Ƙungiyar kare haƙƙin biladama ta Human Rights Watch ta ruwaito cewa aƙalla ƴan Ethiopia 65 ke fuskantar barazanar a yanke musu hukuncin kisa a Saudiyya saboda laifuka masu alaƙa da ƙwayoyi.
Ƙungiyar ta ce hukumomin Saudiyya sun aiwatar da hukuncin kisa kan mutum 3 a ranar 21 ga watan Afrilun 2026, amma daga bisani ta dakatar da aiwatar da hukuncin kan sauran ƴan Ethiopian.
'' Yunƙurin da Saudiyya ke yi na aiwatar da hukuncin kisa kan baƙi daga ƙasashen waje saboda ƙananan laifuka, bayan ta hana a gudanar da bincike yadda ya kamata na nuna tsantsar rashin mutunta rayukansu da ƴancinsu,'' a cewar Nadia Hardman, babbar mai bincike kan ƴan gudun hijira a ƙungiyar Human Rights Watch.
'' Ya kamata abokan hulɗar Saudiyya su shiga tsakani kafin lokaci ya ƙure.'' in ji ta.
Ƙungiyar ta ce ba a shaidawa mutanen laifukan da ake tuhumarsu ba, kuma a cewarsu jami'an tsaro sun yi ta lakaɗa musu duka kafin daga bisani aka tilasta musu sanya hannu kan takardun da basu san menene a cikinsu ba.
Ana tsare da mutanen ne na tsawon fiye da shekaru biyu ba tare da basu damar ɗaukaka ƙara ba.
Ƙungiyar Human Rights Watch ta yi kira ga hukumomin Saudiyya su gaggauta soke batun hukuncin kisa kan ƴan Ethiopia, tare da sake nazari kan dukkanin ƙararrakin da aka shigar kansu bisa dokokin ƙasa da ƙasa da na Majalisar ɗinkin duniya.