Zelensky ya kori babban hafsan sojin Ukraine daga muƙaminsa

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya sallami babban hafsan sojin ƙasar, Oleksandr Syrsky, bayan shafe kwanaki ana zanga-zanga sakamakon sauke matashin ministan tsaro da ke da farin jini.
Zelensky ya sanar a ranar Talata cewa ya naɗa kwamandan rundunar haɗin gwiwa, Mykhailo Drapaty, a matsayin sabon babban hafsan sojin Ukraine.
Syrsky mai shekara 60, wanda ya samu horon soja tun zamanin Tarayyar Soviet, ya riƙe muƙamin tun 2024.
Ana kuma kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin gogaggun kwamandojin Ukraine, musamman bayan ya jagoranci kare birnin Kyiv lokacin da Rasha ta fara mamayar ƙasar baki ɗaya a shekarar 2022.
Sauke shi daga muƙamin ya biyo bayan rikicin siyasa da ya kunno kai bayan gwamnatin Zelensky ta cire ministan tsaro Mykhailo Fedorov daga mukaminsa, lamarin da ya jawo zanga-zanga daga masu goyon bayansa.
A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Telegram, Zelensky ya ce ya yanke shawarar naɗa Mykhailo Drapaty a matsayin sabon babban kwamandan rundunar sojin Ukraine.
Shugaban na Ukraine ya kuma gode wa Syrsky da dukkan sojojin ƙasar saboda rawar da suka taka wajen kare gaban yaƙi da kuma tsaron Ukraine.










