Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 08/08/2025

Wannan shafi ne dake kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 08/08/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin namu na yau, Juma'atu babbar rana.

    Sai kuma gobe Asabar idan Allah ya nuna mana.

    A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

  2. MDD ta nuna damuwa kan ƙaruwar hare-haren ta'addanci a yankin Sahel

    Ofishin kula da yammacin Afrika da Sahel na Majalisar Dinkin Duniya watau UNOWAS ya nuna damuwa kan yadda ake samun karuwa a haren haren kungiyoyin ‘yan ta'adda suke ke kai wa kan iyakokin kasashen yankin.

    Ofishin ya kuma ce kungiyoyi irinsu JNIM da IS sun kula kawance da kungiyoyi masu aikata miyagun laifuka na wasu kasashen duniya.

    Ofishin na UNOWAS ya bayyana haka ne a wani zama na kwamitin tsaro na MDD a birnin New York.

  3. "Rikici ya raba aƙalla dubu 60 da muhallansu a Mozambique"

    Moza

    Asalin hoton, AFP

    Ma’aikatan agaji sun ce sama da mutane dubu sittin ne suka rasa matsugunansu a wani sabon faɗan da ya ɓarke a Arewacin ƙasar Mozambique kuma kusan rabin waɗanda abin ya shafa yara ne.

    Ƙungiyar agaji ta Save the Children ta ce a wata gunduma wasu yan bindiga sun kai hari a ofisoshin ‘yan sanda da makarantu an kuma samu rahotannin sace-sace.

    Ƙungiyar agajin ta ce yaƙin da aka kwashe shekara takwas ana yi da ƙungiyoyi masu ikirarin jihadi ya yi mummunan tasiri kan yara.

    Tun shekara ta 2017 hare-hare a arewacin Mozambique ya raba mutane fiye da miliyan ɗaya da muhallansu.

  4. Ya kamata a dakatar da Wike da Ortom da Ikpeazu daga PDP - Lamido

    Lamido

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi kira da a kora Ministan Abuja, Nyesom Wike da tsohon Gwamnan Benue Samuel Ortom da tsohon Gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu da sauran ƴan PDP da suka yi mata unguwa da kan zabo a zaɓen 2023 daga jam'iyyar.

    Lamido ya bayyana haka ne a zantawarsa da tashar Channels a shirinta na Politics Today a ranar Juma'a, inda ya ce dole uwar jam'iyyar ta ɗauki matakin ba sani ba sabo.

    "Duk irin waɗannan mambobin jam'iyyar da suka mata ungulu da kan zabo irin su Wike da su Ikpeazu da Ortom da sauran su da suka fito fili suka yi adawa da jam'iyyar a zaɓen 2023, sannan kuma suka ce APC za su yi wa aiki a zaɓen 2027 ya kamata a kore su daga jam'iyyar."

    Haka kuma Lamido ya ce zai janye jiki daga taron kwamitin amintattu na PDP har sai an ɗauki matakin da ya dace.

  5. Ƴansanda sun saki Omoyele Sowore

    Sowore

    Asalin hoton, Sowore

    Rundunar ƴansandan Najeriya ta saki ɗangwagwarmaya, Omoyele Sowore bayan kiraye-kirayen da aka yi na buƙatar a sake shi.

    Tsohon ɗantakarar shugaban ƙasan ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook, inda ya alaƙanta sakin nasa da nasarar kiraye-kiran sakin nasa da aka yi.

    Ya rubuta cewa, "Ƴansandan Najeriya sun amsa buƙatar ƴan gwagwarmaya. Yanzu haka an sake ni daga tsare ni da aka yi ba bisa ƙa'ida ba."

    Sai dai ya ce babu wani abin farin ciki a sakin, "amma ina godiya gare ku da jajircewar da kuka yi ba tare da gajiyawa ba."

