Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 04/02/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 4 ga watan Fabrairun 2026.

Taƙaitattu

  • Za mu ɗauko ƙwararru daga China domin inganta matatun man Najeriya - NNPCL
  • Gwamnatin Sokoto ta rage aƙalla kashi 60 a farashin takin zamani ga manoman jihar
  • An fara bincike kan kisan Saif al-Islam Gaddafi
  • Saudiyya za ta fara bai wa raƙuman ƙasarta fasfo
  • Latsa nan domin shiga zaurenmu na Whattsapp
  • Najeriya ta tabbatar da zuwan sojojin Amurka ƙasar
  • Yarjejeniyar taƙaita amfani da nukiliya tsakanin Amurka da Rasha za ta ƙare a yau
  • Har yanzu majalisar dattawa ba ta kammala gyaran dokar zaɓe ba
  • Ukraine da Rasha za su fara tattaunawar zaman lafiya a Abu Dhabi
  • Sojojin Sudan sun ƙwace birnin kudancin ƙasar daga hannun RSF
  • WFP ya dakatar da ayyukansa a wasu sassan jihar Sudan ta Kudu
  • Nawa jihohin Najeriya ke samu daga tarayya kuma yaya suke kashe kuɗin?
  • Ƙasashen da azuminsu zai fi tsawo a 2026

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed, Aisha Babangida da Ahmad Bawage

  1. Mu kwana lafiya

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Mu kwana lafiya.

  2. Gwamnatin Kogi ta ba da umarnin rufe makarantun firamare da na sakandare a jihar

    Usman Ododo

    Asalin hoton, facebook/Ahmed Usman-Ododo

    Gwamnatin jihar Kogi ta bayar da umarnin rufe makarantun firamare da na sakandare a faɗin jihar, wani mataki da ta ce ta ɗauka don kare lafiyar ɗalibai da kuma malamansu.

    Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kingsley Fanwo ya fitar, ya ce an ɗauki matakin ne saboda wasu bayanan sirri na tsaro da suka samu, inda suka ga ya dace a ɗauki matakan kare makarantun.

    Fanwo ya ce ba a rufe makarantun ba don tayar da hankalin ɗalibai, amma saboda kare lafiyarsu ba wai sai wani abu ya faru ba.

    Ya ƙara da cewa gwamna Usman Ododo ya umarci dukkan hukumomi da abin ya shafa da su ɗauki matakai na tabbatar da cewa an koma karatu da zarar an ga babu wani haɗari.

    Kwamishinan ya yaba wa jami'an tsaro kan bayar da bayanan sirri a kan lokaci, inda ya kwatanta cewa hakan zai taimaka wa tsarin tsaron jihar.

    Ya tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnati na iyaƙar koƙarinta wajen shawo kan lamarin, inda ya ce jami'an tsaro na aiki tukuru don gano da kuma kaƙƙaɓe maɓoyar ɓata-gari a faɗin jihar.

  3. Mutum 15 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a tekun Turkiyya

    Kwale-kwale

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumomi a Girka sun ce mutum 15 sun mutu sakamakon hatsarin kwale-kwale a kusa da tekun Turkiyya bayan da jirgin ruwan jami'an tsaron teku da kuma na ƴan ci-rani suka garu da juna.

    Waɗanda suka mutun sun haɗa har da mata huɗu, inda hukumomi suka ɗora alhakin hatsarin kan masu safarar mutane.

    Lamarin ya faru ne ranar Talata a kusa da tekun Turkiyya, wanda kamar sauran tsibirai a Girka ya zama wata mahaɗa na masu neman mafaka da ke tsallakawa zuwa Turai.

    Ministan ma'aikatar kula da ƙaura, Thanos Plevris ya kwatanta mutuwar a matsayin "mai ta da hankali" yayin wata muhawara a majalisar dokokin ƙasar kan ɓullo da hukunci mai tsauri ga masu safarar mutane.

    Ƴan ci-rani da dama ne ke tsallake tekun Mediterranean a kowace shekara don zuwa Turai.

    A bara, sama da ƴan ci-rani 1,700 ne suka mutu ko kuma suka ɓata a hanyar zuwa Turai a tekun Mediterranean da kuma tekun Atlantika, a cewar hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya.

