Gwamnan Nasarawa ya ƙaddamar da aikin faɗaɗa titin Abuja zuwa Keffi
Gwamnatin jihar Nasarawa da ke Arewa maso tsakiyar Nigeria ta yunkuro domin sauwaka wa al'ummominta da ke fuskantar matsalar cunkoson ababen hawa da aka dade ana fama da ita a garin Mararabar Nyanya, da ke karamar hukumar Karu.
An kaddamar da ginin gadoji biyu a titin da ya tashi daga Abuja zuwa Keffi, inda gwamnatin jihar ta ce ana sa ran kammala aikin ne cikin shekaru biyu masu zuwa.
Titin dai ya dade yana jefa matafiya cikin kunci, musamman idan cunkuson ababen hawa na yi kamarin, lamarin dan kan sa wasu su kwashe awanni suna jira.
Kamfanin Paramount ya miƙa tayin sayen kamfanin Warner Brothers a dala biliyan 100
Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin Paramount ya miƙa tayinsa na zunzurutun kudi dala biliyan ɗari da tamanin domin sayen baki daya hannun jarin kamfanin Warner Brothers.
Paramount na yunƙurin doke kamfanin Netflix, wanda aka amince da tayinsa na sayen dakunan daukar fina-finai da kuma bangaren kallon fina-finai ta intanet na kamfanin Warner akan dala biliyan saba'in da biyu a makon da ya gabata kamar yadda aka ruwaito.
Wakiliyar BBC ta ce a baya kamfanin Warner Brothers ya ki amince wa da tayin da Paramount ya yi, amma masu hannun jarin kamfanin ba su riga sun sanya hannu kan yarjejeniya da Netflix ba, wanda hakan ya sa Paramount sake gwada sa'arsa.
Gwamnatin Neja ta karɓi yara 100 da aka ceto
An miƙa wa hukumomin jihar Neja gomman yaran nan da jam'ian tsaron Najeriya suka ceto bayan sun shafe kusan makonni biyu a hannun waɗanda suka yi garkuwa da su.
Yaran sun iso babban birnin jihar Minna a cikin kananan motocin bas, tare da rakiyar motocin sojoji da motoci masu sulke, inda gwamnan jihar Umaru Bago ya tarbe su.
Ana sa ran miƙa yaran ga cocin katolika da kuma hukumomin makarantar.
Yaran na cikin fiye da ɗalibai da ɗari uku da malaman makaranta da aka yi garkuwa da su daga wata makarantar kwana.
Wakilin BBC ya ce hukumomi a kasar sun bai wa makarantar tabbacin za a sako sauran ɗaliban kashi kashi.
Za a samar da jirgin ƙasa da zai kai Qatar daga Saudiyya a awa biyu
Asalin hoton, EPA
Ƙasashen Saudiyya da Qatar sun sanya hannu a yarjejeniyar fara aikin dogo domin samar da jirgin ƙasa da zai riƙa sufurin fasinja a tsakanin biranen ƙasashen biyu.
Ana dai ganin wanna sabuwar yarjejeniyar da ma aikin da za a yi zai ƙara gyara alaƙa tsakanin ƙasashen na Larabawa masu arziki.
Kafar watsa labarai ta gwamnatin Saudiyya ta ce jirgin ƙasan zai iya yin tafiyar sama da kilomita 300 a awa ɗaya, inda fasinjoji za su isa Riyadh daga Doha ko kuma daga Doha zuwa Riyadh a cikin awa biyu kacal. Kamfanonin da za su yi aikin sun ce aikin zai ci kimanin shekara shida ana yi.
A baya dai ƙasashen biyu sun kasace cikin takun-saƙa, inda a shekarar 2017 ne dai dangantaka ta yi tsami tsakanin ƙasashe biyu bayan Saudiyya ta zargi Qatar da zama ta kusa da Iran da taimaka mata wajen goyon bayan ƙungiyoyi masu zafin addini.
Sojojin Isra'ila sun shata layin iyaka a Gaza
Asalin hoton, EPA
Shugaban rundunar sojin Isra'ila ya ce wuraren da sojojin Isra'ilan suka janye a Gaza sabuwar iyaka ce. Laftanar Janar Eyal Zamir, ya yi wannan jawabin ne a yayin da ya ziyarci dakarunsa da ke yankin Falasdinu.
A yankin na Yellow Line, Isra'ila ce ke da iko da fiye da rabin Gaza ciki har da birnin Rafah da kuma birnin Beit Hanoun da ke arewaci.
