Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 13/10/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 13/10/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Jama'a a nan muka kawo karshen wannan shafin na kawo muku labaran kai-tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya nuna mana.

    Da fata kun ji dadin kasancewa tare da mu.

  2. Ana ci gaba da gwabza yaƙi tsakanin mayaƙan M23 da dakarun gwamnati a Congo

    M23

    Asalin hoton, AFP

    Ana ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin mayakan 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda da kuma mayakan da ke samun goyon bayan gwamnati a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.

    Rikicin wanda aka fara a makon daya gabata ,ya sake barkewa yau Litinin, inda rahotanni ke cewa mazauna yankin sun tsere bayan da mayakan suka kona musu gidajensu a yankin Rutshuru da ke lardin arewacin Kivu.

    Wakilin BBC ya ce sabon tashin-hankalin na zuwa ne kwanaki kadan bayan da shugaba Felix Tshisekedi ya bukaci takwaransa na Rwanda Paul Kagame da ya kawo karshen taimakon da yake bai wa masu tada kayar baya a DRC.

    Sai dai Rwanda ta yi watsi da kiran nasa.

  3. Shugaban Madagascar ya sake jawabi ga ƴanƙasar

    Madagascar

    Asalin hoton, Adrian Dennis - Pool/Getty Images

    Shugaban kasar Madagascar Andry Rajoelina ya sake dage jawabin da aka shirya domin ya yi wa al'ummar kasar yayin da ake ci gaba da rade-radi a kan inda ya ke.

    Ofishinsa ya ce sojoji sun yi barazanar kwace kafar yada labaran gwamnati kuma jinkiri da ake fuskanta na da nasaba da tattaunawar da ake yi.

    Rahotoni sun ce mai yi wa Mista Rajoelina ya fice daga kasar kodayake ba bu tabbaci a hukumance kan ya ficen ko yana cikin kasar.

    Dandazon mutane sun sake taruwa a Anta-na-narivo babban birnin kasar domin neman ya sauka daga mulki.

    MDD ta ce mutun akalla 22 ne aka kashe a makoni da aka shafe matasa na zanga-zangar nuna rashin amincewa da gwamnati kan matsalar rashin aikin yi da tsaddar rayuwa.

  4. 'Ban yi tunanin komawa Falasɗinu da rai ba'

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Hamas ta fara mika gawarwakin mutanen da take riƙe da su, a cikin bangare na shirin tsagaita wuta da Trump ya jagoranta.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce kungiyar agaji ta Red Cross ta fada mata cewa ta karbi akwatuna gawa guda biyu.

    Rahotanni kafofin yada labarai sun ce akwai wasu karin akwatuna gawa biyu da tafe Yau dai ta kasance ranar farin ciki a Israila da yankunan Falasdinawa inda aka maida Israilawa 20 da Hamas ta yi grakuwa da su gida da kuma fursonin da aka kwashe a cikin motocin bas domin a maida yankunan Falasdinawa.

    Wani Bafalasdine ya ce bai taba tunanin zai koma gida ba, kuma wannan shi ne karon farko da yake ganin sararin samniya ba tare da katanga ba.

  5. 'Kimamin mutum 300,000 ne suka tserer daga Sudan ta Kudu'

    Sudan ta Kudu

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane dubu dari uku ne suka tsere daga Sudan ta Kudu a bana kadai, saboda karuwar tashin hankali.

    Hukumar kare hakkin bil'adama ta MDD ta ce al'ummomin da suka rasa matsugunansu sun yi gudun hijira zuwa kasashe makwabta, wadanda a yanzu sun tsugunar da 'yan gudun hijira sama da miliyan biyu.

    Wakilin BBC ya ce rahoton baya baya nan na hukumar kare hakkin bildama na MDD ya ce tashin tashin da ya barke ya fi shafar mata.

    Kasar Sudan ta Kudu dai na fama da tashin hankalin da ba a taba ganin irinsa ba tun bayan da aka kawo karshen yakin basasar kasar shekaru takwas da suka gabata.

  6. An sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza

    Shugaban Amurka Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaban Amurka Donald Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump tare da shugabannin Masar da Qatar da Turkiyya sun sanya hannu kan kashi na farko na yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza a wurin shaƙatawa na Sharm el Sheikh da ke Masar.

    An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a gaban shugabannin ƙasashen duniya fiye da 20 wadanda suka halarci taron.

    Yarjejeniyar ta kawo ƙarshen yaƙin Gaza, wanda hakan ya zamo abu mai matuƙar tarihi ga shugaba Trump da kuma shugabannin ƙasashen yankin.

