Rufewa
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 3 ga watan Fabrairun 2026.
Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed, Aisha Babangida da Ahmad Bawage
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Mike Blake/Reuters
Sojojin Amurka sun ce sun harbo wani jirgin sama mara matuki na Iran, da ya kusanci ɗaya daga cikin manyan jiragen ruwan yaƙin Amurka a Tekun Larabawa.
Sun ce jirgin maras matukin ya kusanci jirgin ruwan yaƙi USS Abraham Lincoln cikin yanayi na barazana, ba tare da bayyana manufarsa ba.
Sojojin sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da jirgin ruwan ke ketare tekun, kimanin mil 500 daga gaɓar tekun Iran.
A wani bangare kuma, rahotanni na cewa Iran na neman a sauya wuri da kuma tsarin tattaunawar da aka shirya yi da Amurka a ranar Juma’a.
Shafin watsa labarai na Axios ya ambato majiyoyi biyu na cewa, Tehran na son a sauya wurin tattaunawar daga Santambul zuwa Oman, tare da cewa a gudanar da ita kai-tsaye da Amurka kaɗai.
Majiyoyin sun ce Iran na ja da baya daga fahimtar juna da aka cimma a baya.

Asalin hoton, Reuters
Rahotanni na bayyana cewa an kashe Saif al-Islam Gaddafi, ɗan tsohon shugaban Libya, Muammar Gaddafi.
Ba a dai san musabbabin kashe Saif al-Islam ba zuwa yanzu.
Ƴar uwarsa ta faɗa wa gidan talabijin na ƙasar cewa ya mutu ne a kusa da iyaƙar ƙasar da Aljeriya, ba tare dabayyana ta yanda ya mutu ba.
An daɗe ana daukarsa a matsayin wanda zai gaji mahaifinsa kanal Gaddafi.
Bayan hamɓarar da gwamnatin mahaifinsa a shekara ta 2011, an kama tare da tsare shi a birnin Zintan na tsawon shekara shida.
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta nemi a kama shi kan laifukan take hakkin ɗan'adam a lokacin da aka murkushe masu zanga-zanga a 2011.

Hukumar EFCC mai yaƙi da almundahanar kuɗaɗe a Najeriya ta kama jarumar Kannywood, Samha M Inuwa kan zargin wulaƙanta kuɗin naira.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X, ta ce ta kama Samha ne a yau Talata.
Kama tauraruwar na zuwa ne bayan wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya nuna tana share majina da takardar kuɗi na naira dubu ɗaya.
Hukumar ta ce ba ta yi wata-wata ba wajen kama Samha bayan fitar bidiyon, inda aka cafke ta don ta je ta amsa tambayoyi.
EFCC ta ce tana tsare da jarumar a halin yanzu yayin da ake ci gaba da bincike.
Hukumar ta ƙara da cewa za a tura jarumar zuwa kotu da zarar an kammala bincike.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Reuters
Firaministan Habasha, Abiy Ahmed, ya zargi rundunar sojin Eritiriya da aikata munanan laifuka lokacin yaƙin da ya ɗauki tsawon shekaru biyu a yankin Tigray da ke arewacin Habasha, wanda ya kawo karshe a shekarar 2022.
Sojojin Eritiriya sun yi yaƙi ne tare da sojojin Habasha a kan mayaƙan Tigray domin karɓe iko da yankin, sai dai daga baya alaƙar ƙasashen biyu ta taɓarɓare.
A wani jawabi da ya gabatar a gaban majalisar dokoki, Mista Ahmed ya zargi dakarun Eritiriya a karon farko da kisan kiyashi a birnin Aksum.
Sai dai wani ministan Eritiriya, Yemane Gebremeskel, ya yi watsi da zargin.
Wannan na zuwa ne a wani sabon salo na rikicin alaƙa tsakanin makwabtan ƙasashen biyu na yankin Afirka, waɗanda dangantakarsu ta rikiɗe daga ƙawance zuwa gaba.