    Tun da farko, wasu matasa ne suka gudanar da zanga-zanga a Abuja da Legas da wasu biranen ƙasar, inda suka buƙaci ƴansanda su sake shi ba tare da ɓata lokaci ba.

    A ranar Laraba ne da ƴansanda suka gayyace shi domin amsa wasu tambayoyi, sannan rundunar ta sanar da cewa tana tsare da shi bayan ya ƙi amsa tambayoyi.

  6. Abin da ya sa muke ci gaba da tsare Sowore - Ƴansanda

    Ƴansanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwamishinan ƴansanda mai kula da sashen kai ɗauki na musamman a rundunar ƴansandan Najeriya da ke Abuja, Abayomi Shogunle ya bayyana dalilin da ya sa suke cigaba da tsare ɗanfafutika kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar African Action Congress wato ACC a zaɓen shekarar 2023, Omoyele Sowore.

    Shogunle ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da masu zanga-zangar neman a saki Sowore a ranar Juma'a a Abuja, inda ya ce cewa Sowore ya ƙi yin jawabi ne a lokacin da ƴansanda suke neman jawabin.

    Mutanen sun gudanar da zanga-zangar ne a wasu biranen ƙasar irin su Legas da Abuja da Osun da Oyo, inda suke kira da a gaggauta sakin ɗan gwagwarmayar.

    Tun da farko, Babban Sufeto Janar na ƴansandan Najeriya ne ya aika da takardar gayyata ga Sowore zuwa hedkwatar rundunar a Abuja a ranar Laraba domin amsa wasu tambayoyi, amma sai aka tsare shi har zuwa lokacin zanga-zangar.

  7. "Gwamnatin Najeriya za ta gina hanyar sufurin jirgin ƙasa a Kano"

    jirgin ƙasa

    Asalin hoton, NIGERIA RAILWAY

    Gwamnatin Najeriya ta ce za ta samar da titin dogo domin sufurin jirgin ƙasa a ƙwaryar birnin Kano da ke arewacin ƙasar, wanda zai laƙume naira triliyan 1 da rabi, a kamar yadda shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar wakilai Abubakar Kabir Abubakar ya bayyana.

    Jaridar DailyTrust ce ta ruwaito ɗan majalisar yana bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin ƴan jarida a Kano, inda ya ce shirin zai magance matsalolin da ake fuskanta a ɓangaren sufuri a jihar.

    "Duk wanda ya yi tafiya zuwa Turai ko Asiya zai ga irin waɗannan jiragen ƙasan kuma zai san muhimmancin su. Shirin zai matuƙar taimakawa tattalin arziƙin jihar idan an kammala.''

    Ya kuma ce Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da muhimman abubuwan ci gaba a arewacin ƙasar, kama daga ababen more rayuwa, da fannin lafiya, da noma da ilimi da kuma tsaro, ba kamar yadda mutane da dama ke zargi ba na cewa Tinubu ya mayar da yankin saniyar ware.

  8. Jihohin Najeriya da ke fuskantar ambaliyar ruwa sun ƙaru zuwa 31

    Wani mutum cikin ruwa tsamo-tsamo a gaban wani gida

    Asalin hoton, Getty Images

    Yayin da ake ci gaba da fuskantar saukar ruwan sama a wasu sassan Najeriya, hukumar kula da madatsun ruwa da kuguna ta ƙasar, NiHSA ta yi gargaɗin samun mummunar ambaliya a ƙananan hukumomin 198 cikin jihohi 31 tsakanin 7 zuwa 21 ga watan Agustan da muke ciki.

    Cikin wata sanar wa hukumar ta fitar, ta ce fiye da garuruwa 832 ne ke cikin hatsarin fuskantar ambaliyar.

    Hukumar ta kuma yi gargaɗin lalacewar tituna fiye da 100, yayin da ake fargabar ambaliyar za ta tilasta wa mutane barin gidajensu.

