Daga Haruna Kakangi da Aisha Babangida da Ibrahim Yusuf Mohammed
Mahaukaciyar guguwa ta kashe aƙalla mutum 20 a Madagascar
Asalin hoton, AFP
Aƙalla mutum 20 ne suka mutu bayan wata guguwa mai ƙarfin gaske ta afkawa ƙasar Madagascar, in ji hukumar kiyaye bala'i a tsibirin na tekun Indiya.
Guguwar mai suna Gezani ta afkawa ƙasar a ranar Talata, inda ta ta yi ɓarna babbar tashar jiragen ruwa na tsibirin.
Ofishin kiyaye bala'o'i na Madagascar ya ce an samu "matuƙar tashin hankali" - yana mai ba da rahoton cewa gidaje sun rushe a yankin da abin ya shafa, inda aka gano gawarwakin.
Unguwannin sun faɗa cikin duhu yayin da turakun wutar lantarki suka karye.
Mai yiyuwa ne guguwar ta kasance ɗaya daga cikin mafi muni da aka taɓa samu a yankin da kewayen birnin a zamanin tauraron ɗan adam, a cewar cibiyar hasashen guguwa ta CMRS da tsibirin Reunion na Faransa, wanda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
Amurka ta sake buɗe sararin samaniyar kan iyakar Texas
Asalin hoton, Federal Aviation Administration
Ma'aikatar tsaron Amurka ta "dauki mataki" na kakkaɓe jiragen sama marasa matuƙa da ta ce wani ɓangare ne na wani kutse da aka yi birnin da ke El Paso, Texas, wanda ke kan iyaka da Mexico, kuma ta ɗage umarnin rufe sararin samaniyar yankin na tsawon kwanaki 10.
"An kawar da barazanar, kuma babu haɗari ga tashi ko saukar jiragen da ke jigilar mutane a yankin," Sakataren Sufuri Sean Duffy ya wallafa a shafinsa na X.
A daren ranar Talata ba zato ba tsammani, hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta tarayya (FAA) ta ba da umarnin dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin sama na El Paso har zuwa ranar 20 ga watan Fabrairu, abin da ya haifar da kaɗuwa da ruɗani a tsakanin mazauna yankin da kuma zaɓaɓɓun shugabanni.
Hukumar ta ce a safiyar ranar Laraba an dage dakatarwar kuma jirage za su iya ci gaba da tashi.
An yanke wa mutum 12 hukuncin kisa kan kashe ɗan majalisa a Sri Lanka
Asalin hoton, Getty Images
Wata kotu a Sri Lanka ta yanke wa wasu mutum 12 hukuncin kisa kan kisan taron dangi da suka yi wa wani ɗan majalisa da jami'in tsaronsa lokacin zanga-zangar kin jinin gwamnati a watan Mayun, 2022.
Wasu fusatattun mutane ne suka kashe Amarakeerthi Athukorala da mai kula da shi, bayan da ya yi harbi kan masu zanga-zanga waɗanda ke tare motarsa daga wucewa a Colombo, babban birnin ƙasar.
Haka kuma, an dakatar da aiwatar da hukunci ga wasu mutum huɗu tare da wanke 23 daga zargin.
Ɓarkewar zanga-zanga kan ƙarancin abinci da man fetur a 2022 ta tilasta wa shugaban Sri Lanka Gotabaya Rajapaksa da firaminista Mahindra wanda ɗan uwansa ne yin murabus.
An ɗaure wani Ba'Amurke da yake yi wa China leƙen asiri
Asalin hoton, EPA
Wata kotu a Jamus ta
yanke wa wani Ba'Amurke hukuncin ɗaurin shekaru biyu da watanni takwas a gidan
yari saboda bai wa China wasu muhimman bayanan sirri na soji.
Wanda ake ƙarar, mai
suna Martin D, ya samu bayanan sirri ne a yayin da yake aiki a matsayin ɗan
kwangila a wani sansanin sojin Amurka da ke Jamus.
An kama shi ne a watan
Nuwamban 2024, inda aka tuhume shi da yi wa ƙasashen waje aiki a matsayin
jami'in leƙen asiri.