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar ƴansanda a jihar Abia ta musanta rahotanni da ke cewa an gano wani kunshin bam a wani coci a jihar.
Wata sanarwa da kakakin ƴansandan jihar Maureen Chinaka ta fitar, ta ce ta gudanar da cikakken bincike a yankin, kuma wani abu mai kama da abin fashewa da aka gano.
Ta ƙara da cewa: "Ina tabbatar muku cewa babu wani bam ko abin fashewa da muka gano a yankin. Binciken da jami'an mu suka gudanar ne ya tabbatar da haka."
Ƴansanda sun bayyana cewa wani rodi ne aka gano ba bam ba.
Rundunar ƴansandan jihar ta tabbatar wa al'umma cewa a shirye take wajen kare rayuka da dukiyoyinsu, kuma an girke jami'ai a faɗin jihar baki ɗaya.
Tun da farko, an samu rahotanni da ke cewa an binne wani bam a cocin ranar Litinin, inda aka yi iƙirarin ƙwashe sama da mutum 100 da ke cocin bayan gano wani abu da ake zargin bam ne.

Asalin hoton, Getty Images
Wani ɗalibin makarantar sakandare ya daɓa wa malamarsa wuƙa a kudancin Faransa.
Masu shigar da ƙara sun ce malamar mai shekara 36 na cikin mawuyacin hali.
An kama ɗalibin wanda yake garin Sanary-sur-Mer kan zargin yunkurin kisa.
Faransa ta fuskanci jerin irin waɗannan lamura na ɗaliban da ke far wa malamansu, har ma da abokan karatunsu.
A shekarar da ta gabata ma, an kama wani ɗalibi ɗan shekara 14 da zargin kisan wata malama, bayan daɓa mata wuƙa har lahira.

Asalin hoton, Abubakar Malami/Facebook
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gurfanar da tsohon ministan shari'ar Najeriya, Abubakar Malami tare da ɗansa a gaban kotu, bisa wasu zarge-zarge biyar masu alaƙa da ta'addanci da mallakar makamai ba bisa ƙa'ida ba.
Malami da ɗansa Abdulaziz sun musanta duka zarge-zargen da aka karanta musu a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.
An dai zargi tsohon ministan shari'ar da ƙin gurfanar da mutumin da aka zarga da ɗaukar nauyin ta'addanci da aka damƙa takardun tuhumarsa hannun Malami, lokacin da yake matsayin babban lauyan gwamnati.
DSS ta kuma zargi Malami da Abdulaziz da ɓoye makamai a gidansu da ke unguwar Gesse Phase II a Birnin Kebbi ba tare da sanin hukukomi ba.
Haka kuma hukumar ta tsaron farin kaya ta zargi tsohon ministan shari'ar da tallafa wa ayyukan ta'addanci, yayin da suka zarge shi tare da ɗansa da mallakar nau'ika daban-daban na bindigogi da konsunan zuba harsasai, lamarin da hukumar ta ce ya saɓa wa dokar hana ta'addanci ta 2004.
Sai dai Malami da Abdulaziz sun musanta zarge-zargen.
Daga nan ne lauyan masu ƙara ya nemi kotun ta ci gaba da tsare waɗanda ake zargin a hannun DSS, har zuwa lokacin zaman kotun na gaba.
Sai dai yayin da yake martani, lauyan waɗanda ake ƙara, Shuaibu Aruwan (SAN) ya nemi belinsu da fatar baƙi, saboda a cewarsa sun ƙwace fiye da mako biyu suna tsare a hannun DSS.
To amma alkaliyar kotun mai shari'a, Joyce Abdulmalik ta ce neman beli da fatar baki ya saɓa wa dokar kotun da take jagoranta.
Tana mai cewa kotun na martaba adana bayanai, don haka ta nemi lauyan waɗanda ake ƙarar ya nemi belin a rubuce.
Daga nan ne kuma ta buƙaci hukumar DSS ta ci gaba da tsare Malami da ɗansa, sannan ta saka ranar 20 ga watan Fabrairun da muke ciki don ci gaba da shari'ar.
Tun a watan Disamban da ya gabata ne dai Malamai ya fara fuskantar tuhuma, da farko a hannun hukumar EFCC mai yaƙi da rashawa wadda ta gurfanar da shi a gaban kotu kan zargin almundahanar kuɗaɗe.
A ranar 7 ga watan Janairu wata kotu a Abuja ta bayar da umarnin wucin-gadi na ƙwace wasu kadarorinsa a jihohin Kebbi da Kano da Kaduna da aka ƙiyasta darajar kuɗinsu ta kai fiye da naira biliyan biyu.
Haka kuma kotun ta aika da shi gidan yarin Kuje da ke Abuja, sai dai ƴan kwanaki bayan samun beli, sai hukumar DSS ta kama shi bisa zargin ɗaukar nauyin ta'addanci.

