Mu kwana lafiya
Mun zo ƙarshen rahotonnin a wannan shafi na ranar Laraba.
Muna nan tafe da wasu sababbi gpbe da safe.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/13/2025.
Daga Aisha Babangida, Isiyaku Muhammed da Umar Mikail
Mun zo ƙarshen rahotonnin a wannan shafi na ranar Laraba.
Muna nan tafe da wasu sababbi gpbe da safe.
Yan'uwan wani mutum ɗan Colombia da aka kashe a harin da Amurka ta kai yankin Caribbean sun shigar da ƙara irinta ta farko kan hare-haren da Amurka ke kaiwa a kusa da Venezuela.
Ƴan'uwan na zargin cewa ɗan'uwansu Alejandro Carranza, wanda masunci ne, ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da Amurka ta kai hari kan jirgin ruwansa da ke gaɓar tekun da ke iyaka da Colombia.
Wakiliyar BBC ta ce lauyan yan'uwansa na neman a biya su diyya tare da kawo ƙarshen hare-haren da Amurka ke kaiwa, waɗanda Washington ta ce tana harar masu safarar miyagun ƙwayoyi zuwa Amurka.

Asalin hoton, AFP
Babban birnin Cuba Havana da kuma yankuna da dama na yammacin tsibirin sun tsunduma cikin duhu bayan babban layin wutar lantarkin ƙasar ya samu tangarda.
Matsalar lantarkin ta ƙara ƙamari a wannan makon fiye da yadda aka taɓa gani a baya, yayin da na'urorin samar da lantarkin ƙasar da suka tsufa ke fama wajen biyan buƙatar ƴan ƙasar.
A shekarar da ta gabata ƙasar ta shiga duhu har sau biyar, yayin da Cuba ke ci gaba da fama da karancin man fetur, da abinci, da kuma fuskantar matsalar tattalin arziki mafi muni a gomman shekaru.
Takunkuman da Amurka ta ƙaƙaba wa ƙasar na ci gaba da ta'azzara.

Asalin hoton, Reuters
Isra'ila ta ce ta karɓi wata gawa da Hamas ta ce ta ɗaya daga cikin mutum biyun da suka mutu ne cikin waɗanda aka kama, wanda har yanzu ke cikin Gaza.
Za a kai gawar wajen gwajin ƙwayoyin halitta saboda a tabbatar da cewa ta Ran Gvili ce ɗan Isra'ila, ko kuma ta Sudthisak Rinthalak ce wanda shi kuma ɗan Thailand ne.
Mayaƙan Hamas sun ce an gano gawar ne a arewacin Gaza a yau Laraba.
Tun da farko hukumomin Isra'ila sun ce gawar da Hamas ta ba su a jiya Talata da aka yi wa gwaji ba ta ɗaya daga cikin mutum biyu da ake ci gaba da nema ba ne.

Asalin hoton, EPA
Amurka ta yi barazanar saka takunkumai da hana bizar shiga ƙasar kan duk wanda ta samu da hannu a zargin yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya.
Ministan harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya wallafa a shafinsa na dandalin X cewa matakin martani ne ga matsalar yi wa Kiristoci kisan gilla, zargin da bai bayar da wata hujja a kansa ba.
"Amurka na ɗaukar mataki game da tashin hankali da zalincin da ake yi wa Kiristoci a Najeriya da duniya baki ɗaya," a cewarsa.
"Ofishin harkokin waje zai dakatar da bayar da biza ga waɗanda suka tsara da gangan, ko suka bayar da umarni, ko ɗaukar nauyi, ko take haƙƙin 'yancin yin addini. Matakin hana bizar ya shafi Najeriya da sauran gwamnatoci ko mutane da ke zalintar mutane kawai saboda addininsu."
A yau Laraba ne wani kwamatin Majalisar Wakilan Amurka ya fitar da rahoto kan zargin, inda wasu 'yanmajalisa suka nanata iƙirarin cewa ana kashe Kiristoci da gangan a Najeriya.

