Sojojin Najeriya sun sanar da kama wani fitaccen jagoran ’yan bindiga da ake zargin ya daɗe yana addabar al’ummomi da matafiya a kan hanyar Benue zuwa Taraba.
An samu nasarar kama shi ne a ranar Lahadi, 21 ga Disamba, 2025, a ƙauyen Vaase da ke ƙaramar hukumar Ukum a Jihar Benue, bayan samun sahihan bayanan sirri.
Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojin, Laftanar Umar Muhammad, ya bayyana a Jalingo cewa wanda aka kama Fidelis Gayama na cikin jerin mutanen da hukumomin tsaro ke nema a jihohin Benue da Taraba.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa Gayama na da alaƙa ta kusa da wani fitaccen shugaban ƙungiyar ’yan ta’adda da ake nema, Aka Dogo.
Laftanar Umar Muhammad ya ƙara da cewa ana zargin Fidelis Gayama ne jagoran wata ƙungiyar masu aikata laifuka da ke kai hare-hare kan matafiya da al’ummomi a kan hanyar Kente–Wukari da kuma yankunan iyakar Benue da Taraba.
A cewarsa, wanda aka kama na hannun sojoji a halin yanzu, kuma za a miƙa shi ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da bincike da gurfanar da shi a gaban kotu.