Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/12/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/12/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Rasha ta bayyana goyon bayanta ga Venezuela

    Vene

    Asalin hoton, Getty Images

    Rasha ta ce ta bai wa Venezuela tabbacin samun goyon bayanta, a yayin da Amurka ke ci gaba da kai hari a yankin Caribbean.

    Moscow ta ce ta bayyana matuƙar damuwarta kan kwace jiragen ruwa masu dakon man fetur daga Venezuela da Amurka ke yi a wata tattaunawa ta waya da ministocin harokin wajen kasashen biyu suka yi.

    Tun da farko China ta yi Alla-wadai da matakan da Amurka ke ɗauka na ƙwace jiragen ruwan, inda ta ce hakan ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.

  2. Fitattun Amurkawa da aka bankaɗo a cikin kundin lalata na Epstein

    Amurka

    Asalin hoton, US Department of Justice

    Ma'aikatar shari'a ta Amurka ta fitar da kashi na farko na takardun da ke ƙunshe da bayyanai masu alaƙa da Jeffrey Epstein.

    Takardun sun haɗa da hotuna da bidiyo da kuma sakamakon bincike, kuma ana tsammanin ganin cikakken bayanai bayan Majalisar dokoki ta amince da dokar da ta tilasta fitar da bayanan kundin baki ɗaya.

    Sai dai ƴan jam'iyyun Democrat da Republican sun zargi ma'aikatar shari'a da karya dokar shari'a bayan da ta ce ba za ta iya fitar da dukkan takardun ba a wa'adin da aka ware mata.

  3. Denmark ta gargaɗi Amurka kan naɗa jakada a Greenland

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Denmark ta gargaɗi Amurka, inda ta buƙaci ƙasar da shugabanta Donald Trump da su mutunta ƴancinta, bayan Trump ya naɗa jakada na musamman ga Greenland, yanki mai 'yancin cin gashin kansa a ƙarƙashin Denmark wanda shugaban Amurka a baya ya yi barazanar mamayewa.

    Da maraicen jiya Lahadi ne, Mista Trump ya sanar da sunan wani ɗan siyasan Amurka Jeff Landry a matsayin jakadansa na musamman a Greenland.

    Landry ya ce abin alfahari ne a yi aiki a wannan matsayin, ''wanda zai kai ga ganin Greenland ya kasance wani ɓangare na Amurka''

    Ministan harkokin wajen Denmark ya ce matakin ya yi matuƙar ɓata masa rai.

    Tarayyar Turai ta ce jazamun ne a kare mutuncin iko da iyakokin Jamhuriyar Denmark.

    Shugabannin Denmark da na Greenland sun sha nanata cewa makeken tsaunin na Antatika ba na sayarwa ba ne kuma al'ummar yankin ne za su yanke shawara kan makomarsu da kansu.

  4. MDD za ta zauna domin yaƙin Sudan

    RSF

    Asalin hoton, Avaaz via Getty Images

    Kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya na gab da fara wani zama domin tattauna wa kan matsalar tsaro a kasar Sudan.

    Kasar Sudan ce dai ta bukaci a yi wannan zama, daidai lokacin da 'yan tawayen RSF ke ci gaba da kai munanan hare-hare ga sojoji da farar hula da ya daidaita kasar.

    Dukkan bangarorin biyu sun yi kokarin karbe iko da yankuna masu matukar muhimmanci a Sudan, inda suke kai wa juna harin makaman atilare da na roka da jirage marassa matuka, kuma farar hula suka fi shan wuya a hare-haren.

    Kwamitin tsaron zai saurari bahasi daga bangaren gwamnatin Janar Abdulfatta al-Burhan, da na Muhammad Hamdan Dagalo da ake kira Hemeti, domin samun damar kai kayan agajin abinci da magunguna ga kara yawan kudaden agaji ga kasar ta Sudan.

  5. Ƴanbindiga sun yi garkuwa da matafiya 28 a Filato

    Bindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni sun bayyana cewa ƴanbindiga sun yi awon gaba da matafiya 28 daga garin Zak da ke yankin Bashar a ƙaramar hukumar Wase da ke jihar Filato.

    Wani mazaunin karamar hukumar wanda ya tabbatar wa jaridar Daily Trust faruwar lamarin, ya ce mutanen da aka sace, da suka haɗa da maza da mata da yara na hanyar su ta zuwa garin Sabon Layi ne domin halartar taron Maulidi a jiya Lahadi.