Asalin hoton, NTA
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da naɗin Janar Christopher Musa a matsayin sabon ministan tsaro.
Zaman majalisar ya cika da ruɗani a yau Laraba yayin da wasu 'yanmajalisar ke cewa janar ɗin, wanda shi ne tsohon babban hafsan tsaron Najeriya, ya rusuna ya wuce ba tare da amsa tambayoyi masu yawa ba, da kuma waɗanda suka ce dole sai ya amsa.
Daga ƙarshe dai Shugaban Majalisa Godswill Akpabio ya shawo kan hayaniyar kuma ya amince cewa akwai buƙatar Janar Musa mai ritaya ya amsa tambayoyin da suka dace.
Da yake jawabi, janar ɗin ya bayyana shirinsa na shawo kan matsalar tsaro, da kuma dawo da martabar rundunar sojin ƙasar a idon 'yan Najeriya.
"Wannan ba lokaci ne na yin siyasar "rusuna ka wuce ba". Hatta Donald Trump yana matsa mana. Ba game-garin mutum ba ne, tsohon babban hafsan tsaro ne," kamar yadda Akpabio ya bayyana lokacin da ya miƙe daga kujerarsa lokacin da ake hayaniyar.
Ana sa ran Janar Musa zai fara aiki nan take bayan Mohammed Badaru ya sauka daga muƙamin a ranar Litinin.

Asalin hoton, Getty Images
A garin Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya, wata gobara ta lauƙume rayukan mutum biyar ‘yan gida ɗaya.
Wutar da ta tashi a unguwar Kofar Sauri ranar Litinin da ta gabata, ta fara ci ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare, kamar yadda Salisu Adamu Karama, mai magana da yawun hukumar yan kwana-kwana ta jihar Katsina ya shaida wa BBC.
Ya ƙara da cewa lokacin da jami'ansu suka isa gidan wutar ta riga ta cinye shi.
A wannan lokaci na rani da iskar hunturu, jama’a na fuskantar barazanar tashin gobara a kodayaushe.
Latsa alamar lasifiƙar ƙasa ku saurari ƙarin bayanin da Salisu Karama ya yi wa BBC:

Asalin hoton, Getty Images
Kwamishinan makamashi na Tarayyar Turai Dan Jorgensen ya jinjina wa sabuwar yarjejeniyar da aka samar wadda za ta ga ƙasashen Turai sun daina sayen man Rasha nan da 2027.
Ya ce hakan na nufin ƙasashen Turai za su tsaya da kafarsu wajen samar wa kansu makamashi, inda ya ce a yanzu ba batun Vladimir Putin ya ci gaba da cin dunduniyarsu.
Shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula Von de Leyen ta ce suna biyan Rasha yuro biliyan 12 duk wata domin sayen mai a lokacin da aka fara yaƙin, amma yanzu ya ragu zuwa yuro biliyan ɗaya da miliyan 500 duk wata.

Asalin hoton, NTA
Majalisar Dattawan Najeriya ta shiga hayaniya yayin aikin tantance tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Christoper Musa a matsayin sabon ministan tsaro lokacin da wasu suka nemi ya rusuna ya wuce kawai ba tare da amsa tambayoyi masu yawa ba.
Sanata Sani Musa (jihar Neja) ne ya shawarci majalisar ta bari janar ɗin ya wuce kawai bayan ya amsa 'yan wasu tambayoyi marasa yawa.
Sai dai waɗanda ke adawa da hakan sun haƙiƙance cewa dole ne sai an yi masa tambayoyi masu tsauri, abin da ya jawo hatsaniya tsakanin 'yanmajalisar.
Bayan tsawon lokaci ana hauragiya, Shugaban Majalisa Godswill Akpabio ya miƙe tsaye, wanda ke alamta neman kowa ya shiga taitayinsa bisa dokokin majalisar.
Da yake amsa tambayoyin, Chris Musa ya bayyana damuwa game da ƙaruwar matsalar tsaro a Najeriya, kuma ya yi kira da aka himma wajen aiki da shirin kare makarantu na Safe School Iniative.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Indiya ta soke wani umurni da ta bai wa masu haɗa wayoyin hannu na zamani na su sanya wata manhajar da ta samar ta hana damfara ta intanet da kuma gano wayar da aka sace a cikin kowacce sabuwar waya.
Ƴan adawa da kamfanonin fasaha ta duniya sun bayyana damuwar su kan cewa gwamnati na iya satar bayanan mutane.
Ma'aikatar sadarwa ta India ta ce a yanzu sanya manhajar ba wajibi bane. Tun da farko gwamnati ta ce matakin zai ƙarfafa tsaron intanet.