A karkashin shirin zaman lafiya na Amurka, a nan gaba Isra'ila za ta janye daga wasu wuraren idan har Hamas ta fara ajiye makamanta.
Tun da farko firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce ya yi amanna matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma ya kusa zuwa karshe inda ake sa ran fara amfani da mataki na biyu ba tare da bata lokaci..
Hotuna: Yadda ɗaliban jihar Neja da aka ceto suka isa gidan gwamnati
Da yammacin ranar Litinin 8 ga watan Disamba ne ɗaliban makarantar St Mary's da ke Papiri a jihar Neja suka isa gidan gwamnati bayan an sanar da samun nasarar ceto su.
Sai dai har yanzu babu tabbacin ko an biya kuɗin fansa ko ba a biya ba.
Daga cikin waɗanda suka tarbe su har da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da Gwamnan Neja, Umaru Bago da sauransu.
Har yanzu Syria na buƙatar agajin ƙasashen duniya - MDD
Asalin hoton, UNHCR
Shugaban hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya mai barin gado, ya yi gargadin cewa duk da kasancewa shekara guda da hambarar da gwamnatin shugaba Assad a Syria, har yanzu kasar na bukatar agajin daya kamata a ce duniya ta mayar da hankali a kai wajen taimaka mata.
Filippo Grandi, ya shaida wa BBC cewa, kasar ta Syria na matukar bukatar taimakon kasashen duniya da ma kulawarsu domin ta wattsake daga matsalolin da ta fuskanta a baya.
Wakiliyar BBC ta ce ya bayyana al'ummar Syria a matsayin masu hakuri da juriya to amma idan har ba a inganta rayuwarsu ba, to yana fargabar cewar za a sake barinsu cikin tagayyara.
Ya ce idan har ba a inganta rayuwar 'yan gudun hijirar Syrian miliyan uku ba da kuma tabbatar da mayar da wadanda suka rasa muhallansu gidajensu ba to akwai sauran rina a kaba.
Amurka ta yaba da ceto ɗaliban jihar Neja 100
Asalin hoton, BBC Via Zahradden
Amurka ta yaba wa gwamnatin Najeriya kan ceto wasu daga cikin ɗaliba 100 na makarantar St Marys da aka sace a Papiri da ke jihar Neja, tana mai cewa hakan na nuna sabon kuzari da jajircewar gwamnati wajen tunkarar matsalolin tsaro.
Jami’in Amurka Riley Moore ne ya bayyana haka cikin wani saƙon godiya da ya wallafa a shafinsa na X, bayan ganawar da ya yi da mai ba wa Shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, tare da tawagar 'yan majalisar dokokin Amurka da suka kai ziyara Najeriya.
A cewar jami’in, tattaunawar ta kasance mai zurfi kuma cike da kyakkyawar fahimta, inda aka tattauna kan muhimman matakai da za su inganta tsaro a Najeriya idan aka aiwatar da su yadda ya kamata.
Ya ce "Matakan da aka gabatar za su taimaka wajen tarwatsa ƙungiyoyin ta’addanci a arewa maso gabas da kuma daƙile tsangwamar Kiristoci da ke damun gwamnatin Amurka, musamman a yankin Middle Belt.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Najeriya ta karɓi taimakon gaggawar da Amurka ke nunawa kan batutuwan tsaro yana mai cewa ana matsowa kusa da samar da tsarin haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.
Ya misalta kafa rundunar hadin gwiwa ta Najeriya da Amurka a matsayin babban ci gaba da ke nuna shirin gwamnati na aiki tare da Amurka wajen tunkarar manyan kalubale.
Jami’in ya ce duk da ci gaban da ake samu, akwai sauran muhimman matakai da za a ɗauka, amma abubuwa na tafiya a hanya madaidaiciya.
An tura ƙarin sojoji don taimakon yankunan da ambaliya ta shafa a Sri Lanka
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Sri Lanka ta ce ta aika ƙarin dubban sojoji domin su taimaka a yankunan da suka yi fama da guguwar teku da ambaliya da kuma zarftarewar ƙasa a cikin makonnin da suka gabata.
Wannan matakin na zuwa ne a yayin da ake hasashen ci gaba da samun mamakon ruwan sama a wurare da dama, ciki har da tsakiyar ƙasar da lamarin ya fi shafa.
