Rufewa
Masu bin shafinmu nan muka kawo ƙarshen shafin na yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 01/12/2025
Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida
Masu bin shafinmu nan muka kawo ƙarshen shafin na yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya sun amince da kafa wata gidauniya domin samar da kuɗin yaƙi da matsalar tsaron da ke addabar yankin.
Cikin sanarwar bayan taro da gwamnonin suka fitar, sun ce sun amince kowace jiha ta bayar da naira biliyan ɗaya cikin asusun.
Sai dai gwamnonin ba su yi cikakken bayanin yadda za su riƙa kashe kuɗin.
Dama dai masana tsaro sun jima suna bayar da shawarar aiki tare tsakanin duka jihohin arewa domin magance matsalar tsaron da yankin ke fuskanta.
Yankin arewacin Najeriya ya jima yana fama da matsalar tsaro, inda ƴanbindiga ke kai hare-hare kan fafaren hula tare da garkuwa da su ko kashe su.
Amurka ta sanar da cimma wata yarjejeniya da Birtaniya kan kasuwancin magunguna.
A cikin yarjejeniyar hukumar lafiya ta Birtaniya za ta biya ƙarin kuɗi kan sabbin magungunan da aka haɗa a Amurka.
A nata ɓangaren kuma Amurka za ta cire magungunan da aka haɗa a Birtaniya daga jerin kayyayakin da ta sanya wa haraji.
Sakataren harkokin kasuwanci na Amurka Howard Lutnick ya ce yarjejeniyar za ta tabbatar da cewa dukkanin sabbin magungunan da za a ƙirƙiro a nan gaba, an samar da su ne a Amurka.
Hukumar ƙididdiga ta Najeriya, NBS ta ce arzikin da Najeriya ke samarwa a cikin gida (GDP) ya ƙara da kashi 3.98 cikin 100 a rubu'i na uku na shekarar 2025.
Cikin rahoton da ta fitar, NBS arzikin cikin gida da Najeriya ta samu a watannin rubu'i na uku na shekarar ya zarta wanda ta samu a daidai wannan lokacin na shekarar 2024.
NBS ta ce fannin noma ne kan gaba a samar da arzikin da kashi 3.79 sai harkar masana'antu da ya ƙaru da kashi 3.77.
A baya-bayan nan dai ana samun raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, kamar yadda hukumar ta NBS ke fitarwa, wani abu da gwamnatin ƙasar ke dangantawa da matakan inganta tattalin arziki da take ɗauka.
Ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta sake nanata buƙatar kafa ƴansandan jihohi domin magance matsalolin da yankin ke fuskanta.
Cikin sanarwar bayan taro da ƙungiyar ta fitar bayan kammala taron da ta gudanar a Kaduna, gwamnonin sun yi kira ga majalisar dokokin Najeriya da na jihohi su ɗauki matakan tabbatar da hakan.
Matakin gwamnonin na zuwa ne kwanaki bayan da Shugaban ƙasar Bola Tinubu ya bayar da umarnin ɗaukar sabbin ƴansanda domin magance matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta.
Cikin wata sanarwa da Shugaba Tinubu ya fitar a makon da ya gabata ya ce zai duba yiwuwar amincewa da kafa ƴansandan jihohin.
Ma'aikatar man fetur ta Iraqi ta ce ta gayyaci kamfanoni da dama na Amurka domin sayen ɗaya daga cikin yankuna mafiya arzikin man fetur a duniya da kamfanin Lukoil na Rasha ya shafe shekaru ya na aiki a wurin.
Matakin na zuwa ne bayan rahotannin cewa kamfanin ya sanar da ƙasar cewa ba zai iya ci gaba da aiki a rijiyar man ba, sakamakon takunkuman da Amurka ta lafta masa a watan Oktoba.
Gwamnatin Trump ta kuma ƙaƙaba wa wani babban kamfanin mai na Rasha mai suna Rosneft takunkumi.
Wani mataki da ta kira ƙara matsin lambar tattalin arziƙi kan Rasha domin kawo ƙarshen yaƙin da ta ke yi a Ukraine.
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta yi kira da a faɗaɗa tare da sauƙaƙa hanyar samar da allura rage ƙiba.
WHO ta ce matakin babban ci gaba ne wajen yaƙi da matsalar ƙibar da ta wuce kima a duniya.