Asalin hoton, FACEBOOK/ABBA KABIR YUSUF
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano SEMA, ta sanar da cewa za ta ci gaba da kwashe masu matsalolin lafiyar kwakwalwa daga titunan birnin da kewaye.
Bayanai na cewa akwai ɗumbin masu fama da wannan matsala da ke yawo a titunan birnin Kano, cikin mawuycin hali lamarin da ke ƙara matsalar tsaro.
Hukumar ta SEMA ta ce za ta killace su tare da basu magani, kafin a mayar da su garuruwansu.
Hukumar ta kuma ce gwmnatin Kano ta bijiro da aikin kwashe masu larurar kwakwalwar ne domin a basu kulawar da ta dace a matsayinsu na ‘yanadam tare da saita musu rayuwa don su koma cikin iyalansu.
Babban sakataren hukumar, Abdullahi Isyaku Kubarachi, ya shaida wa manema labarai cewa wannan aiki da suka fara dama yana cikin aikace-aikacensu, inda yace hukumar ta gudanar da aikin ne da dadddare da hadin gwiwar wasu hukumomin tsaro, a wasu kananan hukumomin birnin Kano hudu.
Kubarachi ya ƙara da cewa umarnin da gwamnatin Kano ta basu, shi ne su gudanar da aikin tattara masu matsalar kwakwalwar a ƙananan hukumomin cikin birnin Kano tukuna, sannan yace aikin zai taimaka wajen magance matsalar tsaro.
Sakataren hukumar ta SEMA yace mutanen da basu gamsu da bayanansu ba, saboda sha’anin tsaro su mika su ga jami’an tsaro.
Bayanai na cewa masu matsalar kwakwalwa dai suna fama da matsalolin rayuwa a yankunan Najeriya da dama, inda da dama daga cikinsu, matsalar kwakwalwar ba ta yi tsamari ba, amma saboda rashin kulawa da kuma tsangwama suke ta’azzara halin da suke ciki.

Asalin hoton, X/NEMA
Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA reshen Enugu, tare da haɗin gwiwar rundunar ƴansandan da Sojoji da hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Ebonyi (EBSEMA) sun gudanar da binciken gaggawa kan rikicin ƙabilanci da ya auku a ƙaramar hukumar Oso Edda ta Ebonyi da ya kashe mutum huɗu.
Sanawar da hukumar ta fitar ta ce binciken ya mayar da hankali ne wajen gano musabbabin rikicin da tantance asarar da aka yi, da kuma buƙatun mutanen da lamarin ya shafa.
Shugaban ƙaramar hukumar Oso Edda, Hon. Ekuma Nkama Chima ne ya tarbe tawagar NEMA ɗin jim kaɗan bayan ziyarar da gwamnan Jihar, Francis Nwifuru, ya kai yankin.
Sakamakon binciken ya nuna cewa rikicin ya faru ne a ranar 29 ga Janairun 2026, tsakanin ƙarfe 5:30 na safe zuwa 7:20 na hansti, kuma ya samo asali ne daga rikicin filaye tsakanin ƴan ƙabila huɗu a Oso Edda.
Rikicin ya haddasa lalata gidaje da dama da shaguna da kayayyakin gida da amfanin gona da gonaki, inda asarar ta kai miliyoyin naira.
Haka kuma, mutane da dama sun jikkata, yayin da rahotanni ke nuna cewa mutum huɗu sun rasa rayukansu, sannan wasu da dama sun rasa matsugunansu.
A halin yanzu, mutanen da rikicin ya shafa na samun mafaka ne a gidajen ‘yan uwa da abokai.
Shugabar ofishin NEMA ta jihar, Ngozi Echeazu ta isar da saƙon ta’aziyyar gwamnatin tarayya da NEMA ga iyalan da suka rasa ‘yan uwa da gidaje da dukiyoyinsu sakamakon rikicin.

