Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 30/12/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 30/12/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Ministocin ƙasashen turai sun buƙaci a kai wa fararen hula ɗauki a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministocin kasashe 10 ciki har da Faransa, da Birtaniya, Japan da Canada sun yi gargadi kan mummunan halin jin kai da ake fama da shi a Gaza.

    A sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, sun yi maraba da kawo karshen yakin Gaza, amma sun ce yana da muhimmanci kar a manta da halin da farar hula ke ciki.

    Kididdiga ta baya-bayan nan da aka fitar, ta nuna sama da Falasdinawa miliyan 1 ne ke tsananin bukatar wurin zama a daidai lokacin da ake fama da tsananin sanyi a Gaza.

    Sannan rashin wuri mai tsafta ya bar dubban iyalai cikin hadarin ambaliya. Wannan kira na zuwa ne bayan kiran da kungiyoyin kasashe 25 da ke aiki a Gaza suka, na haramta musu gudanar da aiki a can sakamakon rashin cika sharuddan da ke cikin sabuwar rijistar da Isra'ila ta fitar.

  2. UAE za ta janye sojojinta daga Yemen

    UAE

    Asalin hoton, EPA

    Magoya bayan 'yan aware a Kudancin Yemen sun fantsama tituna suna zanga-zanga, inda Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce za ta kawo karshen ayyukan sojinta a Yemen, sa'o'i kadan bayan Saudiyya ta bukaci ta janye kan zargin taimakawa 'yan awaren.

    Wannan na zuwa ne bayan harin da kawancen Saudiyya ya kai tashar ruwa ta Mukalla da ta zargi Daular Larabawa na amfani da ita domin kai wa 'yan aware makamai da motoci da kayan soji.

    Kamar yadda shugaban gwamnatin Yemen Rashad al-Alimi ya bayyana, ya ce muna da tabbacin Hadaddiyar Daular Larabawa ta kaiwa 'yan aware makamai da motoci da kayan aikin soji ta jiragen ruwa 2 a tashar ruwan Fujaira.

  3. Bai kamata a ɗage fara aiwatar da dokokin haraji ba - Tinubu

    Tinubu

    Asalin hoton, Bayo Onanuga

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce dokokin haraji da ya sanya wa hannu za su fara aiki ne daga 1 ga watan Janairun 2026 kamar yadda aka tsara.

    Tinubu ya bayyana haka ne a matsayin martani bayan an fara kiraye-kirayen ɗage fara aiwatar da sababbin dokokin na haraji bayan an yi zargin akwai cushe a ciki.

    A wata sanarwa da ya fitar, Tinubu ya ce irin wannan gyare-gyaren dama ce da ake samu bayan lokaci mai tsawo da kuma take buƙatar a yi amfani da ita, "domin assasa wani dandamali mai kyau da zai amfanar da ƙasarmu. Ba a tsara sababbin dokokin nan domin ƙara haraji ba, an yi su ne domin samar da daidaito da gyara yanayin harajin ƙasar baki ɗaya."

    Tinubu ya ce bai ga dalilan da za su gamsar da shi amfanin ɗage fara aiwatar da sabbin dokokin ba, inda ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su goyi bayan fara aiwatar da dokokin, sannan ya ƙara da cewa "gwamnatinmu na sane da maganar cushen da ake yi a cikin sabbin dokokin da aka sanya wa hannu."

    "Ina tabbatar da cewa zan yi aiki da majalisun dokoki domin ganowa tare da gyara ɓangarorin da ake zargin akwai matsala. Ina tabbatar wa ƴan Najeriya cewa za mu yi aiki tuƙuru domin tabbatar cewa sabbin dokokin sun amfanar da ƴan Najeriya da ciyar da ƙasar gaba."

  4. APC a Kano ta ce tana maraba da Gwamna Abba

    Abba Kabir

    Asalin hoton, Twitter/Abba Kabir

    Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta ce tana maraba da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf zuwa cikinta, inda ta ce a shirye take ta karɓe shi.

    Jam'iyyar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da shugaban jam'iyyar na Kano Abdullahi Abbas ya fitar, inda ya ce za su ba gwamnan goyon baya, sannan ya nanata muhimmancin haɗin kai da ci gaban jam'iyyar a faɗin jihar Kano baki ɗaya."

    "Bayan gwamnan ya shigo, sauran shugabannin ƙananan hukumomi da ƴan majalisun tarayya da na jihohi da kwamishinoni da sauran masu riƙe da muƙamai duk muna maraba da su."

