Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na yau Alhamis 6 ga watan Fabrairun 2025

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Haruna Kakangi, Abdullahi Bello Diginza, Aisha Aliyu Ja'afar da Ahmad Bawage

  1. Mu kwana lafiya

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Fatan kun ji daɗin kasancewa da mu daga sanyin safiya zuwa yanzu.

    Sai ku tara da mu gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.

  2. Interpol ta kama mutum 30 da ake zargi da aikata miyagun laifuka a Najeriya

    Interpol

    Asalin hoton, Interpol

    Hukumar ƴan sanda ta ƙasa da ƙasa Interpol ta ce wani gagarumin samamen da aka kai a Najeria ya kai ga kama mutane fiye da 30 waɗanda ake zargi da aikata manyan laifuka.

    Hukukomin tsaro 12 na Najeriya ne suka kai samamen.

    Laifukan sun haɗa da yaudarar mutane ta hanyar soyayya da zambar kuɗin Kirifto da kuma masu barazanar fitar da hotunan tsiraci idan ba a ba su kuɗi ba.

    Ƴan sandan sun ƙwace miliyoyin dala da miyagun ƙwayoyi da makamai da motoci da alburusai a samamen da suka kai a cikin kwanaki biyar.

    Akasarin waɗanda aka kama sun kasance masu shekara ƙasa da 35, abin da hukumar ta Interpol ta kira ƙaruwar da aka samu a yawan matasa masu aikata miyagun laifuka a cikin ƙasar.

  3. 'Yunkurin kwashe ƴan Gaza zai kawo cikas wajen tattauna batun tsagaita wuta'

    Masar ta yi gargaɗin cewa goyon bayan da Israila ta nuna wa shirin shugaba Trump na kwashe Falasɗinawa daga zirin Gaza, zai iya kawo cikas ga tattaunawar tsagaita wuta tare da tunzura ɓangarorin biyu su koma faɗa da juna.

    Ma'aikatar harkokin wajen Masar ta ba da misali da kalaman da suka fito daga bakin mambobin gwamnatin Israila.

    Ita ma ƙungiyar ƙasashen Larabawa ta nuna damuwa kan lamarin.

    Kakakin ƙungiyar Jamal Rushdie ya ce Falasɗinawa da Hamas za su yi tunanin cewa abin da ya kamata su yi yanzu shi ne su hau kujerar naki tare da yin watsi da shirin, kuma su cigaba da jajircewa.

    Tun farko, ministan tsaron Israila Isreal Katz ya umurci sojojin ƙasarsa da su ɓullo da wani tsari kan abin da ya kira ƴan Gaza da suka fice daga yankin domin raɗin kansu.

  4. Gobara ta lalata kayan abinci, ta hallaka dabbobi da dama a Kano

    Gobara

    Asalin hoton, TWITTER/@GBOYEGAKOSILE

    Wata gobara a ƙauyen Danzago da ke karamar hukumar Dambatta na jihar Kano, ta janyo asarar dabbobi 78 da suka haɗa da shanu da tumaki da kuma akuyoyi.

    Lamarin ya faru ne a wani gida da aka fi sani da Gidan Ado Yubai ranar Laraba, a cewar mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Yusif Abdullahi.

    Ya ce bayan samun kiran waya daga karamar hukumar Dambatta ne suka aika jami'ansu zuwa wurin, inda bayan isarsu suka samu gidan na Ado Yubai mai ɗakuna kusan 17 da kuma rumbun ajiya na ci da wuta.

    "Wutar ta ƙona shanu biyu da tumaki 36 da akuyoyi 17 da kaji 10 da kuma rumbunan ajiye abinci guda 19," in ji Saminu.

    Sai dai ya ce jami'ansu sun samu nasarar ceto tumaki guda biyu da kuma shanu huɗu, tare da wasu rumbunan adana abinci da sauran kayayyaki, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Abdullahi ya kuma ce ba a samu asarar rai ba, amma jami'insu ɗaya ya samu ƙuna a kafarsa yayin ƙoƙarin kashe wutar.