    Gargaɗin na zuwa ne bayan da farkon makon nan hukumar ta yi gargaɗin samun ambaliyar a jihohin ƙasar 19.

    Tuni dai wasu jihohin suka fara fuskantar ambaliyar.

    Gargaɗin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar Legas ke jajanta wa mazauna unguwar Ikorodu sakamakon mamakon ruwan sama da ake samu a yankin tun daga ranar Litinin da ta gabata.

  9. Ƙasashen duniya na Allah wadai da shirin mamaye Gaza

    Wata mata ɗauke da ƙusnhi tufafinta tana tafiya ciki ɓaraguzan gini a bayan da wani mutum ya juya baya yana tafiya ga kuma wasu gine-gine biyu a bayanta da suka ruguje

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙasashen duniya na ci gaba da yin Allah wadai da shirin Isra'ila na faɗaɗa yaƙin da ta ke yi da Hamas, inda ta bayyana shirinta na mamaye zirin Gaza baki ɗaya.

    Jamus - wadda ke cikin manyan ƙawayen Isra'ila - ta ce ba za ta sake amincewa da fitar da kayan aikin soji da za a yi amfani da su a yankin ba.

    Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya ce sakin yan Isra'ila da aka yi garkuwa da su da kuma tattaunawa kan tsagaita wuta su ne manyan abubuwan da Jamus ta sa gaba.

    Turkiyya ta buƙaci kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya dakatar da shirin na Isra’ila, Yayin da Babban jami'in kare hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk ya ce shirin ya saɓa wa hukuncin kotun duniya.

    A nasa ɓangaren Shugaban hukumar Falasɗinawa, Mahmoud Abbas, ya bayyana matakin a matsayin cikakken laifi yayin da jagoran 'yan adawa na Isra'ila ya ce shirin na iya salwantar da rayukan waɗanda ake garkuwa da su a Gaza .

  10. Har yanzu akwai Isra'ilawa 50 da ake garkuwa da su a Gaza

    Yayin da muka bayar da labarin cewa wasu daga cikin iyalan mutanen da ake tsare da su a Gaza na nuna damuwarsu kan shirin Isra'ila na mamaye Gaza, saboda jefa rayukan mutanen cikin hatsari.

    Har yanzu akwai kimanin mutum 50 da ke tsare a hannun Hamas a Gaza, inda aka yi imanin cewa 20 daga cikin na nan da ransu.

    Mutanen na cikin Isra'ilawa 251 da Hamas ta yi garkuwa da su a lokacin harin da ta kai kudancin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoban 2023, inda aka kashe Isra'ilawa kimanin 1,200.

    Kusan mako guda da ya wuce, Hamas ta fitar da wani bidiyo na ɗaya daga cikin mutanen da take tsare da shi, mai suna Ecyatar David, da aka kama a bikin kalankuwa na Nova.

    Bidiyon ya nuna mutumin a cikin mummunan yanayin rama, inda ɗan'uwansa ya ce ya ''zama tamkar ƙwarangwal''.

    Iyalai da dangin mutanen da ake garkuwar da su, sun jima suna kiran gaggauta kawo ƙarshen yaƙin da kuma sakin ƴan'uwan nasu.

  11. INEC za ta duba yiwuwar bai wa ɗaurarru damar kaɗa ƙuri'a a lokacin zaɓuka

    Hoton hannu mai zabe ana tantance shi

    Asalin hoton, INEC

    Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta ta duba yiwuwar bai wa ɗaurarru damar kaɗa ƙuri'a a lokacin zaɓuka.

    Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana haka ranar Juma'a yayin da ya karɓi baƙuncin shugaban hukumar kula da gidajen yari na ƙasar, Sylvester Ndidi Nwakuche Ofori, da ya buƙaci hakan.

    Mista Ofori ya ce ya kamata hukumar ta duba wannan buƙata tasa saboda su ma ɗaurarru suna da ƴancin zaɓe a ƙarƙashin dokokin Najeriya.

