Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/02/2026

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed da Abdullahi Bello Diginza

  1. An kama tsohon ministan makamashin Ukraine saboda cin hanci

    Rahotanni daga Ukraine sun ce hukumar yaƙi da cin hanci ta kama tsohon ministan shari'a da makamashi na Ukraine, Herman Galushchenko yayin da ya ke yunƙurin tserewa daga ƙasar.

    Mista Galushchenko daya nedaga cikin manyan mutanen da aka samu da hannu a almundahanar dala miliyan 100 a Ukraine a shekarar da ta gabata.

    Ana zargi Mista Galushchenko da tashiyar baki daga ƴan kwangila da aka ba aikin gyaran cibiyoyin makamashi don kare ƙasar daga hare-haren Rasha.

    Masu bincike sun yi imanin wani na hannun daman Shugaba Zelensky ne ya shirya al'amarin

  2. Tinubu zai kai ziyarar aiki Adamawa

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai kai ziyarar aiki jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da fadar shugaban ta fitar, ta ce a lokacin ziyarar ta yini ɗaya, Shugaba Tinubu zai ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar da gudanar.

    Haka kuma a lokacin ziyarar Shugaba Tinubu zai gana da manyan jagororin jihar, ciki har da jami'an gwamnati da sarakunan gargajiya.

    Jihar Adamawa dai na daga cikin jihohin ƙasar da jam'iyyar PDP mai hamayya ke mulki.

    Ziyarar Shugaban zuwa Adamawa na zuwa ne kwana biyu bayan ziyarar Jihar Kebbi da ke arewa maso yamacin ƙasar, inda ya ƙaddamar da wasu ayyuka tare da halartar bikin kamun kifi na Argungu.

  3. Iran za ta halarci tattaunawar nukiliyar da Amurka

    Ƙasar Iran ta ce ministan harkokin wajenta zai je Switzerland don halartar karo na biyu na tattaunawar da ba ta gaba-da-gaba ba da Amurka kan shirin nukiliyan ƙasar.

    A ranar Talata ne Abbas Araghchi zai isa birnin Geneva domin tattaunawar da za a yi da jakadan Amurka na musamman Steve Witkoff da kuma babban mashawarcin Trump, Jared Kushner.

    Tun da farko mataimakin ministan harkokin wajen ƙasar, Majid Takht-Ravanchi ya ce a shirye Iran take ta miƙa wuya, idan har za a ɗage mata takunkuman da aka ƙaƙaba mata, sannan a kauce wa tattauna batun shirinta na makamai masu linzami, ɗaya daga cikin manyan buƙatun Isra'ila.

    Amurka ta girke manyan jiragen yaƙinta biyu a Gabas ta tsakiya, a wani mataki na matsa wa Iran lamba don cimma yarjejeniya.

  4. Tinubu ya nemi a yi bincike kan gobarar Kasuwar Singa a Kano

    Tinubu

    Asalin hoton, Fadar shugaban Naeriya

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya jajanta wa ƴan kasuwar da suka tafka asarar miliyoyin naira da dukiyoyi bayan tashin gobara a Kasuwar Singa da ke jihar Kano.

    Gobarar ta tashi ne da yammacin Asabar amma har safiyar Lahadi wuta na ci, lamarin da ya janyo mummunan asara a kasuwar.

    Shugaba Tinubu - wanda ya nemi Gwamna Abba ya tattara bayanai kan gobarar - ya bayyana lamarin tamkar mummunan bala'i.

    Haka kuma shugaban ƙasar ya nuna damuwarsa musamman kasancewar a mako biyu da suka gabata ma an samu gobara a kasuwar da ta lalata gomman shaguna da dukiyoyi.

    Don haka ne ya nemi a gudanar da cikakken bincike kan dalilan de ke haifar da gobara a kasuwanni, lamarin da ke jefa ƴan kasuwa cikin mummunar asara da damuwa.

  5. Sojojin Amurka sun fara sauka a Maiduguri

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Jiragen saman sojin Amurka sun fara sauka a birnin Maiduguri na jihar Borno, lamarin da ke nuni da fara wani sabon tsarin haɗin gwiwa na tsaro tsakanin Amurka da Najeriya.

    Kafofin yaɗa labaran Najeriya sun ruwaito cewa wani jirgin sojin Amurka ya sauka da daren Alhamis a filin jirgin saman birnin da ke yankin arewa maso gabashin ƙasar.

    Bayanai sun kuma nuna cewa ana sa ran sake saukar ƙarin wasu jiragen a ƙarshen mako a wani ɓangare na shirin aikewa da kusan dakarun sojin Amurka 200.