    Abdullahi Abbas duk za a karɓe su a cikin jam'iyyar APC "a ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

    Ya kuma yi kira ga ƴan jam'iyyar a jihar da su kwantar da hankalinsu, "domin shigowar gwamnan za ta taimaka mana wajen sauƙin samun nasarar APC a Kano, tare da ba mu damar ba Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ƙuri'u mafiya yawa a babban zaɓen shekarar 2027."

    Shugaban jam'iyyar ya ce jam'iyyar na buƙatar haɗin kai da zaman lafiya da girmama juna ne a yanzu, sannan ya ƙara da cewa yunƙurin shigowar Gwamna Abba cikin APC na ƙara nuna ƙwarewar Tinubu a siyasa, wadda ke sa jam'iyyun hamayya ke ƙara sha'awar shiga jam'iyyarsa.

  5. Ɗalibai da ƴan kasuwa sun shiga zanga-zangar tsadar rayuwa a Iran

    Iran

    Asalin hoton, Reuters

    An shiga rana ta uku da fara zanga-zanga kan tashin farashin kayayyaki da faduwar darajar kudin kasar Iran.

    Birnin Tehran ya kasance idan zanga-zangar ta fi karfi, an kuma rufe yawancin kantunan babbar kasuwar Tehran. Wakiliyar BBC ta ce ɗaliban jami'o'i a Tehran da Isfihan sun shiga zanga-zangar da 'yan kasuwa da masu tsaron shaguna da 'yan tireda suka fara a ranar Lahadi.

    Hotuna da bidiyo sun nuna yadda jami'an tsaro suka ja tunga a Tehran da wasu biranen kasar. Gwamnati ta ce mutane su kwantar da hankali kuma ta karbi kokensu za kuma a dauki mataki kan hakan.

  6. NUJ na jimamin ƴan jarida bakwai da suka mutu a hatsarin mota a Gombe

    ...

    Asalin hoton, NUJ

    Ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa (NUJ) ta bayyana jimami kan mutuwar ’yan jarida bakwai da suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a jihar Gombe ranar Litinin.

    Rahotanni sun ce hatsarin ya auku ne sakamakon fashewar taya, yayin da ’yan jaridar ke dawowa daga ɗaurin aure na wani abokinsu a ƙaramar hukumar Kaltungo.

    An tabbatar da cewa mutum huɗu sun jikkata.

    Shugaban NUJ na ƙasa, Alhassan Yahya, ya ce rasuwar ta girgiza al’ummar ’yan jarida a Gombe da ma ƙasar baki ɗaya, yana mai bayyana marigayan a matsayin ƙwararrun ma’aikata masu jajircewa da gaskiya.

    Ya miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan tare da kira da a ƙara tsaurara matakan tsaro a kan hanya domin hana asarar rayuka.

  7. Turkiyya ta kama mutum 357 da ake zargi da alaƙa da ƙungiyar IS

    ...

    Asalin hoton, X/Ali Yerlikaya

    Ministan harkokin cikin gida na Turkiyya, Ali Yerlikaya, ya ce jami’an tsaro sun kama mutum 357 da ake zargi da kasancewa mambobin ƙungiyar IS a larduna 21 na ƙasar, a samamen haɗin gwiwa da aka gudanar a faɗin ƙasar da safiyar Talata.

    Wannan ya biyo bayan wani artabu da ya faru a garin Yalova inda jami’an tsaro uku da kuma ‘yan bindiga shida suka mutu, yayin da wasu jami’ai tara suka jikkata.

    A makon da ya gabata ma, an kama mutum 115 da ake zargin suna shirin kai hare-hare kan waɗanda ba Musulmi ba a lokacin Kirsimeti da Sabuwar Shekara.

    Ministan ya ce samamen ya gudana a wurare da dama ciki har da Ankara da Istanbul da Yalova, yana mai jaddada cewa gwamnati ba za ta bari ta’addanci ya durƙusar da ƙasar ba.

    Jami’ai sun kuma ƙwace takardu, kayan dijital da makamai yayin samamen.

  8. Zelensky ya musanta kai hari kan gidan Putin

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya musanta zargin Rasha cewa Ukraine ta kai hari da jiragen sama marasa matuƙa kan ɗaya daga cikin gidajen Shugaba Vladimir Putin, yana mai cewa ƙarya ce da nufin lalata tattaunawar zaman lafiya.

    Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya yi iƙirarin cewa an kai harin da jiragen yaƙi 91 a yankin Novgorod, lamarin da Rasha ta ce zai sa ta sake duba matsayinta kan shawarwarin zaman lafiya.

