Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahotanni da bayanai na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da duniya 07/06/25

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage

  1. Rufewa

    Nan muka zo karshen rahotanni a wannan shafi.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Ahmad Bawage ke cewa mu zama lafiya.

  2. An ayyana zaman makoki kan mutuwar tsohon shugaban Zambia

    Edgar Lungu

    Asalin hoton, Hindustan Times via Getty Images

    Zambiya ta ayyana zaman makoki na kwanaki bakwai a faɗin ƙasar, kan mutuwar tsohon shugaban ƙasar Edgar Lungu, wanda ya mutu ranar Alhamis a Afirka ta Kudu.

    Za a yi ƙasa da tutoci sannan za a kuma rufe dukkan wuraren nishaɗi daga ranar Lahadi.

    Ana sa ran gawar Mista Lungu za ta isa Zambia a cikin makon nan.

    Gwamnatin ƙasar ta ce za a shirya wa tsohon shugaban ƙasar wanda ya rasu yana da shekara 68 - jana'izar ban-girma.

    Mista Lungu ya mulki Zambiya a matsayin shugaban ƙasa na tsawon shekara shida daga 2015.

  3. An kashe Falasɗinawa shida a wurin rabon agaji a kudancin Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, AFP

    An sake samun afkuwar harbe-harbe a kusa da wurin rabin agaji wanda Isra'ila da Amurka ke goyon baya a kudancin Zirin Gaza.

    Hukumar tsaro ta civil defence karkashin ikon Hamas ta ce an kashe Falasɗinawa shida sannan an jikkata da dama a harbin da Isra'ila ta yi.

    Sojojin Isra'ilar sun ce sun yi harbin ne a matsayin gargaɗi ga waɗanda suke zargi na musu barazana.

    An kashe dubban mutane kwanakin nan yayin ƙoƙarin kai wa wuraren rabon agajin.

    Hukumar da ke kula da wuraren - wadda ta fuskanci suka daga ƙasashen waje - ta ce ta dakatar da aikace-aikacenta domin magance batun yawan jama'a da kuma inganta tsaro.

  4. An samu tashin gobara a masaukin alhazan Najeriya a Shari Mansur

    Aikin Hajji

    Asalin hoton, NAHCON

    Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin gobara a ɗaya daga cikin otal ɗin da alhazan ƙasar ke zaune a ciki a Shari Mansur da ke birnin Makka.

    Wata sanarwa da hukumar ta fitar yau Asabar, ta ce otal ɗin ya kasance yana ɗaukar mahajjata 484, sai dai ba a samu asarar rayuka ba saboda dukkan alhazan na Mina.

    Hukumar agajin gaggawa ta Saudiyya da hukumar gudanarwar otal ɗin ne suka yi ƙoƙarin kashe gobarar.

    Shugaban hukumar Alhazai ta Najeriya, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya bayar da umarnin sauyawa alhazan wurin zama lokacin da kai ziyara wurin.

    Ya jajantawa waɗanda gobarar ta shafa tare ɗaukar alwashin taimaka musu.

  5. Mahajjatan Najeriya lokacin zuwa jifan Shaiɗan a rana ta biyu

    Aikin Hajji

    Asalin hoton, NAHCON

    Mahajjatan Najeriya sun karaɗe tituna a Mina yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa jifan Shaiɗan (Jamarah) a rana ta biyu - a ci gaba da aikin hajji da suke yi.

    Aikin Hajji, ɗaya ne daga cikin shikashikan Musulunci biyar, da ake wajabta wa Musulmai masu hali su yi ko da sau daya ne a rayuwarsu.

    Wannan dai shi ne kusan ibada ta karshe da mahajjatan su ke yi daga cikin manyan ibada da ake gudanarwa.

