Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Talata 12/05/2026

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Usman Minjibir

  1. Starmer na fuskantar matsin lamba ya yi murabus

    Firaministan Biritaniya Sir Keir Starmer na fuskantar matsin lamba da ya yi murabus, sakamakon kashin da jam'iyyarsa ta sha a faɗin Birtaniya a zaɓen da aka gudanar a makon jiya.

    Ƴan majalisar wakilai sama da saba'in ne suka yi kira gare shi da ya sauka daga mulki.

    Wakilin BBC ya ce Birtaniya ta yi Firaminista huɗu a cikin shekaru huɗu da suka gabata. Yanzu kuma ga wani ya tsinci kansa a tsaka mai wuya; yayin da yan jam'iyyarsa ke tayar da ƙayar baya, kuma majalisar ministocinsa ta rabu kan ya tsaya ko ya tafi.

    Manyan ministoci da dama sun buƙace shi da ya fitar da jadawalin saukarsa daga karagar mulki.

    A jiya Litinin Sir Starmer ya dage cewa ba zai yi murabus ba, kuma zai yaƙi duk wani ƙalubale ga shugabancinsa.

  2. Mutum bakwai sun mutu a fashewar da ta faru a Pakistan

    Aƙalla mutum bakwai, har da ƴansanda biyu sun mutu a wata fashewa da ta faru a wata kasuwa da ke a Pakistan.

    Fashewar da ta faru a Serai Naurang ta raunata gomman mutane.

    Wannan ne hari na biyu mafi muni da ya faru a yankin cikin kwana buɗu.

    Sojojin Pakistan sun daƙile hari na uku. Sun ce yunƙurin kutsawa da wata babbar mota cike da abubuwan fashewa kan shingen binciken jami'an tsaro kusa da iyakar Khyber Pakhtunkhwa da Punjab bai yi nasara ba.

    Farar hula ɗaya ne ya mutu a lamarin.

  3. An kashe farar hula fiye da 400 a Afghanistan tun Oktoba - MDD

    Alƙaluman da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar sun ce sama da farar hula ɗari huɗu ne aka kashe a Afghanistan tun watan Oktoba, a rikicin kan iyaka da ya ɓarke tsakanin ta da Pakistan.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce aƙalla mutum ɗari biyu da sittin da tara (269) sun mutu a wani hari da jirgin saman yaƙin Pakistan ya kai kan wata cibiyar gyara halin masu ta'ammali da miyagun ƙwayoyi.

    Iyalan waɗanda harin ya rutsa da su sun ce akasarin waɗanda aka kashe maza ne da ke ƙoƙarin rabuwa da jarabar shan ƙwaya.

    Pakistan dai ta musanta wannan zargin, tana mai cewa tana kai hari ne kan cibiyoyin soji da kayayyakin ayyukan ta'addanci.

    Tana zargin gwamnatin Taliban da ba da mafaka ga mayaƙan da ke kai hare-hare ta kan iyaka.

  4. A binciki "asarar rayuka fiye da 100" sanadin harin soji a Zamfara - Amnesty

    Kungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International ta buƙaci hukumomin Najeriya su gudanar da bincike kan harin da sojoji suka kai ta sama wanda rahotanni suka ce ya kashe aƙalla farar hula 100 a kasuwar Tumfa da ke ƙaramar hukumar Zurmi a Jihar Zamfara.

    A cewar ƙungiyar, tun da ƙarfe 12 na ranar Lahadin da ta gabata ne aka ga jiragen yaƙin soji suna shawagi a saman kasuwar da ke ci mako-mako, kafin su sake dawowa su fara ruwan bama-bamai da misalin ƙarfe 2 na rana.

    Daraktan ƙungiyar Amnesty International a Najeriya, Malam Isa Sanusi, ya ce bisa bayanan da suka tattara, kusan duka waɗanda abin ya shafa farar hula ne.

    "Iran wannan ce ta faru a watan da ya gabata a wani gari tsakanin Borno da Yobe inda aka ka hari a kasuwa aka kashe mutum 10 a harin, cikin waɗanda aka kashe har yanzu ba a samu sheda cewa akwai waɗanda ake zargi mayaƙa ba ne." in ji Isa Sanusi.

    Ya ƙara da cewa a makon da ya gabata ma an samu irin wannan lamari a jihar Neja, inda mutane aƙalla 12 suka rasa ransu - yawancinsu ƙananan yara.

    A cewarsa, tun daga shekarar 2017 ake samun irin wannan lamari a arewa maso gabashin Najeriya musamman a jihar Borno inda a cewarsa,ana kai hare-hare da sunan yaƙi da Boko Haram.

    "Ya kamata gwamnati ta tsaya a yi magana da sojoji, kada aikinsu ya zama sanadin asarar rayukan farar hula da mutanen da ba su ji ba su gani ba." in ji shi.

    A cewarsa, a tsarin doka ta ƙasa ta ƙasa ta ƴancin ɗan'adam, bai kamata a cutar da farar hula ba a duk wani aikin samar da tsaro.

  5. Za mu mayar da martani idan aka kai mana hari - Iran

    Iran ta ce dakarunta a shirye suke su mayar da martani kan duk sabbin hare-hare da za a kai mata, bayan da Shugaba Donald Trump ya ce a halin yanzu yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ƙasashen tana tangal-tangal.

    Kakakin majalisar ƙasar Mohammad Ghalibaf ya ce Iran a shirye take ta fuskanci duk wani abin da ka iya faruwa.

    Wakilin BBC ya ce babbar tambaya a nan ita ce yanzu za a ci gaba da tattaunawa ne ko kuma za a koma a ci gaba da artabu.

    Tun da farko Mista Trump ya yi watsi da daftarin zaman lafiya na baya-bayan nan da Tehran ta gabatar kuma ya ce har yanzu yana fatan samun cikakkiyar nasara.

    Farashin ɗanyen mai dai ya tashi a kasuwar duniya ne bisa fargabar za a ci gaba da gwabza faɗa a yankin na gabas ta tsakiya.

  6. Salam Alaikum

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa na Kai Tsaye, barka da safiyar wannan rana ta Talata.

    Kamar kodayaushe, shafin zai kawo muku labaran da suka shafi yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi kan Iran da abubuwan da suka shafi Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

    Kuna iya zuwa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu rahotannin da ma kallon bidiyo.