Shawarar farko da WHO ta bayar kan amfani da alluran - nau'i GLP-1, samfurin Mounjaro da Ozempic - ta ce amfani da magungunan na tsawon lokaci tare da cin abinci mai lafiya da motsa jiki za su taimaka wajen rage ƙiba.
WHO ta ce tsadar magungunan na daga cikin manyan ƙalubalen samun maganin, lamarin da ya sa mutane da dama ba sa iya samunsa.
Fiye da mutum biliyan ɗaya ne ke fama da matsalar ƙibar da ta wuce kima a duniya.
Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ya ziyarci garin Kwantagora na jihar Neja, inda ya gana da shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Neja,Bishop Bulus Dauwa Yohanna.
Ganawar ta ƙunshi duka iyaye da malaman makarantar St. Mary da ƴanbindiga suka sace ɗalibanta a baya-bayan nan.
Sace ɗaliban ya haifar da ruɗani a Najeriya, musamman faruwarsa ƴan kwanaki bayan sace ɗaliban jihar Kebbi.
Adadin ɗaliban da aka sace ya janyo saɓani tsakanin gwamnati da hukumar makarantar.
Makarantar dai ta ce ɗalibai fiye da 300 aka sace, yayin da gwamnatin jihar Neja da ƴansanda suka nuna shakku game da alƙaluman.
Ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya tare da sarakunan yankin na wata ganawa kan matsalolin tsaron da suka addabi yankin a jihar Kaduna.
Tun da farko ƙungiyar ta yi niyyar gudanar da taron a ƙarshen mako, amma saboda da wasu dalilai ta jinkirta zuwa yau.
Gwamnonin da ke halartar taron sun haɗa da na jihohin Kaduna da Neja da Gombe da Kebbi da Adamawa da Nasarawa da Jigawa da Zamfara da Yobe da sauransu.
Yankin arewacin Najeriya na fama da matsalolin tsaro da ke addabar mutanen yankin.
A baya-bayan nan ne ƴanbindiga suka mai hare-hare kan wasu makarantu tare da sace ɗalibai a jihohin Kebbi da Neja.
Lamarin da ya sa wasu jihohin ƙasare da dama suka ɗauki matakin rufe makarantunsu.
Jakadan Majalisar Dinkin Duniya, Ramtane Lamamra, ya gana da shugaban Sudan kuma shugaban sojoji, Lt Janar Abdel Fattah al-Burhan, a birnin Port Sudan domin tattauna hanyoyin shawo kan mummunar yaƙin basasar da ya dabaibaye kasar, musamman a ɓangaren tsaro da agajin jin kai.
A wata sanarwa da majalisar mulkin kasar ta fitar, Burhan ya bayyana cewa gwamnatin Sudan na neman zaman lafiya ta yadda zai dace da muradun al’ummar ƙasar.
Ya kuma jaddada buƙatar samun haɗin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya domin inganta tsaro da zaman lafiyar kasar tare da cimma muradun aikin jin kai.
Shugaban sojojin ya kuma maimaita cewa wannan yaki zai kare ne kawai idan dakarun soja sun samu nasara gaba daya, tare da janyewar dakarun RSF daga yankunan da take riƙe da su a halin yanzu.
Ma'aikatan ceto a Indonesia na ci gaba da ƙoƙarin ceto waɗanda suka tsira daga mummunar ambaliyar da ta mamaye yankuna da dama na tsibirin Sumatra.
Mutanen da suka mutu zuwa yanzu sun kai kusan ɗari shida.
An kwashe mutum fiye da dubu ɗari biyar da sabai'n daga gidajen su, waɗanda a yanzu ke zaune cikin tantunan wucin gadi.
Wasu daga cikin waɗanda suka tsira a lardin Aceh sun ce ba su ci abinci ba tsawon kwanaki biyu zuwa uku.
Ana ganin cewa har yanzu akwai ɗaruruwan gawarwaki a ƙarƙashin taɓo a cewar hukumar kare aukuwar balao'i ta ƙasar.
Ana ci gaba da matsawa shugaban ƙasar Prabowo Subianto lamba domin ya ayyana dokar ta ɓaci.
Ƙasar Cameroon ta shiga ruɗani bayan mutuwar fitaccen dan adawa, Anicet Ekane, wanda ya mutu a tsare kimanin wata guda bayan kama shi.
