Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Beckham ya zama biloniya na farko daga Burtaniya a fannin wasanni

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 11 zuwa 16 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Coleman zai kawo karshen kaka 17 a Everton

    Seamus Coleman ya sanar da cewa zai kawo karshen rayuwarsa ta taka leda a Everton a karshen kakar wasa ta bana, lokacin da kwantiraginsa zai kare bayan shekaru 17 da ya shafe a ƙungiyar.

    Ɗan wasan mai shekaru 37 ya ce an ba shi damar shiga aikin horaswa a ƙungiyar, amma zai yanke hukunci game da makomarsa ne a lokacin hutun bazara.

    Ɗan wasan tawagar Jamhuriyar Ireland ya koma Everton daga ƙungiyar Ireland, Sligo Rovers a watan Janairun 2009 kan kudi fam £60,000, sannan aka naɗa shi ƙyaftin ɗin ƙungiyar a shekarar 2019.

    A shekarar 2024, Coleman ya karya tarihin yawan buga wasannin Premier League a kungiyar, inda ya zarce tsohon mai tsaron raga, Tim Howard wanda ya buga wasanni 354.

    Yanzu haka tarihin wasanninsa a gasar firimiya ya kai 372, inda ya ci kwallaye 22 tare da bayar da 24 aka zura a raga.

  2. , Daga Jaridu

    Ɗan wasan tsakiya na Uruguay Federico Valverde yana son ya ci gaba da zama a Real Madrid amma, Manchester City da Paris St-Germain suna sanya ido , idan har kulob ɗin Sifaniya ya yanke shawarar cefanar da ɗan wasan mai shekara 27. (AS)

    Paris St-Germain na cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan tsakiyar West Ham da Portugal, Mateus Fernandes, mai shekara 21. (Athletic)

    Arsenal ma tana sha'awar Fernandes kuma a shirye take ta sayar da ɗan wasan tsakiya na Denmark Christian Norgaard, mai shekara 32, wanda bai taka rawar gani ba tun da ya koma filin wasan Emirates daga Brentford a bazarar da ta gabata. (The Times)

    Aston Villa na son ɗaukar ɗan wasan gaban Argentina Matias Soule, mai shekara 23, daga Roma, bayan da kulob ɗin na Italiya ya shirya mayar da zaman aron ɗan wasan Holland Donyell Malen, mai shekara 27, zuwa na dindindin. (Gazzetta dello Sport)

  3. Senesi zai bar Bournemouth da zarar an kammala kakar bana, Bournemouth

    Marcos Senesi, mai tsaron baya na kasar Argentina, zai bar Bournemouth a karshen kakar nan, bayan kwantiraginsa ya kare.

    Ɗan wasan mai shekaru 29 ya yi shekaru hudu tare da kungiyar, wadda yanzu take matsayi na shida a gasar Premier League.

    Tun daga 1 ga watan Janairu, Senesi yana da damar tattaunawa da ƙungiyoyin Turai, yana kuma duba yiwuwar ci gaba da taka leda a gasar firimiya ta Ingila.

    Bournemouth ta bai wa dan wasan sabon kwantiragi, amma sai ya zaɓi ya bar filin wasa na Vitality Stadium a karshen kakar wasa, haka kuma kocin ƙungiyar Andoni Iraola zai bar Bournemouth a karshen kakar nan.

    Idan Bournemouth ta kare a matsayi na shida, hakan zai zama mafi kyawun matsayi a tarihinta a Premier League, kuma tana bukatar karin maki biyu kacal domin kafa sabon tarihin yawan samun maki a kaka ɗaya.

    Har ila yau, Cherries na dab da samun gurbin buga gasar zakarun Turai — inda ake ganin za ta iya samun gurbin UEFA Europa League ko kuma UEFA Europa Conference League.