    Jami'ai sun ce, jiragen na farko nau'in C-17 ne na jigilar kaya kuma suna ɗauke ne da manazarta bayanan sirri da masu ba da shawara da masu horaswa da kuma kayan aiki.

    Jami'ai sun yi nuni da cewa waɗanɗa suka fara isa za su fi mayar da hankali ne kan kafa amintattun hanyoyin sadarwa tare da shirya tsarin tallafi na aiki tare da takwarorinsu na Najeriya.

    Jami'an rundunar sojin Najeriya sun sha jaddada cewa sojojin Amurkan ba za su yi aiki a fagen daga ba.

  6. Shugaban Burundi ya karɓi ragamar jagorancin majalisar AU

    Shugaban ƙasar Burundi, Evariste Ndayishimiye ya karɓi ragamar jagorancin majalisar tarayya Afirka, AU.

    An gudanar da bikin miƙa mulkin ne a birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha , kamar yadda miknistan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar ya bayyana cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

    Mista Tuggar ya ce Najeriya na fatan yin aiki da sabon shugaban ƙungiyar domin ciyar da nahiyar Afirka gaba.

  7. El-Rufai ya zargi ofishin Ribadu da sayo guba 'mai haɗari'

    ...

    Asalin hoton, El Rufa'i/X

    Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya zargi ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, a ƙaƙashin jagorancin Mallam Nuhu Ribadu, da sayo kimanin kilogiram 10 na wani sinadari mai haɗari da ake kira 'thallium sulphate', daga ƙasar Poland.

    El-Rufai ya yi wannan zargin ne a cikin wata wasiƙa da ya aike wa ofishin Ribadu, wadda kuma ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce jagororin adawar ƙasar na neman ƙarin haske game da wannan batun.

    "Sinadarin thallium na da matuƙar haɗari kuma sinadari ne da ba kasafai ake samunsa ba'', kamar yadda wasiƙar El-Rufai ya bayyana cikin wasiƙar tasa.

    Ya ce ya aike da wasiƙar ne domin ya nemi cikakkun bayanai kan yadda aka sayo sinadarin, yayin da ya nuna barazanar da irin wannan sinadari ka iya yi kan lafiyar al'umma.

    El-Rufai ya nemi dalilin shigo da sinadarin da kuma amfanin da za a yi da shi.

    "Ina so in jaddada cewa ba ni da wata manufa ta daban na yin waɗannan tambayoyi, na yi su ne don in tabbatar da cewa an bi tsarin da ya kamata, kuma an bi matakan da suka dace na kare lafiya.''in ji shi

  8. Tchiani ya tafi ziyarar aiki a Aljeriya

    ...

    Asalin hoton, CCPRN

    Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar, Janar Abdourahmane Tiani, ya tashi daga birnin Yamai a yau Lahadi 15 ga watan Fabrairu, 2026, zuwa birnin Algiers na ƙasar Aljeriya, inda zai kai ziyarar aiki da sada zumunci.

    Shugaban Sojin Nijar da sojoji

    Asalin hoton, CCPRN

    Wata sanarwa da ta fito daga shugaban ma'aikata na fadar shugaban ƙasa ta ce, wannan ziyarar za ta zama wata dama ta tattauna batutuwan siyasa da suka shafi nahiyar Afirka baki ɗaya, musamman yankin Sahel.

    Tiani da sojoji

    Asalin hoton, CCPRN

    Tawagar shugaban ta ƙunshi wasu manyan jami'an gwamnatin Nijar da suka haɗa da Ministan tsaro Janar Salifou Mody, da ministan Albarkatun man fetur Mr. Hamadou Tini da Jakadan Nijar zuwa Algeria Mr. Aminou Malan Manzo.

    Sojoji

    Asalin hoton, CCPRN

  9. Ba mu san lokacin da Ukraine za ta iya shiga ƙungiyar EU ba - Kallas

    ...

    Jami'ar kula da harkokin waje na ƙungiyar Tarayyar Turai ya ce mambobin ƙungiyar ba su shirya bai wa Ukraine takamaiman ranar da za ta samu zama mambar ƙungiyar ba.

    Kaja Kalas ta shaidawa wani kwamiti a taron tsaro na Munich cewa har yanzu akwai sauran aiki da yawa da ya rage a yi a ɓangaren nuna cewa Ukraine na cikin nahiyar Turai.

    Madam Kalas ta kuma ce dole ne a tilastawa Rasha yin sassauci don kawo ƙarshen yaƙin.

    Ta ce Rasha ba ta da karfin da ta ke tunanin ta ke da shi, amma ta yi gargaɗin cewa za ta iya samun ƙarin riba a kan teburin tattaunawa fiye da yadda ta samu a fagen daga.

  10. Saudiyya ta buƙaci ƴankasarta su fara duban watan Ramadana ranar Talata

    ...