  4. Majalisar dattijai ta amince da kudirin dokar zaɓen da aka yi wa gyaran fuska

    Senate

    Asalin hoton, National Assembly

    Majalisar dattijan Najeriya ta zartar da dokar zaɓe da aka yi wa garambawul.

    An zartar da ƙudurin dokar ne bayan nazari da amincewa da sassa 155 da ke ƙunshe a cikin ta.

    Ɗaya daga cikin gyare-gyaren da aka yi wa dokar ta 2022 shi ne rage wa’adin da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ke da shi na futar da sanarwar zaɓe daga 360 zuwa kwana 180.

    Hakan ya biyo bayan amincewa da ƙudirin da Sanata Tahir Monguno ya gabatar fna rage kwanakin da ake buƙatar hukumar INEC ta fitar da sanarwar zaɓe.

    Monguno ya bayyana cewa rage wa'adin kwanakin ya zama dole domin hukumar INEC ta cika sharuɗɗan da ake buƙata wajen fitar da sanarwar, inda ya ce tuni aka makara idan aka yi amfani da kwana 360 bisa la'akari da babban zaɓe mai zuwa.

    Majalisar dai ta fuskanci matsin lamba kan abin da wasu suka bayyana a matsayin jan ƙafa wurin amincewa da ƙudirin dokar zaɓen.

  5. 'A shirye muke don tattaunawa da Iran'

    Trump da Ayatollah

    Asalin hoton, EPA

    Sakataren harkokin wajen Amurka ya ce idan Iran na son a yi tattaunawa a wannan makon, Washington a shirye take.

    Sai dai Marco Rubio ya shaida wa manema labarai cewa, dole ne tattaunawar ta shafi shirye-shiryen nukiliya da na makamai masu linzami na Tehran.

    Amurka da Iran na ci gaba da nuna yiwuwar yin wata ganawa a ranar Juma’a, a daidai lokacin da rashin fahimtar juna ke ƙara tsananta tsakanin ɓangarorin biyu.

    Sai dai, jami’an Amurka sun ce Washington za ta ƙi amincewa da buƙatar Iran ta sauya wurin tattaunawar da aka shirya yi daga ƙasar Turkiyya zuwa Oman.

  6. Za mu ɗauko ƙwararru daga China domin inganta matatun man Najeriya - NNPCL

    NNPCL

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya ce yana tattaunawa da wata matatar man fetur a ƙasar China domin inganta matatun man fetur na Najeriya.

    Babban jami'in gudanarwa na kamfanin, Bayo Ojulari ne ya bayyana haka a ranar Laraba, inda ya ce suna buƙatar ƙwararru ne domin mayar da matatun gwamnatin ƙasar su koma aiki da kyau bayan shekarun da suka ɗauka ba sa aiki yadda ya kamata.

    Ojulari ya ce nazarin da suka gudanar bayan ya fara aiki ne suka gano cewa ana asarar kuɗi ne maimakon cin riba wajen gudanar da matatun.

    Ya ce sun amince da ɗauko ƙwararru waɗanda suka san aikin ɓangaren, maimakon ɗauko ƴan kwangila.

    "Shirye-shirye sun yi nisa. Muna ci gaba da tattaunawa da wasu ƙwararru da muke so su inganta mana ayyukan matatun. Kuma gobe wasu daga ciki za su fara zuwa matatun."

  7. Wani hari ya lalata asibitin ƙungiyar MSF a Sudan ta Kudu

    MSF

    Asalin hoton, MSF/Reuters

    Ƙungiyar likitoci ta Medecins sans Frontieres ta ce an lalata ɗaya daga cikin asibitocinta a wani hari da dakarun gwamnati a Sudan ta Kudu suka kai cikin dare.

    Ta ce harin da aka kai jihar Jonglei ya lalata asibitin wanda ke ɗauke da kayan abinci da magunguna.

    An kuma saci abinci a wani ƙarin cibiyar lafiya na ƙungiyar ta MSF.

    Shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya WFP ya dakatar da ayyukansa a jihar Upper Nile, bayan da far wa ɗaya daga cikin motocinsa da kuma sace abinci.

    Ana samun ƙaruwar tashin hankali a makonnin baya baya-nan tsakanin magoya bayan shugaba Salva Kir da kuma abokin gabarsa Riek Machar.

    Lamarin ya ɗaiɗaita mutum sama da 250,000.

  8. Gwamnatin Sokoto ta rage aƙalla kashi 60 a farashin takin zamani ga manoman jihar

    Sokoto

    Asalin hoton, Sokoto state government

    Gwamnatin jihar Sokoto ta ƙaddamar da sayar da takin zamani ga manoman jihar a farashi mai rahusa, wanda a cewar gwamnatin zai ba su damar gudanar da noman rani cikin sauƙi.

    Gwamnan jihar, Ahmed Aliyu ne ya ƙaddamar da rabon takin a ƙaramar hukumar Wurno ta jihar a ranar Laraba 4 ga watan Fabrairu, inda ya ce inganta harkokin noma na cikin manyan ƙudurorin gwamnatinsa.

    Gwamnan ya ce sun sayo tirela 52 na takin Urea da tirela 50 na NPK, kuma za a raba su ne ga ƙananan hukumomin jihar guda 23.

    "Kowace ƙaramar hukuma za ta samu tirela biyu na Urea da tirela ɗaya na NPK, kuma za a sayar ne a farashi mai rahusa."

    Ya ce gwamnati ta rage kashi 62 a farashin takin NPK, da kashi 60 a tankin Urea, sannan ya ce sun yi haka domin ƙananan manoma su samu taki. "Sau uku muna raba takin kyauta a baya, amma sai muka lura asalin manoman ba sa samu. Shi ya sa muka ɓullo da wannan tsarin na sayar da takin kai-tsaye a farashi mai rahusa, sannan muka yi tsarin aiwatar da rabon a bayyane domin ya isa inda ake so."

    Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta bayar da kwangilar gyara madatsar ruwa ta Lugu, sannan ya ce nan gaba za a gyara ta Kware domin amfanin masu noman rani, sannan ya ƙara cewa za su sayo tarakta guda 250 domin sauƙaƙa wa manoman aiki.

  9. An fara bincike kan kisan ɗan tsohon shugaban Libya Saif al-Islam Gaddafi

    Saif al-Islam

    Asalin hoton, Reuters

    Masu shigar da ƙara a Libya sun ce sun kaddamar da bincike kan kisan Saif al-Islam Gaddafi, ɗa ga tsohon shugaban Libya Kanal Muammar Gaddafi.

    An kashe Saif al-Islam mai shekara 53, wanda a baya aka yi yakinin cewa zai gaji mahaifinsa, lokacin da wasu ƴanbindiga huɗu suka kutsa cikin gidansa da ke birnin Zintan, a cewar wata sanarwa da ofishinsa ya fitat.

    "Saif ya mutu ne sakamakon raunukan bindiga," in ji masu shigar da ƙara a Libya ranar Laraba, inda suka ƙara da cewa ana can ana ƙoƙari don ganin an gano waɗanda suka aikata laifin.

    A wasu bayanai na daban, ƴar uwar marigayin ta faɗa wa gidan talabijin na Libya cewa ya mutu ne a kusa da kan iyakar ƙasar da Aljeriya.

    Lauyan Saif al-Islam ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa "wasu mutum huɗu ne" suka yi wa Saif kisan gilla a gidansa da ke birnin Zintan, duk da cewa ba a san wanda ya ɗauki alhakin kisan ba.

    Ofishin mai shigar da ƙara a Libya ya ce an aika ƙwararru kan binciken laifuka na kimiyya zuwa birnin Zintan da ke arewa maso yammacin ƙasar dion gudanar da bincike.

  10. An ba da umarnin dakatar da aikin rusau a tekun Makoko na Legas

    Makoko

    Asalin hoton, Gift Ufuoma/BBC

    Majalisar dokokin Jihar Legas ta ba da umarnin dakatar da duk wani aikin rusau cikin gaggawa a yankunan tekun Makoko da Oko-Agbon da Shogunro, yayin da rusau din da gwamnati ta fara ya raba dubban mutane da muhallansu tun watan Disamban 2025.

