Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/09/2025.

Taƙaitattu

  • Latsa nan ku shiga tasharmu ta WhatsApp
  • Rundunar sojin Najeriya ta musanta yunƙurin juyin mulki
  • Sojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 21 daga hannun 'yanbindiga a jihar Kwara
  • Shugaba Tinubu ya koma Najeriya bayan taron Italiya
  • 'An kashe Falasɗinawa 11 a Gaza'
  • Ba zan yi takarar shugaban ƙasa da Tinubu ba - Wike
  • An gano hanyar gwajin cutar kansa a matakin farko

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi da Umar Mikail

  1. Kullen Allah ta buƙaci Tinubu ya ci gaba da ɗaukar matakan rage farashin abinci

    Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Kullen Allah ta buƙaci shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ci gaba da ɗaukar matakan rage farashin kayan abinci domin wadata ƙasar da abinci da kuma magance tsadar rayuwa.

    Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Hon. Khalil Mohd Bello ya fitar ya ce ƙungiyar ta yi kiran ne sakamakon ƙaruwar gargaɗin da ake samu a duniya game da yiwuwar samun yunwa da kuma rahotonnin ƙaruwar cutar tamowa a Najeriya.

    ''Mun ga irin illar da tashin farashin kayayyaki da tsadar rayuwa suka yi wa al'umma ta yadda da dama ba sa iya sayen abinci', in ji shi.

    A baya-bayan nan ne Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin sauko da farashin abinci domin ''sauƙaƙa talakawan ƙasar'', kamar yadda ya bayyana.

    Kullen Allah ta ce Najeriya ta samu koma baya ta fuskar samar da abinci sakamon ƙaruwar matsalar tsaro a wasu yankunan ƙasar da matsalar sauyin yanayi da wasu matalolin kamar ambaliya.

    Ƙungiyar ta kuma zargi wasu ƴankasuwa da ƙara rura matsalar tsadar abinci a ƙasar, ta hanyar sayen kayan abinci da gayya a lokacin da aka yi girbi tare da ɓoye shi da nufin in ya yi tsada su fito da shi domin cin ƙazamar riba.

    ''Mun yi imanin cewa saka hannun gwamnati wajen bayar da damar shigo da abinci cikin ƙasar, zai taimaka wajen karya farashin kayan abinc a kasuwannin ƙasar'', in ji sanarwar.

  2. Za a fara samar da allurar riga-kafin HIV

    Za a fara samar da sabon maganin riga-kafin kare mutum daga kamuwa da cutar HIV, a ƙasashe masu ƙaramin karfi, a kan farashi mai rahusa daga shekarar 2027.

    Maganin allura mai suna lenacapavi wanda a ƙasashen da suka ci gaba ake sayarwa da dubban daloli a duk shekara, zai koma dala 40 kacal a kowace shekara.

    Wannan sabuwar hanyar riga-kafin za ta bai wa miliyoyin mutane damar ci gaba da rayuwa da kuma kauce wa haɗarin kamuwa da cutar HIV.

    Za a riƙa samar da maganin mai rahusa a Indiya, sannan kuma za a watsa shi a duniya ta hannun gamayyar wasu ƙungiyoyin kiwon lafiya a ƙasashe guda 120.

  3. Shugaban Syria ya yi jawabi a taron MDD karon farko tun 1967

    Shugaban gwamnatin riƙon ƙwaryar Syria Ahmed al-Sharaa ya shaida wa babban taron Majalisar Dinkin Duniya cewa ƙasarsa ta sake ƙwato matsayinta a idon duniya.

    Ahmed al-Sharaa ne shugaban Syria na farko da ya yi jawabi a taron Majalisar Dinkin Duniya tun shekarar 1967.

    A watan Disamban da ya gabata ne, tsoron jagoran ƴantawaye ya jagoranci hamɓarar da gwamnatin Bashar al-Assad.

    Al Sharaa ya ce yaƙin basasa ya ɗaiɗaita Syria, amma ya alƙawarta gudanar da zaɓuka a ƙasar.

    Jawabin da ya yi a taron na New York ya ɗauki hankalin mahalarta taron a Amurka, ƙasar da a baya ta sanya tukwicin dala miliyan 10 ga wanda ya taimaka aka kama shi.

  4. An cimma yarjejeniyar samar wa ƙasashe riga-kafin HIV

    An cimma yarjejeniya da za ta bai wa ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi 120 damar samun sabuwar allurar riga-kafin kamuwa da cutar Sida a farashi mai rahusa.

