Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 02/01/2026.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 02/01/2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Zelensky ya yi shugaban tsaron kasar tayin zama shugaban kasa

    Shugaba Volodymir Zelensky na Ukraine, ya yi wa shugaban hukumar tsaron kasar tayin jagorantar ofishin shugaban kasa.

    Mr Zelensky ya ce Kyrylo Budanov ya na da kwarewar da zai iya kawo sauyi a daidai lokacin da kasar ke bukatar a maida hankali kan batutuwan da suka shafi tsaro da amfani da hanyoyin diflomasiyya da sasantawa.

    Kawo yanzu ba a san ko Mr Budanov zai karbi aikin ba. Ya taka muhimmiyar rawa wajen kai gwamman hare-hare a yakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine, lamarin da ya janyo masa farin jini da daukaka musamman a fannin aikin soji.

    Shugaban ofishin shugaban kasa na yanzu Andrii Yermak ya sauka daga mukamin, tun bayan danbarwar cin hanci da rashawa da ta taso a karshen watan Numbar bara.

  2. Ƴan awaren Yemen sun ce Saudiyya ta kai hari a sansanin sojinta

    Kungiyar 'yan aware mai karfin fada a ji a Yemen, ta ce Saudiyya ta kai hari daya daga cikin sansanonin sojinta da ke kasar.

    Southern Transitional Council, ta ce harin ya hallaka mutane da jikkatar wasu da dama.

    Wanna na zuwa bayan Gwamnan yankin Hadramount Salem al-Khanbasi da Saudiyya ke marawa baya a kudancin Yemen, ya sanar da kaddamar da gwagwarmayar karbe ikon sansanin sojin da 'yan awaren da Hadaddiyar Daular Larabawa ke marawa baya suka karbe.

    Ya ce abin da ke faruwa yanzu aikin hadin gwiwa ne, za a gudanar da aikin cikin lumana, ba kuma kaddamar da yaki za a yi ba.

    Ana nuna damuwa tun bayan 'yan awaren sun karbe ikon yankin da ake fargabar barkewar sabon yaki a Yemen.

  3. Kalmomi 7 da Kwankwaso ya furta suka zama sara

    A yanzu haka za a iya cewa mabiya Kwankwasiyya da ma masu sha'awar siyasa na dakon sabbin kalamai ko kuma furuci daga tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso a daidai lokacin da ake gani a matsayin babban yaronsa a siyasa zai guje masa.

    A kusan kowane yanayi na siyasa walau dai na kamfe ko zaɓe ko kuma tattaunawa da ƴan siyasa, Injiniya Rabi'u Kwankwaso kan hau duro ya rinƙa sakin kalamai da furuci da suka taƙaita ga shi shi kaɗai.

    Masana harshe na alaƙanta kalaman na Kwankwaso da dabarun siyasa na kame zukatan masu sauraro shigen irin waɗanda ƴan siyasar farko-farko kamar Malam Aminu Kano da Abubakar Rimi suka rinƙa yi a duk lokacin da suka hau duro.

  4. Bai kamata a fara karɓar haraji ba tare da cikakken bayani ba -Peter Obi

    Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a Najeriya a Jam'iyyar Labour, Peter Obi kuma jigo a jam'iyyar ADC ya ce babu ƙasar da ke samun cigaban da take buƙata ta hanyar tatsar mutanenta kawai.

    Obi ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya wallafa a shafukansa na sadarwa, inda ya ce ƙasashen da ya ziyarta, abin da ya fahimta shi ne suna gudanar da mulki ne ba tare da ɓoye-ɓoye ba.

    "Maganar gaskiya ita ce dole gwamnati ta riƙa gudanar da mulki a fili, kuma cikin gaskiya da amana, saboda waɗanda ake mulka ba su cancanci ɓoye-ɓoye da rashin gaskiya ba daga waɗanda suke mulkinsu."

    Ya ce shugabanni na gari ba sa tatsar mutane "domin azurta kansu da wasu tsirarun mutane, suna gina amana ne da haɗin kai da aiki tare, wanda shi ne ginshiƙin cigaba mai ɗorewa. Idan har da gaske ake yi game da haraji, dole ya zama an yi bisa gaskiya da amana da kuma fifita jin daɗi da walwalar ƴan ƙasa da cigaban ƙasar."