Rundunar ta ce ta aika sojoji fiye da dubu talatin da takwas domin kai agaji da kuma yin ayyukan gyara a yankuna da abin ya shafa.
Zuwa yanzu alkaluma sun nuna mutum ɗari shida da talatin ne suka mutu a ƙasar
Kotu ta ƙi amincewa da buƙatar Kanu ta canza masa gidan yarin Sokoto
Mai shari'a James Omotosho na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya ƙi amincewa da buƙatar da jagoran IPOB, Nnamdi Kanu, ya gabatar na neman a canza masa gidan yarin da yake a Sokoto zuwa wani kurkuku da ke cikin Abuja ko Jihar Nasarawa.
Kanu, ta hannun hukumar da ke tallafawa raunan da shari'arsu, ya shigar da ƙara ta gaggawa yana neman umarnin da zai saka gwamnatin tarayya ko hukumar gyaran hali ta Najeriya (NCoS) ta hanzarta mayar da shi daga Sokoto zuwa Kuje a Abuja ko Keffi a Nasarawa domin samun damar bin diddigin ɗaukaka ƙarar da yake shirin yi.
Sai dai a ranar Litinin, mai shari’a Omotosho ya ƙi amincewa da bukatar, yana mai cewa ba za a iya bayar da irin wannan umarni ba tare da jin ta bakin gwamnatin tarayya ba..
Kotun dai ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 27 ga Janairu, 2026.
A ranar 20 ga Nuwamba, kotu ta same shi da laifi kan dukkan tuhumar ta’addanci guda bakwai da Gwamnatin tarayya ta shigar, tare da yanke masa hukuncin daurin rai da rai.
Dubban mutane sun tsere daga kan Iyakar Thailand da Cambodia bayan sabon rikici
Dubban mazauna yankunan da ke kan iyakar Thailand da Cambodia sun tsere a ranar Litinin, yayin da wani sabon rikici ya ɓarke, wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum biyar.
Ɓangarorin biyu dai sun ɗora alhakin fara rikicin, lamarin da ya zama mafi muni tun bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da suka cimma a watan Yuli.
Tun watan Mayu, tashin hankali tsakanin ƙasashen biyu ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 40, tare da hana shigo da kaya da kuma takaita zirga-zirga.
Asalin hoton, Reuters
A ranar Litinin, rundunar sojin Thailand ta ce ta mayar da martani ne bayan harbin da sojin Cambodia suka yi a lardin Ubon Ratchathani na ƙasar, ciki har da ƙaddamar da hare-haren sama a kan iyakar da ake takaddama a kai; yayin da ma’aikatar tsaron Phnom Penh ta ce Thailand ce ta fara kai musu hari a lardin Preah Vihear na Cambodia.
Aƙalla soja ɗaya na Thailand da fararen hula huɗu na Cambodia sun mutu, yayin da fiye da mutum goma suka jikkata a fuskar rikicin, a cewar jami’an ƙasashen biyu.
Asalin hoton, Siksaka Pongsuwan
An kashe mutum huɗu a rikicin ƙungiyoyin asiri a Anambra - Ƴansanda
Asalin hoton, AFP
Ƴan sanda a jihar Anambra sun tabbatar da kashe mutum huɗu a rikicin da ke da alaƙa da ƙungiyoyin asiri a kasuwar Afor Nawfia da ke kan Tsofaffin Hanyoyin Onitsha–Awka a daren Lahadi.
An ce waɗanda suka kai harin suna cikin mota ne lokacin da suka buɗe wuta ba kakkautawa kafin suka tsere.
Har yanzu dai ba a san sunayen maharan ko lambar motarsu ba.
‘Yan sanda sun ce duk da cewa an ɗauki matakai kwanaki kafin rikicin, sai dai harin ya faru.
Rundunar musamman ta yaƙi da ƙungiyoyin asiri ta ce ta kama mutum biyu bisa bayanai game da harin inda aka ƙwato makami.
Ƴansandan sun ce waɗanda aka kama suna ba da hadin kai wajen hana sabuwar tashin hankali daga ƙungiyoyin asiri a Awka da kewaye.
‘Yan sanda sun ce bayanan farko daga wurin harin sun taimaka wajen gano masu laifin, kuma ana ci gaba da bincike.
Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda, SP Ikenga Tochukwu,, ya tabbatar wa mazauna cewa za a hukunta masu laifin.