    Asalin hoton, 𝗛𝗮𝗿𝗮𝗺𝗮𝗶𝗻/X

    Kotun ƙolin Saudiyya ta yi kira ga al’ummar Musulmi a faɗin ƙasar da su duba jinjirin watan Ramadan da yammacin ranar Talata 17 ga watan Fabrairu, wanda ya zo daidai da 29 ga watan sha'aban 1447.

    A wata sanarwa da kotun ta fitar a ranar Lahadi, ta buƙaci duk wanda ya ga watan da idanunsa da ya hanzarta kai rahoto kotu mafi kusa, ko kuma ya tuntuɓi cibiya mafi kusa don taimaka musu wajen isa kotu mafi kusa.

    Idan an ga jinjirin watan a wannan daren, za a tashi da azumin watan Ramadana ranar Laraba 18 ga watan Fabrairu 2026.

    Sai dai idan ba a ga wata ba, watan Shaaban zai cika kwanaki 30, wanda hakan zai sanya Laraba ta zama ranar ƙarshen watan, kuma Alhamis 19 ga watan fabrairu za ta zama ranar ɗaya ga watan Ramadana 1447.

  11. Hare-haren Isra'ila sun kashe aƙalla mutum 11 a Gaza

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Jami'an kiwon lafiyan yankin Falasdinawa sun ce aƙalla mutum 11 ne suka mutu a hare-haren da Isra'ila ta kai cikin dare a Gaza.

    Likitoci sun ce aƙalla Falasdinawa huɗu ne suka mutu a wani tanti da ke matsugunin iyalai, sannan an kashe na biyar a Khan Younis da ke kudancin yankin.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce hare-haren ta sama martani ne ga keta yarjejeniyar tsagaita wuta da ta yi iƙirarin cewa ƙungiyar Hamas ta yi -- tana zargin mayaƙan ƙungiyar da fitowa daga ramuka tare da ketare layin rawaya da aka tanada kusa da dakarun IDF.

    Isra'ila da Hamas dai sun sha zargin juna da karya yarjejeniyar tsagaita wuta, wani muhimmin ɓangare na shirin Shugaba Trump na kawo ƙarshen yaƙin Gaza.

  12. Sojojin Faransa sun ƙwace hodar iblis a tekun Pacific

    ...

    Asalin hoton, Préfecture maritime /X

    Rundunar sojin ruwan Faransa ta ce ta ƙwace tan biyu da rabi na hodar iblis daga wani jirgin ruwa a yankin Pacific.

    An kama buhu ɗari na hodar ne a wani samamen haɗin gwiwa da Amurka, da kuma taimakon wani jirgin saman yaƙi na Faransa.

    An bar jirgin ruwan ya ci gaba da tafiya zuwa inda ya nufa, wanda jami’ai ba su fayyace ba.

    A cikin watan da ya gabata, hukumomin Faransa sun kama kusan tan goma sha biyu na hodar iblis a kewayen yankin Polynesia.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce a cikin ƴan shekarun nan masu safarar hodar Iblis da methamphetamine daga kudancin Amurka sun faɗaɗa ayyukansu a cikin tekun Pacific, galibi suna neman bunƙasa kasuwancin na suzuwa Australia da New Zealand.

  13. Najeriya ta gargaɗi ƴan ƙasarta kan masu ɗaukar ma'aikata don yaƙi a ƙasashen waje

    ...

    Asalin hoton, Ministry of Foreign Affairs/X

    Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta nuna fargaba kan abin da ta kira ƙaruwar ƴan ƙasar da ake ɗauka aiki ba bisa ƙa'ida ba domin yaƙi a ƙasashen waje.

    A cikin wata sanarwa aka fitar ranar Lahadi, mai magana da yawun ma’aikatar Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya ce: “’Yan Najeriya da dama da suka fada cikin irin wannan yanayi mara daɗi an tura su zuwa fagen daga bayan an yaudare su tare da tilasta musu sanya hannu kan kwangilolin aikin soja.”

    Jami’ai sun ce bincike da rahotannin tsaro sun nuna cewa an yaudari wasu ƴan Najeriya da alƙawuran samun ayyuka yi masu gwaɓi, ko damar yin karatu cikin sauki.

    A farkon makon nan ne hukumomin ƙasar Ukraine suka ce jami'an leƙen asirin sojinta sun gano gawarwakin wasu ƴan Najeriya guda biyu a yankin Luhansk.

    Sun ce duka mutanen biyu sun sanya hannu kan kwangiloli da rundunar sojin a shekarar 2025, kuma an tura su yankunan da aka mamaye ba tare da wani horo na soja ba.

    A cewar Ukraine, an kashe su ne a ƙarshen watan Nuwamba a lokacin da suke yunƙurin kutsa kai cikin yankunan Ukraine.

