Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku irin wainar da ake toyawa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi a kan Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya na ranar 29/04/2026

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammad da Aisha Aliyu Jaafar

  1. Farashin mai ya kai dala 117 duk ganga

    ,

    Asalin hoton, PA

    Faranshin mai ya yi tashin gwauron zabi bayan labarin tattaunawar Donald Trump da shugabannin kamfanonin mai kan yadda za a tsawaita kulle tashar ruwan Iran da jiragen dakon mai na tsawon watanni.

    Farashin mai nau'in Brent ya aro da kashi biyar cikin 100, inda ya koma dala 117 duk ganga ɗaya.

    Iran na na kawo tsaiko kan ababan hawa a mashigar Hormuz, wata hanya mai muhimmanci da kshi ɗaya cikin biyar na man duniya ke bi.

    Har yanzu mashigar rufe take duk da cimma yarjejeniyar da aka yi tsakanin Amurka da Isra'ila da kuma Iran.

  2. Kotun ƙolin Najeriya za ta yanke hukuncin ƙarshe kan ADC ranar Alhamis

    .

    Asalin hoton, APEX COURT

    Kotun ƙolin Najeriya ta sanya ranar Alhamis 30 ga watan Afirilu, domin yanke hukunci kan shari'ar shugabancin da ta mamaye jam'iyyar adawa ta ADC.

    Kotun ƙolin ta ɗage sauraron ƙarar tun da fari abin da ya sa jam'iyyar adawar ta shigar da ƙarar alƙalin alƙalin kasar kan shari'ar tana cewa tana bahu lokacin da za a yi ta ɗaga sauraron shari'ar ta ta.

    A yau Laraba ne kuma, kotun ta sanar da cewa za ta yanke hukuncin ne a gobe Alhamis da misalin ƙarfe biyun rana.

    David Mark, wanda yake shugabantar ɓangare guda na ADC, ya ƙalubalanci hukuncin 12 ga watan Maris na kotun ɗaukaka ƙara, wadda ta umarci a koma yadda tsarin jam'iyyar yake gabanin kai ƙarar.

    A ƙarar da ya ɗaukaka, tsohon shugaban majalisar dattijan ya ce kotun ta wuce iyakarta kan hukuncin, ya kuma dage kan cewa wannan rikicin na cikin gida ne, wanda doka ba ta baiwa kotun hurumin shiga ba.

    Wasu mambar jam'iyyar ne suka shigar da ƙarar, wanda wani matashi Nafi'u Gombe da ya yi ikirarin shugabancin jam'iyyar yake jagoranta.

    Cikin waɗanda aka shigar ƙasarar akwai Sakatern jam'iyyar na ƙasa Rauf Aregbesola, da Hukumar Zaɓe ta ƙasa INEC da tsohon shugaban jam'iyyar Ralp Nwosu.

    Mark a cikin buƙatarsa na son kotu ta daina amincewa da duk wani tsagen jam'iyyar indai ba wanda yake jagoranta ba, har sai hukuncin ƙarshe da aka yanke na gobe Alhamis.

    Sai dai Nafi'u da abokan da suke tare sun roki kotun ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da Mark ya yi, suna cewa hukuntun kotun baya shi ne daidai.

    Hankalin 'yan Najeriya dai na kan wannan shari'a, musamman a wannan lokacin da ake yi wa ADC kallon babbar jam'iyyar adawa a kasar, wadda ta haɗa manyan jiga-jigan 'yan siyasar da suka yi takara da shugaba Bola Tinubu a 2023.

  3. Yaƙin Iran ya laƙume mana dala biliyan 25 ya zuwa yanzu - Pentagon

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren tsaron A,urka Pete Hegsett da Janarl Dan Kaine shugaban haɗakar tsaro ta Amurka sun kare matakin Doanld Trump na buƙatar ƙara yawan kasafin kuɗi da dala biliyan 1.5.

    Yayin sauraren da aka yi a wata tattaunawa Adam Smith wanda shi ne babban mai bibiya daga Democrat a kwamitin ya tambayi nawa yaƙin Iran ya ci wa Amurka ya zuwa yanzu kuma ko majalisa za ta samu cikakken jerin abubuwan da aka kashe daga hukumar tsaro ta Amurkan Pentagon.