Asalin hoton, Kwankwaso/x
Ƙungiyar Kwankwasiyya ta musanta ikirarin da wasu ke yaɗawa na cewa jagaran tafitar Dokta Rabi'u Musa Kwankwanso ya saka sharaɗin komawarsa APC.
Wasu rahotonni da ke yawo musamman a shafukan sada zumunta sun yin iƙirarin cewa jagoran Kwankwasiyyar na tattaunawa da jiga-jigan APC tare da saka sharaɗin komawarsa jam'iyyar.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, Kwakwasiyya ta bayyana matuƙar damuwa kan yawaitar rahotanni ikirarin ficewar Dokta Kwankwanso daga jam’iyyarsa ta NNPP zuwa jam’iyyar APC.
Ƙungiyar ta bayyana waɗannan rahotanni a matsayin tsagwaran ƙarya marasa tushe kuma an ƙirƙiresu ne domin ruɗar da al’umma.
"Sanata Kwankwaso bai taɓa shiga wata tattaunawa ko ganawa ko shawarwari da jam’iyyar APC ko Shugaba Bola Ahmed Tinubu ko wakilansa ba kan batun sauya sheƙa," in ji sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa "babu wata hujja da ke goyon bayan waɗannan zarge-zarge da ake yaɗawa."
Ƙungiyar ta kuma caccaki wasu kafafen watsa labarai da masu sharhi kan siyasa, tana mai cewa "abin takaici ne a riƙa wallafa zarge-zarge masu girma ba tare da bincike mai zurfi ba ko tabbatarwa daga wanda abin ya shafa ba."
Kwankwasiyya ta bayyana cewa "ganawar da aka taɓa yi tsakanin Kwankwaso da Shugaba Tinubu ta ƙarshe ta faru ne a watan Janairun 2024, kuma babu wata magana da aka yi a lokacin kan ficewa daga jam’iyya ko wata yarjejeniyar siyasa."
Ta ƙara da cewa hulɗar Kwankwaso da shugabanni daga jam’iyyu daban-daban abu ne na al’ada a tsarin dimokuraɗiyya, kuma bai kamata a juya hakan zuwa labaran bogi ba.
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa tana ganin waɗannan rahotanni wani yunƙuri ne na ɓata sunan Kwankwaso da rage tasirinsa a siyasar ƙasa inda ta baƙacin ƴan Najeriya su yi watsi da rahotannin ƙarya.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Rasha ta kai hari kan sashen makamashin Ukraine kamar yadda kamfanin makamashi ta DTEK ya bayyana.
Wannan shi ne hari mafi muni a wannan shekara da aka kai kan cibiyoyin makamashin Ukraine ta hanyar amfani da makamai masu linzami masu yawan gaske.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce Rasha ta yi fatali da shawarar da Amurka ta gabatar na dakatar da hare-hare na dan lokaci, domin nuna goyon bayan ga diflomasiyya, sai tayi gaban kanta wajen kai hare-haren a kwanaki mafi tsananin sanyi a wannan shekarar.
Ya ce a daren jiya yanayin ya sauya zuwa ƙasa da degree 20 a ma’aunin Celsius.
Ana sa ran zagaye na biyu na tattaunawar zai fara gobe.