  4. , Daga Jaridu

    Chelsea na zawarcin golan AC Milan Mike Maignan amma fatan da ƙungiyar ta Stamford Bridge ke da ita na ɗaukar ɗan wasan na Faransa mai shekara 30 na iya fuskantar cikas idan har ba ta samu gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai ba. (Gazzetta dello Sport)

    Ana danganta ɗan wasan Brazil Joao Pedro da Barcelona amma Chelsea ba ta da niyyar cefanar da ɗan wasan mai shekara 24. (Mail)

    Bayer Leverkusen na shirin korar kocinta Kasper Hjulmand wanda ya karɓi ragamar aiki daga Erik ten Hag a watan Satumba. (Sky Sports Germany)

    Shugaban FC Porto, Andre Villas Boas, ya ce ƙungiyar ba ta da kuɗin da za ta iya sayen ɗan wasan gaban Poland Robert Lewandowski mai shekara 37, wanda ake tunanin yana shirin barin Barcelona. (Fabrizio Romano)

  5. Beckham ya zama biloniya na farko daga Burtaniya a fannin wasanni, David Beckham

    Tsohon ɗan wasan tawagar Ingila, David Beckham ya zama na farko daga Burtaniya da ya kai matsayin biloniya a jerin masu kudi, in ji The Sunday Times na shekarar 2026.

    A cewar masu shirya sanar da attajiran duniya, arzikin Beckham da matarsa Victoria Beckham yanzu ya kai fam biliyan £1.185.

    Wannan ya sanya su a matsayi na biyu cikin attajiran a fannin wasanni, bayan iyalan tsohon shugaban Formula 1 Bernie Ecclestone, wanda aka kiyasta dukiyarsa ta kai fam biliyan £2.

    Ɗan wasan golf na Arewacin Ireland, Rory McIlroy yana matsayi na bakwai da fam miliyan £325, bayan da ɗan wasan mai shekaru 37 ya lashe gasar Masters sau biyu a jere.

    A gefe guda kuma, mamallakin wani ɓangaren hannun jari a Manchester United, Jim Ratcliffe, ya sauka daga matsayi na bakwai zuwa na tara a jerin masu kuɗin Burtaniya baki ɗaya, bayan da dukiyarsa ta ragu da fam biliyan £1.85 zuwa £15.194bn.

    Beckham, tsohon ɗan wasan Man United, yanzu yana cikin waɗanda suka yi haɗakar mallakar Inter Miami CF ta Amurka, wadda aka kiyasta ita ce ƙungiyar MLS mafi daraja da ta kai kimar dala biliyan $1.45 (£1.07bn).

    Ɗan shekaru 51, wanda aka ba sarauta a watan Nuwamba, yana kuma matsayin jakadan ga kamfanoni irin su Adidas da Hugo Boss da sauransu.

  6. Matthijs de Ligt ba zai buga wa Netherlands gasar cin kofin duniya, Gasar kofin duniya

    Manchester United ta sanar da cewa mai tsaron bayan Netherlands, Matthijs de Ligt ba zai halarci gasar kofin duniya ta bana ba, bayan da ya amince a yi masa tiyata domin magance matsalar ciwon baya da ta dade tana damunsa.

    Ɗan wasan mai shekaru 26 bai taka leda ba tun bayan nasarar da United ta samu a kan Crystal Palace ranar 30 ga Nuwamba.

    A lokacin, tsohon kocin ƙungiyar, Ruben Amorim ya bayyana cewa matsalar ba mai tsanani ba ce, kuma yana sa ran De Ligt zai dawo kafin wasan gida da West Ham United bayan kwana huɗu.

    Sai dai hakan bai faru ba, duk da yawan sakonnin kwarin gwiwa da kuma sabon kocin, Michael Carrick yana nanata cewa ba sa tunanin sai an yi masa tiyata.

    Amma kokarin da De Ligt ya yi na komawa gudu a filayen atisaye na Carrington a watan da ya gabata bai haifar da sakamako mai kyau ba.

    Tawagar Netherlands za ta fara gasar cin kofin duniya da Japan ranar 14 ga watan Yuni, yayin da United ta ce ba ta sa ran De Ligt zai dawo fili har sai a farkon kakar wasa ta 2026-27.

  7. Man United za ta bai wa Carrick kwantiragin kaka biyu, Manchester United

    Manchester United na tattaunawa da Michael Carrick kan bashi kwantiragin shekaru biyu domin zama babban kocin ƙungiyar.

    Manyan jami’an Man United sun yanke shawarar cewa tsohon ɗan wasan ƙungiyar, shi ne mutumin da ya dace ya jagoranci ƙungiyar.

