Mun kai wa Isra'ila hari da makami mai linzami na Khyber - Iran
Rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta ce ta yi amfani da makaminta mai linzami na Khyber wajen kai hare-haren da ta kai Isra'ila.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, Rundunar IGRC ta ce a hare-harenta kan Isra'ila na baya-bayan nan ta kai hari biranen Tel Aviv da Haifa da Gabashin Birnin Kudus.
Makami mai linzami na Khyber na da ƙarfin da zai iya yion tafiyar kilomita 2,000.
Mataimakin babban hafsan sojojin ƙasar, Mohammad Reza Ashtiani ya bayyana makamin a matsayin ɗaya daga cikin makamai masu linzami na zamani da wani kamfanin ƙasar ya ƙera da manyan kawunan da zai iya ɗaukar abubuwan fashewa masu nauyin kilogiram 1,500.
Haka ma sojojin Iran ɗin sun ce sun kai hare-hare kan sansanin sojin saman Amurka na Ali al-Salem da ke ƙasar Kuwait da kuma wani jrigin ruwa a tekun Indiya.