    ''Da safiyar Litinin ne mutane da ke bin hanyar suka ga mota a kan titi, motar wani shugaban al'ummar Zak. Bayan bincike ne aka gane ita ce motar da ke ɗauke da matafiyan,'' in ji shi.

    Wani mazaunin garin ya kuma shaida wa gidan jaridar cewa zuwa yanzu babu labarin inda mutanen suke.

    Mai magana da yawun ƴansandan ƙasar SP Alabo Alfred ya ce suna bincike kan rahoton faruwar lamarin.

  6. Gwamnatin Najeriya za ta fara gwajin ƙwaya ga masu neman aikin gwamnati

    Tinubu

    Asalin hoton, Tinubu X

    Gwamnatin Najeriya za ta ɓullo da shirin gwajin ƙwaya ga masu neman aikin gwamnati a ƙasar, inda ta ce daga yanzu za a saka gwajin ta'ammali da ƙwaya a cikin abubuwan da suka zama dole kafin a ɗauki mutum aiki a ƙasar.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Segun Imohiosen ya fitar a madadin gwamnatin.

    Ya ce, "don haka ana umartar dukkan manyan sakatarori da shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya a ƙasar da su saka gwajin ƙwaya a cikin abubuwan da ake buƙata kafin samun aikin gwamnati."

    Sanarwar ta ƙara da cewa hukumomin ƙasar za su haɗa hannu da hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi wato NDLEA ne domin samun nasarar wannan aikin.

    Ya ƙara da cewa ɗaukar wannan matakin ya zama dole ne bayan yawaitar ta'ammali da miyagun ƙwayoyi, "musamman a tsakanin matasa a ƙasar nan."

  7. An miƙa wa hukumomin jihar Neja ɗalibai 130 da aka ceto

    Umaru Bago

    Asalin hoton, @HONBAGO

    An miƙa ɗaliban nan su ɗari da talatin da aka ceto daga hannun masu garkuwa da su zuwa hannun hukumomi a jihar Neja.

    Gwamnan jihar, da wasu manyan jam'ian gwamnati ne suka tarbe su a fadar gwamnati da ke babban birnin jihar Minna bayan da suka iso a motoci shida tare da rakiyar jami'an tsaro.

    Hukumomi a Kasar sun ce an ceto yaran ne yayin wani aiki na musamman da jami'an tsaro suka yi, duk da ba su bayar da karin bayani ba.

    Hukumomi sun ce ɗaliban, da malamai bakwai da aka ceto, su kadai ne suka rage a hannun ƴan bindigar cikin waɗanda aka sace daga makarantar kwana ta Katolika ta St Mary da ke Papiri a watan Nuwamba.

  8. Za mu tattauna da Cambodia kan tsagaita wuta ba tare da sa bakin Amurka ba - Thailand

    sojoji

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin wajen Thailand ya ce jami'an gwamnatin Amurka sun yi gaggawar tsara yarjejeniyar kawo ƙarshen rikicinsu na kan iyaka da Cambodia wadda Amurkar ta jagoranta, saboda su bai wa Shugaba Trump damar ya sanya hannu kan ta a wata ziyara da zai kai yankin a watan Oktoba.

    A farkon watannnan ne kasashen suka ci gaba da gwabza faɗa.

    Sihasak Phuangketkeow ya ce ana sa ran ƙasashen biyu za su tattauna kan batun tsagaita wuta a ranar Laraba, sai dai a cewar sa ba tare da sa bakin Amurka ba.

    Jim kaɗan bayan sanar da batun tattaunawar, Cambodia ta zargi Thailand da kaddamar da hare hare ta sama a cikin yankin ta.

    Aƙalla ƴan Cambodia miliyan 1 ne aka raba da muhallansu, mutum arba'in kuma suka rasa rayukansu bayan makonni biyu ana rikici tsakanin ƙasashen biyu.

  9. China ta soki Amurka kan ƙwace tankokin dakon man Venezuela

    ...

    Asalin hoton, Kristi Noem via X/Reuters

    China ta yi alla-wadai da matakin Amurka na ƙwace jiragen ruwa masu dakon man fetur daga Venezuela, inda ta bayyana lamari a matsayin wani babban ƙeta dokar ƙasashen duniya.

    Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen China ya ce mahukuntan Beijing na adawa da duk haramtattun takunkuman da wata ƙasa ta ƙaƙaba.

    Sanarwar ta zo ne bayan jami'an Amurka sun ce gwamnatin Washington na bin sawun wani jirgin dakon mai na uku a tekun Venezuela.