Asalin hoton, PROPHET BERNARD ElBERNARD NELSON-ESHUN/FACEBOOK
Wani shahararren fasto a Ghana, Bernard ElBernard Nelson-Eshun, ya bayyana cewa zai daina wa'azi a bainar jama’a da cikin coci” bayan hasashen siyasa da ya yi ya zama ƙarya.
Faston ya yi hasashen cewa ɗan takarar jam'iyyar adawa NPP, Kennedy Agyapong ne zai lashe zaɓen firaminista amma a ƙarshe ba shi ne ya lashe zaɓen ba lamarin da ya saka hasashen nasa ya zama ƙarya.
Fasto ElBernard ya sa cocinsa inda ya ce babu abin da zai iya hana ɗan kasuwar, Kennedy Agyapong cin zaɓe kan tsohon mataimakin Shugaba, Dr Mahamudu Bawumia.
Amma kuma binciken ra’ayin jama’a kafin zaɓen 31 ga Janairu ya nuna cewa tsohon mataimakin shugaba Bawumia ne ke kan gaba a zaɓen firaministan.
Wasu fastoci kuma sun yi hasashen cewa Dr Bawumia ne zai lashe zaɓen firaminista a 2028.
Faston har littafi ya rubuta da ke ɗauke da babi ɗaya game da hasashen da yadda tsohon ɗan majalisar dattawa mai shekaru 65, Kennedy Agyapong, zai lashe zaɓen.
Amma bayan kaɗa ƙuri’a a cibiyoyin zaɓe 333 a fadin jihohi 16 na Ghana a ranar 31 ga Janairu, ɗan takarar da faston yayi hasashen zai shi bai ci ba inda hukumar zaɓe ta ayyana Bawumia a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Asalin hoton, Dr Nasiphi Moya/X
An yanke wutar lantarkin ofishin jakadancin Najeriya dake birnin Tshwane ta Afirka ta Kudu, sakamakon bashi da ake binsu kan kudin amfani da wutar.
Babban jami’in birnin, Dr Nasiphi Moya, ya bayyana a shafin X cewa an yanke wutar ne saboda ofishin Jakadancin bai biya kudin lantarkin da ya kamata ba.
Sa’o’i kadan bayan haka, Dr Moya ya sanar cewa an dawo da wutar lantarkin.
Wannan ba shine karo na farko da bashi ya jawo yanke wutar lantarki daga ofishin Najeriya a Afirka ta Kudu ba; a watan Janairu na 2023, kamfanin rarraba wutar lantarki na City Power ya yanke wutar Jakadancin Najeriya dake Johannesburg saboda bashin dala 35,000.

Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin jiragen sama na Ethiopian Airlines ya dawo da jigilar fasinjoji zuwa yankin Tigray bayan dakatar da zirga-zirgar na tsawon mako guda sakamakon rikici tsakanin sojojin gwamnatin tarayya da dakarun Tigray.
An dawo da zirga-zirgar ne da safiyar yau, 3 ga Fabrairun 2026, inda jirgin farko daga Addis Ababa ya sauka lafiya a Mekelle, babban birnin yankin.
Majiyoyin BBC sun ce kafin dakatarwar, kamfanin na gudanar da zirga-zirgar jirage takwas a kullum zuwa Mekelle, sai dai a yau an tsara jirage biyar ne kacal.
Kafofin watsa labarai na cikin gida a Habasha sun tabbatar da cewa an dawo da hidimomin sufurin jiragen sama a fadin yankin.
An dakatar da zirga-zirgar ne tun dgaga ranar 29 ga Disambar 2025, daga Addis Ababa zuwa wasu filayen jiragen sama a Tigray, sakamakon ƙarin tashin hankali da fargabar sake ɓarkewar rikici tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyar TPLF.