Lauyoyinsa da jam’iyyarsa ta Manidem ne suka tabbatar da mutuwarsa suna mai cewa Ekane na cikin jagororin haɗakar ‘yan adawa da suka goyi bayan Issa Tchiroma Bakary a zaɓen shugaban kasa da aka gudanar a 12 ga Oktoba.
Mai magana da yawun jam’iyyar ya shaida wa BBC cewa Ekane ya mutu ne a ɗakin asibiti da aka kwantar da shi a cibiyar likitocin soji.
Ya ce matar marigayin ta samu kira zuwa asibitin, amma da ta isa sai kawai aka mika mata gawar mijinta ba tare da wani cikakken bayani ba.
Daga bisani iyalansa suka kai gawarsa dakin ajiye gawa. Wannan yanayi ya haifar da tambayoyi da damuwa daga magoya baya da jama’a baki ɗaya.
Sai dai ma’aikatar tsaron kasar, ta bakin kakakinta Capt. Cyrille Serge Atonfack, ta ce Ekane mai shekaru 74 ya rasu ne sakamakon cututtuka da ya daɗe yana fama da su.
Ya bayyana cewa tun bayan kama shi a ranar 24 ga Oktoba aka kwantar da shi a asibitin rundunar ‘yan sanda, inda likitoci ke kula da shi.
Amma lauyoyinsa sun musanta haka, suna cewa an tuhume shi da laifuka irin su tayar da zaune tsaye duk da cewa ba a taba gurfanar da shi gaban kuliya ba.
Mutuwar Ekane ta tayar da hankula a faɗin ƙasar, inda ɗimbin magoya baya suka taru a hedikwatar jam’iyyar Manidem da ke Douala domin jimami.
Sai dai jam’iyyar ta ce jami’an tsaro sun kewaye ofisoshinta, lamarin da ya kara tsananta yanayin.
Hukumomi sun ce an kaddamar da bincike domin gano hakikanin musabbabin mutuwar Ekane, lamarin da ake sa ran zai ci gaba da daukar hankalin jama’a.
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da jaddada aiwatar da dokar hana sana'ar achaɓa ta shekarar 2013, wani mataki da ta ce zai taimaka wajen kare tsaro da rage laifuka, da tabbatar da doka da oda a fadin jihar.
Ma’aikatar Shari’a ta bayyana cewa dokar, wadda ta dade tana nan daram kuma za a ci gaba da aiwatar da ita sosai.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da babban mai bai wa gwamnan jihar Shawara Kan Harkokin Labarai na Ma’aikatar Shari’a ya fitar
Babban lauyan jiharkuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, ya buƙaci jama’a musamman masu baburan haya wata acaɓa da su yi biyayya ga tanade-tanaden dokar.
Ya tunatar da cewa “Dokar ba sabuwa ba ce, kuma dole a kiyaye ta domin amfanin kowa da kowa.”
A cewarsa, gwamnatin jihar ba za ta lamunci karya dokar ba, musamman a yankunan da aka haramta acaɓa.
Dokar ta hana achaɓa a cikin wasu muhimman ƙananan hukumomin birnin da suka haɗa da Kano Municipal, Gwale, Dala, Nassarawa, Tarauni, Ungogo (Jido), Dawakin Kudu (Tamburawa, Gurjiya da Jido Ward), Fagge da Kumbotso.
Haka kuma, dokar ta tanadi hukunci mai tsauri ga masu karya ta, wanda ya haɗa da ɗaurin watanni shida, tara na Naira 10,000 da kuma yiwuwar ƙwace babur gaba ɗaya.
Ga direbobin da ke aiki a yankunan da aka amince da yin achaɓa, gwamnatin ta nanata wajabcin yin rajista da mai unguwa da sashen ayyuka na ƙaramar hukuma da kuma DPO na yankin su.
Gwamnatin jihar ta yi kira ga direbobi da fasinjoji da shugabannin al’umma da ƙungiyoyin sufuri da su tabbatar da cikakken bin dokar.
Adadin waɗanda suka rasa rayukansu a ambaliyar ruwan da ta afka wa Indonesia makon da ya gabata yanzu ya haura mutum 500.
Masu ceto dai na ci gaba da ƙoƙarin isa yankunan da abin ya shafa.
Ambaliyar ruwan, wadda guguwar da ba kasafai ake samu ba ta haddasa ta samo asali ne daga Tekun Malacca.