    Shugaban kwamitin wucin gadi na majalisar, Hon. Noheem Adams, ne ya bayar da umarnin a ranar Talata, bayan wani babban taro da aka yi da shugabannin al’ummar yankunan.

    Wannan tsoma baki ya zama wani muhimmin mataki na majalisar wajen sanya ido kan ayyukan bangaren zartarwa na sabunta birane, inda majalisar ta ƙara ba da umarnin cewa a biya mazauna yankin da abin ya shafa diyya.

    Majalisar ta kuma ba da umarnin a sanya su a cikin kwamitocin gaba domin tabbatar da ana tafiya tare da mutane da abin ya shafa kai tsaye.

  11. Ukraine da Rasha sun fara tattaunawar zaman lafiya a Abu Dhabi

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Yayin da aka fara tattaunawar zaman lafiya tsakanin Kyiv da Moscow a birnin Abu Dhabi, wani babban jami’in Ukraine a yankin Donetsk ya ce babban makami da Rasha ta harba ya afka wata kasuwa mai cike da jama’a da safiyar yau a garin Druz-kiv-ka.

    Harin ya halaka mutum 7 tare da jikkata wasu 15.

    Duk da rashin ƙwarin gwiwa game da sakamakon tattaunawar, Ukraine ta ce za su fi mayar da hankali kan batutuwan soji, inda tawagarsu ke ƙoƙarin fahimtar abin da Moscow da Washington zasu gabtar.

    Idan har aka tashi ba tare da cimma matsaya ba, akwai yiwuwar Rasha ta ci gaba da kai hare-hare kan Ukraine don ganin ta miƙa wuya.

    A nata ɓangaren, fadar Kremlin ta sake jaddada matsayar ta na neman Ukraine ta mika kusan kashi ashirin cikin ɗari na yankin Donetsk, da take ci gaba da riƙewa.

  12. Saudiyya za ta fara bai wa raƙuman ƙasarta fasfo

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasar Saudiyya ta sanar da shirinta na fara bai wa miliyoyin raƙuman da ke ƙasar fasfo, domin inganta kula da su da kuma sauƙaƙa tsarin gudanar da muhimmin fannin kiwon raƙuma.

    Jami’ai sun ce wannan mataki zai taimaka wajen ƙara yawan amfanin fannin, da inganta inganci, tare da samar da sahihin kundin bayanai da za a rika dogaro da shi wajen tantance shaida da mallakar raƙuma.

    Wani saƙo da ma’aikatar muhalli, ruwa da noma ta wallafa a shafukan sada zumunta ya nuna hoton fasfon, wanda ke da launin kore, tare da tambarin ƙasar da kuma hoton raƙumi mai launin zinariya.

    A shekarar 2024, gwamnatin Saudiyya ta ƙiyasta cewa akwai kusan raƙuma miliyan biyu da dubu dari biyu a ƙasar.

    Saudiyya kuma na shirya gasar kyau na raƙuma a lokacin bukukuwan shekara-shekara, lamarin da ke nuna muhimmancin raƙumi a al’adu da tattalin arziƙin ƙasar.

  13. Ana fargabar waɗanda ƴan bindiga suka kashe a Kwara sun kai 70

    ...

    Jami’an agajin gaggawa na Red Cross a yammacin Najeriya sun ce ana fargabar adadin mutanen da ƴan bindiga suka kashe a jihar Kwara ya kai kusan 70, biyo bayan wani mummunan hari da aka kai a ƙauyen Woro.

    Red Cross ta ce har yanzu akwai mutanen da ba a gano inda suke ba tun bayan harin, inda ƴan bindigar suka kuma banka wa shaguna wuta tare da ƙone gidan sarkin gargajiya na yankin.

    A wani lamari na daban, rahotanni daga jihar Katsina da ke arewacin ƙasar na nuna cewa aƙalla mutum 21 daga cikin mazauna ƙauyuka ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren ƴan bindiga.