    Allurar rigakafin mai suna Lena-capa-vir, wadda ake sayar da ita kan dubban daloli a ƙasashen da suka ci gaba a duk shekara, za ta koma dala 40 kacal daga shekarar 2027.

    Wakilin BBC ya ce wannan sabuwar hanyar rigakafin za ta baiwa miliyoyin mutane da damar ci gaba da rayuwa da kuma kaucewa haɗarin kamuwa da cutar HIV. Ana yin allurar sau biyu a shekara guda.

    Bincike ya nuna cewa allurar na da tasiri fiye da kashi 99 cikin 100 wajen kare mutane daga kamuwa da cutar, kuma ta kasance zaɓi mai sauƙi ga waɗanda ke da matsalar sha magungunan yau da kullum.

  5. Rasha ta yi tir da kalaman Trump kan yaƙin Ukraine

    Fadar gwamnatin Rasha ta Kremlin ta yi watsi da maganganun da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan yakin Ukraine, waɗanda suke nuna alamun ya sauya matsayarsa.

    Bayan ganawa da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a New York, Trump ya ce Ukraine na iya kwato dukkan yankunan da ta rasa, inda ya bayyana Rasha a matsayin kyanwar Lami.

    Ya kuma ce tattalin arzikin Rasha na cikin gagarumar matsala.

    Sai dai mai magana da yawun shugaban Rasha, Dmitry Peskov, ya ce Rasha na nan a kan matsayinta na zakanyar ƙasa, kuma tana cikin kwanciyar hankali ta fannin tattalin arziki.

    Peskov ya tabbatar wa manema labarai cewa babban kuskure ne a yadda cewa Ukraine za ta iya yin nasara wajen ƙarbe ikon yankunanta da ke hannun Rasha.

  6. Jirgi maras matuƙi ya kashe mutum 15 a El-Fasher na Sudan

    Rahotanni daga Sudan na cewa akalla mutum 15 ne suka mutu sakamakon wani harin jirgin yaki maras matuki da ya auku a wata kasuwa da ke birnin El-Fasher.

    Wani ma’aikacin lafiya a asibitin birnin ya ce wasu mutum 12 sun jikkata a harin. Masu rajin kare hakkin bil’adama a yankin sun zargi dakarun RSF da kai harin.

    El-Fasher shi ne birni na ƙarshe a yammacin Darfur da ke ƙarƙashin ikon sojojin gwamnati, anda ya shafe fiye da shekaru biyu suna gwabza yaƙi da dakarun RSF.

    Kawo yanzu, kimanin dubban mutane ne suka mutu a yaƙin, yayin da miliyoyi suka rasa muhallansu.

  7. Najeriya ta nemi izinin shirya gasar Commonwealth Games ta 2030

    Najeriya ta gabatar da buƙatar neman karɓar baƙuncin gasar wasannin tsalle-tsalle ta Commonwealth Games a 2030.

    Gasar da za a yi wa laƙabi da Abuja 2030, za ta zama karo na farko da za a gudanar da ita a nahiyar Afirka tun bayan fara ta kusan shekara 100 - idan Najeriya ta yi nasara.

    "Najeriya ta yunƙura a madadin nahiyar baki ɗaya bisa ƙwarin gwiwar cewa wasannin na 2030 za su buɗe sabon babi na damawa da kowa, da damarmaki, da kuma 'yan'uwantaka," a cewar wata sanarwa da gwamnatin Najeriya ta fitar a shafukan sada zumunta.

    "Ba Abuja kawai muke so a zo ba, muna so Afirka ta zama fagen da ƙasashen Commonwealth za su yi murnar cika shekara 100 tare da kuma ƙarfafa fatan shiga sabon ƙarni mai yalwa."

    Gasar ta Commonwealth Games ta ƙunshi wasannin daban-daban, wadda akan gudanar duk shekara huɗu tsakanin ƙasashe rainon Ingila.

  8. Za mu ɗauki mataki kan Sheikh Lawan Triumph bayan karɓar ƙorafi a rubuce - Gwamnan Kano

    Wasu mazauna birnin Kano a arewacin Najeriya sun yi zanga-zangar lumana game da zargin malamin addini Sheikh Lawan Abubakar Triumph da kausasa kalamai kan Annabi Muhammadu (SAW).