Firaministan Canada ya ce ya kaɗu kan kisan mutum tara a wata makaranta
Asalin hoton, Reuters
Firaministan Canada
Mark Carney ya ce ya kaɗu sosai da mutuwar mutum tara waɗanda aka kashe a wani
harbin kan mai uwa da wabi da aka yi a Lardin British Colombia da ke yammacin
ƙasar a jiya Talata.
Ya bayyana harin a
matsayin tsantsar zalunci, inda ya ce ya dakatar da shirinsa na yin tafiya zuwa
Munich domin wani taron tsaro a yau.
An harbe mutum bakwai
a wata makaranta da ke ƙauyen Tumbler Ridge, yayin da kuma aka gano wasu
gawarwaki biyu a wani gida da ke kusa da wajen.
Aƙalla mutum ashirin
da biyar sun samu raunuka, kuma an gano gawar wanda ake zargi da harbin a cikin
makarantar, ɗauke da raunukan da ake ganin shi ya yi wa kansa.
Ƴansanda sun ce zuwa yanzu ba su gano alaƙar
maharin da makarantar ba.
Gwamnatin Najeriya ta miƙa saƙon taya murna ga gwamnati da al'ummar Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da cika shekaru 47 da juyin juya halin Musulunci.
Wata sanarwa da kakakin ma'aikatar harkokin wajen Najeriya, Kimiebi Ebienfa ya fitar, ta ce bikin mai cike da tarihi ya kasance wani muhimmin lokaci a tarihin Iran na zamani, wanda ke nuni da yadda ƙasar ta jajirce wajen tabbatar da ƴancin kai da ci gaban ƙasa.
Sanarwar ta ƙara da cewa Najeriya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun kwashe shekara hamsin suna hulɗar diflomasiya wadda aka gina kan tushen mutunta juna, da kyakkyawar zamantakewa.
''A wannan muhimmin lokaci, Najeriya ta jaddada aniyarta na ƙara ƙarfafa dangantakar da ke tsakaninta da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ta hanyar inganta tattaunawar diflomasiyya da haɗin gwiwar moriyar juna.'' in ji sanarwar
Birtaniya za ta ƙara yawan sojojinta da ke Norway don magance barazanar Rasha
Asalin hoton, PA Media
Gwamnatin
Birtaniya ta yi alƙawarin ƙara yawan sojojinta da ke ƙasar Norway nan da shekaru uku masu
zuwa, a wani mataki na yaƙi da barazanar Rasha a yankin.
Sakataren tsaron ƙasar
John Healey ya ce adadin sojojin Birtaniya da ke ƙasar Norway zai ƙaru daga
1,000 zuwa 2,000.
A cewar Healey,
Moscow tana "sake karfafa rundunar sojinta da ke yankin, gami da sake buɗe
tsoffin sansanonin yaƙin cacar baka".
Ana nuna irin
wannan damuwar a duk faɗin Turai. Tun bayan da Rasha ta ƙaddamar da cikakken
mamayar ƙasar Ukraine shekaru huɗu da suka gabata.
Shugaba Tinubu ya zaɓi sabon shugaban hukumar Alhazai ta Najeriya
Asalin hoton, Presidency
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya zaɓi Amb. Ismail Abba Yusuf a matsayin sabon shugaban hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON).
Wata sanarwa da ta fito daga mai bai wa shugaban shawara kan yaɗa labarai da dabaru Bayo Onanuga, ta ce a yau Laraba ne shugaba Tinubu ya aike da wasika zuwa ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, inda ya bukaci a gaggauta tabbatar da Ambasada Yusuf ya maye gurbin Farfesa Abdullahi Usman, wanda ya yi murabus a farkon wannan makon, bayan shafe kimanin watanni 14 yana kan muƙamin.
Ambasada Yusuf gogaggen jami'in diflomasiyya ne wanda ya taɓa zama jakadan Najeriya na musamman kuma mai cikakken iko a ƙasar Turkiyya daga 2021 zuwa 2024.
Ana gangamin murnar ranar juyin juya-hali a Iran
Kafar yaɗa labarai ta
Iran na nunawa kai tsaye a talabijin, gangamin da magoya
bayan gwamnati ke yi domin murnar ranar juyin juya hali na musulunci a Iran,
bayan hukumomi a kasar sun buƙaci alumma su nuna wa gwamnati goyon baya.
