Abubuwan da ke faruwa a duniya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 20/01/25

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed da Aisha Aliyu Jaafar

  1. China ta zartar da hukuncin kisa kan mutumin da ya bi ta kan mutane da mota

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Mutane sun ajiye furanni a wajen filin wasa na Zhuhai bayan harin

    Ƙasar China ta zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane biyu da suka aikata laifuka daban-daban da suka yi sanadiyar mutuwar mutane 43.

    Ɗaya daga cikin waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa shi ne Fan Weiqi, wanda ya tuka mota a bi ta kan mutanen da suke atisaye a wajen wani filin wasa a birnin Zhuhai na kudancin ƙasar.

    Mutane 35 ne suka mutu sakamakon wannnan abu da Fan ya aikata wanda ya ce ya yi ne a lokacin da yake cikin jimamin rabuwa da matarsa.

    Mutum na biyu da ake yanke wa hukuncin kisa shi ne Xu Jiajin.

    Wani matashi mai shekara 21 wanda ya kashe mutum takwas da wuka a makarantarsu da ke gundumar Jiangsu.

    China ta fi kowace ƙasa a duniya yanke hukuncin kisa.

  2. Wata kotu a India ta yankewa wanda ya kashe likita hukuncin ɗaurin rai da rai

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a Indiya ta yanke hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan wani mutum da aka samu da laifin kashe wata ƙaramar likita bayan ya yi mata fyaɗe.

    Kisan dai ya janyo cece-kuce da zanga-zanga a faɗin ƙasar.

    Alƙalin ya ƙi amincewa da buƙatar yanke hukuncin kisa amma ya ce Sanjay Roy, wani ɗan agajin asibiti a birnin Kolkata wanda aka yanke masa hukunci a ƙarshen mako, zai shafe sauran rayuwarsa a gidan yari.

    Roy ya ci gaba da cewa ba shi da laifi kuma ana sa ran zai daukaka ƙara kan hukuncin a wata babbar kotu.

    Iyalan likitar da aka kashe sun ce suna son a rataye shi, kuma sun kaɗu matuka kan hukuncin.

    Nan da nan bayan yanke hukuncin, likitoci da dama sun yi zanga-zanga a wajen kotun, suna masu cewa ba su gamsu da bincike da kuma hukuncin da aka yanke.

  3. Tanzaniya ta tabbatar da ɓullar cutar Marburg

    Samia Suhulu Hassan

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabar Tanzaniya ta sanar da ɓullar cutar Marburg mai kama da cutar Ebola, mako guda bayan da ministar lafiyarta ta musanta cewa babu wasu masu ɗauke da cutar a ƙasar.

    Shugabar ƙasar Samia Suluhu Hassan ta bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Litinin cewa hukumomin kiwon lafiya sun tabbatar da ɓullar cutar Marburg guda ɗaya a yankin Kagera da ke arewa maso yammacin ƙasar.

    "Muna da ƙwarin gwiwar cewa za mu sake shawo kan wannan ƙalubalen," in ji Samia, yayin da take magana kan ɓarkewar cutar a Tanzania shekaru biyu da suka gabata.

    A ranar 14 ga watan Janairu, hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ba da rahoton ɓullar cutar Marburg da ake zargin an samu bullar cutar a kasar, bayan da aka samu rahoton bullar cutar guda tara da kuma mutuwar mutane takwas cikin kwanaki biyar a Kagera.

    Sai dai Ministar lafiyar ƙasar Jenista Mhagama ta ce bayan da aka yi nazari a kan samfurori, an gano dukkan waɗanda ake zargin ba sa ɗauke da ƙwayar cutar ta Marburg.

    A taron manema labarai na ranar Litinin, wanda aka gudanar tare da hukumar ta WHO, shugaba Samia ta ce gwamnatinta ta ƙara ƙaimi, kuma an aike da tawaga cikin gaggawa don bin diddigin duk wani lamari da ake zargi.

  4. Natanyahu ya aikewa Donald Trump saƙon taya murna

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya taya Donald Trump murna yayin da aka sake rantsar da shi a matsayin shugaban Amurka.

    Netanyahu ya ce wa'adin mulkin Trump na farko ya kasance "cike da abubuwan da ba a taba gani ba a tarihin ƙawancen da ke tsakanin ƙasashenmu biyu".