China za ta dakatar da zuba jari a fannin mai a Sudan saboda rashin tsaro
Asalin hoton, Getty Images
China na shirin kawo ƙarshen hadin gwiwarta ta shekaru 30 a harkar haƙar mai a Sudan, sakamakon tabarbarewar tsaro a filayen mai na jihar Kordofan ta Kudu da take aiki, kamar yadda gidan jaridar Sudan Tribune ya ruwaito.
Kamfanin mai na gwamnatin China, CNPC, ya nemi ganawa da gwamnatin Sudan a wannan watan don tattauna yiwuwar kawo ƙarshen haɗin gwiwa kafin lokaci.
CNPC ta sanar da ma’aikatar makamashi da haƙar ma’adinai ta Sudan cewa, “Tilas ne ya sa muka nemi ganawar gaggawa a Juba, babban birnin Kudancin Sudan, a watan Disamba don tattauna kawo ƙarshen yarjejeniyar raba riba da kuma yarjejeniyar bututun mai na Field Six.”
Kamfanin ya ce matakin ya biyo bayan rashin tsaro da ya addabi filayen mai.
Tun bayan da dakarun RSF ta ƙwace birnin al-Fashir na Darfur daga hannun sojojin gwamnati a watan Oktoba, faɗa tsakanin sojojin Sudan da RSF ya fi mayar da hankali zuwa yankin Kordofan.
Ma’aikatar makamashi da hakar ma’adinai ta Sudan ta rattaɓa hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa da CNPC ne a watan Satumba 1995
'Ba mu da masaniya kan shirin miƙa wa iyaye ɗaliban da aka ceto'
Mutumin da ya mallaki makarantar St Mary’s Catholic da ke Papiri, Bishop Bulus Dauwa Yohanna, ya bayyana cewa makarantar ba ta samu wani bayani game da tsarin miƙawa iyaye ɗaliban da aka ceto ba duk da rahotannin cewa an ceto ɗalibai 100 daga cikin waɗanda aka sace.
Ya shaida wa BBC cewa duk da cewa makarantar ta samu tabbaci daga ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) cewa an ceto ɗalibai 100, babu wata sanarwa kan lokacin da za a miƙa yaran ga iyayensu a hukumance.
Bishop Yohanna ya ce akwai yiyuwar hukumomi na buƙatar lokaci domin tantance ɗaliban da bayar da taimakon da suke buƙata kafin a sanar da cikakken tsarin mika su ga iyayensu.
A ranar Asabar, makarantar ta gudanar da gajeren taro da iyaye a Papiri don ba su bayanai kan cigaban da aka samu kan kokarin ceto yaran da sakamakon tattaunawar da aka yi da ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, inda iyaye sama da 100 suka halarta.
Ya kara da cewa makarantar ba ta san ainihin inda daliban da aka ceto suke ba.
An kashe ƴan Cambodia huɗu a rikicin sojojin ƙasar da na Thailand
Asalin hoton, Getty Images
Ministan Bayanai na Cambodia, Neth Pheaktra, ya bayyana cewa fararen hula hudu ne suka rasa rayukansu, yayin da mutum tara suka samu raunuka, sakamakon sabon rikici da ya ɓarke tsakanin sojojin Thailand da Cambodia.
Rahotanni sun nuna cewa wannan tashin hankali ya auku ne a lardin iyaka ta arewa na Preah Vihear da Oddar Meanchey.
Pheaktra ya ce dubban mutane ne suka rasa matsuguni sakamakon rikicin, a yayin da ya wallafa wannan bayani a shafinsa na Facebook.
Rashin tsaro na neman fin ƙarfin gwamnatin Najeriya - Kwankwaso
Asalin hoton, Kwankwaso/x
Jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara munana a ƙasar, yana mai cewa matsalolin tsaron "na neman su fi ƙarfin gwamnati".
Ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
Tsohon gwamnan na Kano ya ce alamu na nuna cewa matsalolin tsaro da ke faruwa yanzu ka iya zama babbar barazana ga haɗin kai da kwanciyar hankalin ƙasa.
A cikin saƙonsa, ya ce: "Dukkan alamu na nuna cewa rashin tsaro na neman fin ƙarfin gwamnatin. Wannan na fitowa fili a yadda take barin jihohi su kafa ƙungiyoyin tsaro na ƴan sa-kai ba tare da horo na musamman ba."
"Wannan mataki, ko da an yi shi da kyakkyawar niyya, ya haddasa yaɗuwar ƙananan makamai da manyan makamai a faɗin ƙasa.” in ji shi.