Asalin hoton, NLC/X
Ƙungiyar ƙwadago ta buƙaci ma’aikatan Abuja su koma bakin aiki bayan cimma matsaya da ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike, biyo bayan taron sulhu da aka gudanar domin warware matsalolin da suka haifar da yajin aikin da ake yi.
Taron ya gudana bisa jagorancin shugaban kwamitin majalisar dattawa na Abuja, Sanata Mohammed Bomoi.
Sanarwar da ƙungiyoyin ƙwadagon da suka haɗa da NLC da TUC suka fitar a ranar 3 ga Fabrairu ta ce an yi tattaunawa mai zurfi tsakanin ɓangarorin da abin ya shafa a taron
A cewar sanarwar, "an tattauna dukkan ƙorafe-ƙorafen da mambobin haɗakar ƙungiyar ƴan ƙwadago JUAC suka gabatar tare da magance su ɗaya bayan ɗaya.
A yayin taron, Minista Wike ya tabbatar wa ƙungiyoyin ƙwadago cewa “za a gina dangantaka bisa mutunta juna da kuma ci gaba da tattaunawa a tsakaninsu.”
Haka kuma, an cimma matsaya cewa babu wani ma’aikaci da za a muzanta ko a hukunta sakamakon shiga yajin aikin da aka yi a baya.
Haka zalika, ɓangarorin sun amince cewa dukkan shari’o’in da suka shafi wannan batu da ke gaban Kotun warware matsalolin ƴan ƙwadago ta Ƙasa za a janye su nan take.
Sakamakon haka, ƙungiyar ta umurci ma'aikatan babban birnin tarayya da su koma aiki nan take.

Asalin hoton, Getty Images
Babban Bankin ƙasar Kenya ya haramta wa ƴan ƙasar amfani da kuɗi wajen yin fure da ake cikra da furen kuɗi, wata sabuwar hanya ta bayar da kyauta da ke ƙara yaɗuwa a lokutan bukukuwa.
A cikin wata sanarwa da bankin ya fitar a shafin sada zumunta na X, Babban Bankin ya bayyana damuwarsa cewa yawaitar amfani da takardun kuɗin ƙasar wajen yin fure da kayan ado na lalata ingancin kuɗin, tare da sa su zama marasa dacewa da ci gaba da yawo a kasuwa.
Babban Bankin ya ce abubuwan da ake amfani da su wajen yin furen kuɗin da suka haɗa da allura da gam da sauran kayan liƙa abubuwa na lalata takardun kuɗi, lamarin da ke kawo matsala wajen amfani da su a na’urorin cirar kuɗi da injinan ƙirga kuɗi da na tantancewa.
“Wannan na sa na’urori su ƙi karɓar kuɗin yayin sarrafawa, kuma hakan na haddasa janye kuɗin da maye gurbinsu, wanda ke janyo asara.” in ji sanarwar.
Babban bankin ya kuma tunatar da ’yan ƙasar cewa bisa ga sashe na 367 na Kundin Hukunta Laifuffuka na Kenya, haramun ne lalatawa da gurɓatawa ko raunana takardun kuɗi.
Wannan gargaɗi na zuwa ne ’yan kwanaki kaɗan kafin ranar Valentine, lokacin da aka saba amfani da furen kuɗi wajen nuna soyayya da bikin wannan rana.