    Ya ƙara da cewa: "Na yi imanin cewa idan mu ka sake yin aiki tare za mu ɗaukaka ƙawancen da le tsakanin Amurka da Isra'ila zuwa wani matsayi mafi girma."

    Netanyahu ya gode wa Trump saboda "ƙoƙarin da ya yi na ƴantar" waɗanda aka yi garkuwa da su, kuma "yana fatan yin aiki tare da shi don mayar da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su, da kuma gurgunta ƙarfin sojan Hamas da kawo ƙarshen mulkin siyasarta a Gaza.

    Gaza ba za ta sake yin barazana ga tsaron Isra'ila ba"

  5. Hukumar sadarwa ta Najeriya ta amince da ƙarin kuɗin kirar waya

    NCC Logo

    Asalin hoton, NCC

    Hukumar sadarwa ta Najeriya NCC ta amince da buƙatar kamfanonin sadarwa na ƙara kuɗin kiran waya.

    A cikin wata sanarwar da NCC ta fitar ranar Litinin, ɗauke da sa hannun kakakin hukumar, Reuben Mouka, ta ce an bayar da izinin ƙarin ne bisa ga ikon da take da shi a ƙarƙashin sashe na 108 na dokar sadarwar Najeriya ta 2003 (NCA), don daidaitawa da kuma amincewa da farashi da kuma cajin kuɗaɗen da kamfanonin sadarwa ke yi.

    Sanarwar ta ce kamfanonin sadarwa sun miƙa wannan buƙata ce sakamakon yanayin da ake samu a kasuwa.

    “Ƙarin, ba zai wuce kashi 50 cikin 100 ba, duk da cewa ya yi ƙasa da kashi 100 cikin ɗari da kamfanonin sadarwa suka nema, ya zo ne bisa la’akari da sauye-sauyen da za su yi tasiri ga ɗorewar kasuwanci,'' in ji sanarwar.

    Hukumar ta ƙara da cewa “Ba a kara farashin kiran waya ya ba tun shekarar 2013, duk da ƙarin tsadar gudanar da ayyukan yau da kullum da kamfanonin sadarwa ke fuskanta. Ƙarin, an yi shi ne da niyyar cike wagegen giɓin da ake da shi tsakanin tsadar tafiyar da al'amura da kuma kuɗin kira a halin yanzu tare kuma da tabbatar da cewa an biya wa masu amfani da waya buƙatunsu''.

    Hukumar ta kuma tabbatar da cewa an yanke wannan shawarar ce bayan tattaunawa mai zurfi da manyan masu ruwa da tsaki a sassan gwamnati da masu zaman kansu.

  6. Ƙudurin Trump na korar baƙi abin kunya ne - Fafaroma

    Fafaroma

    Asalin hoton, EPA

    Fafaroma Francis ya ce ƙudurin Shugaban Amurka Donald Trump na ƙorar baƙin haure daga Amurka zai zama abin ''kunya'' idan har ya aiwatar.

    Da yake magana a wani shiri na kafar talibijin na Italiya daga gidansa da ke vatican, Fafaroma Francis ya ce idan aka aiwatar da wannan shirin, "hakan bai dace ba, ba haka ake magance matsala," in ji shi.

    A saƙonsa ga Trump a ranar Litinin, Fafaroma Francis ya miƙa gaisuwa gare shi kuma ya buƙace shi da ya jagoranci al'umma ba tare da ''ƙiyayya da ƙyama ba'' kuma ya dage wajen haɓɓaka '' zaman lafiya da sasanci tsakanin mutane''.

    A shekarar 2016, lokacin da Trump ya lashe zaɓensa na farko, Fafaroma Francis ya ce, "duk mutumin da ba ya tunanin komai sai dai gina katanga, ba sulhunta al'umma, ba Kirista ba ne."

  7. Sarki Charles ya aike da sakon taya murna ga Trump

    ...

    Asalin hoton, PA Media

    Bayanan hoto, Sarki Charles da Donald Trump a London a 2019

    Sarki Charles ya aike da sakon taya murna ga shugaba Trump kan bikin rantsar da shi, inda yake yin la'akari da ɗorewar dangantaka ta musamman da ke tsakanin Burtaniya da Amurka.

  8. Tsohon shugaban ƙasa Biden ya bar Washington

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Tohon shugaban ƙasa Joe Biden da uwargidansu Jill Biden sun hau jirgi mai saukar ungulu na Marine One domin barin birnin Washington DC, inda shugaba Donald Trump da uwargidansa Melania suka rako su don yi musu bankwana.