    Ranar Asabar, Amurka ta tarbe jirgin dakon mai na biyu kwanaki ƙalilan bayan Shugaba Trump ya ba da sanarwar toshe hanya ga dukkan tankokin man fetur da aka haramta wa shiga ko fita Venezuela.

    Jirgin na ɗauke ne da ɗanyen man fetur ɗin Venezuela a kan hanyarsa ta zuwa China.

  10. Ƴansanda sun kama aƙalla mutum 600 a Afirka kan laifukan intanet

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An kama kusan mutum 600 a ƙasashe da dama na Afirka a wani samamen haɗin gwiwa na yaƙi da laifukan intanet da 'yan sandan ƙasa da ƙasa na interpol suka gudanar.

    Jami'an tsaro sun ce samamen wanda aka gudanar da shi a watan da ya gabata a cikin ƙasashen Afirka goma sha tara, ya kai ga nasarar ƙwato kuɗi har dala miliyan uku.

    Rundunar interpol ta ce ta soke adireshin da akan ɗana tarko fiye da dubu shida - waɗanda masu laifi ke turawa ta hanyar imel ko taƙaitaccen saƙo, wanda kuma ke iya illata kwamfuta ko wayar salula.

    Ta kuma ce masu bincike sun ruguza wasu hanyoyin yaudara guda shida waɗanda sau tari akan yi amfani da ita wajen tatsar kuɗi daga kamfanoni ta hanyar toshe harkokin sadarwa na kwamfutocinsu har sai an biya kuɗi.

  11. Sojojin Najeriya sun kama jagoran ƴanbindiga a Benue

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Najeriya sun sanar da kama wani fitaccen jagoran ’yan bindiga da ake zargin ya daɗe yana addabar al’ummomi da matafiya a kan hanyar Benue zuwa Taraba.

    An samu nasarar kama shi ne a ranar Lahadi, 21 ga Disamba, 2025, a ƙauyen Vaase da ke ƙaramar hukumar Ukum a Jihar Benue, bayan samun sahihan bayanan sirri.

    Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojin, Laftanar Umar Muhammad, ya bayyana a Jalingo cewa wanda aka kama Fidelis Gayama na cikin jerin mutanen da hukumomin tsaro ke nema a jihohin Benue da Taraba.

    Ya ce binciken farko ya nuna cewa Gayama na da alaƙa ta kusa da wani fitaccen shugaban ƙungiyar ’yan ta’adda da ake nema, Aka Dogo.

    Laftanar Umar Muhammad ya ƙara da cewa ana zargin Fidelis Gayama ne jagoran wata ƙungiyar masu aikata laifuka da ke kai hare-hare kan matafiya da al’ummomi a kan hanyar Kente–Wukari da kuma yankunan iyakar Benue da Taraba.

    A cewarsa, wanda aka kama na hannun sojoji a halin yanzu, kuma za a miƙa shi ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da bincike da gurfanar da shi a gaban kotu.

  12. Shugabannin Mali, Burkina Faso da Nijar na ganawa kan tsaro a Bamako

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Sojoji masu mulki a Mali da Burkina Faso da Nijar na ganawa a Bamako, babban birnin Mali kan tunkarar taɓarɓarewar tsaron da ke ƙaruwa da kuma barazanar da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi ke yi ga faɗin yankin Sahel.

    Ana kuma sa ran shugabannin za su tattauna batun yunƙurin juyin mulkin da bai yi nasara ba kwanan nan a Benin, har ma da tsare-tsaren kafa wani bankin zuba jari na haɗin gwiwa da wata tashar talbijin ta ɗaukacin yankin.

    Ƙasashen uku sun janye ne daga ƙungiyar Ecowas ta ƙasashen Afirka ta Yamma, sannan suka katse alaƙa da Faransa kafin su ɗauki matakin ƙarfafa dangantaka da Rasha.

  13. Amurka ta tasa jirgin dakon mai a gabar tekun Venezuela gaba

    ...

    Asalin hoton, X/Sec_Noem

    Jami'an Amurka sun ce masu gadin bakin teku sun tasa wani jirgin ruwa na dakon mai a yankin gabar tekun Venezuela gaba.

    Wannan shi ne karo na biyu a ƙarshen makon nan da jami'an na Amurka ke bin wani jirgin ruwa a wannan yanki na Karebiya domin su kama shi.

    Venezuela dai ta zargi Amurka da fashi da kuma satar mutane.