    "Kimanin dala biliyan 25, da kuma wannan gagarumin kaso da kayan yaƙin suka laƙume," in ji Jules Hrst, mai sanya idanu kan harkokin kumar tsaro wanda shi ma ya halarci zaman.

    Na yi farin ciki da aka amsa min wannan tambaya, saboda muma ana ta tambayarmu hakan tun da daɗewa, kuma babu wanda yake ba mu wannan masa." in ji Mr. Smith.

  4. Yadda ficewar UAE daga Opec za ta janyo babban giɓi

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani babban al'amari ne cewa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta sanar da cewa za ta fice daga ƙungiyar Ƙasashe Masu Arzikin man Fetur ta Opec baga-tatan.

    UAE ta kasance mamba a ƙungiyar tun kafin ta zama ƙasa a shekara ta 1971.

    Opec dai ta ƙunshi yawancin ƙasashe daga yankin Gulf masu fitar da man fetur, waɗanda suka shafe tsawon shekaru suna daidaita farashin man fetur ta hanyar ƙara wa ko kuma rage samar da shi. Ta taka rawa sosai a rikicin mai da aka shiga a shekarun 1970.

    Yayin da Saudiyya ta mamaye ƙungiyar wajen samar da mai, UAE ita ce ta biyu wajen samar da mai. Hakan na nufin cewa ƙasar na da muhimmanci a ƙungiyar, saboda tana da ƙarfin iya ƙara samar da mai don rage farashi.

  5. Rikicin Amurka da Iran ka iya jefa mutum miliyan 30 cikin talauci - MDD

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban shirin ci gaban na Majalisar Ɗinkin Duniya Alexander de Crowe ya yi gargaɗin cewa ya ƙin Amurka da Isra'ila da Iran wanda ya ja tashin farashin makamashi da takin zamani ka iya tura mutane sama da miliyan 30 cikin talauci.

    Wannan mayar da hannun agogo baya ne, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a gefen taron ƙungiyar ƙasashe bakwai masu ƙarfin tattalin arziƙi a Paris.

    Ya ƙara da cewa, "Yana ɗaukar gwamman shekaru domin gina al'umma da tabbataccen cigaban tattalin arziƙi, amma kuma makwannin yake ɗauka a yanayin yaƙi a rusa wannan ci gaba".

    De Crowe ya ce: "Mun yi wani bincike mako shida bayan fara wannan yaƙi, muka yi ƙiyasin ko da ya yaƙin zai ƙare a wannan lokaci to mutum miliyan 32 za su faɗa cikin talauci a ƙasashe 160."

    Waƙi ya ja an rufe mashigar Hormuz inda nan ne daya cikin biyar na man duniya da gas ke wucewa.

  6. Lebanon ta zargi Isra'ila da rushe gine-ginen tahirinta

    Isra'ila ta zargi Lebanon da laifukan yaƙi, bayan harin da ta kai kan wani gidan tarihi da ya fi shekara 100.

    Harin ya faru a ne a garin Nabatieh al-Fawqa da ke Kudancin Lebanon, kamar yadda kamfanin yaɗa labaran ƙasar ya bayyana.

    Kamfanin ya ce "Isra'ila ta sake aikata wani laifin yaƙin, inda ta harin ɗaya daga cikin wuraren tahirin da ke Nabatieh al-Fawqa, wanda ya haura shekara 100.

    "Harin wanda aka kai da jirgin yaƙi ya mayar da wurin tamkar kufai, duk da cewa waje ne da aka yi shi da duwatsun da kake iya ganowa daga nesa," in ji Kamfanin yaɗa labaran.

  7. Lokaci na ƙurewa majalisar Amurka kan yaƙin Iran

    W

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka da Iran na duba yiwuwar rashin tabbaas kan yarjejeniyar tsagaita wuta, amma fadar White House ta jaddada cewa za ta ƙara komawa yaƙi har sai Tehran ta amince da sharuɗan da Amurka ta gindaya mata, ciki har da haƙura da shirinta na nukiliya.