    Yanzu kuma za a ci gaba da tattaunawa kan yadda za a aiwatar da sauran sharuɗɗan da ke ke ƙunshe a yarjejeniyar.

    Masu sanya ido na ganin cewa aikin sake ginan yankin Gaza - wanda aka rushe kusan ɗaukacinsa a yaƙin da aka yi na shekara biyu, zai zama babban ƙalubale.

    Wannan ce ranar da kowa ke jira -Trump

    A lokacin da Donald Trump ya yi jawabi, ya bayyana yau a matsayin "ranar da kowa ya yi ta hanƙoro da addu'ar ganin zuwan ta."

    Shugaban na Amurka ya ce "wannan yarjejeniya mai matuƙar tarihi" wadda gungun shugabannin duniya suka sanya wa hannu, na nuna cewa "addu'ar miliyoyin al'umma ta karɓu".

    Daga nan sai ya ce shugabannin sun samu nasarar tabbatar da "zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya", sannan ya taya kowa murna.

    Haka nan Trump ya gode wa shugaban Masar Abdul Fattah al Sisi bisa karrama shi da lambar girmamawa ta ƙasar ta 'Order of the Nile'.

  7. Yadda zaman jin bahasi ya wakana da Sheikh Lawan Triumph a Kano

    Lawal Triumph

    Asalin hoton, Lawal Triumph/Facebook

    Kwamitin shura na jihar Kano ya gudanar da wani zaman jin bahasi da ɗaya daga cikin sanannun malaman addinin Musulunci na jihar, Lawan Triump bayan zargin da aka yi masa na yin kalaman da ba su dace ba a lokacin zaman karatu.

    Sheikh Lawan ya ce yana kira ga waɗanda suka yi ta yaɗa maganganun da su riƙa sauraron karatu cikakke kafin su yanke hukunci.

    "Waɗanda ransu ya ɓaci, ina so su fahimci abin da nake nufi, kuma ina musu nasihi da cewa idan suna so su yi wa mutum hukunci, to su ji zancensa cikakke kamar yadda Allah ya yi umarni.

    "Waɗanda suka yi aikin jefa mutane cikin damuwa kuma, na san akwai waɗanda ba da gangan suka yi ba, ina roƙon allah ya yafe mana baki ɗaya, akwai kuma waɗanda na san da wasu manufofi suka yi, idan suna da rabon shiriya, Allah ya shirya su."

    Ya ce daga cikin zaluncin da za a yi wa mutum akwai "ɗaukar abin da ya fi so a ce ya muzanta shi. Allah ya sani babu abin da na fi so kamar zaman lafiya da kwanciyar hankali da haɓakar tattalin arziki, kuma babu wanda yake cin moriyar zaman lafiya kamar malami saboda sai da zaman lafiya ne al’umma za su fahimci karatu."

    A ƙarshe ya yi addu'ar Allah ya saka wa "gwamna da alheri, Allah ya yi wa wannan kwamitin jagora, ya ba su ikon sauke wannan nauyin. Allah ya sa da jagororancinsu da shawarwarin da za su riƙa ba gwamnati al’umaran Kano su yi kyau."

  8. Kwamishinonin Enugu sun koma APC

    Wasu kwamishohin Enugu da suka koma APC

    Asalin hoton, Dan Nwomeh/X

    Wasu kwamishinonin gwamnatin jihar Enugu sun koma jam'iyyar APC yayin da ake sa ran wamnan jihar Peter Mbah zai koma jam'iyyar daga PDP.

    Cikin wani bidiyo da mataimakin gwamnan na musamman kan kafofin ya da labara, Dan Nwomeh, ya wallafa a shafinsa na X, ya nuna kwamishinonin uku riƙe da tutar APC.

    Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da raɗe-raɗin komawar gwamnan jihar jam'iyyar APC.

  9. Shugaba Trump ya isa Masar don sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

    Trump na sauka daga jirgi

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka donald Trump ya isa birnin Sharm el-Sheikh na ƙasar Masar domin sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

    Taron wanda shugabannin ƙasashen duniya aƙalla 20 za su halarta zai kawo ƙarshen yaƙin a hukumance.

    Trump ya isa Sharm el-Sheikh ne daga Isra'ila inda ya yi jawabi a majaliar dokokin ƙasar.

  10. 'Shugaban Madagascar ya fice daga ƙasar'

    Andry Rajoelina

    Asalin hoton, Reuters

    Rahotanni sun ce shugaban ƙasar Madagascar, Andry Rajoelina, ya fice daga ƙasar, sakamakon matsin lamba da ake yi masa na ya sauka daga mulki.

    Matasan ƙasar sun ɗauki kwanaki suna zanga-zangar neman ya sauka daga mulki.