    Ya ƙara da cewa dole a bayyana yadda kowane haraji yake, "kamar yadda za a karɓa da amfaninsa wajen ciyar da ƙasa gaba. Idan ba a yi haka ba, zai zama kawai an haifar da ruɗani ne da ƙara wa ƴan ƙasar nauyi."

    A ƙarshe ya ce wannan ne karon farko da aka yi cushe a dokar haraji a Najeriya, "domin ita kanta majalisa ta tabbatar akwai sauyi a dokar, amma duk da haka an buƙaci ƴan ƙasar su fara biyan harajin a haka."

  5. China ta nuna goyon baya ga Somaliya bayan Isra’ila ta amince da Somaliland

    Firaministan Somalia Hamza Abdi Barre da jakadan China a Somalia Wang Yu sun gana a Mogadishu, inda suka tattauna yadda za a karfafa haɗin kai bayan Isra’ila ta amince da Somaliland a matsayin kasa mai ‘yancin kanta.

    Jakadan China ya tabbatar da cewa kasar tana goyon bayan cikakken hadin kan kasar Somaliya, yayin da Barre ya jaddada ƙudurin Somaliya na kare muradunta da kiyaye haɗin kan ƙasar.

    Haka zalika, Somalia ta umurci malaman addini a fadin ƙasar su tattauna matsalar shiga tsakani da Isra’ila a cikin hudubobin Juma’a, yayin da wasu ‘yan majalisar da ke wakiltar Somaliland suka gargadi gwamnati kada ta tsaurara matakai kan gwamnatin Hargeisa.

  6. Kotu ta ɗage ƙarar belin Abubakar Malami zuwa 7 ga watan Janairu

    Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta ɗage zaman sauraron buƙatar beli da tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami ya gabatar a kan zargin halasta kuɗin haram har zuwa ranar Laraba 7 ga wannan wata.

    Tun ranar 31 ga watan Disamba, kotu ta tasa ƙeyar Abubakar malami zuwa gidan yarin Kuje.

    EFCC dai ta tuhumi tsohon ministan shari’ar ne da ɗansa Abdul‘aziz da kuma mai ɗakinsa Asabe Bashir kan halasta kuɗin haram har na naira biliyan 8.7, zargin da dukkansu suka musanta.

    Hakan dai na nufin Abubakar Malami zai ci gaba da zama a gidan yarin na Kuje har zuwa tsakiyar makon gobe.

  7. Gwamna Filato, Caleb Mutfwang ya sanar da komawa APC

    Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar APC lamarin da jam’iyyar ta bayyana a matsayin wani muhimmin mataki na kishin ƙasa da nufin yi wa al’ummar jihar da Najeriya hidima.

    A wata sanarwa da kwamitin gudanarwa na APC ya fitar, jam’iyyar ta ya bayyana sauaya shekarsa zuwa jam'iyyar a matsayin gagarumin ci gaba.

    Jam’iyyar ta bayyana cewa rajistar gwamnan a APC wata alama ce ta sabon fata da haɗin kai kan manufa ɗaya, inda ta tabbatar da shirinta na yin aiki tare da shi domin ciyar da muradun al’ummar Filato gaba, tare da ƙarfafa jam’iyyar a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya.

    APC ta ce ta karɓi Gwamna Caleb Mutfwang da hannu bibbiyu, tana mai tabbatar masa da cikakken goyon baya da haɗin gwiwa tare da maraba da shi a matsayin cikakken mamba na jam’iyyar.

  8. Sheikh Abduljabbar na so a mayar da shi gidan yarin Kurmawa na Kano

    Fitaccen malamin addini, Sheikh Abduljabbar Kabara ya buƙaci hukumomi da mahukunta da su gaggauta mayar da shi gidan yarin Kurmawa da ke Kano daga gidan yarin Kuje na Abuja, inda aka kai shi bayan an sauya masa wuri da ya ce an yi masa ba bisa ƙa’ida ba.

    A cikin wata wasiƙa da ya aike wa mahukunta a ranar 01 ga Janairu, 2026, Abduljabbar Kabara ya bayyana cewa watanni uku ke nan da aka sauya masa kurkuku kuma a lokacin sauyin, an hana shi ɗaukar dukkan muhimman takardun shari’arsa, waɗanda ya ce har yanzu suna Gidan Yarin Kurmawa.