    “Kowa zai iya samun kansa a wannan yanayi, idan ya saɓa doka, don haka ya kamata mu duba yadda kula da su, suna da ƴancin da doka ta ba su, ɗaya daga cikin ƴancin kuwa shi ne ƴancin kaɗa ƙuri'a. Kasancewarsu a kurkuku ba zai janye musu ƴancinsu na zaɓe ba,'' in ji Mista Ofori.

    Shugaban hukumar kula da gidajen yarin ya ce akwai ɗaurarru fiye da 81,000 a faɗin gidajen yarin ƙasar, kuma kusan kashi 66 daga cikinsu na zaman jiran shari'a ne.

    Hukunce-hukunce kotuna a 2014 da 2018 sun tabatar da hukuncin bai wa ɗaurarrau damar kaɗa ƙuri'unsu a zaɓukan ƙasar.

    Shugaban hukumar zaɓenya ce INEC ta yi jerin ganawa da hukumar kula da gidajen yarin domin tsara yadda ɗaurarrun za su kaɗa ƙuri'ar tasu, ciki har da samun damar zuwa inda suke ɗaure domin ba su damar jefa ƙuri'a.

    Haka kuma shugaban na INEC ya nemi ɗaukin majalisar dokokin ƙasar domin tabbatar da ƙudurin.

  12. PDP ta gargaɗi mambobinta kan goyon bayan Tinubu a 2027

    Tinubu da Damagum

    Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya/PDP

    Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Tinubu da shugaban PDP Iliya Damagum

    Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta gargaɗi mambobinta da ke nuna goyon bayan sake zaɓen Shugaba Tinubu na APC a 2027.

    Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam'iyyar Hon. Debo Ologunagba ya fitar, PDP ta bayyana hakan da ta ce wasu mambobinta na yi a matsayin yi mata zagon-ƙasa.

    ''Abin taƙaici ne abinda wasu mambobinmu ke yi a kafafen yaɗa labarai, inda maganganunsu da ayyukansu ke nuna goyon baya ko yin wani abu da bai wa ɗan takarar APC nasara a zaɓen 2027,'' a cewar sanarwar.

    PDP ta ce hakan ya saɓa wa dokokin da suka kafa jam'iyyar, kuma barazana ce ga ci gaba da wanzuwar jam'iyyar.

    Jam'iyyar ta kuma ce hakan zai kawo tarin matsalolin da za su haifar da rarrabuwar kawuna a cikinta, wanda kuma cewarta idan ba a magance su ba za su janyo wa jam'iyyar rashin nasara a zabukan da ke tafe.

    Kan haka ne PDP ta yi gargadin sanya takunkumai masu tsauri ga mambobinta da aka kama da wannan laifi.

    Yanzu haka dai Nyesom Wike - wanda babban jigo ne a jam'iyyar ta PDP - na cikin ƙunshin ministocin Shugaba Tinubu na APC.

  13. 'Mamaye Gaza tamkar hukuncin kisa ne ga Isra'ilawan da ke hannun Hamas'

    Wani mutum sanye da riga mai launin ruwan ɗorawa

    Asalin hoton, Reuters

    Yayin da majalisar tsaron Isar'ila ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da ƙwace ikon Gaza, mazauna Isra'ila na ci gaba da bayyana damuwarsu kan matakin.

    Danny Bukovsky mazaunin birnin Tel Aviv ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa matakin na gwamnati ''kuskure ne'' a wannan lokaci.

    “Ina ganin wannan tamkar hukuncin kisa ne ga duka Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su a can'', in ji shi.

    Bukovsky ya ce ya kamata gwamnati ta ɗauki matakin mayar da waɗanda ake garkuwa da su cikin koshin lafiya tukunna.

    “Daga baya idan ma suna son mamaye duka Zirin sai su yi,'' in ji shi.