    Ya ƙara da cewa ana ci gaba da bincike kan musabbabin gobarar.

  5. Buƙatar Trump na sauya wa ƴan Gaza matsuguni maganar banza ce - Hamas

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    "Ba mu buƙatar wata ƙasa ta kula da Gaza, kuma ba mu amince a sauya wa wata al'umma wurin zama ba," a cewar mai magana da yawun Hamas Hazem Qassem.

    Mai magana da yawun Hamas ɗin ya ce "kin amincewa da buƙatar Trump kaɗai bai wadatar ba; haɗin kan Falasɗinawa yana da muhimmanci domin tinkarar batun ɗaiɗaita su", in ji shi bayan da Trump ya sanar da cewa Amurka na shirin karɓe Gaza da kuma sauya wa ƴan zirin matsuguni zuwa makwabtan ƙasashe.

    Qassem ya kuma yi kira ga ƙasashen Larabawa da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da su ɗauki mataki kan shirin Trump, da kuma kiran gudanar da taron gaggawa na ƙasashen Larabawa don tinkarar shirin Trump.

  6. An ɗaure ɗan Uganda a Birtaniya saboda zargin fyaɗe

    Pariyo

    Asalin hoton, South Wales Police

    Bayanan hoto, An samu Philip Pariyo da laifi a watan Disamban 2024

    An ɗaure wani ɗan wasan zari-ruga ɗan asalin Uganda wanda ke zaman mafaka a Wales shekara huɗu da rabi saboda zargin yi wa wata mata fyaɗe a birnin Cardiff.

    Kotun da ke Cardiff ta saurari yadda Philip Pariyo, mai shekara 32 ya zama abokin matar, kafin ya far mata a wani gida a watan Yunin 2021.

    Pariyo ya sha musanta yi wa matar fyaɗe, sai dai an same shi da aikata laifin a watan Disamban 2024.

    Ya wakilci ƙasarsa a gasar zari-ruga na wasannin Commonwealth a 2014 wanda aka yi a Glasgow, kafin a daina ganinsa.

  7. Shugaban Malawi ya umarci sojojin ƙasar su fice daga Kongo

    Kongo

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Ƴan tawayen M23 sun ƙwace iko da birnin Goma a makon da ya gabata

    Shugaban Malawi Lazarus Chakwera ya umarci sojojin ƙasar da su fara shirin ficewa daga aikinsu na wanzar da zaman lafiya da suke yi a gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo.

    Sojojin Malawi na cikin ɓangaren sojojin ƙungiyar ƙasashen kudancin Afrika (SAMIDRC) da aka tura Kongo domin taimakawa wajen daƙile ƙungiyoyi masu riƙe da makamai.

    Aƙalla masu wanzar da zaman lafiya 20, da suka kunshi ƴan Afrika ta Kudu 14 da ƴan Malawi uku aka kashe yayin da ƴan tawayen M23 suka karɓe iko da birnin Goma, babban birnin lardin Kivu a makon da ya gabata.

    Shugaba Chakwera ya faɗa a ranar Laraba cewa matakin da ya ɗauka na nufin "girmama batun ayyana tsagaita wuta da ɓangarori suka yi", duk da cewa ana ci gaba da faɗa.

    Wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin ɗin ƙasar a yammacin ranar Laraba, ya ce janyewar dakarun zai ba da damar tattauna batun samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

  8. Wani mutum sanye da kakin ƴan sanda ya harbe jami'in FRSC a Legas

    FRSC

    Asalin hoton, FRSC

    Wani mutun sanye da kayan sarki na ƴan sanda ya harbe tare da raunata wani jami'in hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) a jihar Legas.

    Lamarin ya faru ne yau Alhamis lokacin da jami'an FRSC reshen jihar Legas ke kan aiki na kaddamar da shirin kakkaɓe masu amfani da lambobin mota na bogi.