A wani jawabi da ya yi
a babban filin taro na Tehran, Shugaban ƙasar Masoud Pezeshkian ya yi Allawadai
da makiyan Iran waɗanda suka yi kokarin kifar da gwamnatinsa, sai dai kuma ya
bai wa ƴan ƙasar haƙuri a inda gwamnati ta gaza.
Ya ce ƙasar mu Iran ba
za ta bayar da kai bori ya hau ba, kuma ƙasar mu Iran ba za ta ja baya ba a
yayin da ake zalunci.
Gangamin na zuwa ne
wata guda bayan daƙile masu zanga zanga da ƙarfin tsiya, da jami'an tsaro suka
yi a zanga zangar gama gari ta ƙin jinin gwamnati, inda aka kashe dubban
mutane.
Firaministan Isra'ila zai gana da Trump
Asalin hoton, Getty Images
Nan gaba a yau ne Firaministan Isra'ila zai gana da shugaba Trump a fadar White House domin wata
tattaunawa da ake sa ran za ta mayar da hankali ne kan Iran.
Ana ganin Mista
Netanyahu zai buƙaci Amurka ta dage kan cewa wajibi ne Tehran ta dakatar da
shirin ta na makamai masu linzami, da kuma goyon bayan da ta ke bai wa
ƙungiyoyi kamar Hezbollah da Hamas.
Tehran ta sha nanata
cewa abin da za ta yarda a tattauna a kai kawai shi ne shirinta na nukiliya.
Ana ganin Iran ɗin ta
shirya rage burin ta a shirin nukiliyar domin ta samu sassaucin takunkumai.
An
samu rahotanni a kafafen yaɗa labaran Isra'ila da ke cewa Isra'ila ta samu
bayanan sirri cewa Iran na sake gina rumbunan makamanta masu linzami.
Manoma da makiyaya sun ƙulla yarjejeniyar sulhu a Filato
Asalin hoton, Getty Images
Manoma da makiyaya a cikin al’ummomi shida na karkara a yankunan Bokkos da Riyom da ke Jihar Filato sun sa hannu a yarjejeniyoyi 25 na sulhu da nufin dawo da zaman lafiya da kawo ƙarshen kashe-kashen da ake yi a yankunan da kuma gina amana bayan shafe shekaru ana fama da rikici.
An cimma yarjejeniyoyin tsakanin maza da mata daga al’ummomin Sha da Bum da Sopp, inda rikice-rikicen da ake fama ta su suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da lalata dukiyoyi kamar yadda gidan talabijin na Channels na ruwaito.
Waɗannan yarjejeniyoyi sun biyo bayan jerin tattaunawa da cibiyar ayyukan sulhu ta IFIT suka shirya, a matsayin wani yunƙuri na karfafa haɗin kai a cikin al’umma da nemo hanyoyin dindindin na magance tashin hankali a yankunan karkara da ke fama da rikici.
Babban shugaban gunduma daga Bokkos, Lazaros David, ya bayyana tsarin sulhun a matsayin mai dacewa da muhimmanci, la’akari da irin ƙalubalen da al’ummomin ke fuskanta.
Najeriya za ta tura dakaru na musamman zuwa jihohin Kwara da Neja
Asalin hoton, Getty Images
Babban hafsan dakarun Najeriya, Janar Olufemi Oluyede ya bayyana cewa Hedikwatar Tsaro za ta tura wani Rukunin Dakaru na Musamman, mai suna ‘Savanah Shield’, domin yaƙar masu iƙirarin jihadi a tsakiyar jihohin Kwara da Neja.
A wani jawabi ga ‘yan majalisa a Abuja ranar Talata, Janar Oluyede ya ce rundunar tana yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa Najeriya ta kasance ƙasa mai zaman lafiya ga ‘yan kasa da masu zuba jari.
“Muna kokarin samar da hanyoyi daban-daban domin shawo kan waɗannan ƙalubale na tsaro da ke addabar ƙasar. An naɗa kwamandan dakarun na musamman kuma muna kokarin samun kayayyakin domin mamaye wannan yanki,” in ji shi.
Sai dai babban hafsan sojin ya bayyana cewa ba zai yi wu rundunar ta iya mamaye duk faɗin Najeriya ba.