    Gwamnatin Najeriya ta ce za ta ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, a daidai lokacin da hare-haren kan fararen hula ke ƙaruwa a sassan arewa da tsakiyar ƙasar.

    Hukumomi da jami’an tsaro sun ce ana ci gaba da bincike da kuma ƙoƙarin gano mutanen da suka ɓace, yayin da al’umma ke fatan ɗaukar matakai masu inganci domin daƙile yawaitar hare-haren ƴan bindiga.

    ...
  14. Yadda ƴanbindiga suka kashe mutum 21 a harin ramuwar gayya a Katsina

    ...

    Asalin hoton, Dikko Radda/X

    Aƙalla mutum 21 ne suka mutu a wani hari da ƴan bindiga suka kai a yankin Tafoki da ke ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina kamar yadda shugaban ƙaramar hukumar ya shaida wa BBC.

    A tattaunawarsa da BBC, shugaban ƙaramar hukumar, Surajo Aliyu Daudawa, ya ce ƴan bindigar sun kashe mutanen ne a matsayin ramuwar gayya bayan kashe wani nasu da aka yi a yankin duk da cewa an yi sulhu da su kusan watanni biyar da suka wuce.

    "Mazauna yankin sun wayi gari cikin tashin hankali bayan harin, duk da cewa kafin hakan ba a fuskanci wata matsala ba tun bayan yarjejeniyar sulhu da aka yi da ƴanbindigar." in ji shi

    Shugaban ya bayyana cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya kai 21, amma babu wanda aka sace.

    Ya kara da cewa rahotanni sun nuna cewa ƴanbindigar sun yi niyyar tafiya da mata, amma shugabanninsu suka hana hakan, suna mai cewa "ba sace-sace ne ya kawo su ba, illa ramuwar gayya."

    Da BBC ta tambaye shi abin da ya jawo maganar ramuwar gayya bayan an yi sulhu, Daudawa ya ce "kwana biyar kafin harin, an samu labarin cewa an sace mutane biyu tare da kwace babur guda ɗaya, sai aka tuntubi ƴanbindigar kamar yadda yarjejeniyar sulhun ta tanada domin su taimaka wajen bincike."

    "Daga baya aka gano cewa mutanen biyu suna gidajensu, amma aka tarar da gawar ɗaya daga cikin ƴan Fulanin dajin da suka je taimaka musu neman mutanen, abin da ya jawo zargin cewa hakan ne ya haddasa harin." in ji shi.

    Shugaban ya ƙara da cewa an riga an yi jana’izar mutanen da aka kashe a garin Doma, yayin da al’umma ke kira ga hukumomi da su dauki matakan da za su hana sake faruwar irin wannan hari, musamman bayan an yi sulhu da nufin dawo da zaman lafiya a yankin.

  15. 'Harin Isra’ila ya kashe mutum 17 a Gaza'

    ....

    Asalin hoton, Reuters

    Aƙalla Falasɗinawa 17 ne suka mutu a harin da Isra’ila ta kai a Arewaci da Kudancin Gaza in ji asibitoci.

    Sojojin Isra’ila sun ce hakan ya faru ne bayan “’yan ta’adda” a cewarsu sun buɗe wuta a arewacin Zirin, inda suka raunata soja sosai a yayin wani aiki kusa da Layin Yellow.

    Sojojin sun ƙara da cewa rukunin sojoji masu manyan motoci da jiragen sama sun kai hari a yankin a matsayin martani ga abin da suka kira “takewa kai tsaye” ga yarjejeniyar tsagaita wuta.

    Hukumomi a asibitoci sun ce an kashe yara shida a harin a birnin Gaza da Khan Younis.

    Asibitin Al-Shifa a birnin Gaza ya ce ya karɓi gawawwakin mutum 13, ciki har da yara biyar, wadanda aka kashe yayin da aka kai hari kan tantuna da gidaje a unguwannin Zeitoun da Tuffah na gabashin birnin.

    Asibitin Nasser a Khan Younis ya ce an kai gawawwakin mutum huɗu asibitin, ciki har da yaro ɗaya bayan harin da aka kai a yankin Qizan Rashwan na kudu.

