'An kama shugaban ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi a Equador'
Shugaban Equador, Daniel Noboa, ya ce an kama shugaban ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi mafi girma a ƙasar, a wani samame na haɗin gwiwa da ƴan sandan Sifaniya.
Mista Noboa ya sanar da kama Wilmer "Pipo" Chavarria ne a wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumuta inda ya ce shugaban ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyin ya ɓoye a Turai, inda yake ci gaba da gudanar da harkokin ƙungiyar tasu, bayan aka yi ƙaryar cewa ya mutu.
Ƴan Equador na kaɗa ƙuri'ar raba gardama kan abubuwan da suka shafi tsaro - da suka haɗa da a bar sojojin ƙasashen waje su kafa sansani ƙasar.
Ƙasar da ke Kudancin Amurka ta sha fama da rikice-rikice a ƴan shekarun nan, lamarin da ake alaƙantawa da ayyukan masu safarar hodar ibilis.