    A wani taron manema labarai ranar Juma’a, Carrick mai shekaru 44 — wanda ke rikon kwarya tun watan Janairu — ya ce za a samu matsaya kan makomarsa “nan ba da jimawa ba”.

    Ba a cire yiwuwar sanar da nadin nasa kafin wasan karshe a gida a kakar bana da Nottingham Forest ranar Lahadi ba.

    Ana sa ran kwantiragin zai kunshi zabin karin shekara guda, idan ya ci gaba da yin abin kirki.

  8. Raducanu za ta ci gaba da aiki da tsohon kociyanta, Tennis

    Emma Raducanu za ta sake haɗuwa da mai horas da ita Andrew Richardson — wanda ya taimaka mata wajen lashe gasar US Open lokacin tana yarinya — a matsayin za su yi hadin gwiwa na dindindin.

    Raducanu da Richardson suna yin aiki tare a hukumance yanzu a Strasbourg domin shirye-shiryen gasar WTA ta kasa da ake yi a kan taɓo, wadda ita ce gasar karshe ta shirin shiga French Open.

    Su biyun sun amince da yarjejeniyar yin aiki tare na dogon lokaci, wanda ke nuna cewa Raducanu na shirin ci gaba da kasancewa tare da Richardson mai shekaru 52 har zuwa Wimbledon Championships da kuma bayan haka.

    Da farko Raducanu ta sake haɗuwa da Richardson a farkon wannan watan a makarantar wasan tennis ta Ferrer Tennis Academy da ke kasar Spain, inda ya shafe shekaru yana matsayin daraktan tennis.

  9. , Daga Jaridu

    Everton da Crystal Palace da Bournemouth sun tuntuɓi FC Midtjylland domin zawarcin ɗan wasan tsakiyar Chile Dario Osorio mai shekara 22. (Give Me Sport)

    Manchester United na sanya ido kan ɗan wasan Sporting Lisbon da ɗan ƙasar Denmark Morten Hjulmand, mai shekara 26, wanda kuma ke jan hankalin Arsenal.(Caught Offside)

    Ɗan wasan tsakiya na Middlesbrough Hayden Hackney, mai shekara 23, na shirin barin kulob ɗin na Riverside idan suka sha kashi a hannun Southampton a wasan kusa da na ƙarshe na neman gurbin haurowa gasar Premier, kuma Newcastle United na iya miƙa tayi kan ɗan wasan na Ingila. (Chronicle)

  10. An samu kuskuren VAR sau 23 a Premier League a bana, VAR

    An tabbatar da karin samun kuskure uku da hukuncin da VAR ta yanke da kawo yanzu suka zama 23 jimilla a bana a Premier League in ji kwamitin nazarin manyan abubuwan da suka faru a wasannin Premier League (KMI).

    Wannan ya nuna karin kaso 35% idan aka kwatanta da kakar bara, inda aka samu 17 a irin wannan mataki a kakar 2024-25, amma har yanzu ya yi kasa da guda 30 da aka yi a kakar 2023-24.

    Kwamitin ya tabbatar da kurakurai uku da suka shafi bugun fanareti, biyu daga ciki kuwa ya kamata a bayar ne saboda jan riga ko rike da aka yi wa ƴan wasa.

    Everton, wadda ita ce kadai ƙungiyar da ba ta samu taimakon hukuncin VAR a bana ba, an hana ta fanareti a wasanta da Manchester City.

    Ƙungiyar da David Moyes ke jan ragama tana gaba da ci 3-2 a filin wasa na Hill Dickinson lokacin, sai aka samu bugun kusurwa inda Bernardo Silva ya rike ɗan wasan Everton, Merlin Rohl — abin da alkalin wasa Michael Oliver bai gani ba.

    Mai kula da VAR, Paul Howard, ya yanke hukuncin cewa an yi riken ne kafin a yi bugun kusurwar, saboda haka bai kamata a bayar da fanareti ba.

    Daga baya, Jeremy Doku ya ci wa City kwallo a karin lokaci, wanda ya sa wasan ya tashi 3-3.

    Wannan ne karo na uku a bana da ya kamata Everton ta samu fanareti ta hanyar VAR, bayan irin haka a wasan da ta sha kashi 1-0 a gida da Arsenal da kuma rashin nasara 2-1 a wajen West Ham United.