    Duk da haka, damar komawa yaƙin zai iya rikita halin da ake ciki da zai ci karo da shawarar ƙarfin yaƙi, wata doka ta 1973 da ya yiakancewa shugaban ƙasa ikon amfani da soji.

    An ba da wa'adin kwana 60 ga shugaban ƙasar domin tabbatar da sojin Amurka sun shiga faɗan ko da babu sahalewar majalisa.

    Yanzu dai za a jira a ga matakin da Fadar White House za ta ɗauka gabanin wa'adin, wanda zai ƙare 1 ga watan Mayu.

    Ƙuri'ar da za a yi za ta dagulawa gwamnatin Trump lamuranta.

    'Yan jam'iyya Republican sune ke da rinjaye a Majalisar wakilan ƙasar da ta dattijai, yayin da ake sa ran waƙin sai gwada ƙarfin goyon bayan da ake da shi a duka ɓangarori biyun, wanda hakan ya sa ba za a iya hasashen kuri'un ba.

  8. Ƴan sanda sun kama mutumin da ake zargi da kai harin wuƙa kan wasu Yahudawa a Landan

    yan sanda da wasu Yahudawa a wurin da aka kai hari

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Ƴan sanda sun kama wani mutum da ake zargi da yunƙurin yin kisa, bayan an kai harin wuƙa kan wasu yahudawa biyu a yankin Golders Green da ke arewacin Landan.

    Mutanen da aka kai wa hari na samun sauƙi a asibiti.

    Wata ƙungiyar tsaro ta alummar Yahudawa ta ce ta kama tare da tsare wani mutum da ke gudu kan wani titi yana ƙoƙarin hai wa yahudawa hari da wuƙa.

    Daga bisani sai ƴan sanda suka kama mutumin da ake zargi.

    A yanzu ƴan sanda sashen yaƙi da ta'addanci ne ke jagorantar gudanar da binciken.

    Suna ƙoƙarin gano tarihin mutumin, da asalinsa da kuma ko shi kaɗai ya kitsa harin.

    Wannan ne hari na baya bayan nan kan jerin munanan hare haren da ake kai wa alummar Yauhudawa a Birtaniya.

  9. Rasha za ta rage girman faretin sojinta na shekara-shekara saboda fargabar hari daga Ukraine

    sojojin Rasha na fareti

    Asalin hoton, Reuters

    Rasha ta sanar da cewa za ta rage girman faretin sojinta na shekara-shekara da ake yi a birnin Moscow, inda za a rage yawan sojoji, kana ba za a yi bajakolin tankuna yaƙi ko makamai masu linzami ba.

    Tana gudanar da wannan biki ne domin tunawa da nasarar da ta samu a Yaƙin Duniya na Biyu, amma a ‘yan shekarun nan Shugaba Vladimir Putin ya riƙa amfani da shi wajen nuna ƙarfin sojojin kasar.

    A cewar wakilin BBC, jami'an ma'aikatar tsaron ƙasar na fargabar Ukraine za ta iya kawowa bukin faretin sojin hari ta hanyar amfani da jirage mara matuƙi.

    Shi ma mai magana da yawun fadar Kremlin, Dmitry Peskov, ya ce ba za a haɗa da manyan makamai a faretin bana ba, domin rage abin da ya kira barazanar hare-haren ta’addanci daga Ukraine.

  10. Yadda wani ɗansanda ya harbe wani matashi a Najeriya

    ..

    Asalin hoton, NIGERIA POLICE

    Hankalin ƴan Najeriya musamman matasa idan ya yi dubu ya tashi sakamakon ganin wani bidiyo da ke waɗari a shafukan soshiyal midiya inda ya nuna yadda wani matashi ke faman roƙon jami'an ƴansanda amma duk da haka suka harbe shi.

    Bidiyon wanda sashen Hausa na BBC Pidgin ya gani ya nuna yadda wanda ake zargin mai suna Mene Ogidi yake zaune a ƙasa kusa da motar ƴansanda, inda suka ɗaure hannayensa da ƙafafunsa.

