Manyan ƙasashen da suka ayyana sojojin juyin-juya-halin Iran a matsayin ƙungiyar ta'addaci

رژه نیروهای سپاه

Asalin hoton, Irna

Bayanan hoto, A cikin ƴan shekarun da suka gabata, ƙasashe da dama sun ayyana dakarun juyin-juya-hali a matsayin ƙungiyar ta'addanci.
    • Marubuci, سعید جعفری
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, روزنامه‌نگار
  • Lokacin karatu: Minti 4

Ministocin harkokin wajen ƙasashen Turai sun ayyana rundunar juyin-juya-halin Iran a matsayin ƙungiyar ta'addanci, lamarin da ya biyo bayan amfani da ƙarfin da ake zargin dakarun na yi wajen 'murƙushe' masu zanga-zanga.

Duk da cewa wannan ne karon farko da Tarayyar Turai ta saka rundunar sojin wata ƙasa a cikin jerin, a wajen dakarun, wannan ba sabon abu ba ne, kasancewar ƙasashen duniya da dama sun ayyana ta a hakan.

Amurka, Afrilun 2019

A watan Afrilun 2019 ne gwamnatin Amurka ta ayyana dakarun na juyin-juya-hali wato IRGC a matsayin ƙungiyar ta'addanci ta ƙasashen waje wato FTO.

Yunƙurin ya haifar da ce-ce-ku-ce, amma a ƙarshe dai Donald Trump wanda a lokacin yake mulki a wa'adinsa na farko ya dage har sai da ya samu nasarar aiwatar da ƙudurin.

Kafin wannan matakin na Amurka, wasu ƙasashen sun riƙa ayyana wasu ɓangarorin na IRGC, irin su dakarun Quds da kwamandojinsu da ma wasu manyan kwamandojin tsaron ƙasar da jagororin siyasa da ma tattalin arzikin ƙasar.

Ƙungiyoyin da suke cikin FTO wato ƙungiyoyin ta'addanci na ƙasashen waje, wasu ƙungiyoyi ne da ƙasar Amurka ke warewa take sa musu ido, waɗanda take ganin za su iya zama barazana ga tsaron ƙasarta.

Akwai bambanci tsakanin jerin ƙasashen FTO na Amurka da sauran ƙasashen da suke ayyana ƙungiyar a matsayin ta ta'addanci saboda yadda Amurka ke da tsare-tsare da dokoki na musamman game da harkokin ƙungiyoyin.

Yawanci na sauran ƙasashen sun fi aiki a cikin ƙasashen, kuma sun fi mayar da hankali kan ayyana ƙungiyoyin da lafta musu takunkumi da ƙwace kadarorinsu a cikin ƙasar.

A watan Afrilun 2019 ne gwamnatin Trump ta ayyana dakarun juyin-juya-hali a matsayin ƙungiyar ta'addanci

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A watan Afrilun 2019 ne gwamnatin Trump ta ayyana dakarun juyin-juya-hali a matsayin ƙungiyar ta'addanci

Amma saka ƙungiya a cikin jerin ƙungiyoyin ta'addancin FTO a Amurka na da tasiri sosai.

A tsarin FTO, duk wata kadara mallakin ƙungiyar, da wasu masu alaƙa da ƙungiyar sun zama na laifi, kuma za su iya fuskantar ƙalubale ko ƙwace a ko'ina ba Amurka kaɗai ba.

Trump ya ɗauki wannan matakin ne watanni kaɗan bayan ya fice daga jarjejeniyar nukiliya ta 2015.

Ƙasashe da dama da suke ƙawance da Amurka sun yi maraba da matakin, inda Saudiyya da Bahrain suka aike wa Amurka da saƙon jinjina kan ɗaukar matakin.

دو پرچم عربستان سعودی و بحرین

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A shekarar 2018, ma'aikatar harkokin cikin gida ta Saudiyya ta ayyana dakarun na IRGC a matsayin ƙungiyar ta'addanci

Saudiyya da Bahrain, Oktoban 2018

Kafin Amurka ta ɗauki matakin a 2019, Saudiyya da Bahrain sun ayyana rundunar a matsayin ƙungiyar ta'addanci a watan Oktoban 2018.