    Babu dai bayanai da ke nuna cewa ko mutumin jami'in ɗan sandan Najeriya ne.

    Haka ma, hukumomin ƴan sanda a jihar ta Legas ba su ce uffan game da lamarin zuwa yanzu, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

  9. 'Muna ci gaba da neman ɓarayin da suka sace kwai fiye da 100,000'

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Yan sanda a jihar Pennsylvania ta Amurka sun ce har yanzu suna neman ɓarayin da suka sace kwai fiye da 100,000 a bayan wata motar dakon kaya.

    A ranar Asabar da ta gabata ne aka sace Kwan da aka yi kiyansi darajarsa ta kai dala dubu arabain.

    Da alama waɗanda ake nema sun yi laakari da tashin gwauron zabon da farashin kwai ya yi a Amurka, shi yasa suka aikata aika aikar.

    Farashinsa ya karu da kashi sistin cikin dari a cikin shekara guda.

    Tashin farashin nada nasaba da annobar murar tsuntsaye da ake fama da ita a cikin kasar wadda ta tilastawa masu kiwo yanka kajinsu

  10. Tinubu ya buƙaci makarantu su ɗauki matakan kare ɗalibai

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, Bola Tinubu/Facebook

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci hukumomin kula da ɓangaren ilimi da su tabbatar da cewa makarantun gwamnati da kuma masu zaman kansu sun bi matakan kariya da aka amince da su.

    Haka na zuwa ne bayan da almajirai 17 suka mutu sanadiyyar wata gobara da ta tashi daddare a ranar Talata a wata makarantar allo da ke garin Ƙauran Namoda da ke jihar Zamfara.

    Yawancin almajiran sun kasance suna barci lokacin da gobarar tashi. Ta kuma raunata wasu bakwai waɗanda ake ci gaba da bai wa kulawa a asibiti.

    A cikin wata sanarwa, shugaba Tinubu ya jajantawa gwamnatin jihar Zamfara da kuma iyalai da suka rasa ƴaƴansu a cikin lamarin.

    Shugaban ya buƙaci dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu a faɗin ƙasar da su fifita kulawa da kuma tsaron ɗalibai a kowane lokaci.

    Ya kuma yi addu'ar samun lafiya ga waɗanda suka jikkata. Sai dai babu bayani karara da ke nuna cewa ko gwmanatin tarayyar ce ta ɗauki nauyin kula da almajiran da suka samu raunuka.

    A ɗaya gefen, ƴan sanda a jihar ta Zamfara sun ce suna gudanar da bincike domin gano abin da ya haddasa gobarar.

  11. Ƴakin Gaza: Isra'ila da Qatar za su cigaba da tattauna batun tsagaita wuta

    Tsagaita wuta

    Asalin hoton, Reuters

    A karshen wannan mako ne ake sa ran wata tawagar Israila za ta je ƙasar Qatar domin ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin Gaza, tare da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.

    Jamian Israilar sun ce tawagar ba za ta yi magana kan mataki na biyu na yarjejeniyar ba kamar yadda aka tsara, amma za su mayar da hankali kan ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar mataki na farko.

    Babu cikakken bayani game da lokacin da Hamas za ta tura tawagarta a tattaunawar da za su yi wadda ba ta ido da ido bace.

    Sai dai mazauna Gazan sun bayana rashin jin daɗinsu kan shawarar da shugaba Trump ya bayar na sauya musu matsuguni.

    "Ba za mu bar ƙasarmu ba, muna nan daram a Gaza duk da cewa an yi mata ƙawanya," in ji wani mutum.

    Iyalan Israilawan da aka yi garkuwa da su sun nuna damuwa kan kalaman baya-bayan nan na shugaba Trump kan Gaza zai iya saka mataki na gaba na yarjejeniyar cikin hadari.

