Mu kwana lafiya
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi.
Mu hadu da ku gobe da safe domin samun wasu sababbi daga sassan duniya.
Umar Mikal ke cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 30/10/2025
Daga Aisha Babangida, Abdullahi Bello, da Umar Mikail
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi.
Mu hadu da ku gobe da safe domin samun wasu sababbi daga sassan duniya.
Umar Mikal ke cewa mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Reuters
Hamas ta miƙa wa kungiyar bayar da agaji ta Red Cross abin da ta ce gawarwakin 'yan Isra'ila biyu ne da take rike da su a Gaza.
An dauki gawarwakin zuwa Isra'ila domin yin gwaji a kansu. Mika gwarwakin wani bangare ne na yarjejeniar tsagaita wuta da Shugaban Amurka Trump ya jagoranci ƙullawa, wadda kuma ta gamu da cikas a farkon makon nan bayan da hare-haren Isra'ila da suka kashe Falasdinawa fiye da 100 a Gaza.
Isra'ila na ci gaba da zargin Hamas da jan kafa wajen mika sauran gwarwakin, sai dai Hamas ta ce abu ne mai wahala a iya gano su gaba daya bayan luguden wutar da Isra'ila ta dauki shekara biyu tana yi a Gaza.

Asalin hoton, Reuters
Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ya yi Allah wadai da ayukkan dakarun RSF a Sudan mai nasaba da cin zarafin ɗan'adam a birnin El-Fasher.
Babban jami'in MDD na hukumar ayyukan agaji, Tom Flesher, ya shaida wa kwamitin tsaron cewa ya zama wajibi a gurfanar da waɗanda aka samu da hannu a kisan jama'a da kuma aikata lalata a birnin El-Fasher.
"Awa ɗaya da ta gabata na yi magana da jami'in hukumar, wanda ya shaida min RSF sun soma bincike kan wadanda ake zargi da cin zarafin jama'a, har ma an kama wasu. Kuma sun yi alkawarin cigaba da kare fararen hula," in ji shi.
Mayaƙan na RSF sun musanta zargin aikata kisan kare-dangi a kan daruruwan fararen hula.

Asalin hoton, @iamElaw
Mataimkain gwamnan jihar Bayelsa a kudancin Najeriya ya shigar da ƙarar majalisar dokokin jihar, da shugabanta, da sufeto janar na 'yansanda kan zargin yunƙurin tsige shi.
Lawrence Ewhrudjakpo ya yi zargi cewa ana yi masa bi ta da ƙulli ne saboda ya ƙi yarda ya bi gwamnan jihar zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya daga PDP, wadda aka zaɓe su a cikinta.
Cikin ƙorafin da ya miƙa wa kotun, Mista Ewhrudjakpo ya ce wasu mambobin majalisar na ƙulla shirin tsige shi daga muƙaminsa.
Rahotonni kuma na cewa majalisar na yi wa wasu shugabannin ƙananan hukumomi barazanar tsigewa saboda sun ƙi barin PDP ɗin.

Asalin hoton, House of Reps
'Yanmajalisar wakilan Najeriya shida daga jihohin Enugu da Filato sun koma jam'iyyar APC mai mulki daga jam'iyyun adawa.
Matakin nasu ya sa jam'iyyar ta Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ta samu rinjayen kashi biyu cikin uku a majalisar mai mambobi 360.
Biyar daga cikin 'yanmajalisar na PDP ne daga jihar Enugua kudancin ƙasar, da kuma ɗaya na Labour Party daga jihar Filato a arewaci, kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ya bayyana.
Adadin mambobin APC sun kai 243 kenan, wanda ya zama 2 cikin 3 na mambobi 360. Rahoton ya bayyana mambobin babbar jam'iyyar adawa PDP sun koma 74, LP 21, NNPP 15, APGA 5, ADC 1, SDP 2, YPP 1.
Wannan cigaban da jam'iyar mai mulki ta samu zai iya ba ta damar sauya duk matakin da take so a majalisar yayin da tuni 'yansiyasar Najeriya suka fara shrin babban zaɓe na 2027.