    Wata mace anye da vaƙar riga

    Asalin hoton, Reuters

    AIta ma Talya Saltzman,da ke zaune a Tev Aviv ta shaida wa Reuters cewa ''ya kamata a kawo ƙarshen yaƙin Gaza saboda sojoji da dama na mutuwa.''

    “Saboda babu wani ƙwaƙƙwaran dalili na yin hakan,” in ji ta.

    “Na san dalilinsu shi ne kawar da Hamas, amma mun kwashe tsawo shekara bitu ba mu iya yin hakan ba. Mun rasa sojoji da yawa kuma ba mu iya ƙwato duka mutanen da ake garkuwa da su ba,'' kamar yadda ta bayyana.

  14. Ku saki Sowore ko ku kai shi kotu - Peter Obi

    Sowore

    Asalin hoton, Sowore/Facebook

    Tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar LP, Peter Obi ya bukaci rundunar ƴansandan Najeriya ta gaggauta sakin ɗan fafutikar nan Omoleye Sowore ko ta gurfanar da shi a gaban kotu.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Mista Obi ya bayyana damuwarsa kan matakin da ƴansandan suka ɗauka na ci gaba da tsare Sowore.

    ''Ina mamakin yadda za a ci gaba da tsare mutumin da ya kai kansa domin amsa gayyatar da ƴansanda suka yi masa'', in ji shi.

    Mista Obi ya ce ɗabi'ar da ƴansandan Najeriya ke nunawa ta fara rusa kyakkyawan fatan da ƴan Najeriya ke da shi kan rundunar ƴansandan.

    A ranar Laraba ne rundunar ƴansanda Najeriya ta tsare Sowore bayan ya amsa gayyatar da rundunar ta yi masa domin amsa wasu tambayoyi.

    Lauyoyinsu sun yi zargin cewa ana ci gaba da tsare shi yanayi na muzgunawa da cin zarafi.

    Tuni dai ƙungiyoyin kare hakkin bil'adama a Najeriya suka fara kiraye-kirayen a sake shi

  15. 'Kawar da Hamas daga Gaza zai ɗauki aƙalla shekara biyu'

    Yayin da Isra'ila ta sanya batun 'Kawar da Hamas daga Gaza' cikin sharuɗɗa biyar da ta gindaya na kawo ƙarshen yaƙin Gaza, masana sun ce wannan sharaɗi zai ɗauki lokaci kafin ya cika.

    Wakilin sashen Larabci na BBC, Mohamed Taha ya ce kawar da Hamas daga jagorancin Gaza zai kasance abu mai wahala.

    Ya ce babban hafsan sojin ƙasa na Isra'ila ya ƙiyasta cewa hakan zai iya ɗaukar shekara biyu kafin a iya kawar da Hamas gaba ɗaya.

  16. Matan Zamfara sun yi zanga-zanga kan ƙaruwar hare-haren ƴanbindiga

    Gwamnan Zamafara riƙe da abin magana yana zaune a kan kujera sanye tufafi masu launin makuba

    Asalin hoton, Dauda Lawal/Facebook

    Ɗaruruwan mata ne tsofaffi da masu shawarya suka gudanar da zanga-zangar lumana a Gusau babban birnin jihar Zamfara sakamakon ƙaruwar hare-haren ƴanbidida a jihar.

    Matan waɗanda suka fito daga garin Jimrawa na yankin ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda sun koka kan yadda suka ce ƴanbindiga na ci gaba da addabarsu da jerin hare-hare tare da sace musu mutane, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Zanga-zangar matan na zuwa aƙalla mako biyu bayan wasu zarga-zanga biyu da aka gudanar a brnin na Gusau, bayan da masu zanga-zangar suka yi iƙirarin cewa hare-haren ƴanbindigar sun kashe fiye da mutum 100 a ƙauyukan Mada da Ruwan Baure da fegin Baza da Lilo da kuma Bangi.