Sun ɗauki matakin ne domin daƙile abin da suka kira "yunƙurin Iran na tayar da zaune tsaye a yankin,"

A lokacin, ma'aikatar harkokin cikin gida na Saudiyya da jami'an tsaron Bahrain sun sanar da cewa dakarun na da hannu a wasu ayyukan da suka kira na ta'addanci, musamman ayyukan ƙungiyoyinsu maru riƙe da bindiga a Yemen da Iraq da Syria da Bahrain.

Iran ta mayar da martani da kakkausar murya, inda ta zargi Saudiyya da Bahrain da zama ƴan amshin shata ga Amurka.

Shekara biyar bayan ɗaukar matakin ne Iran da Saudiyya suka cimma yarjejeniyar gyara alaƙa bayan wata zama da suka yi a China, kuma tun daga lokacin ne aka ga alaƙa tsakanin ƙasashen biyu na gyaruwa.

Matsin lamba daga iyalan waɗanda harin jirgin saman PS752 ya taka rawa wajen tursasa Canada ta saka dakarun a matsayin ƙungiyar ta'addanci

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Matsin lamba daga iyalan waɗanda harin jirgin saman PS752 ya taka rawa wajen tursasa Canada ta saka dakarun a matsayin ƙungiyar ta'addanci

Canada, Yunin 2024

A watan Yunin 2024 ne Canada ta ayyana dakarun na IRGC a matsayin ƴan ta'adda a ƙarƙashin dokokin ƙasar.

Ƙasar ta ɗauki matakin ne bayan daɗewa ana fafata da tafka muhawara kan ayyukan ƙungiyar, da kuma matsin lamba daga iyalan waɗanda harin jirgin saman PS752, wanda ƙungiyar ta kakkaɓo a watan Janairun 2020.

Gwamnatin Canada ta ce ta ɗauki matakin ne saboda samun hannun dakarun a ayyukan ta'addanci, ciki har da murƙushe wasu da tauye haƙƙin ɗan'adam da sauransu.

Iran dai ta nuna rashin jin daɗinta kan matakin, lamarin da ta kira da siyasa.

Ƙasashen Latin Amurka, 2025

Hukumomi a Australia sun ce dakarun IRGC suna a hannu a wasu aikace-aikacen ta'addanci

Asalin hoton, Irna

Bayanan hoto, Hukumomi a Australia sun ce dakarun IRGC suna a hannu a wasu aikace-aikacen ta'addanci

A ƙasashen Latin Amurka, a shekarar 2025 aka yi ta rububin ayyaka dakarun ƙungiyar a matsayin mambobin ƙungiyar ta'addanci, inda Paraguay da Ecuador suka shige gaba.

Paraguay ta ayyana dakarun ne a matsayin ƴan ƙugiyar ta'addanci a ranar 24 ga Afrilun 2025, inda gwamnatin ƙasar ta ce ta ɗauki matakin ne domin yaƙi da ta'addanci da kuma tsaro a duniya, lamarin da Amurka ta yi maraba da shi.

Ita kuma ƙasar Ecuador ta ɗauki matakin ne a ranar 15 ga Satumban 2025, inda ta saka hannu a doka mai lamba 128, wadda ta ayyana dakarun na Iran da ƙungiyar Hamas da Hezbollah a matsayin ƙungiyoyin ƴanta'adda.

Australia kuma ta alaƙanta ƙungiyar da ta'addanci ne a watan Nuwamban 2025. Matakin ya biyo irin tsarin Amurka ne, musamman kan ƙwace kadarorin ƙungiyar da masu alaƙa da ita.

Argentina, a Janairun 2026

Ajantina ta sanar ne a watan Janairun 2026 cewa ta saka sashen dakarun juyin-juya-hali na Quds a cikin ƙungiyoyin ta'addanci.

Amma ita Ajantina ba kamar sauran ƙasashen ba, ita Quds kawai ta ayyana ba dakarun baki daya ba.

Ajantina ta ƙara da cewa ta ɗauki matakin ne bayan nazarin bayanan sirrin da suka yi kan rahoton ayyukan ta'addanci a ƙasar, ciki har a harin ofishin jakadancin Isra'ila na dandalin Amaya Jewish na 1994, wanda kotun ƙasar ta taɓa banƙado hannun Iran da Hezbollah da dakarun Quds.

Gwamnatin Iran ta soki matakin, wanda ta bayyana da siyasa da zama ƴan amshin shata ga Amurka da Isra'ila.