Asalin hoton, EPA
Shugaban Lebanon Joseph Aoun ya umurci dakarun sojin ƙasar da su dauki matakan fuskantar duk wani sojan Israila da ya tsallaka iyakar kudancin kasar.
Wannan na faruwa ne bayan wata kafar yaɗa labaran Labanon ta bayar da rahoton cewa sojojin Isra'ilar sun mamaye garin Blida da ke kan iyaka, kuma sun yi harbin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya.
Gwamnatin ta Lebanon ta ce ta samu bayanan sojoji sun kuma kai hari a wani wurin ibada.
Sai dai sojojin na Isra'ila sun ce sun kai samamen ne a ginin saboda suna zargin mayaƙan Hezbollah na amfani da shi.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nemi sababbin hafsoshin tsaron ƙasar su zage damtse domin magance sababbin barazanar tsaro da ke kunnowa.
Da yake magana bayan bikin ƙara wa shugabannin rundunonin soji girma yau Alhamis a Abuja, Tinubu ya ce: "Barazanar tsaro na ƙara sauyawa a kodayaushe, kuma abin da ya fi damun gwamnatinmu shi ne ɓullar sababbin ƙungiyoyin 'yanbindiga a arewa ta tsakiya, da arewa maso yamma, da wasu yankunan kudanci."
A jiya Laraba ne majalisar dattawa da ta wakilai suka amince da Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin babban hafsan tsaro, da Manjo Janar Waidi Shaibu a matsayin hafsan sojan ƙasa, da Rear Admiral Idi Abbas hafsan sojan ruwa, da Air Marshall Kennedy Aneke hafsan sojan sama, da Manjo Janar Emmanuel Undiendeye shugaban tattara bayanan sirri na soja.
"Ba zai yiwu mu ƙyale wannan sabuwar barazanar ta ci gaba ba. Dole ne mu ɗauki mataki da wuri. Mu sare kan macijin," in ji Tinubu.
Yayin bikin an ƙara wa Olufemi Oluyede muƙami zuwa janar, Waidi Shaibu zuwa laftanar janar, Idi Abbas zuwa Vice Admiral, da Kevin Aneke zuwa air vice marshall, da kuma Emmanuel Undiendeye zuwa laftanar janar.

Asalin hoton, @The Governor of Bauchi State
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya sanya hannu kan ƙudirin doka da ke neman ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi 29 a cikin jihar.
Muƙaddashin mataimakin majalisar dokokin Jihar, Musa Yerima ne ya tura wannan ƙudiri zuwa ga majalisar dokokin Najeriya, domin neman amincewarta kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A halin yanzu dai jihar BAuchi - wadda ke yankin arewa maso gabashin Najeriya na da ƙananan hukumomi 20.
Idan aka ƙara sabbin 29 ɗin da ake son ƙirƙira, jihar za ta samu jimillar ƙananan hukumomi 49, yayin da ake ƙiyasin cewa jihar na da yawan jama’a kusan miliyan 10.
A cikin wasiƙar da Yerima ya aika wa shugaban kwamitin Majalisar Dattijai kan sake duba kundin tsarin mulki, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana cewa majalisar dokokin jihar ta amince da dokar kafa sabbin ƙananan hukumomin a shekarar 2025.
Ya kuma ce sabbin ƙananan hukumomin ba za su fara aiki ba sai Majalisar Tarayya ta amince da su, kamar yadda sashe na 8 na kundin tsarin mulki na 1999 ya tanada.
Yerima ya ƙara da cewa an bi dukkan ƙa’idojin doka na kundin tsarin mulki wajen zartar da wannan ƙudiri.