    Masu zanga-zangar sun dangana da farfajiyar gidan gwamnatin Kano, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tarɓe su tare da yi musu jawabi.

    A baya-bayan nan ne aka ga malamin a wani bidiyo yana musanta batun cewa haihuwar Annabi da kaciya, kamar yadda wasu litattafai suka ruwaito, ba karama ba ce saboda "ana iya haihuwar sauran mutane ma da kaciyar".

    A cewar malamin, karama na nufin "wani abin al'ajabi da Allah yake bai wa annabawa su kaɗai". Kazalika, malamin ya ce ruwayoyin ba su inganta ba.

    Gwamna Abba ya umarci masu ƙorafin da su kwantar da hankali, inda ya nemi su rubuto masa takardar koke a hukumance ta hannun ofishin sakataren gwamnati.

    "In Allah ya yarda za mu ɗauki matakin da bai saɓa wa Shari'a ba," in ji gwamnan.

    "Abin da nake so shi ne ku koma ku rubuto wa gwamna takarda, wadda ita ce za a yi amfani da ita daga nan har zuwa ƙolin ƙoli."

    Masu ƙorafin sun amince su kai wa gwamnan takardar da ya nema da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar gobe Alhamis.

  9. Labarai da dumi-dumi, Shugaban Malawi Lazarus Chakwera ya amsa shan kaye a zaɓen shugaban ƙasa

    Shugaban Malawi Lazarus Chakwera ya amince da shan kaye bayan sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a yau Laraba.

    Ɗantakarar adawa Arthur Peter Mutharika na jam'iyyar Democratic Progressive Party ne ya lashe zaɓen.

    "Sakamakon zaɓen ya nuna ƙarara cewa babban abokin adawata Farfesa Mutharika ya samu ƙuri'u mafiya yawa. Saboda haka, na kira Mutharika domin taya shi murna kan nasarar da ya samu," in ji shugaban cikin wani jawabi da ya yi 'yan mintuna da suka wuce.

    Ana sa ran hukumar zaɓe Malawi Electoral Commission za ta sanar da nasarar tasa.

  10. Labarai da dumi-dumi, Guguwa ta kashe mutum 17 a Taiwan

    Adadin mutanen da suka mutu sakamakon guguwa ta ɓalle wata madatsar ruwa a Taiwan sun ƙaru zuwa 17.

    Madatsar ruwan ta Matai'an Creek ta ɓalle ne sakamakon ruwan saman sama da Guguwar Ragasa ta haddasa, inda ta hankaɗo miliyoyin litar ruwa zuwa cikin gari.

    Wasu masana harkokin yanayin ƙasa sun bayyana yanayin a matsayin tsunami, inda aka ƙiyasta cewa ta hankaɗo kusan ruwa tan miliyan 15.4.

    Sakamakon haka, gadoji sun karairaye, sannan ruwan ya yi toroƙo har tsawon gini mai bene a wasu yankunan.

  11. 'Yan cirani za su jefa ƙasashen Yamma cikin mummunan hali - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ƙasashen Yamma za su shiga cikin "mummunan hali" idan har ba su dakatar da kwararar 'yan cirani ba.

    Ya ce buɗe iyakoki ya zama babban ƙalubale, sannan ya zargi Majalisar Dinkin Duniya (MDD) da taimaka wa kwarar da baƙin hauren ke yi zuwa ƙasashen Yamma.

    Kazalika, ya kuma yi watsi da batun hasashen sauyin yanayi da MDD ta yi, inda ya buƙaci a daina amfani da makamashi maras gurbata muhalli.

    Tun da farko babban sakatare na MDD, Antonio Guterres, ya ce duniya ta shiga wani zamani na ruɗani da rashin kwanciyar hankali mai saurin kawo wahalhalu marasa iyaka.

  12. Kashim Shettima zai yi wa taron MDD jawabi a yau

    Nan gaba a yau Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima zai gabatar da jawabin ƙasar a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) da ke gudana a birnin New York na Amurka.

    Ana sa rana Shettima zai gabatar da jawabin a madadin Shugaba Bola Tinubu a tsakanin ƙarfe 3:00 na rana zuwa 9:00 na dare agogon New York a taron wanda shi ne karon 80.

    Fadar shugaban Najeriya ba ta fayyace abin da Shettima zai tattauna a kai ba, amma akwai yiwuwar zai jaddada kiran a bai wa nahiyar Afirka kujerar dindindin a Kwamatin Tsaro na MDD kamar yadda ya yi a shekarar da ta gabata.