    Duk Isra’ila da Hamas suna zargin juna da ƙeta yarjejeniyar kusan kullum tun bayan da tsagaita wutar ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba.

    Ma’aikatar lafiyar Hamas a Gaza ta ce aƙalla mutum 529 aka kashe daga harin Isra’ila, yayin da sojojin Isra’ila suka ce an kashe sojojin su guda huɗu daga hare-haren Hamas.

  16. WFP ya dakatar da ayyukansa a wasu sassan jihar Sudan ta Kudu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shirin Abinci na Duniya (WFP) ya dakatar da ayyukansa a wasu sassan Jihar Upper Nile ta Sudan ta Kudu bayan harin da aka kai wa wasu ayarin jiragen ruwa guda 12 da ke ɗauke da fiye da tan 1,500 na kayan agaji.

    Shirin ya ce wasu matasa masu ɗauke da makamai ne suka kai wa jiragen ruwan hari tare da sace kayan agajin da suka haɗa da kayan abinci da waɗanda ba abinci ba a ƙarshen makon da ya gabata.

    A cikin wata sanarwa da WFP ɗin ya fita a ranar Laraba, ya ce sun tilasta dakatar da duk ayyukansu a ƙaramar ƙukumar Baliet bayan faruwar lamarin.

    “An kai hari sau da dama kan kayan abinci masu muhimmanci fiye da tan 1,500 da aka tura,” in ji sanarwar.

    Shirin ya nemi gwamnatin Sudan ta Kudu da shiga tsakani cikin gaggawa domin dawo da kayan da aka sace.

    “Ba za mu yarda da harin da ake kai wa ma’aikatan jin kai ba, muna kira ga dukkan ɓangarorin da ke rikici da juna su girmama rawar da ma’aikatan jin kai ke takawa da kuma kiyaye wurare ajiye kayan aikin da ake amfani da su wajen bayar da agaji,” in ji WFP.

    A halin yanzu, rikici na kara tsananta a wasu sassan Jihar Jonglei, inda rahotanni ke nuni da cewa sojojin gwamnati sun sake karbar wasu yankuna da sojojin adawa na SPLA-IO ke riƙe da su

  17. Sojojin Sudan sun ƙwace birnin kudancin ƙasar daga hannun RSF

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Sudan sun ce sun ƙwace birnin Kadugli, babban birnin jihar Kordofan ta Kudu daga hannun dakarun RSF bayan ƙawanyar da suka wa birnin sama da shekaru biyu, kamar yadda jaridar Sudan Tribune mai zaman kanta ta ruwaito.

    Ƙwace birnin Kadugli ya bai wa sojojin gwamnati damar haɗa birnin da Dilling, gari na biyu mafi girma a Kordofan ta Kudu wanda sojojin suka kwace a ranar 26 ga watan Janairu.

    Shugaban ƙasar Sudan kuma babban hafsan soji, Laftanar Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya yaba da ƙwarewar da dakarun suna nuna wajen ƙwace birnin, yana mai cewa za a ci gaba da ayyukan soja har sai an sake karɓar cikakken iko da ƙasar.

    Shugaban ya ce yana maraba da kiraye-kirayen ƙasa da ƙasa na tsagaita wuta, amma ya jaddada cewa duk wata yarjejeniyar tsagaita wuta dole ne ta zo bayan RSF ta janye daga biranen da take riƙe da su.

    A halin da ake ciki, aƙalla fararen hula takwas ciki har da mata da yara sun rasa rayukansu, yayin da wasu 11 suka jikkata, bayan wani harin jirgin sama maras matuƙi kan wata cibiyar lafiya a Kadugli, sa’o’i kaɗan bayan sojoji sun shiga birnin.

  18. Najeriya ta tabbatar da zuwan sojojin Amurka ƙasar

    ...

    Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya tabbatar wa BBC cewa wata ƙaramar tawagar sojojin Amurka tana aiki a cikin ƙasar.

    Ya ce sojojin na Amurka za su kasance suna bayar da horo ga sojojin Najeriya domin shiryasu wajen gudanar da ayyuka.

    Ministan bai bayyana yawan sojojin ba, ko lokacin da suka isa ƙasar, ko inda aka jibge su, ko tsawon lokacin da za su zauna a Najeriya ba.