    Ƙaramar hukumar Kaura Namoda na daga cikin ƙananan hukumomin jihar da hare-haren yanbindiga ke ci gaba da addaba.

    Mazauna jihar sun ce rashin hanyoyi masu kyau na kawo wa jami'an tsaro tarnaƙi wajen isa yankunan, lamarin da ke bai wa ƴanbindigar dmar cin karensu babu babbaka.

  17. Sharuɗɗa biyar da Isra'ila ta gindaya don kawo ƙarshen yaƙin Gaza

    Hoton tankokin yaƙin Israi'la

    Asalin hoton, Reuters

    Majalisar tsaron Isra'ila ta gindaya wasu sharuɗɗa da ta ce cika su ne kaɗai zai bayar da tabbacin kawo ƙarshen yaƙin Gaza.

    Sharuɗɗan sun haɗa da:

    • Ƙwace makamai daga hannun mayaƙan ƙungiyar Hamas.
    • Rusa dakarun mayaƙan ƙungiyar Hamas
    • Miƙa wa Isra'ila dukkan mutanen da Hamas ke riƙe da su, masu rai da ma matattu.
    • Miƙa ikon tsaron birnin Gaza hannu dakarun Isra'ila.
    • Samar da gwamnatin farar hula, wadda ba ta Hamas ko Hukumar Falasɗinawa

    Tun da farko majalisat amince da mamaye ilahin birnin na Gaza, wani abu da wasu ƙasashen duniya da ƙungiyoyin agaji ke kallo a matsayin abin da zai sake haifar da kashe-kashe a yankin

  18. 'Aƙalla mutum 24,000 ne suka ɓata saboda Boko Haram a Najeriya'

    wani jami'in soja sanye da abin rufe fuska, riƙe da bindiga yana kallon gefe, a bayansa kuma akwai motar sojoji

    Asalin hoton, AFP

    Kungiyar Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa aƙalla ‘yan Najeriya 24,000 ne suka ɓata tun daga shekarar 2014 waɗanda galibinsu yara ne ƙanana, sanadiyyar rikicin Boko Haram.

    Kakakin ƙungiyar Aliyu Dawobe ya shaida wa BBC cewa jihohin Borno da Yobe da Adamawa ne kan kan gaba inda suke da adadiu 16,000.

    Aliyu Dawobe ya ce ƙungiyarsu ta samu ƙorafe-ƙorafe daga mutane daban-daban da ƴan'uwansu suka ɓata, kuma tana bakin ƙokarinta wajen taimaka musu domin gano yaran.

    ICRC ta ce ko a wannan shekarar kadai ta gano mutum 11 ƙari kan mutane 13 da aka gano a 14.

    Kakakin ƙungiyar ya ce wasu daga cikin ririn waɗannan mutane sun watsu ne cikin duniya, yayin da wasunsu ke tsare a hannun hukumomi, wasu kuma sun sake garuruwa.

  19. Ghana ta ƙaddamar da bincike kan hatsarin jirgin sojin ƙasar

    JIRGIN DA YA FADI ƘASA CIKIN DAJI

    Asalin hoton, GHANA AIR FORCE

    Jami'ai a Ghana sun ƙaddamar da bincike domin gano musababbin hatsarin wani jirgin soji mai saukar ungulu da ya yi sanadiyar mutuwar ministan tsaro da na muhalli da wasu mutum shida.

    Shugaban Ghana John Mahama ya tabbatar wa iyalan mamatan da al'ummar ƙasar cewa rundunar soji ta ƙaddamar bincike na musamma kan musassabin hatsarin.

    Jirgin ya ya yi hatsari ne kan hanyarsa daga Accra zuwa wani taron yaki da hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba a garin Obuasi na yankin Yammacin ƙasar.

  20. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a, da Hausawa ke yi wa kirari da Hajji babbar rana.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a wannan shafi bisa kulawar Usman Minjibir, domin kawo muku halin da duniya ta wayi gari.

    Ku kasance a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.