  11. Mbappe da Dambele za su wakilci Faransa a gasar kofin duniya 2026, Gasar kofin duniya

    Kylian Mbappe da mai riƙe da ƙyautar Ballon d'Or, Ousmane Dembele, suna cikin jerin ƴan wasa 26 da za su wakilci Faransa a gasar cin kofin duniya a 2026.

    Olivier Giroud ne kan gaba a yawan ci wa tawagar ƙwallaye fiye da Mbappe, inda yake da 57 a raga, shi kuwa ɗan ƙwallon Real Madrid yana da 56.

    Ana sa ran Mbappe ne zai ci gaba da ƙyaftin ɗin tawagar, wanda ke jinya da bai samu damar buga El Clasico ba da Barcelona ta yi nasarar cin Real Madrid 2-0 ta lashe La Liga kuma na biyu a jere.

    Dembele kuwa ya ci ƙwallo 35 tda lashe Champions League tare da Paris Saint-Germain a kakar da ta gabata, lamarin da ya sa ya zama ɗan wasan Faransa na biyu a wannan ƙarni da ya lashe Ballon d'Or. Duk da haka, har yanzu bai ci ƙwallo ba a gasar kofin duniya duk da kasancewa cikin tawagar gasar biyu da suka gabata.

    Michael Olise na Bayern Munich da kuma abokin wasan Dembele a PSG, Desire Doue, suna cikan jerin ƴan wasan a gurbin masu cin ƙwallaye, yayin da ɗan wasan Manchester City Rayan Cherki da kuma mai tsaron bayan Arsenal, William Saliba ke cikin ƴan wasa bakwai daga Premier League.

    Lucas Hernandez da ɗan wasan tsakiya N'Golo Kante da Mbappe da Dembele suna cikin ragowar tawagar Faransa da ta lashe kofin duniya a 2018.

    Deschamps, wanda ya kai Faransa wasan ƙarshe a kofin duniya sau biyu a jere, ya gayyaci wasu ƴan wasa da aka yi mamaki, wanda daga wannan gasar zai yi ritaya a matsayin kocin Faransa.

    Ba a saka ɗan wasan Real Madrid Eduardo Camavinga da na Tottenham, Randal Kolo Muani cikin waɗanda aka sanar ba, duk da cewa suna cikin tawagar 2022.

    Haka kuma mai tsaron ragar PSG, Lucas Chevalier bai samu gurbi ba, inda mai tsaron ragar Lens, Robin Risser wanda bai taɓa bugawa Faransa wasa ba tare da Brice Samba suna matsayin masu taimaka wa Mike Maignan.

    Hugo Ekitike na Liverpool, wanda ya samu mummunan raunin a watan Afrilu na jinya, har karshen kakar bana, ba zai buga gasar kofin duniya ba.

    Faransa za ta fara wasanninta da Senegal a New Jersey ranar 16 ga watan Yuni, sannan ta kara da Iraq ranar 22 ga watan Yuni da kuma Norway ranar 26 ga watan Yuni a rukuni na I.

    Tawagar ƴan wasan Faransa da za su buga kofin duniya a 2026

    Masu tsaron raga: Mike Maignan (AC Milan), Robin Risser (Lens), Brice Samba (Rennes)

    Masu tsaron baya: Lucas Digne (Aston Villa), Malo Gusto (Chelsea), Lucas Hernandez (Paris St-Germain), Theo Hernandez (Al Hilal), Ibrahima Konate (Liverpool), Maxence Lacroix (Crystal Palace), Jules Kounde (Barcelona), William Saliba (Arsenal), Dayot Upamenaco (Bayern Munich)

    Masu buga tsakiya: N'Golo Kante (Fenerbache), Manu Kone (Roma), Adrien Rabiot (AC Milan), Aurelien Tchouameni (Real Madrid), Warren Zaire-Emery (Paris St-Germain)

    Masu cin ƙwallaye: Maghnes Akliouche (Monaco), Bradley Barcola (Paris St-Germain), Rayan Cherki (Man City), Ousmane Dembele (Paris St-Germain), Desire Doue (Paris St-Germain), Michael Olise (Bayern Munich), Kylian Mbappe (Real Madrid), Jean-Phillipe Mateta (Crystal Palace), Marcus Thuram (Inter Milan)

  12. Arteta ya ce watakila Timber ya warke kafin Champions League, Champions League

    Kocin Arsenal, Mikel Arteta, ya ce akwai “yiwuwar” Jurrien Timber zai murmure kafin wasan ƙarshe a Champions League, yayin da ɗan wasan ke jinya.

