AFCON 2025: Najeriya 2-1 Tanzaniya

Wannan shafi ne da ya kawo muku bayanai kan wasan Najeriya da Tanzaniya a gasar kofin nahiyar Afirka ta 2025 da ake yi a Moroko.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Ibrahim Mohammed, Isiyaku Muhammed

  1. Najeriya ta yi nasara a wasan farko

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Mun gode ƙwarai da kuka kasance tare da mu yayin da Najeriya da Tanzaniya suka buga wasansu na farko a gasar cin kofin Afirka ta 2025 a ƙasar Moroko, inda Najeriya ta yi nasara.

    Najeriya za ta yi wasanta na biyu da ƙasar Tunisiya a birnin Fes ranar Asabar da yamma.

    Ita kuma Tanzaniya za ta yi karawa ta biyu da Uganda a birnin Rabat a ranar ta Asabar da yamma.

    Za ku iya karanta bayanai kan gasar cin kofin Afirka a shafinmu na bbchausa.com da kuma shafukanmu na sada zumunta.

    Ku shiga zaurenmu na WhatsApp domin samun bayanai da ɗumi-ɗumi kan AFCON da ma sauran abubuwan da ke faruwa a doron duniya.

  2. Magoya bayan Najeriya bayan an tashi wasa

    ...

    Magoya bayan Najeriya na murmushi har kunne bayan nasarar da Super Eagles ta yi kan Tanzaniya a wasanta na farko a gasar AFCON 2025 a Moroko.

    ...
    ...
    Bayanan hoto, ...
    ...
    ...
  3. A yanzu kenan Najeriya ta lashe 14 daga cikin wasa 21 na farko da ta buga a gasar cin kofin Afirka (AFCON).

    Ta yi canjaras a 2 sannan ta yi rashin nasara a 5.

    A yanzu Najeriya ta zura jimillar ƙwallaye 148 a gasar.

  4. , Najeriya 2-1 Tanzaniya

    Ɗan wasan baya na Najeriya Semi Ajayi, wanda ya zura ƙwallon farko da kai, shi ne aka bai wa kyautar ɗan wasa mafi ƙwazo a karawar.

    Ɗan wasan na baya na Najeriya ya taka muhimmiyar rawa.

  5. AN TASHI WASA, Najeriya 2-1 Tanzaniya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Najeriya ta kammala wasan farko na gasar kofin Afirka ta 2025 da nasara bayan doke Tanzaniya da ci 2-1 bayan an yi mummunan artabu.

  6. ƘARIN LOKACI, Najeriya 2-1 Tanzaniya

    An ƙara minti uku bayan cikar lokaci.

    Ko za a samu sauyi?

    A jiya an ci ƙwallo uku a wasa biyu a minti na 90 waɗanda suka tantance sakamakon wasannin.

  7. Saura ƙiris Tanzania ta farke

    A daidai minti 85 Tanzania ta samu wata babbar damar farkewa, amma ɗan wasan gabanta ya ɓarar, inda ya harba ƙwallon ta yi waje.

  8. An canja Osimhen

    Kocin Najeriya ya canja Osimhen, inda ya maye gurbinsa da Paul Onuachu.

  9. Ƴan Moroko na son Osimhen, Isaiah Akinremi

    Victor Osimhen

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Victor Osimhen

    Masoya ƙwallon ƙafa ƴan Moroko, wasunsu sanye da hulunan bukukuwan kirsimeti na ta kiran sunan Osimhen.

  10. Ƴan Najeriya sun ruɗa fili da bushe-bushe, Isaiah Akinremi

    Za a iya jin ƙarar bushe-bushe da kaɗe-kaɗe daga magoya bayan Najeriya waɗanda ke sanye da rigunan Najeriya masu launin shuɗi.

    Sun ruɗa fili da bushe-bushe musamman bayan da Lookman ya zura ƙwallo ta biyu.

  11. ƘIRIS!, Najeriya 2-1 Tanzaniya

    Ademola Lookman ya yi wani juyin masa a kusa da ragar Tanzaniya cikin minti na 67 sannan ya buga wani shot amma ba ta shiga ba.

  12. Najeriya ta sauya ƴan wasa biyu, Najeriya 2-1 Tanzaniya

    Najeriya ta cire ƴan wasa Akor Adams da Samuel Chukwueze, inda ta maye gurbinsu da Moses Simon da Fisayo Dele-Bashiru.

  13. Idan Najeriya na so ta yi nasara dole ta zage damtse - Oliseh, Najeriya 2-1 Tanzaniya

    Idan har Najeriya na so ta yi nasara a wannan wasan to tana buƙatar ta nuna wa Tanzaniya fin ƙarfi ta hanyar ƙwace ƙwallo daga ƙafar ƴan Tanzaniya.

    "Idan kana kan gaba a wasa, kamata ya yi ka ƙara matsa ƙaimi ka nuna wa abokin hamayyarka cewa kana so ne ka ƙara cin ƙwallo," in ji Oliseh.

    A halin yanzu ƴan wasan Tanzaniya na ci gaba da tattaɓa ƙwallo.

  14. Goaaaaal!!.... Najeriya ta zura ƙwallo ta biyu, Najeriya 2-1 Tanzaniya

    Ademola Lookman

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ademola Lookman

    Najeriya ta mayar da martani nan take, inda Ademola Lookman ya zura ƙwallo mai ƙayatarwa.

    Hakan na zuwa ne kimanin minti biyu bayan Tanzaniyaa ta farke.

  15. Goaaaal! Tanzaniya ta farke, Najeriya 1-1 Tanzaniya

    Tanzania ta farke a minti 48.

    Tanzaniya ta ci ƙwallo mai kyau bayan tattaɓa ƙwallo dama da hagu kafin jefa ta a raga.

  16. Goall.... amma kash!

    Osimhen ya zura ƙwallo ta biyu bayan Adams ya jefa masa ƙwallo daga nesa, amma lafari ya ce akwai satar gida.

    Lafari ya duba VAR, a ƙarshe ya ce tabbas akwai satar gida saboda haka babu ci.

  17. An dawo hutun rabin Lokaci, Najeriya 1-0 Tanzaniya

  18. An tafi hutun rabin lokaci, Najeriya 1-0 Tanzaniya

    Ƙwallon da ɗan wasan Najeriya Samuel Ajayi ya zura a ragar Tanzaniya ita ce ta raba gardama a wannan wasa kafin zuwa hutun rabin lokaci.

    Amma tabbas ba ƙaramin ƙoƙari golan Tanzaniya Zuberi Foda ya yi ba lokacin da ya tare ƙwallo gab da hura usur na zuwa hutun rabin lokaci.

  19. , Najeriya 1-0 Tanzaniya

    An ƙara minti ɗaya kafin a tashi hutun rabin lokaci a wannan wasa mai ƙayatarwa.

  20. Saura ƙiris, amma kash!

    A gab da tafiya hutun rabin lokaci ne Ndidi ya yi duma daga nesa, inda golan Tanzania ya yi amai, ta faɗo hannun Chukweze, amma kash! ya ɓarar.