Asalin hoton, Reuters
Fadar Kremlin ta ce shugaba Putin a shirye yake ya amince da wasu ɓangarori na daftarin shirin samar da zaman lafiya a Ukraine da Amurka ta gabatar.
Mai magana da yawun fadar Dmitry Peskov ya kuma ce Putin a shirye yake ya gana da masu shiga tsakani na Amurka ko sau nawa ake buƙata domin kawo ƙarshen yaƙin.
Peskov ya ce kuskure ne a riƙa cewa Moscow ta ƙi amincewa da dukkanin abubuwan da Amurka ta gabatar. Kalaman nasa na zuwa ne bayan wata ganawa ta sa'o'i biyar da aka yi tsakanin Putin da wakilan Amurka a Moscow ba tare da cimma nasara ba.
Wakilin BBC ya ce a bayyane ya ke cewa har yanzu akwai batutuwan da Rasha ba za ta amince da su ba cikin daftarin shirin samar da zaman lafiyar.
Wani muhimmin batu har yanzu shi ne makomar yankunan Ukraine da dakarun Rasha suka kwace iko da su.

Asalin hoton, Getty Images
Mai taimaka wa shugaba Bola Tinubu kan yaɗa labarai, Daniel Bwala, ya bayyana cewa Gwamnatin ƙasar ƙarƙashin jagorancin Tinubu ba ta lamuntar tattaunawa da ƙungiyoyin ‘yan bindiga ko na ta’addanci.
Yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, Bwala ya ce matsalolin tsaro a Najeriya suna da sarkakiya sosai, har suna iya tura kowace gwamnati ga yanke shawarar da ba ta dace ba a wasu lokuta.
Ya ce a wasu lokutan, gwamnatoci sun taba shiga tattaunawa saboda buƙatar ceto rayukan jama’a.
Ya ce, “A da akwai lokacin da gwamnati ta shiga tattaunawa da ƴanbindiga, kuma ina tunawa El-Rufai ya taba magana cewa a wancan lokacin akwai manufofi da ke ba jihohi da gwamnatin tarayya damar tattaunawa idan halin da ake ciki ya tilasta hakan kuma tattaunawa ce kadai hanyar ceto su, to wasu lokuta gwamnati za ta yi abin da ya dace domin ceto su.”
Sai dai Bwala ya ce shugaba Tinubu ya zo da tsauraran mataki na “ba tattaunawa da ƴanbindiga” saboda biyan kudin fansa ko tattaunawa da ‘yan bindiga na ƙara tallafa wa ta’addanci."
Ya bayyana cewa kuɗin fansa da ake biya kan garkuwa da mutaneshi ƴan bindigar da amfani da su domin sayen ƙarin makamai.
“A saboda haka, gwamnatin Tinubu ba ta yarda da tattaunawa da ƴanbindiga kwata-kwata ba,” in ji shi.

Asalin hoton, Nigeria Senate
Ƙudirin da ke neman a gyara dokar yaƙi da ta’addanci domin a ɗauki garkuwa da mutane da makamantansu a matsayin ta’addanci ya samu amincewar Majalisar Dattawa, inda ya tsallake karatu na biyu.
Ƙudirin, wanda Sanata Opeyemi Bamidele ya dauki nauyinsa, ya tanadi hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane ba tare da wani zaɓin tara ba.
Sanata Bamidele ya ce wannan kudiri ya yi daidai da kokarin majalisar na baya-bayan nan na yin aiki tare da gwamnatin tarayya domin kawo ƙarshen matsalolin tsaron da ke addabar ƙasar.
Ya tunatar da cewa makonni uku da suka gabata Majalisar ta yanke shawarar samar da doka mai karfi da za ta mayar da hankali kan yawaitar satar mutane a fadin Najeriya.
Yayin gabatar da ƙudirin, Sanatan ya bayyana garkuwa da mutane a matsayin daya daga cikin manyan laifuka da kungiyoyin miyagu ke amfani da su wajen tara kudi, wanda hakan ya haifar da tsoro a cikin al'umma tare da kawo cikas ga karatun yara a jihohi da dama.
Sanatocin da suka tattauna kan kudirin sun jaddada cewa hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane zai zama babban gargaɗi ga masu aikata laifin.
Wasu ƴan majalisar kuma sun buƙaci a samar da tsauraran matakai ga bankunan da za a same su suna taimakawa wajen mu'amalar kudaden masu garkuwa da mutane, yayin da wasu suka nemi a daina bai wa ‘yan ta’adda afuwa.
Majalisar ta tura kudirin ga kwamitocin hadin gwiwa na Shari’a da hakkokin ɗan adam da Sashen tattara bayanan sirri domin zurfafa nazari, tare da umarnin su gabatar da rahotonsu cikin makonni biyu.

