Ƙasashe 10 da suka fi fama da cin hanci da rashawa a duniya

Asalin hoton, Getty Images
Cin hanci da rashawa gagarumar matsala ce da ke addabar ƙasashen duniya tare da haifar da matsalolin tattalin arziki.
Ƙasashen duniya da dama na fama da matsalar ta cin hanci da rashawa, wani abu da ke kawo tarnaƙi ga ci gaban ƙasashen.
Gwamnatocin ƙasashe a matakai daban-daban kan kafa hukumomin yaƙi da matsalar, a wani mataki da kawar ko rage matsalar baki ɗaya.
Ƙungiyar Transperancy International mai yaƙi da cin hanci da rashawa a duniya ta ce duk da ci gaban da aka samu a yaƙi da cin hanci da rashawa a duniya, matsalar ta ci gaba da kasancewa babbar barazana ga ci gaban ƙasashen duniya.
A rahotonta na shekara-shekara kan alƙaluman cin hanci a duniya, 'Corruption Perceptions Index' (CPI) ƙungiyar ta fitar da jerin matsayin da kowace ƙasa ke kai a yaƙi da matsalar cin hanci a shekarar 2025.
Ana tantance matsayin rashawa a kowace ƙasa ne ta hanyar la'akari da makin ta suka samu, daga 0 zuwa 100.
Maki 0 na nufin ƙasa na cikin matsanancin rashawa, yayin da maki 100 ke nufin ba ta da matsalar rashawa.
Transperancy International ta ɗora alhakin ƙaruwar cin hancin a wasu ƙasashen kan rashin ɗaukar matakan da suka dace daga gwamnatocin ƙasashen.
A cikin rahoton nata Tranperancy International ta lissafa matsayin yaƙi da rashawa a ƙasashen duniya 182.
Kan haka ne muka duba ƙasashe 10 da rahoton ya nuna su ne kan gaba wajen fuskantar matsalar cin hanci da rashawa.
10. Koriya ta Arewa
Koriya ta Arewa ce ƙasa ta 10 cikin ƙasashen da cun hanci da rashawa ya yi katutu, kamar yadda rahoton CPI na 2025 ya nuna.
Ƙasar - wadda ke yankin Asiya - ta yi iyaka da ƙasashen China da Rasha da kuma Koriya ta Kudu.
Asusun bayar da lamuni na Duniya, IMF ya yi kiyasin cewa a 2025 arzikin da ƙasar ke samu a cikin gida ya kai dala tiriliyan 1.86 a 2025.
Koriya ta Kudu na fama da matsalolin tattalin arziki sakamakon ɗimbin takunkuman ƙasashen duniya da yawan kashe kuɗaɗen ƙasar a fannin soji.
Wasu bayanai na nuna cewa ƙasar na kashe kusan kashi 33 na arzikinta a fannin sojin ƙasar.
9. Siriya
Siriya ce ƙasa ta tara cikin jerin ƙasashen da suka fi fama da matsalar cin hanci da rashawa a duniya, kamar yadda rahoton CPI na 2025 ya nuna.
Siriya - wadda ke yankin Gabas ta Tsakiya - ta kwashe shekaru da dama tana fama da rikice-rikicen siyasa da na ƙungiyoyin ƴanbindiga.
Babbar hanyar samun kuɗin shigar ƙasar shi ne noma, wanda ya fuskanci koma-bayan tun bayan fara yaƙin basasar ƙasar a 2011.
Hasashen IMF ya nuna cewa arzikin cikin gida da Siriya ta samu a 2023 ya kai dala biliyan 19.99, wani abu da ke nuna mummunan koma-bayan tattalin arzikin da ƙasar ta samu tun bayan faran yaƙin basasar.
8. Nicaragua

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasar Nicaragua - wadda ke yankin Tsakiyar Amurka - ta kasance ta bakwai cikin ƙasashen duniya da suka fi fama da matsalar cin hanci da rashawa.
A shekarar 2025 an yi hasashen cewa ƙarfin tattalin arzikin ƙasar zai ƙaru zuwa daga biliyan 17 zuwa dala biliyan 20.69, sakamakon ci gaban da aka samu a fannin gine-gine.
Noma da kiwo ne manyan abubuwan da ƙasar ta dogara da su wajen samun ku,ɗin shiga.
Ƙasar kan fitar da gahawa da shanu da zinare da kuma sikar zuwa ƙasashen waje.
7. Sudan
Ƙasar Sudan - wadda ke fama da yaƙin basasa - ta takasance bakwai cikin jerin ƙasashen duniya da cin hanci da rashawa ke addaba a cewar rahoton CPI.
Tattalin arzikin Sudan ya fuskanci mummunan koma-baya tun bayan fara yaƙin basasar ƙasar a 2023.
Ƙasar - wadda ke yankin tsakiyar Afirka - na fuskantar mummunan hauhawar farashi da faɗuwar darajar kuɗin ƙasar.
Fitar da mai da haƙar ma'adinai da fannin noma su ne manyan hanyoyin samun ku,ɗin shigar ƙasar, to sai dai sun fuskanci koma-baya tun bayan fara yaƙi basasar ƙasar.
6. Eritrea
Eritrea ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen duniya mafiya ƙarancin ci gaba.
Ƙasar na yankin gabashin Afirka, wadda ta yi iyaka da ƙasashen Ethiopia da Sudan da kuma Djibouti.
Rahoton Transperancy International ya sanya kasar a matsayi na shida cikin jerin ƙasashen da suka fi fama da matsalar cin hanci da rashawa a faɗin duniya.
Tattalin arzikin ƙasar ya dogara ne kan noma da haƙar ma'adinai da kuma tallafi daga ƙasashen duniya.
5. Libya