    Ƴansanda sun ce al'amarin ya faru ne ranar Lahadi ta ƙarshen mako.

    A bidiyon, matashin wanda ke zaune a ƙasa yana roƙon dansandan cewa shi ba shi da masaniyar abun da ake tuhumar sa da shi inda ya ce zai nuna musu mutumin da ya aiko shi domin ya karɓi kaya.

  11. Ukraine ta ce za ta ci gaba da tsananta hare hare kan Rasha

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaba Zelensky ya ce Ukraine za ta ci gaba da tsananta hare haren da take kai wa cikin Rasha da kuma ƙara nisan hare haren.

    Sojojin Ukraine sun ce a cikin dare, sun yi nasarar kai hari kan wani bututun mai a birnin Perm, wanda ke da nisan kilomita 100 daga iyakar ƙasar.

    Kalaman mista Zelensky na zuwa ne a yayin da gobara ke ci gaba da ci a matatar man Rasha da jirage marasa matuƙan Ukraine suka kai wa hari a tashar jirgin ruwa na Tuapse.

  12. Ana gudanar da zanga-zangar ƙin baƙin hauren da ke zaune a Afirka ta kudu

    masu zanga zanga a Afrika ta kudu

    Asalin hoton, BBC / Thuthuka Zondi

    Ana gudanar da zanga-zangar ƙin baƙin haure da ke zaune a Afirka ta kudu ba bisa ƙa’ida ba a birnin Johannesburg.

    Daruruwan masu zanga-zangar sun taru suna rera waƙoƙi, yayin da suke tattaki ta tsakiyar birnin zuwa ofisoshin gwamnati.

    Zangar-zangar, wanda wata ƙungiyar masu adawa da ƴan ci rani ta shirya, na cikin wani gagarumin kamfe da ke kiran a tsaurara matakai kan ƴan kasashen waje marasa takardun zama.

    Ana kara nuna damuwa kan rahotannin ƙaruwar hare-haren kyamar baƙi da ake kai wa kan ‘yan kasashen waje.

  13. Tinubu ya bai wa sabbin jakadun Najeriya kyautar filaye a Abuja

    Wiki da wasu sabbin jakadun Najeriya

    Asalin hoton, Daniel Achiniru

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince tare da bayar da umurnin bai wa sabbin jakadun da ya naɗa filaye a babban birnin ƙasar Abuja.

    Ministan babban birnin ƙasar Barr Nyesom Wike ne ya sanar da umurnin shugaban ƙasar a yau Laraba, a lokacin wata ziyarar aiki da sabbin jakadun suka kai mishi, bisa jagorancin babban sakataren ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Ambasada Dunoma Umar Ahmed.

    Wike ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne da nufin samar wa jakadun wuraren zama na din din din a babban birnin ƙasar, tare da tabbatar da cewa suna da masauki a lokacin da suka dawo Najeriya domin bai wa shugaban ƙasar bayanai game da aikinsu da kuma bayan sun kammala aiki.

    Ministan Abujan ya kuma buƙace su da su kasance ido da kuma kunnen Najeriya a yayin da suke aikinsu, inda ya jaddada cewa hallayarsu da yadda suka wakilci ƙasar zai nuna yadda duniya za ta kalli ƙasar.

  14. Human Rights Watch ta nemi Saudiyya ta soke hukuncin kisa da ta yanke wa wasu ƴan Ethiopia

    .

    Asalin hoton, AFP

    Ƙungiyar kare haƙƙin biladama ta Human Rights Watch ta ruwaito cewa aƙalla ƴan Ethiopia 65 ke fuskantar barazanar a yanke musu hukuncin kisa a Saudiyya saboda laifuka masu alaƙa da ƙwayoyi.

    Ƙungiyar ta ce hukumomin Saudiyya sun aiwatar da hukuncin kisa kan mutum 3 a ranar 21 ga watan Afrilun 2026, amma daga bisani ta dakatar da aiwatar da hukuncin kan sauran ƴan Ethiopian.