    Ya ce "Rashin kasancewar takardun shari’ata a hannu na haifar min da damuwa, ganin cewa ban san yanayin halin da waɗannan takardun nawa suke ciki ba a halin yanzu, alhali doka ta tanadi cewa na kasance ina da damar kula da irin waɗannan takardu da kai na.

    Saboda haka, "Ni Abduljabbar Kabara ina kira ga hukumar gidan kurkukun Najeriya da sauran hukumomin da abin ya shafa da su yi gaggawar maida ni daga ina aka ɗakko ni wato kurkukun Kurmawa kenan domin na samu damar duba takardun shari’a ta tare da tabbatar da lafiyarsu da kuma kasancewarsu ƙarƙashin kulawata." in ji shi.

  9. Trump ya yi barazanar kai wa masu zanga-zanga a Iran ɗauki

    Shugaba Amurka, Donald Trump ya gargaɗi Iran kan kisan masu zanga-zangar lumana a ƙasar, inda ya ce Amurka za ta kai musu ɗauki.

    A saƙon da ya wallafa a shafin sada zumunta ya ce Amurka ta gama saita bindigarta da harsasai ta na shirin tahowa.

    Sai dai wani mai bai wa jagoran addini Ayatullah Ali Kamenei shawara ya maidawa shugaban Amurkar martanin kada ya kuskura ya yi musu katsalandan a harkokin ƙasarsu in ba haka ba za a fuskanci tashin hankali a yankin.

    Kwanaki 6 kenan da fara zanga-zangar tsadar rayuwa da karyewar darajar kudin ƙasar wadda 'yan kasuwa da ɗalibai fara.

  10. Kotu ta amince da belin kwamishinan kudi na jihar Bauchi

    Kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bai wa kwamishinan kudi na jihar Bauchi, Yakubu Adamu beli a kan takardar lamuni na naira miliyan 500 da kuma sharaɗin sai ya kawo mutum biyu da za su tsaye masa.

    Alkalin kotun, Justice Emeka Nwite, ya umurci cewa mutanen da za su tsaya masa su kasance suna da fili a yankunan Maitama da Asokoro ko Gwarimpa da ke Abuja, inda za a tabbatar da takardun kadarorin a wajen magatakarda.

    Haka zalika, mutanen biyu za su shaida wa kotu halin arzikinsu.

    Kotun ta kuma ce kwamishinan kuɗin da waɗanda za su tsaya masa za su miƙa fasfo ɗinsu ga magatakardan kotun kuma ba za su iya fita daga ƙasar ba sai da izinin kotu, sannan kuma za su miƙa hoton fasfo biyu ga kotun.

    Alƙalin kotun wanda ya bayar da umarnin a riƙe kwamishinan a gidan yarin Kuje da ke Abuja har sai an cika sharuɗɗan belinsa ya ɗage shari’ar zuwa ranar 20 ga Janairu, 2026.

    EFCC dai ta zargi kwamishinan kuɗin da halasta kuɗaɗen haram har na wajen dala miliyan 9.7.

  11. Ma'aikatan jinya a Kaduna sun yi barazanar tafiya yajin aiki

    Ma’aikatan jinya a jihar Kaduna sun yi barazanar tafiya yajin aiki a shekarar 2026 saboda rashin samun ƙarin girma da suka zargi hukumomin lafiya da yi

    Wannan yajin aikin na iya kawo cikas ga ayyukan kiwon lafiya a jihar idan ba a gyara ba.

    Shugaban ƙungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma na Najeriya (NANNM) ta jihar, kwamared Ishaku Yakubu ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda ake watsi da ci gaban ma’aikatan jinya.

    Ya ce, “Mun fuskanci matsaloli da dama, ciki har da rashin gudanar da tsarin ƙarin girma a ma’aikatar lafiya da wasu hukumominta,” inda ya bayyana cewa hakan yana rage ƙwarin gwiwa da aiki tukuru.

    Ya ƙara da cewa ƙungiyar ba za ta ci gaba da jure jinkirin da ke cutar da ci gaban sana’a da darajar ma’aikatan jinya ba.

  12. Gobara ta kashe kusan mutum 40 a Switzerland

    Ɗaruruwan mutane ne suka halarci taron addu'oi da aka yi kafin binne mutanen da suka mutu a yayin wata gobara da ta tashi a wani wajen shan barasa da ke Switzerland.

    Jami'an Switzerland sun ce kusan mutum 40 aka tabbatar da mutuwarsu inda aƙalla wasu 150 kuma suka jikkata.

