Shirin Trump na karɓe iko da Gaza ba abu ne mai yiwuwa ba amma yana da tasiri - Sharhi

Asalin hoton, Reuters
Shirin da Donald Trump ya bayyana na karɓe iko da zirin Gaza ba abu ne mai yiwuwa ba. Shirin na buƙatar haɗin kan ƙasashen Larabawa waɗanda su kuma sun riga sun yi watsi da shirin.
Ƙasashen da Trump ke neman son mayar da al'ummar Falasɗinawa sun haɗa da goyon bayansu sun haɗa da Jordan da Masar da kuma Saudiyya wadda ake sa ran za ta goyi bayan ƙudirin.
Ko da ƙawayen Amurka da Isra'ila na yammaci ba su goyi bayan ƙudirin ba.
Duk da cewa wasu Falasɗinawa ka iya amincewa su fita daga zirin, To amma ko da miliyan ɗaya sun fice to akwai ragowar miliyan ɗaya da rabi da za su ci gaba da kasancewa a Gaza.
Kenan bisa hasashe sai dai Amurka ta yi amfani da ƙarfin tuwo ta fitar da su wani abu da ba zai samu karɓuwa ba hatta a cikin Amurkar tun bayan mamayar da Amurkar ta yi a Iraƙi a 2003.
Wannan zai kawo ƙarshen duk wani shirin da aka daɗe ana yi wajen ganin an samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu - wato burin kawo ƙarshen rikicin da aka shafe ƙarni guda ana gwabzawa ta hanyar kafa ƙasar Falasɗinawa mai ƴanci tare da ƙasar Isra'ila.
Gwamnatin Netanyahu dai ba ta goyon bayan kafa ƙasar Falasɗinawa kuma bayan kwashe dogon lokaci ana gaza cimma kafa 'ƙasashen biyu ga al'ummar guda biyu' ta zama tamkar tatsuniya.
Sai dai kuma kafa ƙasashen biyu masu cin gashin kansu shi ne babban burin Amurka a tsare-tsarenta na ƙasa da ƙasa tun farkon shekarun 1990s.
Haka kuma shirin na Trump zai karya dokokin ƙasa da ƙasa, irin waɗanda Amurkar ke zargin ƙasar Rasha da yi a Ukraine da wanda take zargin China da yi a Taiwan.
Me haka ke nufi ga Gabas ta Tsakiya?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Me ya sa aka nuna damuwa kan hakan idan dai ba an san cewa abin na daf da kasancewa lokacin da Trump yake sanarwa yayin da Netanyahu ke kallon sa cike da annashuwa?
Amsar ita ce kalaman na Donald Trump duk da cewa sabbi ne amma za su yi tasiri.
Irin yamutsa hazon da kalaman na Trump suka yi na ɗan wani lokaci ka iya gurgunta yarjejeniyar tsagaita wutar da ke tangal-tangal. Wani babba a ƙasashen Larabawa ya shaida min cewa kalaman ka iya "yi wa yarjejeniyar kisan mummuƙe".
Da ma dai rashin tarbin yadda shugabancin Gaza zai kasance a gaba ta kasance wata siɗira da ta zama matsala ga yarjejeniyar.
Yanzu Trump ya ƙara wata matsalar kuma ko da shirin nasa bai kasance ba to ta bar babban tabo a zukatan Falasɗinawa da Isra'ila.
Shirin ka iya haifar da wasu mafarke-mafarke da tsare-tsaren Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi da suka amannar cewa dukkanin yankin wato tsakanin bahar-rum da kogin Jordan da wataƙila ma abin da ya wuce nan ƙasar Yahudawa ce da ubangiji ya mallaka musu.
Shugabanninsu na cikin gwamnatin Benjamin Netanyahu kuma su ne suka rufa masa asiri a gwamnatance, al'amairn ya sa su farin ciki. Suna son yaƙin Gaza ya ci gaba inda suke da burin nan gaba za su fitar da Falasɗinawa daga Gaza sannan su maye gurbinsu da Yahudawa.
Ministan kuɗin Isra'ila, Bezalel Smotrich ya ce Trump ya samar da amsar da suke neman dangane da makomar Gaza a nan gaba tun bayan ranar 7 ga watan Okotoban 2023.
Yanzu dai ƴan ƙungiyar Hamas da sauran mayaƙan Falasɗinawa ka iya bai wa Donald Trump amsa ta hanyar nuna ƙarfin da suke da shi kan Isra'ila.
Fiye da Falasɗnawa 700,000 kodai sun bar zirin Gaza don gudun yaƙi ko kuma an tilasta su barin zirin sakamakon ayyukan dakarun Isra'ila. Sai ba a bar wasunsu su sake komawa gidajen nasu ba kuma Isra'ila ta yi dokoki da ke ba ta damar ƙwace kadarorinsu.
Tsoron yanzu da ake da shi shi ne irin wannan ka iya ci gaba da faruwa.
Falasɗinawa dai sun yi imanin cewa Isra'ila na amfani da yaƙi kan Hamas domin ruguza Gaza da fitar da al'ummar daga ƙasarsu.
Ɗaya daga cikin zarge-zargensu shi ne Isra'ila na aikata laifukan ƙare dangi - kuma yanzu za su iya imani da cewa Trump na goya wa Isra'ilar baya.
Me ya sa Trump ya furta kalaman?
Saboda Trump ya faɗi abu ba lallai ya kasance ba.
Akwai yiwuwar Donald Trump na haddasa ruɗani ne a daidai lokacin da yake aiki a kan wani shirin na daban.
A daidai lokacin da duniya ke ci gaba da mayar da martani dangane da batun karɓe iko da Gaza, Donald Trump ya ƙara wallafawa a shafinsa na Truth Social cewa yana sha'awar komawa "tattaunawa kan makamashin nukiliya da Iran."
Gwamnatin Iran dai ta musanta cewa tana son cimma makamin nukiliya, sai dai ana tafka muhawara a Tehran dangane da o akwai buƙatar samar da makamin na nukiliya kan barazanar da suke fuskanta domin kare kansu.
Firaiministan Isra'ila ya kwashe shekaru yana neman Amurka da taimakon Isra'ila su ruguza cibiyoyin makamashin na nukiliya na Iran. Cimma yarjejeniya da Iran ba ya cikin tsarin Trump.
A karon mulkinsa na farko, Netanyahu ya yi ta abubuwan da har suka ja hankalin Trump ya fice daga yarjejeniyar da Iran wadda tsohon shugaban Amurka, Barrack Obama ya cimma da Iran ɗin.
Idan Trump na son faranatawa Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi a daidai lokacin da yake son burge Iraniyawa, to ya yi nasara.
To sai dai kuma ya buɗe ƙofar rashin tabbas dangane da makomar yanki mai fama da rikici a duniya.











