Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta yi kira da a dakatar da aiwatar da sabuwar dokar haraji da ake shirin fara aiki da ita a ranar 1 ga watan Janairun 2026.
Wannan dai na zuwa ne bayan zargin cewa an sauya ko kuma yin cushe a dokar da aka fitar saɓanin abin da majalisar ƙasar ta amince da shi.
Wannan batu ya fara fitowa ne makon da ya gabata bayan wani ɗan majalisar wakilai daga Sokoto, Abdulsamad Dasuki, ya bayyana cewa akwai bambance-bambancen a dokar da ya lura da su.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, NBA ta ce lamarin na tayar da “hankali dangane da sahihanci da gaskiya da amincin tsarin dokokin Najeriya.”
Ƙungiyar ta nemi a gudanar da cikakken bincike a bayyane domin fayyace yadda aka samu dokokin tare da jaddada cewa dole ne a dakatar da duk wani shiri na aiwatar da dokar har sai an warware batun.
Shugaban NBA, Afam Osigwe, ya ce "zargin ya sanya ayar tambaya kan tsari da bin doka wajen samar da dokoki."
Ya kara da cewa "Irin wannan rikici na iya haifar da matsalolin tattalin arziki tare da tayar da hankalin ’yan kasuwa da masu zuba jari da haifar da rashin tabbas ga jama’a da hukumomin da dokar ta shafa.
A watan Yuni ne Shugaba Bola Tinubu ya rattaɓa hannu kan kudurorin gyaran haraji guda huɗu, inda suka zama doka bayan dogon muhawara.