Ambaliyar ta shafi jihohi uku kuma ta shafi rayuwar kusan mutum milyan 1.4, a cewar hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasar.
Har yanzu ba a san inda mutum 500 suke ba, yayin da dubban mutane ne suka samu raunuka.
Indonesia dai na daga cikin ƙasashen Asiya da suka fuskanci ruwan sama mai tsanani a kwanakin baya.
Ma'aikatan agaji na ƙoƙarin kai ɗauki ta hanyar tafiya a ƙafa ko kan babur, domin hanyoyin da yawa ba su iya ɗaukar manyan motocin ceto.
Hotunan da suka fito daga yankunan sun nuna gadoji da ambaliya ta wanke da hanyoyi cike da laka da tarkace, da kuma manyan katakai da suka taru wuri guda.
A daidai lokacin da ake ci gaba da ta'aziyya da jajen rasuwar fitaccen Malamin addinin musulunci, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, har yanzu ana ci gaba da tattaunawa kan rayuwa da rasuwar malamin.
A ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamban 2025 shahararren malamin ya rasu a wani asibiti da ke Bauchi.
Dubban mutane ne suka halarci jana'izar marigayin, ciki har da Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima da gwamnoni da sarakuna da sauran mutane, har da ƙasashen waje.
Sheikh Shariff Ibrahim Saleh ne ya jagoranci yi wa malamin sallah a masallacin Idi na garin Bauchi kafin a binne shi a masallacinsa da ke garin da misalin ƙarfe 6:45, kuma an binne shi ne kusa da wasu daga cikin iyalansa da suka rasu a baya.
Rundunar sojin Amurka ta bayyana cewa sojojinta sun lalata wasu wurare fiye da 15 da aka ɓoye makamai mallakar mayaƙan ISIS a kudancin Syria.
Rundunar ta ce ta yi wannan aiki ne da haɗin gwiwar ma'aikatan ma'aikatar harkokin cikin gidan Syria a farkon makon nan a Damascus.
Babban kwamandan rundunar, Admiral Brad Cooper, ya ce ya yi amannan cewa mayaƙan ba za su iya kai wasu hare-hare ko ina ba a yanzu.
An dai galaba a akan mayakan a Syria da Iraqi a shekaru shida da suka gabata.
Masar ta bayyana cewa an sako ’yan ƙasar uku da aka yi garkuwa da su a yammacin Mali a bara watan da ya gabata.
Wata majiyar kafar yaɗa labarai ta Sky News Arabia da ke Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ruwaito a ranar 9 ga Nuwamba cewa ƙungiyar JNIM wadda ke da alaka da Al-Qaeda ta nemi kuɗin fansa na dala miliyan 5 kafin a saki mutanen.
Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta bayyana a shafinta na Facebook cewa an saki mutanen ne bayan haɗin kai mai ƙarfi da gwamnatin Mali ta hanyar ofishin jakadancin Masar da ke Bamako tare da dukkan hukumomin gwamnati.
Ma’aikatar ta kuma sake jaddada wa ’yan Masar da ke Mali su bi dokoki da ƙa’idojin hukumomin yankin, su kuma riƙa ɗaukar katin shaidarsu a koda yaushe, sannan ta gargaɗe su da guje wa yin tafiya zuwa wajen birnin Bamako.
Wata ƙugiya da ke yaƙi da rashawa da cin hanci ta CPAC- 1 ta bayyana damuwa matuƙa kan harin ’yan bindiga da ya shafi wasu yankunan jihar Kano, tana mai cewa abin da ya faru ya zama “kamar wata hanya da zai karya lafazin tsaron Arewa.”
A cikin wata sanarwa da ta fitar a Abuja a ranar Litinin, 1 ga Disambar 2025, ƙungiyar ta ce shiga Kano da ’yanbindiga suka yi barazana ce babba ga tattalin arziki da zaman lafiya da al’adun arewacin ƙasar.
Ta ce Kano, wadda ta shahara a matsayin cibiyar kasuwanci da ilimi, na fuskantar haɗarin zama wata sabuwar mafakar ’yan bindiga idan ba a tunkari lamarin da gaggawa ba.
Kungiyar ta kuma yi Allah-wadai da yadda wasu ’yan siyasa ke ƙoƙarin amfani da rikicin tsaro domin samun ribar siyasa.