  12. Tinubu ya sauke Farfesa Aisha Maikudi daga shugabancin Jami'ar Abuja

    Farfesa Aisha Maikuɗi

    Asalin hoton, Family

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sauke Farfesa Aisha Maikudi daga muƙaminta na shugabancin Jamai'ar Yakubu Gawon da ke Abuja da aka fi sani da Jami'ar Abuja.

    Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ranar Alhamis, ya ce shugaba Tinubu ya maye gurbinta da Farfesa Lar Patricia Manko da za ta riƙe muƙamin a matsayin riƙo na wata shida.

    To sai dai sanarwar ta ce sabuwar shugabar riƙon ba za ta iya neman muƙamin idan lokacin neman matsayin ya zo ba.

    A watan Yunin shekarar da ta gabata ne dai aka naɗa Farfesa Aisha Sani Maikudi a matsayin shugabar jami'ar bayan cikar wa'adin mulkin shugaban jami'ar na shida, Farfesa Abdulrasheed Na'Allah.

    Naɗin nata ya haifar da ce-ce-ku-ce a jami'ar, inda wasu ke cewa ba ta cancanta da matsayin ba.

    Haka kuma shugaba Tinubu ya naɗa Sanata Lanre Tejuoso, a matsayin sabon shugaban gudanarwar jami'ar, wato Pro Chancellor.

    Sanarwar ta kuma ce shugaban ƙasar ya sauke shugaban Jamai'ar Nsukka, Farfesa Polycarp Emeka Chigbu, inda ya maye gurbinsa da Farfesa Oguejiofu T. Ujam a matsayin shugaban riƙo na tsawon wata shida.

  13. Majalisar Wakilan Najeriya ta bayar da shawarar ƙirƙiro sabbin jihohi 31

    wakilai

    Asalin hoton, NASS

    Kwamitin sake nazarin kundin tsarin mulkin Najeriya na majalisar wakilan ƙasar ya bayar da shawarar ƙirƙiro ƙarin sabbin jihohi 31 a ƙasar.

    Mataimakin kakakin majalisar wakilan ƙasar, Hon.Benjamin Kalu ne ya bayyana haka lokacin da ya karanto wasiƙar kwamitin, a zaman majalisar da ya jagoranta yau Alhamis.

    Idan aka amince da buƙatar adadin jihohin Najeriya zai kai 67.

    Ga jerin sabbin jihohin da kwamitin ya bayar da shawarar ƙirƙira daga wasu jihohin ƙasar na yanzu:

    Arewa ta Tsakiya

    • Benue Ala daga jihar Benue.
    • Okun daga jihar Kogi.
    • Okura daga jihar Kogi.
    • Confluence daga jihar Kogi.
    • Apa-Agba daga jihar Benue.
    • Apa daga jihar Benue.
    • Abuja dada babban birnin ƙasar.

    Arewa maso Gabas

    • Amana daga jihar Adamawa.
    • Katagum daga jihar Bauchi.
    • Savannah daga jihar Borno.
    • Muri daga jihar Taraba.

    Arewa maso Yamma

    • New Kaduna da daga jihar Kaduna State.
    • Gurara daga jihar Kaduna.
    • Tiga daga jihar Kano.
    • Kainji daga jihar Kebbi.
    • Ghari daga jihar Kano.

    Kudu maso Gabas

    • Etiti daga duka jihohin yankin shida.
    • Adada daga jihar Enugu.
    • Urashi daga duka jihohin yankin shida.
    • Orlu daga jihar duka jihohin yankin shida.
    • Aba daga duka jihohin yankin.

    Kudu maso kudanci

    • Ogoja daga jihar Cross River.
    • Warri daga jihar Delta.
    • Bori daga jihar Rivers.
    • Obolo daga jihohin Rivers da Akwa Ibom.

