Abin da ya kamata ku sani kan azumin Ramadan na 2026

.Ramadhani

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

A ranar 18 ko 19 ga watan Fabrairun 2026 ne ake sa ran al'ummar Musulmi a faɗin duniya za su tashi da azumin watan Ramadan na wannan shekara.

Azumi dai na ɗaya daga cikin shika-shikan Musulunci, wanda kuma ibada ne da ake yi a kowace shekara.

Yayin da azumin ke ƙaratowa, ga wasu abubuwa da suka kamata ku sani.

Me ake nufi da azumi?

Azumi na nufin ƙaurace wa ci da sha da kuma jima'i daga fitowar alfijir (lokacin yin sahur) zuwa faɗuwar rana (lokacin buɗe-baki).

Ta yaya ake fara azumi?

Azumi na farawa ne da zarar mutum ya ɗaura niyyar yin azumi a matsayin ibada, sannan ya kauce wa abin da zai karya azumin, tun daga ketowar alfijir zuwa faɗuwar rana.

Sai dai yana wajabta ne ga baligi, mai hankali kuma mai lafiya.

An halasta ajiye azumi ga maras lafiya har sai ya warke da kuma matafiyi.

Waye ya kamata ya yi azumi?

Duk wanda ya cika waɗannan sharuɗa, to yana da damar yin azumi:

  • Wanda ya balaga
  • Mutumin da yake cikin hankalinsa - duk wanda yake da matsalar ƙwakwalwa har ta kai ba ya gane abin da azumi ke nufi, to azumi bai hau kansa ba
  • Dole ne baligin mutum ya yi azumi har sai idan ba shi da lafiya ko kuma yana fama da matsananciyar cuta, kamar tsananin ciwon suga ko kuma kasala da rashin karfin jiki sakamakon tsufa
  • Matafiyin da bai yi tafiya ta tsawon mil 48 ba
  • Mace mai juna biyu ko mai shayarwa muddin ba za ta jigata ba

Me mutum zai yi idan ya kasa yin azumi?

.ramadhan

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Idan mutum yana kokwanto kan ba zai iya yin azumi ba saboda rashin lafiya, to kamata ya ziyarci likitan da ya san addini kuma wanda ya san muhimmancin azumi.

Duk da cewa lafiyar mutum tana da muhimmanci, mu tabbata mun yi azumi in har za mu iya kada mu shantake saboda irin alfanun da ke cikin azumi.

Ga matafiya, duk da cewa an ɗauke musu azumi, idan za su iya yi suna da damar yin haka in har ba za su wahala ba.

Duk da cewa yara ba sa azumi sai shekarunsu sun kai, amma a yi koƙarin ƙarfafa musu gwiwar yin azumi tun suna yara idan za su iya, kuma in har ba zai shafi lafiya ko karatunsu ba.

A muhallin da ake cin abinci tare lokacin Sahur da kuma buɗe-baki da kuma yin sallar Asham tare (a gida ga ƴan mata da uwayensu) zai taimaka sosai wajen assasa ƙauna tsakanin yara - hakan zai kuma saka su tashi da ƙwaɗayi da ƙaunar son yin azumi.

Idan har ta kai mutum ba zai iya azumi ba akwai yanayin da addini ya bayar da damar ciyarwa ko kuma ramako.

Saukar da Al-Qur'ani cikin Ramadan

Manzon Allah S.A.W ya fara karɓar wahayi ne da Suratul Alaq a cikin watan Ramadan.

Allah S.W.T ne ya fara rubuta Al-Qur'ani a Lawhul Mahfuz.

Daga nan sai aka sauko da shi zuwa sama ta ɗaya a daren Laylatul-Qadr, dare mai matuƙar muhimmanci ga dukkan Musulmi a watan azumi.

Wannan na nufin cewa a watan azumi ne aka fara saukar da Al-Qur'ani mai tsarki ga Annabi Muhammad (SAW).

Allah ya zaɓi sauko da Al-Qur'ani mai tsarki a watan ne domin nuna irin muhimmanci da watan ke da shi.

Mutane na cin dabino

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana son cin dabino lokacin buɗe-baki

Buɗe ƙofofin Aljannah da rufe na Jahannama

Idan watan azumi ya gabato, ana buɗe ƙofofin Aljannah tare da rufe na wutar Jahannama - ana kuma ɗaure shaiɗanu.

Yana da sauƙi a samu damar shiga Aljannah da kuma wahalar shiga wuta lokacin watan azumi, saboda Allah yana ba da tarin lada ga duk aikin alheri da kuma wahala wajen aikata saɓo.

Wani dalili ɗaya shi ne ana ɗaure Shaiɗan a watan azumi saboda shi ne yake rinjayar mutane wajen aikata zunubi.

Wannan ne ya kawo mu ga tambayar: Me ya sa wasu ke aikata zunubi lokacin watan azumi?

Malaman addini sun bayyana cewa watakila hakan na faruwa ne saboda ba duka shaiɗanu aka ɗaure ba: waɗanda suka fi haɗari ne kaɗai (kamar yadda wani Hadisi ya bayyana).

Ko kuma mutane sun saba da aikata zunubi har abin ya zama jiki a wajensu, kuma akwai wahalar dainawa.

Alfanun yin azumi ga lafiya

Azumi na da alfanu da kuma albarka daban-daban. Alfanun sun hada da:

1. Azumi na gyara jikinmu.

2. Muna rage ƙiba.

3. Rage barazanar kamuwa da ciwon suga.

4. Rage barazanar kamuwa da ciwon zuciya ta hanyar rage hawan jini da daidaita ƙiba da sauran abubuwa masu lahani.

5. Taimakawa wajen girman sabbin ƙwayoyi a ƙwakwalwa.

6. Bincike ya nuna cewa yin azumi na rage haɗarin kamuwa da cutuka irin su kansa da cutar mantuwa.

Haka kuma, azumi na saka mu gano abin da marasa galihu a faɗin duniya ke fuskanta, da kuma gode wa Allah kan irin ni'imar da ya yi mana.

Sai dai, abin da Al-Qur'ani mai girma ya koya mana kan azumi shi ne: yana taimakon mu wajen ƙara tsoron Allah S.W.T. da kuma yadda zai kare kan mu idan muka ji buƙatar saɓa wa Allah.

Abubuwan da ke karya azumi

Akwai abubuwa da dama da mutane ke tunanin ba sa karya azumi amma kuma bisa haƙiƙa suna karya azumin. Haka kuma akwai abubuwan da jama'a ke tunanin suna karya azumi amma kuma ba sa karyawa.

Wannan ya sa BBC ta tuntuɓi Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, malamin addinin Musulunci a Kano domin jin abubuwan da suke karya azumi.

Shehin malamin ya ce abubuwan da suke karya azumin sun haɗa da:

  • Cin abinci da gangan
  • Shan ruwa da gangan
  • Saduwa da iyali
  • Ƙaƙaro amai
  • Zuwan jinin al'ada ko biƙi
  • Rashin ɗaukar niyyar azumin
  • Yin ƙaho
  • Fasa azumin
  • Ridda
  • Fitar da maniyyi