    A wannan makon Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ya bayar da umarnin hana shigarwa ko fitar da man da aka sanya wa takunkumi Venezuela.

    Amurka ta yi zargin cewa jiragen na ɗauke da man da aka sanya wa takunkkumi, wanda ta ce ana amfani da kuɗinsa wajen tafiyar da ta'addanci na miyagun kwayoyi, amma kuma ba ta bayar da shedar hakan ba.

  14. Ƴan adawar Somaliya sun ba gwamnati wa’adin gaggawa kan zaɓen 2026

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu manyan ’yan adawar siyasa a Somalia sun yi barazanar shirya nasu zaɓen shugaban ƙasa da na majalisa idan shugaba Hassan Sheikh Mohamud bai kira taron haɗin kan ƙasa cikin wata guda ba domin cimma matsaya kan tsarin zaɓen da aka shirya yi a 2026.

    An yanke wannan shawara ne bayan wani taro da aka yi a birnin Kismayo, a kudancin gaɓar teku wadda tsohon shugaban ƙasa Sharif Sheikh Ahmed da tsofaffin firaministoci suka halarta, tare da shugabannin jihohin Puntland da Jubbaland

    Waɗannan ’yan siyasa sun zargi Shugaba Mohamud da gazawa wajen cika ayyukan ƙundin tsarin mulki da kuma yin sakaci wajen yaƙi da ƙungiyar al-Shabab.

    Sun kuma yi zargin cewa shugaban ƙasa ya mallaki filayen gwamnati don amfanin kansa, tare da yin gyare-gyaren kundin tsarin mulki ba tare da shawarar kowa ba.

    A cewarsu, wa’adin majalisar dokoki zai ƙare ne a ranar 14 ga Afrilu 2026, yayin da na shugaban ƙasa zai ƙare a ranar 15 ga Mayu 2026. Don haka suka buƙaci Shugaba Mohamud ya kira taron dukkan masu ruwa da tsaki na siyasa cikin wata guda, wato kafin 20 ga Janairu 2026.

  15. Amurka za ta ware dala miliyan 200 don tallafa wa cibiyoyin lafiya na Krista a Najeriya

    ...

    Asalin hoton, Nigeria Presidency/Getty

    Amurka ta rattaɓa hannu kan wata yarjejeniya ta haɗin gwiwa a fannin inganta kiwon lafiya lafiya mai ɗorewa na tsawon shekaru biyar da Najeriya, wadda ta kai kimanin dala biliyan 5.1.

    Shirin na da nufin inganta tsarin lafiyar ƙasar karkashin tsarin Amurka na samar da lafiya ga al'ummar duniya ta America First Global Health Strategy.

    A karkashin wannan yarjejeniyar, Amurka za ta bayar da tallafi na dala biliyan 2.1, yayin da Najeriya za ta zuba dala biliyan 3 a kiwon lafiya a cikin shekaru biyar.

    Daga cikin tallafin, za a ware kimanin dala miliyan 200 domin tallafawa sama da cibiyoyin lafiya na addinin Kirista guda 900, don fadada damar samun kulawa ga cututtuka kamar HIV da TB, zazzabin cizon sauro, da kula da uwa da jariri.

    Wannan shi ne mafi girman haɗin gwiwa da kowace ƙasa ta yi tun lokacin da aka kaddamar da tsarin.

    Yarjejeniyar za ta ƙarfafa tsarin kiwon lafiya na Najeriya, ta ceci rayuka, kuma ta ƙara ƙarfafa haɗin kai tsakanin Amurka da Najeriya.

  16. Ba ma tunanin abubuwan da suka faru a baya – Kocin Super Eagles

    ...

    Kocin tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya, Eric Chelle ya ce a halin yanzu ƴan wasansa sun mayar da hankali ne kan wasansu na farko a gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON) inda za su fafata da tawagar ƙasar Tanzania ranar Talata mai zuwa.

    Da ya ke jawabi a taron maneman labarai da aka yi a filin wasan birnin Fez Chelle ya bayyana cewa tawagarsa ta yi baƙin cikin rasa gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026 amma hakan ba zai sa ta yi ƙasa a gwiwa wurin neman yin nasara a gasar AFCON ba.

    Da ya ke amsa tambaya kan batun ci gaba da jan ragamar tawagar bayan wannan gasar, kocin na Super Eagles ya ce za su zauna da hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya (NFF) domin tattauna batutuwan da suka shafi kwantiraginsa bayan kammala gasar.