    Sojojin Amurka da na Najeriya sun shafe shekaru masu yawa suna gudanar da bayar da horo na haɗin gwiwa, da nufin ƙarfafa ƙwarewar Najeriya a fannin tattara bayanan sirri da yaƙi da ta’addanci.

    Shugaban sojin Amurka a Afirka AFRICOM, Janar Dagvin R. M. Anderson, ya shaida wa manema labarai a ranar Talata cewa tura sojojin Amurka zuwa Najeriya ya kasance ne bisa buƙatar gwamnatin Najeriya, kuma hankalinsu ya ta’allaka ne kan tallafi wajen tattara bayanan sirri.

    Najeriya ta ƙara haɗin gwiwa da Amurka ne a daidai lokacin da take fuskantar manyan ƙalubalen tsaro, ciki har da hare-haren ‘yanbindiga da sace-sacen mutane don neman kuɗin fansa, da yaɗuwar ‘yan bindiga.

  19. Yarjejeniyar taƙaita amfani da nukiliya tsakanin Amurka da Rasha za ta ƙare a yau

    Shugaban Rasha Vladimir Putin da shugaban Amurka Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Yarjejeniyar da aka cimma ta ƙarshe kan taƙaita amfani da makaman nukiliya tsakanin Rasha da Amurka za ta ƙare a yau Laraba.

    Hakan zai kawo ƙarshen duk wata iyaka a dokance da ƙasashen ke da ita ta adadin makaman nukiliya da za su ajiye cikin shirin ko-ta-kwana.

    Yarjejeniyar wadda aka sanya wa hannu a shekarar 2010 ta taƙaita yawan makaman nukiliya da kowacce daga cikin ƙasashen za ta ajiye cikin shirin ko-ta-kwana zuwa kimanin 1,500.

    Duk da cewa sun jingine yarjejeniyar tun shekara uku da suka gabata, amma an yi amannar cewa ƙasashen biyu sun ci gaba da yin biyayya ga sharuɗɗanta.

    Masana na fatan cewa kawo ƙarshen yarjejeniyar zai samar da sabuwar dama ta tattaunawa kan sanya ido ga mallakar makamai tsakanin ƙasashen duniya.

    Sai dai wasu na fargabar cewa hakan na iya haifar da wani yanayi na rige-rigen mallakar makamai, yayin da ƙasashe da dama ke ƙoƙarin ganin sun mallaki makamin nukiliya.

  20. Har yanzu majalisar dattawa ba ta kammala gyaran dokar zaɓe ba

    ...

    Asalin hoton, Nigeria Senate

    Majalisar Dattawan Najeriya har yanzu ba ta cimma matsaya kan ƙudirin gyara sassan dokar zaɓen 2022 da aka gano cewa suna da matsala ba bayan da ta kasa yanke hukunci a ranar Talata, duk da shafe sama da sa'o'i huɗu tana nazarin rahoton wani kwamitin wucin-gadi na mambobi bakwai a wani zama na musamman.

    Majalisar ta fara tattaunawa ne kan rahoton kwamitin da aka kafa a makon da ya gabata domin tattarawa da daidaita ra’ayoyi da gudummawar ’yan majalisa kan ƙudirin dokar, kafin daga bisani ta koma zama na musamman domin duba takardun da suka shafi ƙudirin.

    Sai dai bayan komawa zaman, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ƙi bayyana sakamakon tattaunawar da aka yi, lamarin da ya sa ya ɗage zaman majalisar zuwa ranar aiki ta gaba.

    A makon da ya gabata ne Majalisar Dattawan ta kafa kwamitin mambobi bakwai domin tattarawa da daidaitawa da kuma tace ra’ayoyi da shawarwarin sanatoci kan Kudirin gyaran dokar zaɓe ta 2022, tare da umarnin gabatar da rahoton kwamitin ga majalisar a ranar Talata mai zuwa.

    An ɗauki wannan mataki ne bayan majalisar ta shafe sama da sa'o'i biyu tana duba tanade-tanaden ƙudirin dokar a wani zama na musamman.