Asalin hoton, Nigerian Army
Sabon Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Laftanar janar Olufemi Olatubosun Oluyede, ya karɓi ragamar aiki daga hannun tsohon hafsan, Janar Christopher Gwabin Musa mai barin gado.
Wannan al’amari ya gudana ne a wani gagarumin biki da aka gudanar a hedkwatar rundunar sojin ƙasa a Abuja, inda manyan jami’an tsaro da sauran manyan baƙi suka halarta.
Hakan na zuwa ne bayan da majalisar dattawa ta tabbatar da amincewarta da sabon nadin sabbin hafsoshin sojin ƙasar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa majalisar a makon da ya gabata.
A jawabin sa bayan karɓar ragamar aiki, Janar Oluyede ya gode wa shugabannin ƙasa bisa amincewa da shi, tare da yin alkawarin ci gaba da gina rundunar sojin Najeriya bisa gaskiya da tsari, da ƙwarewa, domin tabbatar da tsaro a fadin ƙasar.
Tsohon hafsan sojin, Janar Christopher Musa, ya yaba wa jami’ansa bisa sadaukar da kai da yin aiki tukuru, tare da kira da su su ci gaba da bayar da haɗin kai ga sabon kwamandan.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa gwamnatinsa ta rage wasu harajin da ta ɗora kan kayayyakin da ake shigo da su daga China, matakin da ya kawo ɗan sauƙi ga kamfanoni da dama da rikicin kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
Haka kuma, bayan ganawar da Trump ya yi da shugaban China Xi Jinping, Trump ya ce sun cimma matsaya kan batun ma’adinan “rare earths” da ya kasance ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka haddasa rikici tsakanin ɓangarorin biyu.
Bayan wannan sanarwa, gwamnatin China ta bayyana cewa ta dakatar da aiwatar da wasu matakan da suka shafi takunkumin fitar da ma’adinan “rare earths”, wanda hakan ke nuna alamar sassaucin dangantaka tsakanin manyan kasashen biyu a fagen kasuwanci.

Asalin hoton, Reuters
Shugaban dakarun RSF, Janar Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, ya ayyana bincike kan abin da ya bayyana a matsayin take haƙƙi da ake zargin dakarunsa sun aikatawa yayin ƙwace birnin El-Fasher.
Wannan sanarwa ta Hemedti ta zo ne bayan rahotannin kisan jama’a da dama da aka yi bayan mamayar da RSF ta yi wa birnin a yankin Darfur a ranar Lahadi.
Ana sa ran Majalisar Tsaron Majalisar Dinkin Duniya za ta yi zama kan lamarin Sudan, wadda ke cikin shekararta ta uku na yaƙin basasa tsakanin sojoji da dakarun RSF.
Shugaban RSF ya yi magana ne bayan fushin duniya kan rahotannin kisan jama’a da dama a El-Fasher, wanda aka bayyana a bidiyo a shafukan sada zumunta da sojojinsa suka wallafa.
Hemedti ya nuna alhini kan masifar da ta rutsa da mutanen El-Fasher, sannan ya amince cewa sun take haƙƙin mutane wanda kwamitin bincike da aka tura birnin zai gudanar.

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan takarar jam’iyyar adawa a Kamaru Issa Tchiroma ya sha alwashin ci gaba da dagewa har sai ya yi nasara kan Shugaba Paul Biya yana mai cewa shi ne ya samu yawan ƙuri’u a zaɓen..
Tchiroma ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su ci gaba da zanga-zangar nuna rashin amincewa da sakamakon zaben da ya bayyana Paul Biya a matsayin wanda ya ci zaɓen.
Wannan na zuwa ne yayin da wata ƙungiyar al’umma ta yi Allah wadai da mutuwar mutane da kama-karya da aka yi yayin zanga-zanga a birane da dama na ƙasar.
Shugaba Paul Biya, wanda shi ne tsohon shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya mai shekaru 92, yana mulkin Kamaru tun shekarar 1982.
Zaben ranar 12 ga Oktoba da aka bayyana sakamako a ranar Litinin ya ƙara jefa ƙasar cikin tashin hankali, yayin da masu sukar Biya ke zarginsa da amfani da hukumomin gwamnati wajen riƙe mulki da ƙarfi da karfe.