    Kudu maso Yamma

    • Toru-ebe daga jihohin Delta da Edo da kuma Ondo.
    • Ibadan daga jihar Oyo.
    • Lagoon daga jihar Lagos.
    • Ijebu daga jihar Ogun.
    • Oke-Ogun daga jihohin Ogun da Oyo da kuma Osun
    • Ife-Ijesha daga jihohin Ogun Oyo da kuma Osun.
  14. Babu buƙatar tura sojojin Amurka Zirin Gaza bayan ficewar Falasɗinawa - Trump

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ba sai an buƙaci tura dakarun Amurka ba, cikin shawarar da ya bayar na karɓe iko da yankin Zirin Gaza bayan fitar da Falasɗinawa fiye da miliyan biyu daga yankin.

    Cikin wani sabon saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, shugaban ya ce Isra'ila za ta kula da yankin a madadin Amurka, idan yaƙin ya ƙare.

    Bayan shan suka da shawarar ke sha a faɗin duniya, sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya dage cewa fitar da Falasɗinawa zai kasance na wucin-gadi kawai, kuma ba an yi hakan ba ne domin ''cutar da su''.

  15. Koriya ta Kudu za ta sanya kyamarorin gano tsuntsaye a filayen jiragen sama

    tsuntsaye

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin Koriya ta Kudu sun bayar da umarnin sanya kyamarorin gano tsuntsaye a filayen jiragen saman ƙasar, bayan hatsarin jirgin da tsuntsaye suka haddasa ya kashe mutum 79 a watan Disamban da ya gabata.

    Har yanzu ana ci gaba da bincike game da hatsarin na jirgin kamfanin Jeju Air, wanda da farko direban jirgin ya bayar da rahoton karo da tsuntsu kafin faɗuwar jirgin.

    Haka kuma za a girke na'urorin hana ƙananan halittu kusantar filayen jiragen sama a faɗin ƙasar.

    Jami'ai a ƙasar sun ce za su tabbatar an kai wuraren da ke jan hakalin tsuntsaye, kamar bola ko wajen zuba shara nesa da filayen jiragen sama, domin kauce wa hatsari.

  16. MDD ta yi gargaɗin samun mummunan bala'i a jihohin Sudan biyu

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa jihohi biyu a yankin kudancin Sudan na dab da faɗawa mummunan bala'i bayan da sabon rikici ya ɓarke a cikinsu.

    A makon da ya gabata ne faɗa ya ɓarke a jihohin Kordofan da Kudu da Blue Nile, tsakanin sojojin gwamnati da mayaƙan SPLM da ba sa biyayya ga kowa.

    Majalisar Dinkin Duniyar ta ce mutum 80 ne suka mutu a babban birnin jihar Kordofan, inda ake tsare da fararen hula ake amfani da su a matsayin garkuwa.

    An toshe hanyoyin isar da kayan agaji ga ɗimbin mutanen da ke cikin tsananin buƙatar tallafi a cewar Majalisar Dinkin Duniyar.

    An dai kwashe fiye da shekara biyu ana yaƙi a ƙasar Sudan tsakanin sojojin gwamnati da dakarun RSF, lamarin da ya jefa miliyoyin mutane cikin tsananin yunwa da tagayyara.

  17. Ƴan bindiga sun sace tsohon shugaban NYSC na Najeriya

    'yanbindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu ƴanbindiga ɗauke da makamai sun sace tsohon shugaban Hukumar yi wa Ƙasa Hidima ta Najeriya, NYSC, Manjo Janar Mahrazu Tsiga, mai ritaya.

    Kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida na jihar, Dakta Nasiru Mu'azu ya tabbatar wa BBC cewa an sace Manjo Janar Tsiga a garin Tsiga da ke yankin ƙaramar hukumar Bakori, ranar Laraba da daddare.

    ''An sace shi ne tare da wasu mazauna garin 13 ciki har da mata biyu, a lokacin da maharan suka auka wa garin, ko da yake daga baya mutum huɗu sun kuɓuta'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

    Duk da cewa ƙaramar hukumar Bakori na fama da matsalar 'yanbindiga, amma garin Tsiga bai saba fuskantar irin wannan matsala ba.