    Ana ci gaba da bincike domin gano abin da ya haddasa gobarar, sannan kuma mutanen da suka tsira da ga wutar sun ce ba mamaki barasar da ke cikin wajen ce ta kara rura wutar.

    Ganau sun ce wutar ta yadu a wajen shan barasar cikin sauri abin da ya hana da yawan mutane tsira da ga wutar.

  13. An fara sauraron ƙarar neman belin tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami

    Kotun tarayya da ke Abuja ta fara sauraron ƙara kan neman belin tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami, wanda ke tsare a gidan yari na Kuje da ke Abuja.

    Malami tare da ɗansa Abdulaziz da ɗaya daga cikin matansa, Bashir Asabe, suna fuskantar shari’a ne kan zargin halasta kuɗaɗen haramun bisa tuhume-tuhume 16 da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta shigar a kansu.

    Ana zargin su da halasta kuɗaɗen haram har naira biliyan 8.7 inda dukkaninsu suka musanta zargin lokacin da aka gurfanar da su a gaban kotu a ranar 29 ga Disamba, 2025.

    Bayan musanta laifin, mai hhari’a Emeka Nwite ya bayar da umarnin tsare su a gidan yarin Kuje har zuwa ranar 2 ga Janairu, 2026, inda kotun za ta saurari ƙarar neman belinsu a rubuce da lauyoyinsu suka shigar.

  14. Sojojin Colombia sun kashe jagoran gungun ’yan daba da FBI ke nema

    Dakarun Colombia sun ce sun kashe babban jagoran ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin 'yan dabar da ake tsoro a ƙasar.

    Mosquera Serrano, da akafi sani da "Giovanni San Vicente ko kuma The Old Man, na jagorantar ƙungiyar Tren de Aragua.

    Ana zarginsa da bawa ƙungiyar umarnin safarar miyagun ƙwayoyi da kuma aikata wasu muggan laifuka.

    Mosquera Serrano, shi ne jagoran ire-iren waɗannan ƙungiyoyin na farko da ke jerin sunayen da hukumar FBI ke nema ruwa a jallo da aka kama.

    Sai da aka sanya ladan dala miliyan biyar ga duk wanda ya bayar da bayani akan inda ya ke.

  15. 'Ƴanjarida 128 aka kashe a 2025 a faɗin duniya'

    Ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasashen duniya (IFJ) ta bayyana cewa an kashe jimillar ’yan jarida 128 a faɗin duniya a shekarar 2025, inda fiye da rabin su a yankin Gabas ta Tsakiya.

    IFJ ta ce wannan adadi ya ƙaru idan aka kwatanta ta da na shekarar 2024, lamarin da ke nuna tabarbarewar yanayin tsaro ga ma’aikatan kafafen yaɗa labarai a duniya.

    Sakataren janar na ƙungiyar, Anthony Bellanger, ya ce wannan alƙaluma ba wai kididdiga kaɗai ba ne, illa wani babban gargaɗi ga duniya baki ɗaya.

    A hirarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP, ya jaddada cewa haɗarin da ’yan jarida ke fuskanta yana ƙara tsananta yayin gudanar da aikinsu.

    IFJ ta nuna damuwa ta musamman kan halin da ake ciki a yankunan Falasɗinawa, inda ta ce ’yanjarida 56 ne suka mutu a shekarar 2025 sakamakon ci gaba da yaƙin Isra’ila da Hamas a Gaza.

    Haka kuma an kashe ’yan jarida a ƙasashe irin su Yemen da Ukraine da Sudan da Peru da India, in ji shi.

    Baya ga kashe-kashen, IFJ ta ce a halin yanzu akwai ’yan jarida 533 da ke tsare a gidajen yari a faɗin duniya, adadi da ya ninka fiye da sau biyu cikin shekaru biyar da suka gabata.

  16. A shirye nake na tattauna da Amurka kan safarar miyagun ƙwayoyi - Shugaban Venezuela

    Shugaban ƙasar Venezuela, Nicolas Maduro ya ce a shirye ya ke ya haɗa kai da Amurka wajen tattaunawa akan abubuwan da suka shafi safarar miyagun ƙwayoyi da takunkumi akan mai da kuma kwararar baƙin haure.

    Cikin wata hira da aka yi dashi a kafar yaɗa labaran ƙasar wadda aka naɗa, ya ce yana mai farin cikin tattaunawa da gwamnatin Trump a kodayaushe kuma a ko ina ta buƙata.