    Zelensky ya ce wannan “ƙarya ce daga Kremlin, yana gargaɗin cewa zargin na iya zama hujjar ci gaba da kai ƙarin hare-hare kan Ukraine, har ma da Kyiv.

    Ya buƙaci ƙasashen duniya da kada su yi shiru, yana jaddada cewa Rasha na neman dalilan ci gaba da yaƙi maimakon cimma tsagaita wuta ne kawai.

  9. Ƴansanda a Kebbi sun ce suna bincike kan abun da ya fashe a asibitin Bagudo

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ƴan sandan Jihar Kebbi ta ce ta fara gudanar da cikakken bincike kan abun da ya fashe a asibitin gwamnati da ke Bagudo da safiyar ranar Talata.

    A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Bashir Usman, ya fitar, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun ɗauki matakan gaggawa nan take bayan samun rahoton faruwar lamarin.

    Sanarwar ta ce jami’an tsaro na haɗin gwiwa, waɗanda suka haɗa da ƴan sanda da sojoji da kuma ƴan sa-kai na yankin, sun yi gaggawar kewaye asibitin tare da tabbatar da tsaro domin hana yaɗuwar fargaba ko tashin hankali a tsakanin al’umma.

    Haka kuma, rundunar ta ce an tura ƙwararrun jami’an EOD-CBRN, wato masu ƙwarewa wajen kwance abubuwan fashewa da binciken sinadarai masu haɗari, zuwa wurin domin gudanar da bincike mai zurfi da tantance ainihin abin da ya faru.

    Ƴan sandan sun tabbatar da cewa babu asarar rai da aka samu sakamakon lamarin, sai dai wani gini a cikin harabar asibitin ya lalace, inda aka ce mutanen da ke ciki sun riga sun fice kafin aukuwar ƙarar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa kwamishinan ƴansandan jihar ya bayar da umarnin ƙara tura jami’an tsaro na musamman zuwa yankin domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron lafiyar jama’a.

    Rundunar ta shawarci mazauna Bagudo da ma sauran jama’a da su kwantar da hankulansu tare da gujewa kusantar asibitin na ɗan lokaci, domin bai wa jami’an tsaro damar kammala aikinsu ba tare da wata tangarda ba.

  10. Kotu ta tura Malami da iyalinsa gidan yarin Kuje

    ...

    Asalin hoton, EFCC/Facebook

    Bayanan hoto, Abubakar Cika Malami lokacin da ake zaman kotu a ranar Talata a Abuja.

    Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare tsohon ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, tare da mai ɗakinsa da kuma ɗansa Abubakar Abdulaziz Malami a gidan yarin Kuje, bayan da suka ƙi amince wa da tuhume-tuhume 16 da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gabatar a kansu.

    Malami dai zai kasance a gidan yarin har zuwa ranar 2 ga Janairun 2026, lokacin da lauyoyinsa za su yi jawabi kan buƙatar belinsa a rubuce.

    An gurfanar da su a gaban kotun a ranar Talata, inda suka bayyana ƙin amincewa da zargin da ya shafi halasta kuɗaɗen haram da mallakar kadarori ba bisa ƙa’ida ba.

    ...

    Asalin hoton, EFCC/Facebook

    Bayanan hoto, Mai ɗakin Abubakar Malami, Hajiya Asabe Bashir lokacin zaman kotu a Abuja ranar Talata.

    EFCC ta gabatar da tuhume-tuhume 16 a kan Malami, ɗansa da Hajiya Asab Bashir, tana zargin su da halasta kuɗaɗen haram da kuma mallakar kadarori da darajarsu ta haura naira biliyan 8.7.

    A cewar hukumar, ana zargin waɗanda ake tuhuma da amfani da asusun bankuna da dama tare da kamfanoni a tsawon kusan shekaru goma, domin mallakar kuɗaɗen da ake zargin sun samo su ta hanyoyin da ba su dace da doka ba.

    Kotu da ƙi amince wa da buƙatar belin da aka yi ta baki a ranar Talata inda Alƙali Emeka Nwite ya ce hakan zai zama katsalandan ga hukumar EFCC da ke shari’a da Malami.

    ...

    Asalin hoton, EFCC/Facebook

    Bayanan hoto, Abubakar Abdulaziz Malami wanda ɗa ne ga tsohon minista, Abubakar Malami yayin zaman kotun na ranar Talata a Abuja.
  11. Firaminista mace ta farko a Bangladesh, Khaleda Zia ta rasu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaminista mace ta farko a ƙasar Bangladesh, Khaleda Zia, kuma babbar abokiyar adawar tsohuwar shugaba Sheikh Hasina da aka kifar, ta rasu tana da shekaru 80 bayan shafe dogon lokaci tana fama da rashin lafiya.