Don haka, ya buƙaci a ƙarfafa ayyukan hukumomi kamar ’Yan sanda da Hukumar Tsaro da Kula da Fararen Hula (NSCDC) domin aikin hadin gwiwa da sojoji.
Ba a dai yi wani ƙarin bayani ba kan wannan aikin sojin, amma alamu na nuna cewa sojojin za su gudanar da ayyukansu domin daƙile yiwuwar hare-hare, bayan sake bazuwar ayyukan ‘yanbindiga zuwa kudancin Najeriya, bayan aikata ɓarna da sace mutane a Arewa maso Gabas na tsawon lokaci.
Hare-haren da aka kai kan al’ummomi a Kwara sun nuna taɓarɓarewar matsalar tsaro a Najeriya da yaƙin da sojoji ke yi tun tsawon lokaci kan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da ‘yan ta’adda da masu iƙirarin jihadi.
A makon da ya gabata, gwamnatin Kogi ta sanar da rufe wasu kasuwanni da tashoshin mota a sassan jihar a matsayin matakin tsaro don dakile ayyukan ƴanbindiga.
Gwamnatin jihar ta kuma rufe makarantu a wasu wurare domin hana yiwuwar hare-hare.
Kogi na makwabtaka da jihar Kwara, inda sama da mutum 100 suka rasa rayukansu a Woro da wasu al’ummomi sakamakon farmakin masu iƙirarin jihadi.
Najeriya na ci gaba da yaƙi da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da dama, yayin da Amurka ta kai hare-haren kan ‘yanbindiga a ƙasar.
Sojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a Borno
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun daƙile wani hari da mayaƙan ISWAP suka kai kan sansanin sojin Auno a Borno, sannan suka kaddamar da harin ramuwar gayya wacce ta lalata kayan yaƙi da dabarun ‘yan ta’addan.
Rundunar ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar wa manema labarai.
Sanarwar ta ce "A daren 5 ga Fabrairun 2026, mayaƙan ISWAP sun kai hari kan wani sansanin sojoji amma Sojojin sun dakile harin cikin tsari da ƙwarewa."
Bayan daƙile harin, a ranar 9 ga Fabrairu, sojojin tare da hadin gwiwar dakarun sa kai ta CJTF suka ƙaddamar da samame ta ramuwar gayya a kan mayaƙan ISWAP ɗin a layin Komala da ke ƙaramar hukumar Konduga.
A yayin samamen, sojojin sun kashe mayaƙan Iswap 16, yayin da sauran suka tsere da raunuka masu tsanani.
Haka kuma, sojojin sun ƙwato fiye da kekuna 20 da kayayyakin yaƙi da dama da makamai da sauran kayan amfani na ‘yan ta’adda.
Sojojin sun kuma kama wasu mutane da ake zargin suna tura ƙwayoyi da sauran kayan aiki don taimakawa ayyukan ISWAP a yankin Bukarti.
UAE ta musanta samar da makamai ga dakarun RSF a Sudan
Asalin hoton, Getty Images
Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta musanta zarge-zargen da ake yi cewa ta samar tare da taimakawa wajen jigilar makamai da kayan yaƙi ga dakarun RSF ta Sudan.
A cikin wata sanarwa, UAE ta ce ba ta tura “kowanne makami ko harsashi ko jirgi mara matuƙi ko wasu kayan yaƙi ga RSF ba."
Sanarwar ta biyo bayan rahotannin jaridu da ke zargin cewa UAE ta taimaka wajen horar da mayaƙan RSF da samar musu da tallafin dabaru da kayan aiki.
UAE ta sake jaddada cewa ba ta cikin rikicin Sudan kuma ba ta shiga wani faɗa ba.
Yaƙin basasar Sudan dai ya fara ne a watan Afrilun 2023 sakamakon rikici tsakanin Sojojin Sudan (SAF) da RSF.
Har yanzu ba a samu nasarar kawo zaman lafiya mai ɗorewa ba a yunƙurin samar da sulhu da Amurka da Saudiyya ke jagoranta a Jeddah.
Gwamnatin Habasha na shirin tura sojoji zuwa arewacin ƙasar da ke fama da rikici
Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni daga Habasha na nuni da cewa gwamnatin ƙasar na shirya sojoji daga yankunan rikici na Amhara da Oromia domin tura su zuwa arewacin kasar, watakila yankin Tigray da kuma kan iyakar Afar.