    To amma kwamishinan tsaron ya ce a baya-bayan nan sau uku masu garkuwa da mutane na shiga garin tare da sace mutane.

    Kwamishinan tsaron ya kuma yi zargin cewa masu tsegunta wa 'yanbindiga bayanai ne suka tsegunta musu shigar tsohon Janar ɗin zuwa garin ''saboda a ranar Laraba da rana ne ya shiga garin, kuma da daddare suka je suka ɗauke shi''.

    ''Daga bayanan da muka samu tsohon janar ɗin bai je garin da rakiyar jami'an tsaro ba, ya je ne da direbansa kawai'', a cewar kwamishinan.

    Ya kuma ce gwamnati da jami'an tsaro na ƙoƙari domin tabbatar da ceto mutanen da 'yanbindigar suka sace.

  18. 'Za mu tabbatar ba a cutar da ƴan ƙasarmu da aka kora daga Amurka ba'

    Narendra Modi

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

    Ma'aikatar harkokin wajen Indiya ta ce gwamnatin ƙasar na aiki da Amurka domin tabbatar da cewa ba a cutar da 'yan ƙasar da aka kora daga Amurka ba idan aka mayar da su gida.

    Subrahmanyam Jaishankar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga majalisar dokokin ƙasar, kwana ɗaya bayan mayar da ɗaruruwan Indiyawa da aka zarga da shiga Amurka ba bisa ƙa'ida ba.

    Mista Jaishankar ya ce hukumomin Amurka sun sanar da gwamnatin Indiya cewa mata da ƙananan yaran da ke cikin mutanen ba a cutar da su ba.

    An yi ƙiyasin cewa akwai dubban Indiyawa da ke zaune a Amurka ba tare da cikakkun takardun izini ba, kuma Amurka na shirin mayar da su gida.

  19. 'Yantawayen M23 na gangami a birnin Goma

    Goma

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yantawayen DR Congo da ke samun goyon bayan ƙasar Rwanda, na gudanar da gangami a Goma, karon farkon tun bayan ƙwace birnin a makon da ya gabata.

    Dandazon mutane ne suka toshe manyan tituna a kusa da babban filin wasa na Unity da ke birnin, inda ake sa ran shugaban 'yantawayen, Corneille Nangaa, zai bayyana.

    Akwai rahotonnin samun harbe-harbe a yankin, yayin da mutane ke ci gaba da tserewa daga birnin.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutum 3,000 ne ake sa ran an kashe a lokacin ƙwace Goma.

    'Yantawayen sun kuma ƙwace birnin Nyabibwe mai arzikin ma'adanai, duk kuwa da iƙirarin tsagaita wuta.

    Tuni dai kotun sojin DR Congo ta bayar da sammacin kama Corneille Nangaa saboda zargin aikata laifukan yaƙi da cin amanar ƙasa.

  20. An samu gawar ɗan majalisar Anambra da aka yi garkuwa da shi

    Justice Azuka

    Asalin hoton, Justice Azuka/others

    An tsinci gawar ɗan majalisar jihar Anambra, Justice Azuka mai wakiltar ƙaramar hukumar Onitsha ta Arewa, gunduma ta farko.

    Gidan talbijin na Channels ya ruwaito cewa haɗin gwiwar jami'asn tsaron ƙasar ne suka gano gawar a gadar 2nd Niger Bridge.

    A watan Disamban da ya gabata ne aka sace ɗan majalisar a birnin Onitsha.

    Bayan shafe makonni ana bincike jami'an tsaro daga Abuja, suka kama wasu mutane da ake zargi da sace ɗan majalisar, inda suka kai jami'an har inda suka jefar da gawar Mista Azuka.

    Wannan shi ne karo na biyu da ake sace tare da kashe wani ɗan majalisar jihar ta Anambra a shekarun baya-bayan nan.

    A shekarar 2022 ma an sace wani ɗan majalisa mai suna Okey Okoye, inda daga baya kuma aka kashe shi a wani yanki na jihar.