    To amma cikin hirar , Maduro ya ƙi tabbatar da ko kuma ƙaryata iƙirarin da shugaba Trump ke yi na cewa sojojin ƙasarsa na kai hare-hare akan jiragen ruwan Venezuela wanda suka ce ana safarar miyagun ƙwayoyi da su.

    Tun daga watan Satumba ne dakarun Amurka suka ƙaddamar da hare-hare da dama akan jiragen ruwan dake sintiri a tekun Caribbean da kuma na gabashin tekun Pacific.

  17. Zanga-zangar tsadar rayuwa a Iran ta yi sanadin mutuwar mutum shida

    Mahukunta a Iran sun ce aƙalla mutum 6 ne suka mutu a yayin zanga-zangar ƙin jinin gwamnati da aka shiga kwana 5 ana yi saboda tashin farashin kayayyaki da kuma faɗuwar darajar kudin ƙasar.

    An zargi mutum 30 da tayar da zaune tsaye a lardin Malard da yammacin Tehran inda aka kama su bayan da jami'an tsaro suka gano su.

    An ƙona motoci a yayin da jami'an tsaro da kuma masu zanga-zangar suka yi taho mu gama.

    Wasu bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda sojoji ke mayarwa da masu zanga-zangar martani da jefansu da duwatsu inda suke watsa musu barkonon mai saka hawaye.

  18. Ƴansanda sun dakatar da kamen motoci masu gilashi mai duhu

    Rundunar ƴansandan Najeriya ta sanar da dakatar da kamen motoci masu gilashi mai duhu a faɗin ƙasar, biyo bayan umarnin kotu na wucin-gadi da ya hana aiwatar da dokar.

    A sanarwar da ta fitar a shafinta na X, rundunar ta ce matakin dakatarwar ya biyo bayan ƙarar da ke gaban kotu, inda aka umurci rundunar ta dakata da aiwatar da dokar har sai an yanke hukunci.

    Tun a ranar 15 ga Disamba, 2025 ne rundunar ta bayyana aniyarta ta fara aiwatar da dokar mallakar lasisin amfani da gilashin mota mai duhu daga ranar 2 ga Janairu, 2026, tana mai cewa hakan na da nufin ƙarfafa tsaro da kare lafiyar jama’a.

    Sai dai a wata sanarwa da kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin ya fitar, ya ce an miƙa wa rundunar umarnin kotu a ranar 17 ga Disamba, 2025, wanda ya hana ci gaba da aiwatar da dokar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar ta riga ta bayyana a gaban kotu, ta gabatar da ƙorafe-ƙorafen farko tare da neman kotun ta janye umarnin dakatarwar.

    An ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 20 ga Janairun 2026 domin ci gaba da shari’a, yayin da dokar za ta ci gaba da kasancewa a dakace har sai kotu ta yanke hukunci ko ta janye umarnin.

    Rundunar ta kuma tabbatar wa al’umma cewa za ta sanar da su duk wani sabon mataki ko bayani bayan hukuncin kotu, domin kiyaye zaman lafiya da tsaron ƙasa.

  19. Shugabannin ƙasashen Afirka biyar da suka yi murabus bisa raɗin kansu

    Duk da yadda ake kallon Afirka a matsayin makwanta rikice-rikicen siyasa, a wani ɓangaren kuma akwai shugabannin ƙasashe a nahiyar da suka ajiye mulki bisa raɗin kansu kafin wa'adinsu ya ƙare.

    Tun bayan samun ƴancin kai daga mulkin mallaka, ƙasashen nahiyar da dama sun fuskanci matsaloli daban-daban na rikice-rikicen siyasa da juyin mulki da kashe-kashen da suka faru a sanadiyar juyin mulki da suka dabaibaye nahiyar.

    Ganin yadda nahiyar take fama da shugabannin masu mulki tamkar sarauta, sai samun waɗanda suke barin mulki da kansu ya zama abin ban mamaki.

    Wannan ya sa muka rairayo wasu shugabannin ƙasashe guda biyar a nahiyar waɗanda suka ajiye mulki kafin wa'adin mulkinsu.

  20. Assalamu alaikum

    Jama'a barkan mu da wannan safiya ta Juma'a daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu ci gaba daga inda muka tsaya a jiya na labaran kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.