Asalin hoton, Kano State Government
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatin jihar na shirin samar da jirage marasa matuƙa da sauran kayan aikin tsaro domin sa ido da kuma ɗaukar mataki cikin gaggawa don kare rayuka da dukiyoyin mazauna yankunan iyakar Kano da Katsina.
Wannan bayani na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Laraba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake ziyartar sansanonin rundunar hadin gwiwa (JTF) domin tantance yadda suka shirya daƙile hare-haren ‘yan bindiga da suka auku a kwanakin baya a ƙananan hukumomi guda uku na Tsanyawa da Shanono.
Ya kuma yi kira ga al’ummar da ke zaune a yankunan da abin ya shafa da su taimaka wa rundunar JTF da bayanai masu amfani game da motsin ‘yan bindiga.
Gwamnan ya ce yayin da ya kai ziyara ga Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu kan lamarin, shugaban ya amsa buƙatar da aka gabatar masa cikin sauri."
Ya umarci JTF da su yi Iya kokarinsu wajen tabbatar da kuɓutar da mutanen da aka sace a kananan hukumomin Tsanyawa da Shanono daga hannun ‘yan bindigar.
"Mun san cewa suna kai hari kan al’umma ba gayra ba dalili, musamman a Tsanyawa da Shanono. Rayuka da dama sun salwanta, yayin da wasu kuma aka kai su daji. Insha Allah, za a dawo da wadanda aka sace ga iyalansu," in ji shi.
Gwamna Yusuf ya kara da cewa, "Mun yi wannan ziyarar ne domin tantance halin tsaro da kuma tattauna da ku, haka zalika saboda ƙarfafa gwiwar ku wajen yin aiki tuƙuru."
Ya bayyana damuwarsa cewa irin wannan rashin tsaro a Kano sabon lamari ne da ba a saba gani ba, amma gwamnatin jihar na yin duk mai yiwuwa tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro domin magance matsalar.
A yayin ziyarar, Gwamna Yusuf ya taya iyalan wadanda aka sace jimami tare da tabbatar masu cewa za a dawo da su cikin gaggawa.
An ruwaito cewa mutum 5 da 10 ne aka sace a Tsanyawa da Shanono, ciki har da mace daya da ta rasa rayuwarta sakamakon hare-haren.

Asalin hoton, AFP
Ministocin harkokin wajen ƙasashen ƙungiyar Nato na taro domin tattauna batun yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine da kuma batutuwan da suka shafi tsaro.
A yayin jawabin buɗe taro, shugaban ƙungiyar, Mark Rutte ya ce "Rasha na shirin yin fito na fito na dogon lokacin sannan Rasha ta karya dokokin ƴancin sararin samaniyyar ƙasashe."
Ya ƙara da cewa Russia tana "aiki na ƙut da ƙut da China da North Korea da Iran "domin lalata ƙasashenmu da kuma raba kan ƙasashe dangane da dokokin ƙasa da ƙasa," in ji Rutte.
Daga ƙarshe mista Rutte ya ce dole ne ƙasashen ƙungiyar su haɗa ƙarfi wuri guda su kuma nuna shi.

Asalin hoton, Tinubu/X
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci manyan hafsoshin tsaro da hukumomin tattara bayanan sirri su kara inganta dabaru da samar da sakamako mai gamsarwa a yakar matsalolin tsaro da ke addabar wasu sassan kasar.
Wannan kira na shugaban ya biyo bayan wani muhimmin taro da ya gudanar da shugabannin tsaro a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Taron, wanda aka yi a sirrance ya ɗauki fiye da sa’a guda a ranar Talata, inda shugaban ya tattauna da manyan hafsoshin soji da na na tattara bayanan sirri kan matakan da ake bukata don kawo karshen barazanar tsaro.
Rahotanni sun ce tattaunawar ta yi zurfi, inda shugaban ya yi nuni da buƙatar samun sauyin sakamako cikin gaggawa.
Da yake jawabi bayan kammala taron, babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya bayyana cewa zaman ya kasance mai matukar muhimmanci.
Ya ce "Shugaban kasa ya gabatar da sabbin umarni da hanyoyin da ya ke ganin za su taimaka wajen inganta yaƙi da dukkan nau’ikan rashin tsaro a ƙasar."
Janar Oluyede ya kara da cewa akwai sabbin manufofi da aka tsara domin tabbatar da cewa an tunkari duk wata barazana cikin tsari da kuma hadin kai.