    Marigayiyar ta yi niyyar sake tsayawa takarar firaminista karo na uku a watan Fabrairu mai zuwa, lokacin da Bangladesh ke shirin gudanar da zaɓe na farko tun bayan juyin juya halin jama’a a ƙarshen shekarar 2024 da ya kifar da mulkin Sheikh Hasina.

    Khaleda Zia ta samu shiga fagen siyasa ne bayan kisan gillar da aka yi wa mijinta, tsohon shugaban ƙasa Ziaur Rahman. Daga bisani, a shekarar 1991, ta kafa tarihi ta zama firaminista mace ta farko a Bangladesh.

    Rayuwarta ta siyasa ta kasance mai cike da rikice-rikice, inda ta fuskanci lokutan shiga gidan yari da tsarewar gida, tare da tsawon takaddama ta siyasa tsakaninta da Sheikh Hasina.

    Daga baya an wanke ta daga zargin cin hanci, kuma an ba ta damar tafiya birnin London domin neman magani ne kawai bayan Sheikh Hasina ta rasa mulki.

    A ranar Litinin dai likitoci suka bayyana cewa lafiyarta ta yi tsanani inda daga bisani jam’iyyarta ta Bangladesh Nationalist Party (BNP) ta sanar a shafin Facebook cewa: “Shugabarmu da muke ƙauna ta rasu da misalin ƙarfe 6 na safe a yau Talata.”

    Bayan bayyana labarin rasuwarta, jama’a da dama sun hallara a wajen Asibitin Evercare da ke Dhaka, inda ake kula da ita kafin rasuwarta.

  12. EFCC za ta gurfanar da tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami a Abuja

    ...

    Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC za ta gurfanar da tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami a gaban kotun tarayya da ke Abuja ranar Talata.

    Za a gurfanar da shi tare da dansa, Abubakar Abdulaziz Malami, da wata mata mai suna Hajia Bashir Asabe.

    EFCC ta shigar da tuhume-tuhume guda 16 a kansu, waɗanda suka shafi safarar kuɗaɗen haramun masu girma da mallakar kadarori ba bisa ƙa'ida ba da darajarsu ta haura Naira biliyan 8.7.

    Ana zargin sun ɓoye kudaden ta hanyar asusun bankuna da kamfanoni da kuma sayen manyan gidaje a Abuja da wasu jihohi tsakanin shekarar 2015 zuwa 2025.

    Zargin ya haɗa da amfani da kamfanoni irin su Metropolitan Auto Tech Ltd da Meethaq Hotels Ltd wajen ɓoye kudade sama da biliyan daya, da kuma sayen gidaje masu tsada a Maitama da Garki da Jabi da Asokoro da Gwarimpa.

    Hukumar ta ce laifukan sun saɓawa dokar hana safarar kuɗaɗen haram na shekarun 2011 da 2022, kuma ta shirya gabatar da shaidu daga jami’an bankuna da masu canjin kudi da wakilan kamfanoni domin tabbatar da tuhume-tuhumen.

  13. NNPP ta kori shugabanta na jihar Kano, Hashim Dungurawa

    ..

    Asalin hoton, Dungurawa/Facebook

    Jam'iyyar NNPP a Kano ta ce ta kori shugabanta na jihar, Hashim Suleman Dungurawa, bisa zargin haddasa fitina da raba kan ƴan jam'iyyar a faɗin jihar.

    Shugaban jam'iyyar NNPP na mazaɓar Gargarir da ke ƙaramar hukumar Dawan Tofa inda Hashim Dungurawa ya fito, Shu'aibu Hassan shi ne ya sanar da korar a wani bidiyo na minti 1:13 sannan kuma ya tabbatar wa da BBC.

    Shu'aibu Hassan ya ce sun kori shugaban jam'iyyar NNPP ɗin ne bisa wasu dalilai guda shida.

    "Sakamakon zama da shugabannin jam'iyya suka yi na mazaɓar Gargari da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, mun amince da korar Hashin Sulaiman Dungurawa daga shugabancin jam'iyyar NNPP na jihar Kano saboda da dalilai kamar haka: Haddasa fitina a cikin jam'iyya da raba kan ƴan jam'iyya da rashin iya shugabancin a matakin jam'iyya da rashin daraja ƴan jam'iyya a matakin mazaɓarsa da kuma rashin mutunta mai girma gwamnan jihar Kano tare kuma da yi wa jam'iyya zagon ƙasa da korar ƴan jam'iyya masu muhimmanci daga jam'iyya

    Don haka daga wannan rana ta 30 ga watan Janairu na 2025 ka da ya sake ayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyya na jiha," in ji Shu'aibu.