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasar Libya - wadda ke yankin arewacin Afirka - ta kasance cikin rikice-rikice tun lokacin jyin-juya halin ƙasashen Larabawa na 2011.
Rahoton CPI na 2025 ya saka ƙasar matsayi na biyar da aka fi samun matsalar cin hanci da rashawa.
Libya na daga cikin ƙasashen Afirka da suke da arzikin mai, to amma rikice-rikicen siyasa da shugabanci sun sa ƙasar ta faɗa matsin tattalin arziki.
4. Yemen
Yemen - wadda ke yankin gabas ta Tsakiya - na daga cikin ƙasashen da ke fama da rikece-rikicen ƙungiyoyin ƴanbindiga.
Rahoton CPI na 2025 ya saka ƙasar matsayi na huɗu cikin ƙasashen da suka fi fama da cin hanci da rashawa.
Tattalin arzikin Yemen na fama da matsi sakamakon hauhawar farashin, wanda aka ƙiyasta zai iya ƙaruwa da kashi 18.5 cikin 100 a 2026.
Ƙasar ta dogara da fannin noma da kuma tallafin jinƙai da take samu da ƙungiyoyi da ƙasashen duniya.
3. Venezuela

Asalin hoton, Getty Images
Venezuela ƙasa ce da ke yankin kudancin Amurka mai ɗimbin arzikin man fetur maƙale a ƙarƙashin ƙasa.
Sai dai rashin tsarin shugabanci mai kyau ya jefa ƙasar cikin matsin tattalin arziki.
Rahoton CPI 2025 ya sanya ƙasar matsayi na uku inda aka fi fama da matsalar cikin hanci da rashawa.
Ƙasar ta yi ƙaurin-suna a harƙar safarar miyagun ƙwayoyi da ayyukan ƙungiyoyin yan daba.
A baya-bayan nan sojojin Amurka suka kama shugaban ƙasar, Nicolas Maduro kan zargin safarar ƙwayoyi da makamai.
2. Somaliya
Ƙasar Somaliya da ke yankin gabashin Afirka ce ta biyu a wannan jeri.
Somaliya na fama da ayyukan ƙungiyoyin ƴan bindiga masu iƙirarin jihadi.
Ƙasar - wadda galibi ta dogara da fannin noma - ta yi hasashen tara arzikin cikin gida da ya kai dala biliyan 11.68 – dala biliyan 13.89 tsakanin 2022 zuwa 2025.
Wata ƙiddiiga ta nuna cewa kashi 70 cikin 100 na al'ummar ƙasar na rayuwa cikin matsanancin talauci.
Hanyoyin samun kuɗin shigar Somaliya sun haɗa da kiwon dabbobi da noma da kuma tallafi daga ƙungiyoyi da ƙasashen duniya.
1. Sudan ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images
Sudan ta Kudu ce ƙasa ta farko da aka fi fama da matsalar cin hanci da rashawa a duniya, kamar yadda rahoton CPI ya nuna.
A shekarar 2011 ƙasar ta ɓalle daga cikin Sudan, sakamakon rikice-rikice tsakanin ƙabilun ƙasar kan tattalin arziki .
Tattalin arzikin ƙasar ya dogara kacokan kan mai, wanda ya kai kashi 90 cikin 100 arzikin da ƙasar ke samu a cikin gida.
To sai dai bayan ɓallewa daga Sudan a 2011, ƙasar ta fuskanci koma-baya sakamakon rikice-rikice da ambaliya ruwa da kuma faɗuwar farashin man fetur.
Ƙasashen da babu yawan cin hanci da rashawa
Haka kuma rahoton ya lissafo ƙasashen da ke kan gaba wajen yaƙi da cin hanci da rashawa.
Ƙasashen da rahoton ya ce ba a fiya samun matsalar cin hanci da rashawa ba a duniya sun haɗa da:
- Denmark
- Finland
- Singapre
- New zealand
- Norway
- Sweden
- Switzerland
- Luxembourg
- Netherland
- Jamus
A wane matsayi Najeriya take?
Najeriya ta kare kambinta a matsayin ta 37 a cikin ƙasashen duniya masu fama da matsalar cin hanci da rashawa a duniya a shekarar da ta gabata.
Rahoton shekara ta 2025 daga ƙungiyar yaƙi da rashawa ta Transparency Internation ya nuna cewa a tsawon shekara uku Najeriya ta kasance tana da maki 26 cikin 100.
Hakan ya sanya Najeriya a matsayi na 142 daga cikin ƙasashe 182 da ƙungiyar ta yi nazari a kai.
Rahoton hukumar ya nuna cewa tun daga shekara ta 2022, matsalar cin hanci ta ragu da maki biyu a Najeriya.
A shekarar 2025 Najeriya ta samu maki 26 daidai da makin da ta samu a 2024, sama da abin da ta samu a 2023, lokacin da take da maki 25.











