Rundunar ƴansandan Najeriya daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar ta tabbatar harin da Boko Haram ta kai a wata makaranta da ke ƙauyen Mussa a ƙaramar hukumar Askira-Uba ta jihar.
Rundunar ta ce maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 9 na safiyar Juma'a a makarantar, wadda ta firamare ce da sakandare.
Kakakin rundunar ta jihar Borno, Nahum Daso ya shaida wa BBC cewa suna zargin ƴan Boko Haram ko tsaginta na Iswap ne ke da alhakin kai hari. "Sun kai harin ne sai ɗaliban suka watse," in ji Daso.
Ya ce binciken farko-farko ya nuna cewa, "Ba mu da tabbacin ko an sace ɗalibai, amma mun samu labarin cewa akwai ɗaliban da suka tsere suka shiga cikin daji," in ji shi.
Har yanzu dai babu ƙungiyar da ta ɗauki alhakin kai hari.
Sai dai wani mazaunin yankin, Bukar Buba ya shaida wa BBC cewa maharan sun sace wasu ɗaliban daga makarantar, wadda ya bayyana da Central Primary School, inda ya ce ƴarsa na cikin waɗanda aka sace.
"Sun sace kusan ɗalibai 43, mafi yawansu masu shekara tsakanin 3 zuwa 6," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa amma an sace har da ɗalibai manya da suka kai shekara 15.
Buba ya ƙara da cewa mazauna yankin sun ga lokacin da maharan suke tafiya da ɗaliban ta saman dutse.
Jihar Borno ta kwashe sama da shekara 10 tana fama da rikice-rikicen Boko Haram, inda ita da tsagin Iswap suke kai hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hula da sauransu.