Wata jam’iyyar adawa a yankin Amhara ta yi zargin cewa sojojin gwamnati na janyewa daga yankin, tana gargadin cewa hakan na iya haifar da rashin tsaro idan kungiyar FANO ta yi yunƙurin kwace garuruwa.
A ɗaya ɓangaren kuma, ƙungiyar TPLF ta zargi gwamnatin tarayya da shirin sake ƙaddamar da wani sabon yaki a Tigray.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar 9 ga Fabrairu 2026, ƙungiyar ta yi kira ga ƙasashen duniya su matsa wa gwamnatin Habasha lamba domin dakatar da shirye-shiryen soja tare da hana sake ɓarkewar rikici.
Majalisar dokokin Amurka ta gabatar da ƙuduri kan zargin musguna wa Kiristoci a Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
Kwamitin majalisar wakilan Amurka ya gabatar da wani ƙudiri na neman ɗaukar mataki kan zargin musguna wa kiristoci da ayyukan wasu ƙungiyoyin ƴan bindiga a Najeriya.
Ƙudirin mai suna taken 'Nigeria Religious Freedom and Accountability Act' ya buƙaci Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya riƙa gabatar wa kwamitocin harkokin wajen majalisa rahoto duk shekara kan kokarin magance musguna wa Kiristoci a Najeriya.
Haka kuma ƙudirin ya buƙaci a duba yiwuwar ayyana wasu kungiyoyin da ake dangantawa da "makiyaya Fulani a matsayin kungiyoyin ta’addanci na ƙasashen waje."
Bugu da ƙari, ƙudirin ya kuma buƙaci a sanya takunkumi kan wasu mutanen da ake zargi suna da alaƙa da cusguna wa kiristoci.
Ana buƙatar ƙudirin ya samu amincewar majalisun dokoki biyu kafin ya zama doka.
Matakin na zuwa ne bayan Amurka ta sanar da shirin tura sojoji 200 zuwa Najeriya domin horas da sojojin ƙasar kan yaƙi da masu tayar da ƙayar baya.
Ana sa ran za su isa Najeriya cikin makonni masu zuwa, inda za su haɗu da wata ƙaramar tawaga da aka riga aka tura tun farko.
Kakakin rundunar sojin Najeriya, Janar Samaila Uba, ya tabbatar da batun ga BBC, yana cewa hakan ya biyo bayan gayyata da buƙatar gwamnatin Najeriya, kuma ya dace da shawarwarin kwamitin hadin gwiwar Amurka da Najeriya.
Trump ya yi barazanar ɗaukar mataki mai tsauri kan Iran kan shirin nukiliya
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ƙasarsa zata ɗauki wani mataki mai tsauri idan har Iran bata cimma yarjejeniya akan shirinta na nukiliya ba.
Cikin wata hira da aka yi dashi kafin tattaunawar da ya yi da ya yi da firaiminstan Isra'ila Benjamin Netanyahu a Washington, Trump ya ce ya zaci gwamnatin Iran na son a cimma yarjejeniyar ne.
Tun da farko ya ce yana duba yiwuwar aikewa da jirgi na biyu zuwa Gabas ta tsakiya.
Ba dai a sanar da lokacin da za a sake tattaunawar gaba ba tsakanin Amurka da Iran.
Za a samu faɗuwar damina da wuri - NIMET
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya, NiMet, ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama ko faɗuwar damina da wuri a jihohin Kano da Neja da Ribas da kuma wasu jihohi goma sha biyu na ƙasar.
Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, SAN, ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Talata yayin ƙaddamar da hasashen yanayi na shekara ta 2026 da NiMet ta fitar.
Ya gargaɗi manoma da kada su yi gaggawar yin shuka, inda ya ce duk da an fara samun ruwan sama a wasu sassan ƙasar, kakar damina ta gaskiya ba ta fara ba.
Ya ce an samu ruwan sama tun da wuri a wasu jihohi kamar Legas da Ribas da Bayelsa da sauransu, amma har yanzu ba a shiga ainihin lokacin damina ba. Ya kuma yi nuni da cewa ana sa ran yanayi mai tsanani tsakanin watan Maris da Mayu na bana.