    Sai dai Ben White ya gama buga sauran wasannin bana, sakamakon raunin da ya ji, yayin da Timber ya shafe watanni biyu baya taka leda saboda jinya.

    Waɗannan raunuka sun jefa Arsenal cikin matsala a gefen dama a tsaron baya kafin wasannin ƙarshe a Premier League da Burnley da kuma Crystal Palace, tare da babban wasan gasar zakarun Turai da Paris Saint-Germain ranar 30 ga Mayu a Budapest.

    Hakan na iya sa Cristhian Mosquera ko kuma Riccardo Calafiori su maye gurbinsu.

    Arsenal tana da saura wasa biyu kacal ta lashe kofin Premier League na farko tun shekarar 2004 idan har ta yi nasara a jere.

    Idan Arsenal ta doke Burnley ranar Litinin, hakan zai tilasta sai Manchester City ta yi nasara a Bournemouth daga nan a fayyace mai kofi a ranar karshe.

    Arteta ya bayyana cewa bai kalli wasan da City ta doke Palace 3-0 a ranar Laraba ba, saboda yana halartar liyafa tare da babban mai tallafa wa ƙungiyar, Emirates.

    Da aka tambaye shi ko yana jin kamar ya kusa taɓa kofin Premier League, Arteta ya ce:

    “Ina jin muna da wata dama ranar Litinin domin matsawa kusa da kofin. Wannan shi ne kawai abin da nake tunani.

  13. Colombia ta bayyana ƴan wasa 55 na wucin gadi domin gasar cin kofin duniya, Gasar kofin duniya

    Kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Colombia, Nestor Lorenzo, ya bayyana jerin ƴan wasa 55 na wucin gadi domin FIFA World Cup a ranar Alhamis.

    Jerin yan ƙwallon sun haɗa da fitattun kamar Luis Diaz da ƙyaftin, James Rodriguez, tare da wasu sunaye da suka ba mutane mamaki irin su Sebastian Villa da Juan Guillermo Cuadrado.

    Lorenzo zai rage su zuwa ƴan wasa 26 kafin ranar 29 ga Mayu.

    Kocin ya nuna cikakken goyon baya ga James duk da ƙarancin lokacin da ya samu yana taka leda a wannan kakar, yana cewa ɗan wasan “har yanzu muhimmi ne a gare mu.”

    An sanya Colombia a rukuni na K, inda za ta kara da Uzbekistan da Portugal da kuma Jamhuriyar Congo a gasar da Amurka da Mexico da kuma Canada.

    Kafin fara gasar, tawagar Colombia za ta buga wasannin sada zumunta da Costa Rica a Bogota sannan ta fafata da Jordan a San Diego.

  14. Mitoma ya ji raunin da ya sa ya kammala wasannin kakar bana, Brighton

    Kaoru Mitoma ba zai samu buga sauran wasanni biyu na ƙarshen kakar bana, kuma akwai yiwuwar ba zai buga gasar cin kofin duniya ba.

    Ɗan wasan tawagar Japan ya samu raunin ne a karawar da Brighton ta doke Wolverhampton Wanderers 3-0 a ƙarshen makon da ya gabata.

    Kocin Brighton, Fabian Hurzeler, ya shaida wa manema labarai kafin tafiyar su zuwa Elland Road domin fafatawa da Leeds United a ranar Asabar cewa Mitoma ya ji raunin da ba zai buga wasa biyun da suka rage ba a bana a Premier Leahue.

    Haka kuma kociyan ya kara da cewa Mats Wieffer da Diego Gomez suna fama da raunuka, amma Hurzeler ya ce akwai yiwuwar su buga wasan Elland Road, yayin da Brighton ke ƙoƙarin neman gurbin zuwa gasar zakarun Turai ta baɗi.

