, saboda sojin ƙasar na ƙara samun gogewa a fagen daga da sanin makaman zamani da sojin Rasha ke amfani da su.

Asalin hoton, Kaduna Gov/X
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bai wa masu zanga-zangar tsadar rayuwa da aka saki kyautar manyan wayoyi da kuɗi kimanin naira 100,000.
Gwamnan ya kuma alƙawarta bai wa mutum 39 'yan jihar da aka saka -horo domin sake musu tunani, tare da ba su jari, idan sun kammala samun horon.
Sakataren gwamnatin jihar, Abdulkadir Meyere ne ya bayyana haka, kamar yadda jaridun ƙasar suka ruwaito.
Ya ƙara da cewa gwamnan jihar ya bayar da umarnin da ya karɓi takardun matasan da suka kammala karatu a cikinsu.
“Gwamna ya alƙawarta cewa za a bayar da jari ga wasunsu domin su fara sana'a, yayin da za a koya wasu sana'o'in wasu kuma gwamnati za ta ɗauke su aiki,” in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin Kamaru sun ce aƙalla mutum huɗu sun mutu yayin da ba a san inda 50 suke ba, bayan da motocin fasinja da ma'aikatan hanya suka maƙale sakamakon zaftarewar ƙasa a yammacin ƙasar.
Wurin da lamarin ya faru, kan babban titi ne da ya haɗa Dschang a yankin yammacin ƙasar da babbar cibiyar kasuwancin Kamaru wato Douala.
Ministan ayyuka na ƙasar, Emmanuel Nganou Djoumessi ya ɗora alhakin matsalar kan sauyin yahayi da ya ce ta haddasa mamakon ruwan sama.
To amma gwamnan Lardin Yammacin ƙasar, Augustin Awa Fonka ya ce lalacewar titunan yankin na daga cikin manyan dalilai.
A wannan shekara yankin Yammacin Afirka ya fuskanci ambaliya mafi muni cikin gomman shekaru, lamarin da ya haddasa mutuwar fiye da mutum 1,000 tare da raba dubbai da muhallansu.

Asalin hoton, Other
Har yanzu ana ci gaba da jimamin rasuwar babban hafsan sojin ƙasan Najeriya, Taoreed Abiodun Lagbaja, wanda tuni shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayar da umarni a rage ɗagawar da ake wa tutocin Najeriya a ƙasar.
Janar Lagbaja ne dai mutum na uku da ya rasu a lokacin da yake riƙe da muƙamin babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya.
Lagbaja ne babban hafsan sojin ƙasan Najeriya 23, kuma ya riƙe muƙamin ne tsakanin Yunin 2023 zuwa Nuwamban 2024, inda ya rasu yana da shekara 56 a duniya bayan fama da jinya.

Asalin hoton, Defence HQ
Baya ga Janar Lagbaja ga wasu manyan hafsoshin sojin ƙasar biyu da suka rasu lokacin da suke riƙe da muƙamin.
Laftanar Janar Attahiru
Attahiru shi ne babban hafsan sojin ƙasan Najeriya 21, wanda ya riƙe muƙamin tsakanin Janairun 2021 zuwa Mayun 2021, bayan ya maye Latfanar Janar Tukur Buratai.
Attahiru ya rasu yana da shekara 54 a hatsarin jirgin sama wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna.

Asalin hoton, Defence HQ
Attahiru ya ƙarbi ragamar shugabantar rundunar sojin ƙasa ne a daidai lokacin da rashin tsaro a arewa ya yi ƙamari.
Joseph Akahan
Joseph ne babban hafsan sojin ƙasan Najeriya na biyu, wanda ya riƙe muƙamin lokacin yana muƙamin Laftanar Kanal, kuma ya yi shekara ɗaya da wata tara, daga Agustan 1966 zuwa Mayun 1968, inda ya rasu yana da shekara 31.
Ya kasance cikin jagororin juyin mulkin 1966, kuma ya rasu ne a hatsarin jirgin sama a lokacin yaƙin basasar Najeriya.
Shi ne ya jagoranci ƙwato yankin Bonny daga wajen sojojin Biyafara, sannan ya kafa sansanin sojin ruwan Najeriya.

Asalin hoton, Getty Images
Masu buƙata ta musanman a Najeriya sun koka ga gwamnatin Bola Ahmad Tinubu cewa suna fuskantar ƙalubale na tsadar rayuwa, wanda a yanzu abincin da za su ci tare da iyalansu ke neman gagararsu.
Sun ce yanayin da ƙasar ke ciki ne ke tilasta musu fita cikin birane domin samun abin da za su ci, tare da ciyar da iyalansu.
Sai dai sun yi ƙorafin cewa maimakon samun abincin, sauna ƙarewa a hannun hukumomin da suke kama su tare da zarginsu da haifar da barazana ga tsarin birane da tsaro.

Asalin hoton, Abba Kabir/Facebook
Gwamnatin Kano ta fara tantancewa tare da yi wa ƴan ƙasashen waje mazauna jihar rajista da irin kasuwancin da suke yi.
An fara rajistar ne daga Kantin Kwari, domin tattara bayanan ƴan ƙasashen waje da suke zaune a jihar da sanin haƙiƙanin irin kasuwancin da suke yi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a jiya Laraba, wasu ƴan ƙasashen waje, musamman ƴan China da India sun je wajen rajistar domin a tantance su.
Sun kai takardu irin ru fasfo da sauran bayanansu, sannan wasu sun zo abokan kasuwancinsu ƴan jihar ta Kano domin tsaya musu.
Barista Tijjani Ahmed Falgore, wanda jami'i ne na ma'aikatar kasuwanci, wanda kuma yake cikin kwamitin rajistar, ya ce wasu ƴan ƙasashen wajen suna zaune ne a ƙasar ba tare da biyan haraji, wanda hakan ne ya sa aka ƙafa kwamitin.
"Maƙasudin shi ne a tantance daɗewarsu a ƙasar da kuma irin kasuwancin da suke yi a Kano," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa akwai sama da ƴan ƙasashen waje 6,000 a Kano.
An kafa kwamitin ne a ƙarƙashin Alhaji Lawal Isa Kibiya, wanda tsohon jami'in shigi da fice.

Asalin hoton, Reuters
Aƙalla mutum 40 ne hare-haren Isra'ila suka kashe a Lebanon a jiya Laraba, kamar yadda ma'aikatar lafiyar Lebanon ta bayyana.
Wani jami'in gwamnatin Isra'ila ya ce sun kai hare-haren ne a yankunan Baalbek da Bekaa kan ƴan ƙungiyar Hezbollah.
Ma'aikatar al'adu ta ƙasar Lebanon ta ce ɗaya daga cikin hare-haren ya lalata wani tsohon gini wanda aka yi tun a zamanin daular Usmaniyya a birnin Baalbel, wanda a da yake ƙarƙashin kulawar hukumar kula tayan tarihi ta Majalisar Ɗinkin Duniya wato Unesco.
A ɗaya ɓangaren kuma, wata roka da Hezbollah ta harba daga Lebanon ta kashe wani ɗan Isra'ila a kusa da Kibbutz da ke arewacin Isra'ila.