    Aikin hajji

    Asalin hoton, NAHCON

    Aikin Hajji

    Asalin hoton, NAHCON

    Aikin Hajji

    Asalin hoton, NAHCON

    Aikin Hajji

    Asalin hoton, NAHCON

    Alhazan Najeriya

    Asalin hoton, NAHCON

    Alhazan Najeriya

    Asalin hoton, NAHCON

    Alhazan Najeriya

    Asalin hoton, NAHCON

    Alhazan Najeriya

    Asalin hoton, NAHCON

    Alhazan Najeriya

    Asalin hoton, NAHCON

  6. 'Birtaniya ta kasa rage yawan kuɗaɗen tallafin da take kashewa ga masu neman mafaka'

    Mafaka

    Asalin hoton, EPA

    Alkaluman da gwamnatin Biritaniya ta fitar sun nuna cewa, gwamnatin ƙasar ta kasa rage yawan kuɗaɗen tallafin da take kashewa ga masu neman mafaka a da ke zaune a otal a Birtaniya.

    Ana hasashen za a kashe kusan dala biliyan uku na kuɗaɗen raya ƙasashen ketare kan masaukin masu neman mafaka cikin shekarar da muke ciki, kasa kaɗan da abun da aka kashe a bara.

    Yayin da ya kamata a kashe kudaden agaji a kasashen waje, dokokin kasa da kasa sun ce za a iya kashe su wajen tsugunar da masu neman mafaka da suka isa ƙasar a yan kwanakin nan.

    Wakilin BBC ya ce ba wai wannan yana nufin kawai gwamnati ta kasa cika alkawarinta na rage abin da take kashe wa ba ne wajen biyan hotal ɗin masu neman mafaka, illa har ma da cewa a yanzu babu wadataccen kudin da za a kashe wajen ayyukan jin-kai a kasashen waje.

  7. Harin Rasha ya hallaka mutum aƙalla uku a Ukraine

    Kharkiv

    Asalin hoton, Reuters

    Wani mummunan harin jirage marasa matuki da Rasha ta kai birnin Kharkiv a Ukraine, ya kashe aƙalla mutum uku, tare da jikkata fiye da 20.

    Jami'ai a yankin sun ce an kai harin ne da daddare, inda aka yi amfani da jirage marasa matuki sama da 50 da makaman linzami da kuma bama-bamai.

    Sun ce cikin waɗanda suka jikkata har da wata karamar yarinya da wani yaro.

    Hotuna sun nuna yadda harin ya lalata rukunin gine-gine da kuma gidaje.

    Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce harin ya nufi kan masana'antun sojin Ukraine, ciki har da wurare da ake ajiye jirage marasa matuki.

  8. Ambaliyar da ta afku a Mokwa kaddara ce daga Allah - IBB

    IBB

    Asalin hoton, Social Media

    Tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar da ta afku a garin Mokwa da ke jihar Neja wadda ta laƙume rayuka sama da 200, a matsayin "abin takaici, sai dai kaddara ce daga Allah".

    Babangida ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin tawagar gwamnatin jihar karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar Yakubu Garba, da suka kai masa gaisuwar sallah a gidansa da ke Minna, kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito.

    Yayin da yake miƙa sakon ta'aziyyarsa ga mutanen Mokwa da ma ɗaukacin al'ummar jihar kan bala'in da ambaliyar ta haddasa, Babangida ya buƙaci da su ci gaba da yi wa waɗanda suka rasu addu'a.

    "Abin da ya faru a Mokwa abin takaici ne, sai dai haka Allah ya tsara. Lamari ya fi karfin mu, shi ya sa yana da kyau mu ci gaba da yin addu'a ga mutanen da suka rasu," in ji IBB.

  9. Peter Obi ya yi kira ga Musulmai su ci gaba da sadaukarwa da kuma jajircewa

    Peter Obi

    Asalin hoton, Peter Obi

    Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, ya yi kira ga Musulmin Najeriya da su ci gaba da jajircewa da kuma yin sadaukarwa.

    Mista Obi ya bayana haka ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a don taya al'ummar Musulmi murnar bikin babban sallah.

    Ya ce irin wannan lokaci na murnar bikin sallah, tunatarwa ce na ƙarfin imani, yin ladabi da kuma kaskantar d akai.

    Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya yi fatan cewa murnar bikin wata dama ce ga shugabannin Najeriya a dukkan mataki, na su yi duba kan ɗabi'un kyakkyawan shugabanci.

    "Ina taya illahirin al'ummar Musulmi murnar bikin sallah. Ina fatan wannan lokaci zai ƙara ƙarfafa mana haɗin-kai da kuma zaburar da mu wajen aiki don samar da Najeriya mai nagarta. Eid Mubarak," kamar yadda Mista Obi ya bayyana.

  10. An yi jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya Mohammed Uwais

    Uwais

    Asalin hoton, Nigeria Supreme Court

    An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai shari'a Mohammed Uwais.

    An yi jana'izar ce a babban masallacin ƙasa da ke Abuja.

    Ya rasu ranar Juma'a yana da shekara 89, kamar yadda iyalansa suka tabbatar.

    Ya riƙe mukamin alkalin alkalan Najeriya daga 1995 har zuwa 2006 lokacin da ya yi ritaya.

    Bayan ritayarsa, marigayi shugaban Najeriya Umaru Musa Yar'Adua ya naɗa shi ya jagoranci kwamitin yi wa ɓangaren zaɓe garambawul, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen ƙoƙarin inganta tsarin zaɓen Najeriya.

  11. Amurka na buƙatar sabuwar jam'iyyar siyasa - Elon Musk

    Elon Musk

    Asalin hoton, Getty Images

    Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon Musk, ya kara ruruta wutar rikicin da ke tsakaninsa da shugaban Amurkar Donald Trump, yana mai cewa ƙasar na buƙatar sabuwar jam’iyyar siyasa.

    Ya ce wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da ya nemi mutane su kaɗa a dandalin shi na X, ta nuna cewa kashi 80 cikin 100 na mutane miliyan biyar da rabi da suka amsa, sun amince da shi cewa ya kamata a samar da wata sabuwar jam’iyya ta waɗanda ra'ayinsu ya sha bamban da na manyan jam'iyyun ƙasar Republican da Democrat.

    Mista Trump ya shaida wa manema labarai cewa shi ba ya ta tsohon aminin na sa, don haka can da su gada.

    A birnin Washington, manyan 'yan jam'iyyar Republican na ta nuna goyon bayansu ga Donald Trump.

    Kakakin Majalisar Wakilan kasar Mike Johnson, ya yi gargaɗi game da kalubalantar shugaban.

  12. Tuwon Sallah: Ina zamani ya kai shi?

    Tuwon sallah

    Asalin hoton, KHADIJA DANFULOTI

    Saɓanin shekarun baya, lokacin da matan gida kan shafe tsawon wunin jajibere da daren sallah, suna haƙilon shirya tuwon sallah, a zamanin yau, kuna iya cin girkin sallah, ba tare da hayaƙi ko ƙauri sun bulbule ku ba.

    Kwance cikin falon gida, babu kwaramniya da yarfe gumi a ɗakin girki, kuna iya buɗe kwano kawai, ku ci tuwon sallah mai daɗin gaske cikin annushuwa.

    "Da sallah, akwai manyan mutane da manyan mata, saboda ba sa son wahala, za su zo, su ce a yi musu abincin sallah. Kuma idan an yi musu, za mu ɗauka mu kai musu har gida", in ji wani mai gidan abinci da ake kira Shawarma House a Kano.

    Ya ce abokan hulɗa kan zo tun sallah saura mako biyu, su ce a yi musu girkin shinkafa nau'i uku ko huɗu da dahuwar kaza nau'i biyu. Idan sun gama, sai su zuba a mazubai su kai wa mutum har gida.

  13. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu barkan mu da warhaka.

    Fatan ana ci gaba da shagulgulan sallah lafiya.

    Ku kasance da mu a wannan shafi domin kawo muku yadda bukukuwan sallah ke ci gaba da gudana a ƙasashen Musulmi da kuma sauran labarai a faɗin duniya.

    Ahmad Bawage ne zai kasance da ku.