    Bayan haka mataimakin shugaban ƙasar zai gana da takwarorinsa na ƙasashen dunya, inda tun a jiya Talata ya tattauna da shugabar Namibia Nandi-Ndaitbia.

  13. Darajar naira ta ɗan ƙaru bayan CBN ya rage kuɗin ruwa

    Darajar naira ta ɗan ƙaru bayan sanar da matakin Babban Bankin Najeriya na rage yawan kuɗin ruwa da maki 50 zuwa kashi 27 cikin 100, kamar yadda rahoton Channels TV ya bayyana.

    Kazalika, shi ma farashin ɗanyen mai ya ɗan ƙaru zuwa dala 67.82 zuwa ƙarfe 5:00 na safiyar yau Laraba, inda ya ƙaru da santi 19 - ko kuma kashi 0.3 cikin 100 - kan kowace ganga ɗaya.

    An canzar da nairar kan N1,487.36 kan dala ɗaya ranar Talata a kasuwar hukuma.

    An rufe kasuwar canjin kuɗi ta jiya Talata nairar tana da ƙarin darajar kashi 0.08 idan aka kwatanta da 1,488.60 da aka canzar da ita kafin haka, kamar yadda bayanan CBN suka nuna.

  14. An kwashe 'yan Najeriya 145 da suka maƙale a Aljeriya

    Hukumar bayar d aagajin gaggawa ta Najeriya Nema ta karɓi 'yan Najeriya 145 da aka kwashe zuwa gida bayan sun maƙale a Aljeriya ranar Litinin.

    Hukumar National Emergency Management Agency ta ce mutanen sun sauka a filin jirgin sama na Legas da misalin ƙarfe 12:15 na rana a jirgin Air Algeria.

    Nema ta ce ƙungiyar kula da 'yan cirani ta International Organization for Migration (IOM) ce ta ɗauki nauyin kwaso mutanen bisa haɗin gwiwa da gwamnatin Najeriya.

    Mutanen sun haɗa da maza manya 132, da yara tara, da jarirai huɗu.

    A ranar Alhamis da ta gabata ma aka kwaso wasu 'yan Najeriya 148 zuwa gida bayan sun maƙale a Sudan, a cewar Nema.

  15. 'Yanfashin daji sun sace mutum takwas a jihar Kwara

    Wasu 'yanbindiga da ake zaton 'yanfashin daji ne sun kai mummunan hari a ƙaramar hukumar Patigi da ke jihar Kwara a tsakiyar Najeriya, inda suka kashe mace mai ciki da kuma sace wasu da dama ranar Talata.

    Rahoton jaridar Daily Trust ya ambato mazauna yankin na cewa maharan sun yi garkuwa da mutum takwas, bayan raunata wasu da dama.

    Wani ɗan sa-kai da jaridar ta tattauna da shi ya ce an kai hare-haren ne kwana ɗaya bayan dakarun tsaro sun fafata da 'yanbindigar lokacin da suka sace shanu masu yawa, inda aka kashe aƙalla huɗu daga cikin maharan.

    Shaidu sun ce maharan sun shafe awanni suna harbe-harbe kafin jami'an tsaro su isa wurin.

  16. Trump ya sauya matsaya kan yaƙinmu da Rasha - Zelensky

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce an samu gagarumin sauyi kan matsayar Donald Trump game da yaƙin kasarsa da Rasha bayan shugaban na Amurka ya ce Ukraine za ta iya kwato yankunanta da aka mamaye.

    Bayan wata ganawa da shugabannin biyu suka yi a kebe a New York, Mista Zelensky ya yi maraba da abin da ya kira ci gaba da aka samu game da matsayar shugaban yanzu.

    Wakilin BBC ya ce shugaban Ukraine din ya ce alakarsu da Trump yanzu ta inganta sosai fiye da a baya, sannan kuma ya tabbata Amurka za ta bai wa Ukraine duk wani goyon baya da taimakon da take buƙata nan gaba.

    Tun da farko Shugaba Trump ya bayyana Rasha a matsayin ƙasar da ke kallon kanta a matsayin wadda ta fi kowacce kasa karfin soji, alhali kuma abin ba haka yake ba.

  17. Maraba

    Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na ranar Laraba.

    Ku biyo mu domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.

    Umar Mikail ne ke tare da ku zuwa ƙarfe 4:00 bisa kulawar Haruna Kakangi.