  15. , Daga Jaridu

    Bayern Munich ta cimma yarjejeniya da Anthony Gordon kuma ta fara tattaunawa da Newcastle United kan sayen ɗan wasan gaban na Ingila, mai shekara 25. (Bild)

    Tsohon ɗan wasan Ingila Mason Greenwood, mai shekara 24, yana shirin ci gaba da zama a Marseille duk da cewa ana alaƙanta shi da manyan ƙungiyoyin Turai kamar Juventus, da Borussia Dortmund da Atletico Madrid. (Sun)

    Chelsea da Manchester United sun sanya ɗan wasan gaban Real Sociedad ɗan ƙasar Sifaniya Ander Barrenetxea, mai shekara 24, a jerin sunayen waɗanda za su yi zawarci a wannan bazarar. (Marca)

    Manchester United ta shirya zawarcin ɗan wasan tsakiyar Nottingham Forest ɗan ƙasar Ingila Elliot Anderson, mai shekara 23. (Give Me Sport)

  16. Union Saint-Gilloise ta lashe Belgium Cup na biyu a cikin kaka uku, Belgium CUP

    Union Saint-Gilloise ta lashe Belgian Cup a karo na biyu cikin shekaru uku, bayan da ta doke Anderlecht da ci 3-1 bayan ƙarin lokaci.

    A wasan da aka fafata a ranar Alhamis, Union ta buƙaci ƙarin lokaci domin tabbatar da nasara bayan an tashi 1-1 cikin mintuna 90 na wasan.

    Ƙungiyar ta fara cin kwallo a minti na 74 ta hannun ɗan wasan tawagar Argentina, Kevin Mac Allister, bayan da ta mamaye wasan gaba ɗaya.

    Sai dai an soke ƙwallon da ƙyaftin ɗinta ɗan asalin Ingila, Christian Burgess, ya ci da cewar an yi satar gida, bayan da VAR ta bibiyu abinda ya faru kafin cin wallon.

    Anderlecht ta farke a minti na 80 ta hannun Mihajlo Cvetkovic daga bugun tazara, duk da cewa magoya bayanta sun jefa abun da yake sa hayaki cikin fili wanda ya sa aka dakatar da wasan na ɗan lokaci saboda rashin ganin filin sosai.

    A ƙarin lokaci kuwa, ƴan wasan da aka sauya suka zama jarumai — Mohammed Fuseini da Kevin Rodriguez — sune suka ci ƙwallaye cikin mintuna 10 na farkon ƙarin lokaci.

  17. Kerr za ta bar Chelsea a karshen kakar bana, Ƙwallon kafar mata

    Sam Kerr — wadda ita ce mafi yawan cin ƙwallo a tarihin Women's Super League mai takaleda a ƙungiyar mata ta Chelsea — za ta bar stamford Bridge bayan kwantiraginta ya ƙare a wannan bazarar.

    Kerr mai shekara 32 ta zura ƙwallaye 115 a wasa 157 da ta bugawa Chelsea, kuma wasanta na ƙarshe zai kasance a gida da Manchester United ranar Asabar.

    Ƴar wasan tawagar Australia, wadda ta koma Chelsea a watan Nuwamban 2019, ta taimaka wa ƙungiyar lashe kofunan WSL guda biyar, FA Cup uku, League Cup uku da kuma FA Community Shield.

    Kerr ta lashe ƙyautar takalmin zinariya sau biyu, sannan aka zaɓe ta a matsayin Gwarzuwar ƴar wasan WSL a shekarar 2022, tare da lashe kyautar Professional Footballers' Association ta gwarzuwar ƴar wasan da magoya baya suka zaɓa a shekarar 2021 da kuma 2022.

  18. Sinner na kara yin fice a gasar ƙwallon tennis a duniya, Ƙwallon tennis

    Jannik Sinner ya karya tarihin Novak Djokovic na yawan cin wasanni a jere a gasar ATP Masters 1000, bayan da ya samu nasara ta 32 a jere da kaiwa wasan daf da ƙarshe a Italian Open.

    Ɗan wasan Italy wanda ke matsayi na ɗaya a duniya ya yi nasarar doke ɗan wasa mai matsayi na 12, Andrey Rublev, da ci 6-2, 6-4.

    Sinner na ci gaba da fafutukar zama mutum na biyu bayan Djokovic da zai lashe dukkanin gasar Masters 1000 guda tara — wato mafi girman matakin gasar tennis bayan Grand Slam.