    A na shi ɓangaren sabon kyaftin ɗin tawagar Super Eagles Wilfred Ndidi ya yi iƙirarin cewa a shirye su ke su ga cewa sun taka rawar gani a gasar.

    Ndidi ya ƙara da cewa ba ya jin wani ƙarin matsin lamba a kansa bayan da ya karɓi muƙamin kyaftin ɗin tawagar daga hannun Troost Ekong wanda ya yi murabus ana daf da fara gasar ta Morocco.

    Ya buƙaci ƴan Najeriya da su bai wa tawagar goyon baya domin ganin cewa ta taɓuka abin-a zo-a gani a gasar.

  17. Gwamnatin Najeriya ta ayyana hutun Kirsimeti da sabuwar shekara

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun 25 da 26 ga Disamba da kuma 1 ga Janairu 2026, a matsayin ranakun hutu na ƙasa.

    Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan inda ya ce an ba da hutu a waɗannan ranaku ne domin murnar Kirsimeti da rana ta farko bayan Ranar Kirsimeti wato Boxing day da kuma sabuwar shekara.

    Ministan ya yi kira ga ‘yan Najeriya "Da su yi tunani kan darajoji na soyayya da zaman lafiya da tawali’u da sadaukarwa da murnar haihuwar Yesu Almasihu.

    Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan ƙasa, ba tare da la’akari da addini ko ƙabilanci ba, da su yi amfani da lokacin bukukuwa wajen addu’a don zaman lafiya da tsaro da ci gaban ƙasa.

    Ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya da "‘Su ci gaba da kiyaye doka da lura da tsaro a lokacin bukukuwan, yayin da ya yi masu fatan Kirsimeti mai albarka da sabuwar shekara mai albarka."

  18. Yadda tawagar Najeriya ke atisaye gabanin wasanta da Tanzaniya

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton ku kalli bidiyon

    Tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya na ci gaba da yin atisaye gabanin wasanta da Tanzaniya da za a fafata a ranar Talata a gasar cin kofin Afirka (AFCON).

    Ƴan wasan na gudanar da atisayen ne domin ƙara ƙarfafa jiki da haɗin kai.

    Atisayen na gudana ne a filin wasa da ke birnin Fez na ƙasar Morocco, inda koci da tawagarsa ke mayar da hankali kan dabarun wasa da haɗin kai tsakanin ƴan wasan.

    An ga ’yan wasan suna yin atisayen motsa jiki, wuce-kwallo da dai sauransu kafin wasa.

  19. Ba zan iya yi wa ƴan Najeriya albishir a gasar Afcon 2025 ba - Zaidu Sanusi

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton ku kalli bidiyon

    Dan wasan Super Eagles, Zaidu Sanusi, ya ce ba shi da wani albishir da zai bai wa ƴan Najeriya dangane da nasara a wasan da za su fafata da Tanzania a ranar Talata, a gasar Afcon ta 2025 da ake yi a Morocco.

    Sanusi ya shaida wa BBC cewa abin da yafi mayar da hankali a kai shi ne abin da ƙwallo ke ba shi a matsayin kwarewa da hidima ga ƙasa.

    Sai dai kuma ɗan wasan na Najeriya ya yi kira ga ’yan Najeriyar da su ci gaba da ba su goyon baya tare da yi musu addu’a a duk inda suke, yana mai cewa hakan na ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen fuskantar manyan ƙalubale a wasannin ƙasa.

    "Goyon bayan jama’a na da matuƙar tasiri wajen ƙarfafa ’yan wasa su ba da mafi kyawun abin da suke da shi domin ɗaukaka tutar Najeriya," in ji Sunusi.

  20. Yunwa ta kashe sama da ƴan gudun hijira 50 a arewacin Habasha

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla ƴan gudun hijira 50 ne suka mutu sakamakon yunwa a yankin Tigray na arewacin Habasha cikin watanni biyar da suka gabata, a cewar tashar labarai ta gwamnatin yankin, Tigray TV.

    Rahoton ya ce ana zargin gwamnatin tarayya da ci gaba da kakaba takunkumin tattalin arziki da na man fetur a yankin, duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a 2022 wadda ta kawo ƙarshen yaƙin basasa na tsawon shekaru biyu.

    Halin jin ƙai a yankin na cikin mawuyacin hali sakamakon illolin yaƙin da aka yi tsakanin 2020 zuwa 2022 da fari da kuma dakatar da tallafin agaji.

    Rahoton ya ƙara da cewa mutanen da ke zaune a cibiyar sun rasa muhallansu ne a lokacin yakin.