  14. Iran ta shirya sassantawa kan shirin nukiliyarta

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani ministan Iran ya shaida wa BBC cewa ƙasarsa a shirye ta ke ta yi sasanci don cimma yarjejeniyar nukiliya da Amurka idan Amurkawa na son tattaunawa kan ɗage takunkuman da aka ƙaƙaba mata.

    Jami'an Amurka sun sha nanata cewa Iran ce ke kawo cikas a tattaunawar da ake yi tsakanin ƙasashen biyu.

    A ranar Asabar ɗin da ta gabata, sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce shugaba Donald Trump ya fi son ƙulla yarjejeniya da Iran, amma a cewarsa yin hakan abu ne mai matuƙar wahala.

    Amma a wata hira da BBC a Tehran, Majid Takht-Ravanchi, mataimakin ministan harkokin wajen Iran, ya ce Iran ta zura wa Amurka ido ne ta ga ta nuna cewa lallai ta na son ƙulla yarjejeniya, inda ya ƙara da cewa: "Idan da gaske suke yi, na tabbata za mu kasance a kan hanyar cimma yarjejeniya."

    Trump ya yi barazanar kai hare-hare kan Iran matuƙar ba a iya cimma yarjejeniyar daƙile shirinta na nukiliya ba, inda Amurka ta ƙara ƙarfin sojojinta a yankin.

  15. Ghana ta zargi ɗan Rasha da yaɗa bidyon tsiraicin wasu matan ƙasar

    Ghana ta nemi Rasha ta mika mata wani ɗan ƙasarta da ake zargin ya nadi bidiyon jima'in da ya yi da wasu mata yan Ghana, har ma ya wallafa shi a Internet ba tare da izininsu ba.

    Ministan Sadarwa na Ghana Sam George ya ce ya nemi haɗin kan jakadan Rasha a Accra don a tabbatar da cewa an yi wa matan adalci.

    Rasha dai ba ta mayar da ƴan ƙasarta da ake zargi da aikata laifi a wata ƙasa.

    Ministan ya ce za a yi shari'ar wanda ake zargi a bayan idonsa, idan bai bayyana ba.

    Wasu bayanai a Internet sun nuna cewa ana zargin mutumin da aikata irin waɗanan laifuka a Kenya ma.

  16. An yi zanga-zangar adawa da gwamnatin Iran a wasu ƙasashen duniya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An yi zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin Iran a birane da dama a faɗin duniya, a wani gangami da aka kira "Ranar yaƙi da zalunci ta duniya" wanda jagoran ƴan hamayya na ƙasar kuma ɗan hamɓararen Shah na Iran, Reza Pahlavi ya kira.

    A birnin Los Angeles, da ke zaman birni mafi yawan Iraniya ke zaune a ciki a wajen ƙasar, sama da mutane dubu ɗari uku suka fito don yin alla-wadai da kisan masu zanga zanga da ake zargin gwamnatin Iran ta yi a baya bayan nan.

    Ko da a shekaranjiya Juma'a an yi irin wannan gagarumin gangami a birnin Toronto da ke ƙasar Canada da kuma birnin Munich na Jamus, inda shugabannin duniya suka taru don gudanar da taron tsaro na duniya.

    An kuma yi zanga-zanga a wasu birane da dama a Turai, da Australia, da New Zealand da Koriya ta Kudu.

    Rahotanni na nuna cewa wannan ita ce zanga zanga mafi girma da ƴan hamayyar da ke zaune a wajen Iran suka taɓa yi.

  17. An gano yadda aka kashe jagoran adawa na Rasha

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Alexei Navalny

    Ƙasashe biyar na Turai sun ce gwaje-gwajen da aka yi wa gawar jagoran ƴan hamayyar Rasha Alexei Navalny, sun nuna cewa ya mutu ne sakamakon sanya masa gubar da aka samu daga wasu nau'ikan kwaɗi da ke rayuwa a Ecuador.

    An rauwaito cewa gubar na janyo mutuwar ɓarin jiki, da kuma toshewar numfashi, kuma ana samunta ne kawai daga irin waɗanan kwaɗin da ake samu a dazukan kudancin Amurka

    Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta yi watsi da zargin da ta bayyana a matsayin labarin ƙanzon kurege.

    Moscow ta yi iƙirarin cewa Mista Navalny ya mutu ne sakamakon dalilan rashin lafiya.Matarsa Yulia Nalalny, ta gode wa kasashen saboda abin da bayyana a matsayin kokarin gano gaskiya.

    An yi gwajin a ɗakunan gwaje-gwaje a Sweden, da Faransa, da Netherlands, da Jamus, da Birtaniya.

  18. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Lahadi.

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.