Rahoton Nimet ya nuna cewa za a samu ruwan sama mai yawa a sassan kudancin ƙasar a wannan shekarar, sannan ya yi hasashen fara damina da wuri da kuma ƙarewarta da wuri ko a makare, tare da yiwuwar yanayi mai tsananin a 2026.
Rahoton ya ce ana sa ran fara damina da wuri a jihohin Bayelsa da Ribas da Akwa Ibom da Cross River da Benue da Kogi da Nasarawa da Oyo, da kuma wasu sassan Kebbi da Neja da Jigawa da Katsina da Kano da Adamawa da Taraba. Amma ana sa ran fara damina a makare a jihar Borno.
Cikakken bayani daga rahoton ya kuma nuna cewa ana sa ran damina za ta ƙare da wuri fiye da yadda aka saba a wasu sassan jihohin Ogun da Osun da Ondo da Imo da Ribas da Akwa Ibom da Kogi da Neja.
Za a iya kama ni nan ba da daɗewa ba - El-Rufa'i
Asalin hoton, KDGOV
Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai kuma jigo a jam'iyyar hamayya ta ADC ya yi zargin cewa dole ne ta sa wasu yan siyasa ke sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki ko kuma ci gaba da zama a cikinta.
Tsohon gwamnan na yin wannan zargi ne yayin da hada-hadar siyasa ke neman ɗaukar harama gabanin babban zaɓen ƙasar na shekara ta 2027.
A baya-bayan nan El-Rufa'i ya tsananta sukar da yake yi wa gwamnatin shugaban Najeriya Bola Tinubu da kuma jam'iyyar APC mai mulki, wadda a ƙarƙashinta ne ya yi gwamnan jihar Kaduna na shekara takwas.
A wata tattaunawa da BBC, El-Rufa'i ya ce duk da cewa ba a riga an kama shi ba, amma an kama na kusa da shi, kuma yana tunanin za a iya zuwa kansa nan ba da daɗewa ba.
“An kama mutum wajen guda huɗu waɗanda muka yi aiki da su a Kaduna, saboda haka ni ma lokaci ne, ni ma za a neme ni,” in ji El-Rufa'i a tattaunawar tasa da BBC.
A baya-bayan nan kame da kuma shari'ar da ake yi wa tsohon ministan shari'a na Najeriya, Abubakar Malami sun ɗauki hankali, inda har yanzu yake riƙe a hannun hukuma.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar EFCC ta zargi Malami da laifukan da suka haɗa da amfani da muƙami ba bisa ƙa'ida da kuma safarar haramtattun kuɗade.
Haka nan daga baya an sake kama shi inda hukumomin ƙasar ke tuhumar sa da ayyukan tallafa wa ta'addanci.
Malami, wanda ake kallo a matsayin jigo a tafiyar ƴan adawar shugaba Bola Tinubu a Najeriya ya musanta zarge-zargen.
Ƙasashe 10 da suka fi fama da cin hanci da rashawa a duniya
Asalin hoton, Getty Images
Cin hanci da rashawa gagarumar matsala ce da ke addabar ƙasashen duniya tare da haifar da matsalolin tattalin arziki.
Ƙasashen duniya da dama na fama da matsalar ta cin hanci da rashawa, wani abu da ke kawo tarnaƙi ga ci gaban ƙasashen.
Gwamnatocin ƙasashe a matakai daban-daban kan kafa hukumomin yaƙi da matsalar, a wani mataki da kawar ko rage matsalar baki ɗaya.
Ƙungiyar Transperancy International mai yaƙi da cin hanci da rashawa a duniya ta ce duk da ci gaban da aka samu a yaƙi da cin hanci da rashawa a duniya, matsalar ta ci gaba da kasancewa babbar barazana ga ci gaban ƙasashen duniya.
A rahotonta na shekara-shekara kan alƙaluman cin hanci a duniya, 'Corruption Perceptions Index' (CPI) ƙungiyar ta fitar da jerin matsayin da kowace ƙasa ke kai a yaƙi da matsalar cin hanci a shekarar 2025.
Ana tantance matsayin rashawa a kowace ƙasa ne ta hanyar la'akari da makin ta suka samu, daga 0 zuwa 100.