Amurka ta yaba wa gwamnatin Najeriya kan ceto wasu daga cikin ɗaliba 100 na makarantar St Marys da aka sace a Papiri da ke jihar Neja, tana mai cewa hakan na nuna sabon kuzari da jajircewar gwamnati wajen tunkarar matsalolin tsaro.
Jami’in Amurka Riley Moore ne ya bayyana haka cikin wani saƙon godiya da ya wallafa a shafinsa na X, bayan ganawar da ya yi da mai ba wa Shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, tare da tawagar 'yan majalisar dokokin Amurka da suka kai ziyara Najeriya.
A cewar jami’in, tattaunawar ta kasance mai zurfi kuma cike da kyakkyawar fahimta, inda aka tattauna kan muhimman matakai da za su inganta tsaro a Najeriya idan aka aiwatar da su yadda ya kamata.
Ya ce "Matakan da aka gabatar za su taimaka wajen tarwatsa ƙungiyoyin ta’addanci a arewa maso gabas da kuma daƙile tsangwamar Kiristoci da ke damun gwamnatin Amurka, musamman a yankin Middle Belt.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Najeriya ta karɓi taimakon gaggawar da Amurka ke nunawa kan batutuwan tsaro yana mai cewa ana matsowa kusa da samar da tsarin haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.
Ya misalta kafa rundunar hadin gwiwa ta Najeriya da Amurka a matsayin babban ci gaba da ke nuna shirin gwamnati na aiki tare da Amurka wajen tunkarar manyan kalubale.
Jami’in ya ce duk da ci gaban da ake samu, akwai sauran muhimman matakai da za a ɗauka, amma abubuwa na tafiya a hanya madaidaiciya.