    '' Yunƙurin da Saudiyya ke yi na aiwatar da hukuncin kisa kan baƙi daga ƙasashen waje saboda ƙananan laifuka, bayan ta hana a gudanar da bincike yadda ya kamata na nuna tsantsar rashin mutunta rayukansu da ƴancinsu,'' a cewar Nadia Hardman, babbar mai bincike kan ƴan gudun hijira a ƙungiyar Human Rights Watch.

    '' Ya kamata abokan hulɗar Saudiyya su shiga tsakani kafin lokaci ya ƙure.'' in ji ta.

    Ƙungiyar ta ce ba a shaidawa mutanen laifukan da ake tuhumarsu ba, kuma a cewarsu jami'an tsaro sun yi ta lakaɗa musu duka kafin daga bisani aka tilasta musu sanya hannu kan takardun da basu san menene a cikinsu ba.

    Ana tsare da mutanen ne na tsawon fiye da shekaru biyu ba tare da basu damar ɗaukaka ƙara ba.

    Ƙungiyar Human Rights Watch ta yi kira ga hukumomin Saudiyya su gaggauta soke batun hukuncin kisa kan ƴan Ethiopia, tare da sake nazari kan dukkanin ƙararrakin da aka shigar kansu bisa dokokin ƙasa da ƙasa da na Majalisar ɗinkin duniya.

  15. Kotu ta hana INEC amincewa da babban taron ADC na ƙasa

    hoton alamar jamiyyar ADC

    Asalin hoton, ADC/X

    Wata babbar kotun Tarayya a Abuja ta hana INEC amincewa da babban taron ADC na ƙasa da ta gudanar a baya-bayan nan, sannan ta hana hukumar amincewa ko kuma halartar wani taro da ADC ɓangaren David Mark zai shirya.

    Mai shari'a Joyce Abdulmalik wadda ta yanke hukuncin, ta kuma dakatar da Sanata David Mark da sauran shugabbanin jamiyyar daga shiga ayyukan zaɓɓaɓun shugabannin jamiyyar a jihohi.

    Mai magana da yawun tsagin na Mark, Faisal Kabir ya ce hukuncin bai ba su mamaki ba, amma dole ƴan adawa su fitar da ƴan takara ko ta yaya ne.

  16. Farashin ɗanyan mai ya sake tashi a kasuwannin duniya

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin ɗanyan mai ya sake tashi a kasuwannin duniya, bayan rahotannin cewa Amurka na shirin tsawaita toshe tashohin jiragen ruwan Iran.

    Farashin ɗanyan man Brent ya haura zuwa dala ɗari da sha biyar duk ganga.

    Hakan na nuna ƙaruwar dala biyar kan yadda farashin yake a yammacin jiya Talata.

    Iran ta dakatar da sufurin jirage ta Mashigar Hormuz, muhimmiyar hanyar da aƙalla kashi ɗaya cikin biyar na mai da iskar gas da ake amfani da su a duniya ke bi.

    Mashigar na ci gaba da kasance a rufe duk da tsagaita faɗa tsakanin Iran da Amurka da Isra'ila.

  17. Iran ta yanke hukuncin kisa kan fiye da mutum ashirin tun soma yaƙi -MDD

    wani mutum zai rataya kansa, da idonsa rufe da farin ƙyalle

    Asalin hoton, EPA

    Majalisar ɗinkin duniya ta ce tun soma yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran, gwamnatin Iran ta yanke hukuncin kisa kan aƙalla mutum ashirin da ɗaya, tare da kama fiye da dubu huɗu.

    An kama da dama daga cikinsu ƙarƙashin dokar tsaro ta ƙasar mai cike ta taƙaddama.

    Sanarwar Majalisar ɗinkin duniyar ta ce an da dama daga cikin fursunonin na fuskantar azabtarwa, wani lokacin kuma a ɓatar da su, yayin da a wau lokutan kuma akan nuna su a talibijin suna amsa aikata laifuka, da kuma barazanar zartar musu da hukuncin kisa.