    Kafofin yada labaran Faransa sun ce an fitar da shugaban daga ƙasar ne a cikin wani jirgin sojin Faransa a jiya Lahadi.

    Yayin da suke cewa an fice da shi ne bayan amincewar shugaba Emmanuel Macron.

    Hukumomin Faransa sun ce ba sa shisshigi a harkokin cikin gida na ƙasar .

    Ƴan adawa a majalisaer dokokin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa za su fara zaman tsige Mista Rajoelina.

  11. Trump ya kama hanyar Masar don halartar taron zaman lafiya

    Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya kama hanyar zuwa Masar domin halaratr taron zaman lafiya.

    Trump zai bikin wanda shugabannin ƙasashen duniya aƙalla 20 za su halarta da nufin sanya hannu kan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin Gaza a hukumance.

    Tun da safiya ne Trump ya Isa Isra'ila, inda ya yi jawabi a majalisar dkokin ƙasar.

    Ya samu rakiyar firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu har zuwa filin jirgin saman Ben Gurion da ke wajen birnin Tel Aviv.

    A yanzu shugaban na Amurka zai isa birnin Sharm el-Sheikh da ke Masar domin halartar taron.

  12. 'Lokaci ya yi da ƙasashen Gabas ta Tsakiya za su daina kashe kuɗi kan makamai'

    Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaba Trump na Amurka ya ce lokaci ya yi da ƙasashen Gabas ta Tsakiya za su daina haifar da makiya da hanyar ƙera makamai.

    Yayin da yake jawabi ga majalisar dokokin Isra'ila, Mista Trump ya ce lokaci ya yi da za su haɗa kai domin ciyar da yankin gaba.

    ''A maimakon ƙera makamai, ya kamata ƙasashen su mayar da hankali wajen kashe kuɗaɗensu wajen gina makarantu da samar da magunguna da haɓaka masana'antu da kuma fannin ƙirƙirarriyar basira ta AI'', in ji shi.

    Ya ƙara da cewa ƙofa a buɗe take ga kowa a yankin domin ciyar da ƙasashen gaba.

    "Har ma Iran, wadda ta haifar da kashe-kashe da yawa a Gabas ta Tsakiya, ƙofa a buɗe take domin aiki tare'', in ji shi.

  13. Isra'ila ta saki Falasɗinawa 1,968 daga gidajen yarinta

    Wasu Falasdinawa da aka saki yau daga gidanjen yarin Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumar kula da gidajen yarin Isra'ila ta sanar da sakin Falasɗinawa 1,968 fursunoni da waɗanda aka tsare, a wani ɓangare na yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Gaza.

    An saki Falasɗinawan da rukuni biyu, na farko daga gidan yarin Ofer zuwa wasu sassan Gaɓar Yamma.

    Rukuni na biyu kuwa an sake ne daga gidan yarin Ketziot da ke Kerem Shalom a kudancin Isra'ila, ɗaya daga cikin hanyoyin shiga Gaza.

    An kai Falasɗinawan Ramallah a Gaɓar Yamma da Khan Younis da ke kudancin Gaza.

  14. Ka amince da ƙasar Falasɗinu: Ɗanmajalisar Isra'ila ya faɗa wa Trump yana tsaka da jawabi

    Danmajalisar Isra'ila

    Asalin hoton, X / Ayman Odeh

    Wani ɗanmajalisar dokokin Isra'ila ya katse Trump a daidai lokacin da yake tsaka da jawabi a majalisar dokokin.

    Ayman Odeh, wanda aka fitar daga zauren jim kaɗan bayan katse jawabin shugaban na Amurka - ya wallafa abin da ya faɗa a lokacin da Trump din ke tsaka da jawabi.

    "Sun fitar da ni ne saboda kawai na zo da wata ƙaramar buƙata, wadda ƙasashen duniya da dama suka amince da ita, wato amincewa da ƙasar Falasɗinu'', kamar yadda ya wallafa a shafin nasa.

    "Amincewa ita ce abin da ya fi: Mutanen ne guda biyu, ba wanda zai shigar wa wani.''

  15. Isra'ila ta cimma abin da take so da taimakon Amurka - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce da taimakon Amurka, Isra'ila ta cimma duk abin da take buƙata a yaƙin Gaza.

    Mista Trump ya ce ba don Amurka ta samu nasarar lalata cibiyoyin nukiliyar Iran a farkon shekarar nan ba, da ba a samu damar cimma wannan yarjejeniya ba.

    "Mun yi duk abin da ya kamata a yankin gabas ta Tsakiya domin kare Isra'ila'', in ji shi.