    Ɗan wasan mai shekara 24 yana nuna karin samun gogewa, kafin fara French Open ranar 24 ga watan Mayu, wanda shi ne kawai babban kofin da ya rage masa domin cika tarihin lashe dukkanin Grand Slam a rayuwarsa.

    Haka kuma ya haɗu da fitaccen ɗan wasa, Rafael Nadal na ƙasar Spain a matsayin mutum na biyu da suka kai wasan kusa da na ƙarshe a dukkanin gasar Masters 1000 guda biyar a kakar wasa guda.

    A wasan gaba, Sinner zai kara da ɗan ƙasar Russia Daniil Medvedev ko kuma ɗan wasan Spain da aka ba damar shiga daga baya, Martin Landaluce, domin neman gurbin wasan ƙarshe.

  19. PSG ce ta lashe Ligue 1 na bana na biyar a jere, PSG

    Paris Saint-Germain ta lashe Ligue 1 na bana karo na 14 a tarihinta — kuma karo na biyar a jere — bayan ta doke babbar abokiyar hamayyarta Lens.

    PSG na buƙatar kunnen doki kawai domin tabbatar da kofin kakar nan, kasancewar Lens na baya da maki shida.

    Kwallayen da Khvicha Kvaratskhelia da wanda ya maye gurbinsa, Ibrahim Mbaye, suka ci a filin Stade Bollaert-Delelis suka tabbatar wa PSG da kofin saura wasa ɗaya a kammala kakar nan.

    PSG ita ce ƙungiyar da ta fi kowacce lashe Ligue 1, yayin da Saint-Etienne ke biye da kofuna 10.

    PSG ta lashe Ligue 1 sau 12 cikin shekaru 14 da suka gabata, kuma za ta je wasan ƙarshe a lig da abokiyar hamayyarta Paris FC a ranar Lahadi.

    Haka kuma za ta kara da jagorar Premier League, wato Arsenal, a wasan ƙarshe a Champions League ranar 30 ga watan Mayu yayin da take neman kare kambunta na Turai.

    A gefe guda kuma, Lens za ta fafata da Nice a wasan ƙarshe a Coupe de France ranar 22 ga watan Mayu.

  20. Carrick na cikin ƴan takarar gwarzon kocin Premier League na bana, Manchester United

    Kocin riƙon kwarya na Manchester United, Michael Carrick, ya shiga cikin jerin ƴan takarar ƙyautar gwarzon kociyan Premier League na shekarar nan.

    Carrick, wanda ya jagoranci wasa 15 tun bayan da ya maye gurbin Ruben Amorim a watan Janairu, yana takara tare da kocin Arsenal, Mikel Arteta da kuma na Manchester City, Pep Guardiola, wadanda ke fafatawa wajen kokarin lashe kofin bana.

    Sauran waɗanda ke takara har da kocin Bournemouth, wanda zai bar aikin horar da ƙungiyar a bana, Andoni Iraola, da kuma na Brentford Keith Andrews, tare da kocin Sunderland Regis le Bris.

    A bangaren gwarzon ɗan wasa na shekara nan kuwa, daga cikin ƴan wasa takwas da za a zaɓi gwani akwai uku daga Arsenal — David Raya da Gabriel da kuma Declan Rice — tare da ƴan wasan Manchester City biyu Antoine Semenyo da kuma Erling Haaland.

    Haka kuma an saka kyaftin ɗin Manchester United, Bruno Fernandes da ɗan wasan Brentford Igor, Thiago da kuma na Nottingham Forest, Morgan Gibbs-White cikin jerinsu.

    A bangaren ƙyautar fitatcen Matashin Ɗan Wasa na Shekara — ga ƴan wasan da shekarunsu ba su wuce 23 ba a farkon kakar — akwai ɗan ƙwallon West Ham United, Mateus Fernandes da na Newcastle United Lewis Hall da na Brentford, Michael Kayode da kuma ɗan wasan Manchester United Kobbie Mainoo.

    Ƴan wasan Bournemouth, Junior Kroupi da Alex Scott da na Manchester City, Rayan Cherki da Nico O'Reilly, su ma suna cikin jerin takwas da za a zaɓi ɗaya.

    Za a tantance waɗanda za su yi nasara ne ta hanyar haɗa ƙuri’un jama’a da kuma ra’ayoyin kwararrun masana ƙwallon ƙafa.