    Tsohuwar mataimakiyar shugaban ƙasa Kamala Harris da mijinta Doug Emhoff sun shiga mota yayin da su ma suka bar harabar majalisar dokokin ƙasar.

  9. Makomar mu za ta yi kyau - Trump

    Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Trump ya yi la'akari da farfaɗowar da ya yi a siyasance inda ya ce "Amurka wasun yi magana". "Na tsaya a gabanku a matsayin shaida cewa kada ku taɓa yarda cewa wani abu ba zai yiwu ba. A Amurka, yin abin da ba zai yiwu ba shine inda mu ka fi yin fice," in ji Trump.

    A ƙarshe ya ce ba za a ci galabar Amurka kuma ba za ta ji tsoron kowa ba "Ba za mu yi kasa a gwiwa ba, daga yau, Amurka za ta zama ƙasa mai ƴanci, mai cin gashin kanta da ƴancin kai," in ji shi.

    "Makomar mu za ta yi kyau, kuma mun sabon babin ci gaban mu ya fara daga yau."

  10. Trump ya zargi China tafiyar da al'amura a mashigar Panama

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Trump yana magana ne game da mashigar Panama, inda ya ce “kyauta ce wauta wadda bai kamata a yi wa Panama ba'', in ji shi

    Ya yi iƙirarin cewa "China tana aiki a" mashigar ruwan Panama. "Ba mu bai wa China ba. Kuma za mu karɓo kayan mu," in ji shi. Magoya bayansa sun jinjina masa a lokacin da ya faɗi hakan yayin da Biden da Harris ke zaune a cikin jama'a.

    Shugaba Trump a farkon wannan watan ya ƙi yanke hukunci kan cewa zai yi amfani da ƙarfin soji ya ƙwace mashigar.

    Ya yi bayani kan lamarin ne a yayin wani taron manema labarai inda ya kuma yi iƙirarin cewa sojojin ƙasar China ne ke tafiyar da mashigin ruwan na Panama.

  11. Mun ayyana dokar ta-ɓaci a kan iyakokin mu - Trump

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Yanzu dai Trump yana ba da cikakken bayani kan wasu umarnin zartarwa da yake shirin aiwatarwa a yanzu da yake shugaban ƙasa.

    A yau, in ji shi, zai rattaba hannu kan wani umarni na zartarwa wanda zai ayyana dokar ta ɓaci a kan iyakar Amurka da Mexico.

    Nan da nan za a dakatar da duk wani shige da fice ba bisa ƙa'ida ba, ya kuma ƙara da cewa gwamnati za ta fara aikin tasa ƙeyar miliyoyin ''masu aikata laifuka'' zuwa inda suka fito.

    Ya yi magana game da wasu ayyukan da yake shirin yi, ciki har da maido da abin da ake kira 'Remain a Mexico' da tura ƙarin sojoji da ma'aikata zuwa kan iyaka.

  12. Akwai dalilin da ya sa aka ceci raina - Trump

    Yanzu dai Trump yana magana ne akan yunƙurin kisan gillar da aka yi masa.

    Ya fara da cewa ba za a kawo cikas a makomar al’ummar Amurka ba.

    Da yake yin tsokaci kan yunƙurin da aka kan rayuwarsa, ya ce a cikin shekaru takwas da suka gabata an yi masa "gwaji fiye da kowane shugaban ƙasa".

    Ya ƙara da cewa wasu sun yi ''ƙoƙarin daƙile manufarmu" kuma sun yi ƙoƙarin ƙwace ƴancinsa "da kuma rayuwata". Ya ce akwai ''dalilin da ya sa aka ceci ransa" - wanda shi ne sake ''dawo da Amurka kan ganiyarta'' - takensa na yaƙin neman zaɓe guda biyu.

  13. Komawa kan mulki cikin ƙwarin gwiwa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Trump ya ci gaba da cewa nan ba da jimawa ba Amurka za ta zama ƙasa "mafi girma, mafi karfi, kuma za ta yi fice fiye da kowane lokaci".

    Ya ce ya koma kan kujerar shugaban ƙasa “ya na mai kwarin gwiwa da kuma kyakkyawar fata” kuma wannan ne “farkon sabon zamani mai ban sha’awa na samun nasarar ƙasa”.