Asalin hoton, Getty Images
Wani babban jami’i a Ma’aikatar Harkokin Afirka ta Amurka, Nick Checker, ya gana da mahukuntan ƙasar Mali a birnin Bamako, a wani yunƙuri da Amurka ke yi na gyara dangantakarta da ƙasashen yankin Sahel da juyin mulki ya shafa.
Nick Checker ya gana da ministan harkokin wajen Mali a ranar Litinin, ganawar da ke nuna wani mataki na buɗe sabon babi a dangantakar Amurka da Mali.
Mahukuntan Mali sun yi maraba da matakin gwamnatin Amurka na amincewa da mutunta ikon ƙasar, tare da nuna aniyarta ta farfaɗo da haɗin gwiwar ɓangarorin biyu.
Ƙoƙarin Washington na yin aiki tare da gwamnatocin soja a yankin Sahel mai fama da matsalar tsaro na zuwa ne a daidai lokacin da Rasha ke ci gaba da faɗaɗa tasirinta a nahiyar Afirka.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin ƙasar Malawi ta sanar da ɓullar ƙwayar cutar polio nau’i na biyu, bayan gano ta a wasu samfurorin muhalli.
Sakataren ma’aikatar lafiya da tsabta, Dan Namarika, ya bayyana cewa an gano ƙwayar cutar ne ta hanyar sa ido na yau da kullum kan ruwan magudanan bayan gida a wurare biyu da ke birnin kasuwanci na Blantyre.
Ma’aikatar lafiya ta yi gargaɗin cewa kwayar cutar na da matuƙar hatsari ga lafiyar jama’a, kuma tana iya haddasa shanyewar gabobi da ba ta warkewa, musamman ga yara, irin yadda kwayar cutar shan inna ta asali ke yi.
Ta ce duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da kamuwar cutar ga wani mutum ba, gano ƙwayar cutar a muhalli na nuna yiwuwar yaɗuwarta idan ba a ɗauki matakan kariya cikin gaggawa ba.
Gwamnatin ta bayyana cewa tuni ta fara ɗaukar matakan gaggawa, ciki har da ƙara sa ido, wayar da kan jama’a, da kuma shirye-shiryen ƙarin kamfen ɗin rigakafin cutar polio a wuraren da abin ya shafa.
Haka kuma, an buƙaci iyaye da masu kula da yara su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun karɓi dukkan allurar rigakafin shan inna domin kare su daga kamuwa da cutar.

Asalin hoton, Getty Images
Kotun warware matsalolin ma’aikata ta ƙasa ta bayar da umarnin wucin-gadi da ke hana manyan ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya, ciki har da NLC da TUC, tare da wasu ƙungiyoyi uku, yin yajin aiki ko zanga-zangar da suka shirya farawa.
Mai shari’a Emmanuel Subilim ne ya bayar da umarnin a birnin Abuja, bayan sauraron buƙatar gaggawa da Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike, tare da hukumar ma'aikatan babban birnin tarayya FCTA suka shigar.
Alƙalin ya umurci waɗanda ake ƙara, tare da wakilansu ko jami’ansu, da su dakatar da duk wani nau’i na yajin aiki ko zanga-zanga har zuwa lokacin da za a saurari buƙatar da aka gabatar.
Haka kuma, kotun ta umurci hukumomin tsaro da ke cikin ƙarar da su tabbatar da cewa an kiyaye doka da oda, tare da hana duk wani rikici a Babban Birnin Tarayya.
Lauyan da ke wakiltar minista Wike da FCTA, Ogwu Onoja, ya shaida wa kotu cewa shugaban ƙungiyar ƙadago ya fitar da wata sanarwar tattara mambobi da ƙungiyoyin haɗin gwiwa domin shirya babbar zanga-zanga a ranar 3 ga Fabrairu, lamarin da ya ce ya saɓa wa umarnin kotu.
Sanarwar, wadda shugabannin ƙungiyoyin biyu suka rattaɓa wa hannu, ta umurci ma’aikatan da ke yajin aiki da su ci gaba, bisa hujjar cewa lauyansu, Femi Falana, ya shigar da ƙara zuwa kotun ɗaukaka ƙara kan hukuncin wucin-gadin da kotu ta yanke.
Haka kuma, an ce haɗakar ƙungiyar ƴan ƙwadago ta JUAC ta fitar da wata sanarwa da ke umartar dukkan ma’aikata da su ci gaba da yajin aikin, matakin da ɓangaren masu ƙara suka ce na iya haddasa rushewar doka da oda a Babban Birnin Ƙasa.
Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 10 ga Fabrairu.