Sai wani lokacin
Ƙarshen rahotonni kenan a wannan shafi na labarin wasanni.
Mu haɗu da ku a wani lokacin.
Wannan shafi na kawo muku rahotonni kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni na ranar 13 ga watan Yuni, 2024.
Umar Mikail
Ƙarshen rahotonni kenan a wannan shafi na labarin wasanni.
Mu haɗu da ku a wani lokacin.

Asalin hoton, EPA
Mai masaukin baƙin gasar ƙasashen Turai Jamus ta fara wasa da ƙafar dama bayan nasarar doke Scotland 5-1.
Matasan ‘yan wasa Florian Wirtz da Jamal Musiala ne suka fara ci wa Jamus ƙwallayen, sai kuma Kai Havetz da ya ci ta uku a bugun finareti bayan bai wa ɗn wasan Scotland Ryan Porteous jan kati daf da tafiya hutun rabin lokaci.
Bayan dawowa daga hutun ne kuma Niclas Füllkrug ya ƙara ta uku a ragar Scotland, kafin Antonio Rudiger na Jamus ɗin ya ci gida.
Sai dai ba a tashi daga wasan ba sai da Emery Can ya ci wa masu masaukin baƙin ta biyar, wanda ya ba ta damar ɗarewa saman teburi da maki uku.
A gobe Asabar kuma wasannin za su ci gaba, inda Hungary za ta fafata da Switzerland, da wanda Italiya za ta kara da Albania. Sai kuma wasa mai zafi tsakanin Sifaniya da Croatia.

Asalin hoton, EPA
Ƙasa da awa ɗaya ya rage Jamus ta buɗe gasar Euro 2024 da wasa tsakaninta da Scotland.

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, @BVB
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Dortmund da ke buga Bundesliga ta Jamus ta sanar da Nuri Sahin a matsayin kocinta bayan raba gari da Edin Terzic a jiya Alhamis.
Matashin kocin mai shekara 35 ya saka hannu kan yarjejeniyar da za ta ƙare a watan Yunin 2027.
Tsohon ɗan wasan Real Madrid da Liverpool, Sahin ya shafe mafi yawan rayuwar ƙwallonsa a Dortmund.
"Alfarma ce babba a wajena na zama kocin Borussia Dortmund. Ina gode wa kowa da kowa da irin ƙwarin gwiwar da suka nuna a kai na," in ji shi kamar yadda ya faɗa wa shafin intanet na kulob ɗin.
"It is a great honor for me to be the coach of Borussia Dortmund. I would like to thank everyone in charge at the club for the trust they have placed in me
Shi ne mataimakin Terzic kafin kocin ya nemi katse yarjejeniyarsa da kulob ɗin.
Sahin ya yi ritaya da taka leda a kulob ɗin Antalyaspor ta Turkiyya a shekarar 2022.

Asalin hoton, Reuters
Manchester United ta miƙa tayin fan miliyan 35 ga Everton domin ɗaukar ɗan wasanta Jarrad Branthwaite.
Sai dai kulbo ɗin ya yi watsi da tayin, inda rahotonni suka ce ya yi ƙasa sosai da farashin fan miliyan 80 da Everton ke nema.
Tuni ɗan wasan bayan ya amince wa United zai koma Old Trafford.
Saia dai BBC Sport ta fahimci cewa Everton ba ta son sayar da Branthwaite mai shekara 21, wanda wasu da dama ke cewa ya kamata a saka shi cikin tawagar Ingila ta gasar Euro 2024.
Kulob ɗin na ganin cewa nan gaba kaɗan ɗan wasan zai shiga cikin tawagar Ingila tana mai kwatanta shi da Harry Maguire da Josko Gvardiol.
Branthwaite ya ja hankalin duniya ne a matsayina na lamba ukun Everton, kuma ya taimaka mata wajen kauce wa sauka daga gasar Premier League.

Asalin hoton, PA Media
'Yan awanni kawai suka rage kafin wannan filin ya maƙare da 'yan kallo.
Za a ga 'yan kallo a wannan filin na Football Arena da ke birnin Munich.
Ko baƙi (Scotland) za su fi masu masaukin baƙi (Jamus) sowa?

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya ta sanar da shirinta na ɗauko mai horarwa daga ƙasar waje domin yunƙurin kawo gyara a wasannin tawagar ƙasar ta Super Eagles.
Nigeria Football Federation (NFF) ta ce za ta ɗauko mai ba da shawara kan wasanni wato Technical Adviser a Turance don ya jagoranci wasannin neman shiga gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2025 da kuma na Kofin Duniya da suka rage.
Bayan rashin nasarar da Super Eagles ɗin ta yi a wasannin da ta buga zuwa yanzu, Ministan Wasanni John Eno ya bai wa NFF wa'adi domin shawo kan matsalar ta hanyar sauya tawagar kociyoyin ƙungiyar.
Kazalika, ya nemi cikakken bayani daga NFF game da yadda Najeriya ta buga wasanni biyu - ta yi canjaras da Afirka ta Kudu sannan Benin ta doke ta a wasannin neman shiga Kofin Duniya.
Latsa nan domin karanta cikakken labarin

Asalin hoton, Getty Images
Yau Juma'a za a fara gasar cin kofin nahiyar Turai ranar Juma'a gasa ta 17 da ake kira Euro 2024 da Jamus za ta karbi bakunci.
Ana kuma sa ran buga wasan karshe ranar 14 ga watan Yuni, kuma duk wadda ta yi nasara za ta buga wasan karshe da duk wadda za ta lashe Copa America na bana.
Sunan kofin shi ne 2025 CONMEBOL–UEFA Cup of Champions da aka kulla yarjejeniya tsakanin nahiyar Turai da ta Kudancin Amurka .
Za a kara a Euro 2024 tsakanin tawaga 24, inda Georgia ce kadai da za ta fara buga gasar nahiyar Turai a karon farko a tarihi.
Italiya ce mai rike da kofin Euro 2020, bayan da ta doke Ingila a wasan karshe a bugun fenariti a Wembley.
Latsa nan domin karanta cikakken labarin

Asalin hoton, Getty Images
A yammacin yau Juma’a za a fara gasar ƙasashen Turai ta Euro 2024 karo na 17 a tarihi.
Mai masaukin baƙi Jamus da ta ci gasar sau uku za ta buɗe da wasa tsakaninta da Scotland da ƙarfe 8:00 agogon Najeriya da Nijar.
Za a buga wasan ne a filin wasa na Football Arena da ke birnin Munich.
Tawagar ƙasa 24 ne za su nemi lashe kofin gasar tun daga yau har zuwa 14 ga watan Yuli a filayen wasa 10, inda za a buga jimillar wasa 51.
Ita kuwa mai riƙe da kofin da ta ɗauka a 2020, Italiya za ta fara nata wasan da Albania a gobe Asabar, a rukuni mai zafin gaske da ya ƙunshi Sifaniya da Croatia.
Duk tawagar da ta yi nasarar cin kofin za ta samu kyautar yuro miliyan takwas, ta biyu kuma ta samu miliyan biyar, sai waɗanda suka kai zagayen kusa da na ƙarshe kuma da za su tashi da yuro miliyan hurhuɗu.
Yau take ranar Euro 2024!
Ma'abota BBC Hausa barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarin wasanni na kai-tsaye.
Za mu kawo muku yadda ƙasashen Turai ke shirin fara fafatawa a gasar Euro 2024 a Jamus.
Ku biyo ni Umar Mikail don sanin yadda take kasancewa a duniyar wasanni.