Farashin kayan abinci ya tashi sakamakon bukukuwan ƙarshen shekara - NBS

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƙididdigar ƙasa ta Najeriya (NBS) ta bayyana cewa farashin kayan abinci ya hau ta dalilin bukukuwan karshen shekara da kuma matsalolin tsaro a watan Nuwamba 2025.
Wannan ya sa matsakaicin hauhawar farashin kaya a wata-wata ya kai kashi 1.22 cikin 100, mafi girma cikin watanni hudu, inda masana ke hasashen irin wannan yanayi zai ci gaba a watan Disamba.
Haka zalika, hauhawar farashin abinci a wata-wata ya kai kashi 1.13 cikin dari, mafi girma cikin watanni uku, sakamakon ƙaruwar farashin wasu kayan abinci da ake amfani da su a kowace rana.
Wannan ya nuna yadda buƙatun ƙarshen shekara da matsalolin tsaro ke shafar rayuwar talakawa musamman wajen samun kayan abinci.
Sai dai, NBS ta bayyana cewa, duk da tashin farashin wata-wata, matsakaicin hauhawar farashi na shekara-shekara ya ci gaba da raguwa na tsawon watanni takwas, daga kashi 16.05 cikin dari a watan Oktoba zuwa kashi 14.45 cikin 100 a watan Nuwamba.
Wannan raguwa ta nuna cewa hauhawar farashin kaya gaba ɗaya yana raguwa a hankali duk da tashin farashin abinci a wasu lokuta.
A bangaren abinci, NBS ta nuna cewa farashin abinci a shekara-shekara ya kai kashi 11.08 cikin 100 wanda ya ragu sosai idan aka kwatanta da kashi 39.93 cikin dari da aka samu a Nuwamba 2024.
Amma a wata-wata, farashin abinci ya tashi da kashi 1.13 cikin 100, musamman farashin tumatir da dankalin da rogo da barkono da ƙwai da naman shanu da albasa da dai sauransu.

