    Shugaban na Amurka ya ce ''tare da taimakon Amurka, Isdra'ila ta cimma duk ain da take so, don haka yanzu lokacin zaman lafiya ya yi da c gaban yankin Gabas ta Tsakiya.

    Nan gaba ne Mista Trump zai wuce zuwa Masar domin halartar taron zaman lafiyar yankin.

  16. Yau rana ce mai muhimmnaci a Gabas ta Tsakiya - Trump

    Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaba Trump na Amurka ya ce yau rana ce mai cike da muhimmanci ga yankin Gabas ta Tsakiya.

    Yayin da yake jawabi a gaban majalisar dokokin Isra'ila, Mista Trump ya gode wa firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, wanda ya kira "mutum mai cikakken ƙwarin gwiwa".

    Lamarin da ya sa wasu dandaon ƴanmajalisar suka amsa da "Bibi" inkiyar da ake yi wa Netanyahu.

    Haka kuma Shugaba Trump ya gode wa ƙasashen Larabawa da ya ce sun taimaka wajen ''cimma gagarumar nasarar'' kawo ƙarshen yaƙin Gaza.

    A yanzu "Zaman lafiya ya dawo cikin Isra'ila, da kuma ilahirin yankin Gabas ta Tsakiya", a cewar Trump.

  17. 'Netanyahu ba zai halarci taron zaman lafiya a Masar ba'

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ba zai bi Trump zuwa Masar don halartar taron zaman lafiya da za a gudanar a ƙasar ba, kamar yadda ofishinsa ya bayyana.

    Tun da farko fadar shugaban ƙasar Masar ta fitar da sanarwar cewa Netanyahu zai bi Trump domin halartar taron, wanda shugaba Trump da wasu shugabannin ƙasashen duniya kusan 20 za su taru a yau domin sanya hannu kan kawo ƙarshen yaƙin Gaza.

    Sanarwar da ofishin Netanyahun ta fitar ta ce ba zai halarci taron ba ne saboda kusancin taron na bikin shekara-shekara na Yahudawa wato Sukkot.

  18. Yau an kawo ƙarshen yaƙin Gaza - Netanyahu

    Netanyahu da Trump a majalisar dokokin Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce a yau an kawo ƙarshen yaƙin Gaza da aka shekara biyu ana gwabzawa.

    Yayin da yake jawabi a gaban majalisar dokokin ƙasar da Trump ta halarta, Netanyahu ya ce ''A yau ne kalandar Yahudawa ta nuna kawo ƙarshen yaƙin da aka ɗauki shekara biyu ana gwabzawa.''

    Mista Netanyahu ya kuma jinjina wa sojojin Isra'ila da suka rasu a lokacin yaƙin, inda ya ambata sunayen wasu daga cikin waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata.

    "Saboda jajircewar waɗannan gwarazan ne ƙasar mu ta ci gaba da wanzuwa har ya zuwa yanzu... da muka samun zaman lafiya'', a cewar Netanyahu.

  19. Hotunan yadda Falasɗinawa suka haɗu da ƴan'uwansu

    Ƴan'uwa da iyaye da dangi sun rungume ƴan'uwan da aka sako daga gidajen yarin Isra'ila.

    Wani Bafalasɗine da ƴan'uwansa

    Asalin hoton, Reuters

    Rukunin Farko na manyan motoci 38 ɗauke da fursunonin ya isa Ramallah da ke Gaɓar Yamma.

    Wasu dangi sun rungume juna

    Asalin hoton, Reuters

    Ana sa ran sakin Falasɗinawa kusan 2,000 daga gidajen yarin Isra'ila, kamar yadda yarjejeniyar ta tanada

    Wasu fursunoni

    Asalin hoton, Reuters

    Wani mutum ya rungume ƴarsa bayan sako shi

    Asalin hoton, Reuters

  20. Hatsarin mota ya kashe mutum 42 a Afirka ta Kudu

    Motar da ta faɗi

    Asalin hoton, Supplied

    Ƴan Zimbabwe da ƴan Malawi 42 ne suka mutu bayan da motarsa ta yi hatsari a Afirka ta Kudu a kan hanyarsu ta zuwa ƙasashensu.

    Hatsarin ya auku ne ranar Lahadi da daddare yayin da motar ke tsaka da tafiya a kan babban titin N1 a lardin Limpop mai tsaunuka, kamar yadda jami'an sufurin ƙasar suka bayyana.

    Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya miƙa saƙon alhinin rasuwar mutanen da suka haɗa da ƙananan yara bakwai.

    Mista Ramaphosa ya ce wannan bala'i ne da ya shafi duka ƙasashen uku.