    Ya ƙara da cewa, "Rana ta haskaka duniya baƙi ɗaya kuma Amurka na da yin amfani da wannan damar domin samun ci gaban da ba a taɓa."

  14. Trump yi yi kakkausar suka ga gwamnatin Biden

    Donald Trump a cikin jawabinsa ya soki gwamnatin Biden, musamman matakan da ta ɗauka a kan iyakokin ƙasar.

    Ya ce gwamnati da ta gabata ta samar da mafaka ga "manyan masu aikata laifi" waɗanda suka shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba.

  15. Amurka ta buɗe sabon babin ci gaba daga yau - Trump

    Donald Trump a lokacin da yake jawabi

    Donald Trump ya fara jawabinsa a matsayinsa na shugaban ƙasa da yin jawabi ga takwarorinsa shugabannin ƙasar da sauran waɗanda suka halarci taron, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Kamala Harris da tsohon shugaban ƙasar Joe Biden.

    ''Sabon babin ci gaban Amurka zai fara ne daga yau'' in ji shi ''Daga yau, ƙasarmu za ta fara samun ci gaba kuma za a mutunta a duniya''

    "Zan sanya muradun Amurka a gaban komai."

  16. An rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban Amurka

    Donald Trump lokacin da ya sha rantsuwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Donald Trump ya sha rantsuwar kama aiki, inda yanzu haka ya zama shugaban ƙasar Amurka na 47.

    Wannan ne karo na farko da shugaban ƙasar da ya sha kaye a zaɓe ya sake komawa shugaban ƙasa, tun daga shekarun 1890.

    Yanzu haka ana jiran Trump ya gabatar da jawabi.

  17. An rantsar da JD Vance a matsayin mataimakin shugaban ƙasar Amurka

    An rantsar da JD Vance, kuma yanzu shi ne mataimakin shugaban ƙasar Amurka a hukumance.

    ...

    Asalin hoton, Reuters

  18. Lokacin da Donald Trump ya sumbaci matarsa Melania gabanin shan rantsuwa

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
  19. Abubuwan da Trump zai yi a ranar farko bayan shan ranstuwa

    Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya isa majalisar dokoki inda za a rantsar da shi, amma bayan rantsar da shi, ya shirya wasu jerin matakai da zai zartas, waɗanda za su fara aiki. Ga wasu daga cikinsu.

    Shige da fice::

    • Trump zai ayyana dokar ta-ɓaci a kan iyakar ƙasar don aikewa da ƙarin sojoji da ma'aikata
    • Zai umarci jami'ai su ci gaba da ginin katangar kan iyakar Amurka da Mexico
    • Shugaban na son soke izinin zama ɗan ƙasa ga ƴaƴan baƙin haure da suka shiga Amurka ba bisa ƙa'ida ba
    • Yana shirin mayar da tsarin da ake kira 'Remain-in-Mexico', wanda ke buƙatar baƙi su yi zaman jira a Mexico yayin da suka miƙa buƙatar neman mafaka.

    Tattalin Arziki:

    • Trump na shirin kafa dokar ta-baci a ɓangaren makamashi na ƙasar, wanda a cewarsa zai bai wa ƙasar damar samar da albarkatun ƙasa da kuma samar da ayyukan yi.
    • Har ila yau, yana son "kawo ƙarshen batun tilasta aiki da motoci masu amfani da lantarki" da kuma ƙoƙarin da ake yi na daƙile zaɓin masu amfani kayayyaki, a cewar gwamnatinsa.
    • A cewar jaridar Wall Street, Trump na shirin bai wa gwamnati umarnin sake fasalin alaƙar kasuwancin tsakanin Amurka da China - amma bai shirya sanya sabbin haraji ba.

    Batutuwan da suka shafi jinsi:

    • Yana shirin aiwatar da dokar da za ta kawo ƙarshen tsarin DEI, wanda ke tabbatar da daidaito kan batun jinsi a cikin gwamnatin tarayya"
    • Wani umarni na zartarwa zai "bayyana cewa manufar Amurka ce ta tabbatar da jinsi biyu kaɗai- namiji da mace" waɗanda ba za a iya sauya su ba.
  20. Joe Biden da Kamala Harris a wurin rantsar da Donald Trump

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris a cikin Majalisar Dokokin Amurka gabanin rantsar da zababben shugaban ƙasar, Donald Trump.

    An fashe da tafi a lokacin da suka shigo.