Kullen Allah ta buƙaci Tinubu ya ci gaba da ɗaukar matakan rage farashin abinci

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Kullen Allah ta buƙaci shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ci gaba da ɗaukar matakan rage farashin kayan abinci domin wadata ƙasar da abinci da kuma magance tsadar rayuwa.
Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Hon. Khalil Mohd Bello ya fitar ya ce ƙungiyar ta yi kiran ne sakamakon ƙaruwar gargaɗin da ake samu a duniya game da yiwuwar samun yunwa da kuma rahotonnin ƙaruwar cutar tamowa a Najeriya.
''Mun ga irin illar da tashin farashin kayayyaki da tsadar rayuwa suka yi wa al'umma ta yadda da dama ba sa iya sayen abinci', in ji shi.
A baya-bayan nan ne Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin sauko da farashin abinci domin ''sauƙaƙa talakawan ƙasar'', kamar yadda ya bayyana.
Kullen Allah ta ce Najeriya ta samu koma baya ta fuskar samar da abinci sakamon ƙaruwar matsalar tsaro a wasu yankunan ƙasar da matsalar sauyin yanayi da wasu matalolin kamar ambaliya.
Ƙungiyar ta kuma zargi wasu ƴankasuwa da ƙara rura matsalar tsadar abinci a ƙasar, ta hanyar sayen kayan abinci da gayya a lokacin da aka yi girbi tare da ɓoye shi da nufin in ya yi tsada su fito da shi domin cin ƙazamar riba.
''Mun yi imanin cewa saka hannun gwamnati wajen bayar da damar shigo da abinci cikin ƙasar, zai taimaka wajen karya farashin kayan abinc a kasuwannin ƙasar'', in ji sanarwar.