"Zargin da gwamnatin Kano ta yi kan wasu ’yan siyasa, kamar yadda kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ibrahim Wayya, ya bayyana, ba abin watsarwa ba ne saboda haka ya kamata hukumomin tsaro su binciki lamarin don gano gaskiya tare da ɗaukar matakin da ya dace." in ji sanarwar.
Kungiyar ta danganta yawaitar hare-haren da ake gani a Kano da yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla tsakanin al’ummomi da ’yan bindiga a Jihar Katsina.
"Bayanan da aka samu daga mazauna yankin sun nuna cewa maharan na shigowa Kano ne daga Katsina."
Kungiyar ta nemi a sake duba dabarun yaƙi da ’yan bindiga, ta na mai cewa duk wata tattaunawa da ’yan bindiga dole ne ta fara da mika makamansu.
Hukumomi sun ce wasu ’yan bindiga sun kai hari wani coci a jihar Kogi inda suka yi awon gaba da masu bauta da dama ciki har da fasto da matarsa a safiyar Lahadi.
Maharan sun kai harin ne a sabon cocin Cherubim and Seraphim da ke Ejiba, wani ƙauye a ƙaramar hukumar Yagba West, inda suka fara harbe-harbe suka sa jama’ar cocin gudu da tsira.
Har yanzu dai hukumomi na ƙoƙarin tantance adadin waɗanda aka sace.
Wani babban jami’in gwamnatin jihar a Lokoja ya tabbatar da faruwar lamarin ga BBC, amma ya ce ana ci gaba da samun ƙarin bayani.
Mai magana da yawun gwamnatin Kogi, Kingsley Fanwo, ya ce suna aiki tare da jami’an tsaro da ƙungiyoyin sa-kai na yankin domin bin diddigin maharan.
Ya ce, "Akwai bayanan da suka tabbatar da harin, kuma na san cewa rundunar tsaro ta jami’an gwamnati da ta sa-kai na aiwatar da abin da ya kamata su yi.”
Fanwo ya ƙara da cewa, “maharan sun san cewa jihar Kogi za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin an kuɓutar da duk wani ɗan jihar da aka sace.”
Wannan lamari ya faru ne a lokacin da ake fama da tashin hankalin ’yan bindiga da sace-sace a arewa da tsakiyar Najeriya, lamarin da ya sa makarantu da wuraren ibada suka zama abin hari.
A makonnin baya, ’yan bindiga sun sace ɗalibai sama da 300 daga wata makarantar Katolika a jihar Neja, sannan an sace wasu ’yan mata daga makarantar kwana a jihar Kebbi.
A Kwara ma an sace masu bauta daga wani coci abin da ya sake tayar da jijiyoyin wuya game da rashin tsaro a yankunan karkara.
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari a ƙauyen Chacho da ke ƙaramar hukumar Wurno ta Jihar Sokoto, inda suka yi garkuwa da amarya da ƙawayenta da wasu mazauna yankin har mutum 18.
Daga cikin waɗanda aka sace, mutane uku ne suka samu damar kuɓuta, lamarin da ya faru kwana ɗaya kafin ɗaura auren amaryar.
Sanata Ibrahim Lamido, mai wakiltar yankin, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su ƙara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
"Wannan abu idan ana ganin shi yana faruwa a ƙauyuka toh nan gaba birni zai shiga, saboda haka a ajiye siyasa a ƙasa, a zo a haɗa kai a yi harkar tsaro." in ji Sanatan.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa babu wani saƙo ko kira daga masu garkuwan har yanzu.
A cewar mazaunin, "wannan ba shi ba ne karo na farko da irin wannan harin ya faru a yankin ba, domin kusan sau shida kenan da ’yan bindiga suka afka musu, sai dai wannan shi ne mafi muni."
Wani mazaunin ya ƙara da cewa al’ummar garin na cikin damuwa saboda hare-haren da ke faruwa kusan kullum, kuma ba su da jami’an tsaro sai dai ’yan sa-kai da suke biyansu daga aljihunsu.
"Muna kira ga gwamnati ta kawo dauki, domin halin da muka tsinci kanmu a ciki ya yi muni." in ji shi.
Matsalar tsaro a Arewa maso Yammacin Najeriya ta ci gaba da zama babbar kalubale ga jami’an tsaro da al’ummar yankin, lamarin da ke barazana ga zaman lafiya da rayuwar yau da kullum.