Asalin hoton, EPA
Wani rikici na neman ɓallewa a Isra'ila dangane da wani ƙudiri da zai tilasta wa Yahudawa masu tsaurin kishin Yahudanci shiga aiki soji, waniabu da ake ganin zai yi wa gwamnatin Isra'ila zagon ƙasa da kuma raba kan kasar.
Ra'ayoyin jamaa'a a ƙasar ya rabu dangane da batun kuma ana ganin wannan shi ne babbar barazana ga firaiministan ƙasar, Benjamin Netanyahu.
A yanzu haka dai ƴan majalisar dokoki na duba yiwuwar yin wani ƙudiri da zai yaye kariyar da aka bai wa masu tsaurin kishin Yahudanci daga shiga aiki soji.
Wata majiya ta sojin Isra'ila ta ce a bara kawai an ɗauki sojoji 24,000 amma 1,200 ne kawai na masu kaifin kishin Yahudancin ne suka amsa kira.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a Indonesia na fadi tashin kai kayan agaji ga al'ummomin da hanyoyin kai wa gare su suka katse a Sumatra, sama da mako ɗaya bayan da mamakon ruwan sama ya fara yi wa tsibirin ta'annati.
Mutanen da lamarin ya rutsa da su sun zarta 750, amma kuma dubbai na cikin matuƙar buƙatar abinci da ruwa da sauran muhimman kayayyakin buƙatu.
Ana kai kayan agajin ne ta jiragen sama ko na ruwa, saboda tituna da gadoji yawanci duk sun lalace.

Asalin hoton, Kwara State Government
Masu bauta 38 da aka sace a cocin Kwara da ke ƙaramar hukumar Eruku a ranar 18 ga Nuwamba, 2025, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku tare da jikkatar wani sun koma gida lafiya bayan an kubutar da su.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙaramar hukumar Ekiti, Dada Sunday ya fitar a daren Talata, ya tabbatar da cewa gwamnan jihar, AbdulRahman AbdulRazaq ne ya miƙa waɗanda aka ceto ga shugaban ƙaramar hukumar Ekiti, Honourable Awelewa Olawale Gabriel, a birnin Ilorin.
Da yake karɓar wadanda aka ceto, Awelewa ya bayyana godiyarsa ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da gwamna AbdulRazaq da duka hukumomin tsaro bisa gaggawa da ƙoƙari wajen ceton mutanen.
Ya ce aikin haɗin gwiwar jami’an tsaro da gwamnati ya taimaka wajen kammala ceto cikin lokaci, tare da ba wa wanɗanda aka kuutar cikakkiyar kulawa.
Sanarwar ta ce tawagar waɗanda aka ceto ta isa garin Eruku da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin Talata, inda dangi da mazauna yankin suka tarbe su cikin murna da farin ciki.
Shugaban ƙaramar hukumar ya tabbatar wa mazauna yankin cewa gwamnati za ta ci gaba da bai wa tsaro mahimmanci, tare da ƙarfafa matakan kare rayuka da dukiyoyi a dukkan gundumomi 10 na yankin.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta ayyana dokar ta-ɓaci kan rashin tsaro a ƙasar tare da bayar da umarnin ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki bayan sace ɗalibai sama da 300 a wani kome na ayyukan ƴan bindiga a tsakiyar watan Nuwamba a fadin arewa maso yammacin ƙasar.
Hari mafi muni da ya faru shi ne wanda ƴan bindiga suka kai ranar 21 ga watan Nuwamba inda suka sace ɗalibai da malamai kimanin 300 a makarantar St Mary's Catholic School da ke jihar Neja.
Akwai mutane aƙalla 50 da suka kuɓuta, kamar yadda rahotanni suka bayyana, sai dai har yanzu sauran na hannun ƴan fashin daji.
Hakan na zuwa ne kwana hudu bayan wasu ƴan bindigar sun yi garkuwa da ƴanmata 25 daga makarantar gwamnati ta mata da ke ƙaramar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi.
Ɗalibai biyu suka tsere daga hannun ƴan bindigar yayin da aka sako guda 23 a ranar 25 ga watan Nuwamba, inda gwamnati ta ce ta tattauna ne da ƴan bindigar.