    Shugaban hukumar kare haƙƙin biladama na Majalisar Volker Turk ya ce ana take wa Iraniyawa haƙƙinsu ta munanan hanyoyi, ya kuma yi Allawadai da katse intanet da gwamnatin ƙasar ta yi.

  18. Jakadiyar Amurka a Ukraine ta ajiye aiki

    Muƙadashiyyar jakadan Amurka a Ukraine ta ajiye aikin ta, a yayin da rahotanni ke cewa ta fusata ne da matsayar Trump kan rikicin da ake yi a can.

    Julie Davies ta soma aikin ne ƙasa da shekara guda, kuma rahotanni na cewa tana ganin Mista Trump ya gaza wajen bai wa Ukraine tallafin da take buƙata.

    Wanda ya gabaceta ma ajiye aikinsa ya yi, inda yake zargin cewa Amurka na lallaɓa Rasha.

    Sai dai ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta musanta cewa an samu wani rashin jituwa, inda ta jaddada cewa Ms Davis ta yi ritaya ne kawai.

  19. Faransa ta buƙaci ƴan ƙasarta da ke Mali su gaggauta ficewa

    Titi da ababen hawa na wucewa, sai hayaƙi da ke tashi a nesa

    Asalin hoton, Getty Images

    Faransa ta yi kira ga ƴan ƙasarta da ke Mali da su yi gaggawar ficewa.

    Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta bayyana cewa rashin tsaron da ake fama da shi a ƙasar bayan munanan hare haren da mayaƙa masu iƙirarin jihadi ƴan awaren Tuareg suka kai a ƙarshen mako ne yasa ta ɗauki matakin.

    Irin girman harin da mayaƙan suka kai, da kuma janyewar sojojin Mali da na hayar Rasha daga wasu garuruwa ne suka sanya fargaba kan ƙarfin gwamnatin mulkin sojin ƙasar ƙarƙashin Kanal Assimi Goita.

    A jiya Talata, shugaban mulkin sojin yayi wa ƴan ƙasar jawabi, inda ya tabbatar musu cewa an shawo kan lamarin.

    An kuma ga hotunansa tare da jakadan Rasha a ƙasar, da kuma lokacin da ya kai ziyara asibiti.

  20. Najeriya ta buƙaci Afirka ta Kudu ta kare ƴan ƙasarta daga hare haren ƙyamar baƙi

    Yan Afirka ta Kudu suna zanga zanga

    Asalin hoton, BBC/Thuthuka Zondi

    Hukumar kula da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje (NIDCOM) ta buƙaci gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi gaggawar bai wa ƴan Najeriya da sauran ƴan ƙasashen Afirka da ke ƙasar kariya, a yayin da ake samun rahotannin hare haren nuna ƙyamar baƙi da yi musu barazana da kuma tsangwamarsu.

    A cikin wata sanarwa da shugabar hukumar Abike Dabiri-Erewa ta sanya wa hannu, ta bayyana damuwa kan yadda lamarin kai hari kan ƴan ƙasar ke ƙara ta'azzara duk da tattaunawa tsakanin gwamnatocin ƙasashen biyu.

    '' A yayin da mutane da dama ke sa ran samun kwanciyar hankali bayan tattaunawa tsakanin gwamnatocin biyu, lamarin na ƙara tsananta ne,'' in ji ta.

    Hukumar ta ce tana samun rahotannin cewa yara ƴan Najeriya na tsoron zuwa makaranta, yayin da ƴan kasuwa ke ta rufe shagunansu saboda tsoron a kai musu hari, ko a sace kayayyakinsu.

    Ta kuma ce rahotanni sun bayyana an kai sabbin hare hare cikin sa'oi 72 da suka gabata.

    NIDCOM ta shawarci ƴan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu su kasance masu bin doka da oda, kuma su ƙauracewa wuraren da aka fi samun tashin hankalin musamman cikin dare, inda kuma ta tabbatar da cewa ana ci gaba da aikin haɗin gwiwa tsakanin ofishin jakadancin Najeriya a Pretoria da Johannesburg da kuma ma'aikatar harkokin wajen Najeriyar domin shawo kan lamari.