'Iran ta sake kai hari sansanin sojin Amurka a Bahrain'
Dakarun juyin juya halin Iran, IGRC sun ce sun kai harin ''manyan makamai'' masu linzami kan sansanin sojin Amurka da ke Bahrain.
IRGC ta ce ta kai harin ne a matsayin martani ga wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba na cewa Amurka ta kai hari a wata cibiyar tace ruwa sha a wani tsibiri da ke mashigin Hormuz.
"A matsayin martani ga harin da Amurka ta kai daga sansanin Juffair a kan tashar Qeshm, wannan sansanin na Amurka ya fuskanci mummunan hari daga rundunar IGRC'', a cewar wata sanarwa da IGRC ta fitar ta hanyar kafar yaɗa labaran Fasrna mai alaƙa da IGRC.
A halin da ake ciki kuma, ana jin ƙarar sautin na'urorin ankararwa a Bahrain, inda ma'aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ta buƙaci 'yan ƙasar da mazauna yankin su nufi wani wurin ɓuya mai aminci.
A cikin 'yan mintoci da suka gabata ne ma'aikatar cikin gidan Bahrain ta wallafa a shafinta na X cewa an samu tashin gobara da ƙonewar wasu gine-gine a Manama, babban birnin Bahrain, inda ta ce jami'an kashe gobara na ƙoƙarin kashe wutar.