Kwankwaso ya kuma nuna damuwa kan yadda ake samun ƙaruwa a tsangwama da azabtar da ’yan Najeriya musamman daga wasu yankuna.
Kwankwaso ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta hanzarta ɗaukar mataki kafin lamura su lalace gaba ɗaya.
'Syria har hanzu na buƙatar tallafin gaggawa duk da sauyin gwamnati'
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya mai barin gado, ya yi gargaɗin cewa duk da kasancewa shekara guda da hamɓarar da gwamnatin shugaba Assad a Syria, har yanzu ƙasar na buƙatar agajin daya kamata ace duniya ta mayar da hankali a kai wajen taimaka mata.
Filippo Grandi, ya shaida wa BBC cewa, ƙasar na matukar buƙatar taimakon ƙasashen duniya da kulawarsu.
Ya bayyana al'ummar Syria a matsayin masu haƙuri da juriya to amma idan har ba a inganta rayuwarsu ba, to yana fargabar cewar za a sake barinsu cikin tagayyara.
Ya ce idan har ba a inganta rayuwar 'yan gudun hijirar Syrian miliyan uku ba da kuma tabbatar da mayar da waɗanda suka rasa muhallansu gidajensu ba to akwai sauran rina a kaba.
Sabon rikici ya ɓarke tsakanin sojojin Thailand da Cambodia
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Thailand ta ce an kashe sojojinta aƙalla biyu a yayin wani sabon rikici da ya barke tsakaninta da makwabciyarta Cambodia.
Dukkan ɓangarorin biyu na zargin juna da fara takalar fadan.
Rundunar sojin saman Thailand ta ce ta daƙile wasu hare-hare da sojojin Cambodia suka kai a kan iyakarsu da ake rikici akanta.
Cambodia dai ta musanta cewa ita ta fara takalar fadan inda ta buƙaci masu sanya idanu na ƙungiyar da ke kula da ƙasashen yankin da su gudanar da bincike akan zargin.
Firaiministan Malaysia Anwar Ibrahim, wanda ke taimakawa wajen ganin an ƙulla yarjejeniyar tsagaita wutar da bata samu nasara ba a tsakanin ƙasashen, ya ce ya damu matuƙa a game da hare-haren baya bayan nan da ake kai wa.
Abin da ganawar Atiku da Jonathan ke nufi - Masana
Asalin hoton, Getty Images
Muhawara ta barke a fagen siyasar Najeriya, bayan wata ganawa da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar, ya yi da tsohon shugaban kasar Good Luck Ebele Jonathan.
'Yan siyasar biyudai basu fito fili sun yi bayanin abubuwan da suka tattauna ba, amma mutane da dama na alakanta ganawar ta su da shirye shiryen tunkarar zaben shugaban kasar na 2027.
Ana dai rade radin cewa dukkansu, na da sha'awar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Ganawar jiga jigan 'yan siyasar ta gudana ne a Abuja inda Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban Najeriyar Good Luck Jonathan har gida, duk da irin tsamar siyasar da ke akwai a tsakaninsu, duba da cewa Atikun na cikin wadanda suka jagoranci kifar da gwamnatin Jonathan a zaben 2015.
An ceto wasu daga cikin ɗaliban da aka sace a Papiri ta jihar Neja
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da ceto ɗalibai 100 daga cikin mutane 315 da ’yan bindiga suka sace a Makarantar St. Mary’s da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwara a Jihar Neja.
’Yan bindigar sun kai farmakin ne a ranar 21 ga Nuwamba, 2025, inda suka mamaye makarantar suka tafi da mutum 315 da suka haɗa da ɗalibai 303 da malamai 12.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro tare da mafarauta na yankin sun bazama cikin dazuzzukan da ke makwabtaka da Papiri domin neman waɗanda aka sace.
A rana ta farko bayan harin, yara 50 sun yi nasarar tserewa kuma suka koma hannun iyalansu lamarin da ya kawo addadin waɗanda suka rage a hannun ƴan bindigar zuwa mutum 265 kafin wannan sabon cigaba na ceto wasu daga cikinsu.
Gwamnatin Jihar dai ta bayyana cewa kafin aukuwar lamarin ta samu sahihan bayanan sirri game da yiwuwar tashin hankula a sassan jihar Neja da ke arewacin ƙasar, saboda haka ta dakatar da ayyukan gine-gine tare da rufe makarantun kwana a yankunan da abin ya shafa.