    Wannan dai na zuwa ne kwana ɗaya bayan da bayanai suka karaɗe Kano cewa gwamna Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa zuwa APC mai mulki.

  14. Trump na fatan cimma zango na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

    ...

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce yana fatan a cimma zango na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza cikin gaggawa, tare da gargadin cewa Hamas za ta fuskanci matsala mai tsanani idan ba ta ajiye makamanta ba da wuri.

    Shugaban Amurka, wanda shirin zaman lafiyarsa mai maki 20 ke buƙatar kungiyar Hamas ta ajiye makamai, ya fadi hakan ne yayin ganawarsa da firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, a Florida a ranar Litinin.

    A taron manema labarai bayan ganawar, Trump ya ce Isra’ila ta bi shirin dari bisa dari duk da cewa har yanzu sojojinta na ci gaba da kai hare-hare a Gaza.

    Trump ya kuma ce Amurka na iya goyon bayan wani babban hari kan Iran idan ta sake komawa gina shirye-shiryen makaman linzami ko na nukiliya.

    A martanin wannan barazana, babban mai ba da shawara ga jagoran Iran, Ali Shamkhani, ya ce duk wani hari kan Iran zai fuskanci “amsa mai tsauri nan take.”

    Da aka tambaye shi yadda Hamas da Isra’ila za su koma zango na biyu na yarjejeniyar, Trump ya ce: “Da wuri-wuri yadda za mu iya. Amma dole ne a ajiye makamai.”

    Game da Hamas, ya ce: “Idan ba su ajiye makaman kamar yadda suka amince ba, to za su fuskanci matsala mai tsanani.”

  15. Abin da harin bam da ƴanbindiga suka kai a Zamfara ke nufi

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayan harin bama-bamai da rahotanni ke cewa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane aƙalla 11 a babbar hanyar Dansadau zuwa Gusau a jihar Zamfara ta Arewa maso yammacin Najeriya, ƴan Najeriya sun fara bayyana damuwa kan yadda harin ya faru da kuma abin da zai iya biyo baya.

    Shaidu sun tabbatar da cewa tashin bama-baman ya ritsa da babbar mota ɗaukar kaya da kuma Babura, lamarin da ya jefa tsoro a zukatan jama'ar yankin.

    Gwamnatin Zamfara ta hannun ɗaya daga cikin masu magana da yawun gwamnan, Mustapha Jafaru Kaura ta tabbatar wa BBC faruwa lamarin, amma a nata ɓangaren ta tabbatar da mutuwar mutum bakwai.

    Gwamnatin dai na zargin wannan wani salon harin ramuwar gayya ne ƴanbindigar suka ƙaddamar bayan kisan da ƴan sa-kai suka yi wa wasu daga cikin su a makon jiya a yankin.

  16. Abin da ya sake jefa 'yan Najeriya cikin matsalar ƙarancin wutar lantarki

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    'Yan Najeriya sun kara samun kansu cikin matsala ta karancin wutar lantarki sakamakon lalacewar da aka samu daga babban layin samar da lantarki na kasar, a ranar Litinin.

    Kamfanonin raba wutar lantarkin sun sanar da katsewar wutar a ranar Litinin din da misalin karfe biyu na rana.

    Wannan matsala ta sake kunno kai a Najeriyar bayan watanni da ta auku a watan Satumba.

    Da yake tabbatar da matsalar, a wata sanarwa da ya sanya a shafinsa na X, kamfanin samar da lantarkin na yankin babban birnin tarayya Abuja (AEDC), ya bayyana wa wadanda yake bai wa wutar cewa, matsalar ta faru da misalin karfe 02:02 na ranar, lamarin da ya janyo daukewar wutar a fadin yankunan da yake ba su lantarkin.

  17. Assalamu alaikum

    Masu bibiyarmu, Barkanmu da war haka, da fatan muna cikin ƙoshin lafiya.

    Kamar kullum, a yau ma wannan shafi na Kai Tsaye zai kawo rahotanni da labarai na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran kasashe makwabta.

    Sai ku ci gaba da bibiyar mu domin sanin halin da duniya take ciki a yau Talata.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.