Asalin hoton, Getty Images
A jiya Laraba ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da sauya ra'ayinsa kan jerin masu laifi da ya yi wa afuwa, bayan ƙorafe-ƙorafe daga al'ummar ƙasar.
Tun farko jerin sanayen ya ɗauki hankalin al'umma ne bayan shugaban ya yi afuwa ga mutanen da ake ganin ba su dace ba.
Sai dai kundin tsarin mulkin Najeriya ne ya ba shi damar yin afuwa ga duk wanda ya ga dama.
Sanarwar da fadar shugaban Najeriya ta fitar a ranar Larabar ta ce an rage yawan waɗanda aka yi wa afuwa daga 175 zuwa 116.
Duk da haka batun ya ci gaba da janyo martani daga masana da masu lura da al'amuran yau da kullum.
A tattaunawarsa da BBC, Audu Bulama Bukarti, masani kan shari’a da tsaro a ƙasashen Afrika, ya ce siyasa na daga cikin manyan dalilan da suka tursasa wa Tinubu sauya ra'ayi game da afuwar.
“Duk da cewa shugaban ƙasa ya bi ƙa’ida wajen zaɓen wadanda ya yi wa afuwa, ba doka ce ta tilasta masa ya janye afuwar ba, siyasa ce ta sa ya canza ra’ayi.
"Ya ga yadda mutane suka nuna rashin jin daɗi, sannan ya fahimci cewa ci gaba da yin afuwar ga mutum 175 na iya kawo matsala ga siyasar sa, shi ya sa ya rage wasu daga cikin jerin mutanen,” in ji Bukarti.
Al'ummar Najeriya sun yi ƙorafi kan yadda aka sanya sunayen mutanen da aka yanke wa hukunci kan safarar ƙwaya da kuma masu manyan laifuka, kamar Maryam Sanda, wadda aka yanke wa hukuncin kisa bayan kashe mijinta.
Sai dai Bulama Bukarti ya ce akwai kuma hanyoyi biyu da za a iya kallon wannan mataki na shugaba Tinubu.
“Na farko, matakin na nuna cewa fadar shugaban ƙasa na sauraron ra’ayin ‘yan Najeriya, kuma idan suka nuna rashin jin daɗi, za a gyara abin da ya dace. Na biyu, wasu na ganin gwamnati ba ta tsayawa ta tsefe abubuwa, wato ba ta tsayawa ta yi dubi na tsanaki ga abubuwa kafin aiwatarwa.”
“Wannan karo na uku ko na hudu ne da shugaban ke aiwatar da wani abu sai ya janye bayan an yi ca. Ina ganin fadar shugaban ƙasa ya kamata ta yi tsanaki kafin fitar da sanarwa,” in ji Bukarti.

Asalin hoton, Tanzania Electoral Commission INEC
Hukumar zaɓe ta Tanzaniya (INEC) ta fara bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka fara gudanarwa a jiya Laraba.
Har yanzu dai yankuna huɗu kacal ne suka samu nasarar miƙa sakamakonsu.
Daga cikin sakamakon da aka tattara, 'yar takarar shugaban ƙasa ta jam’iyyar mai ci ta CCM, Samia Suluhu Hassan, ce ke kan gaba bisa kuri’un da aka ƙididdige.
Haka zalika, an samu rahotannin zanga-zanga a yankin Meriwa, a babban titin dake tsakanin Dodoma da Dar es Salaam, inda 'yan sanda suka tarwatsa masu zanga-zangar das hayaƙi mai sa hawaye da harsasai.
An kuma rufe titin Singida zuwa Arusha saboda tsoron sake ɓarkewar zanga-zangar.

Masu zanga-zangar adawa da gwamnati sun ci gaba da gudanar da zanga-zanga a rana ta biyu na zaɓen shugaban ƙasar Tanzaniya a Dar es Salaam.
'Yan sanda sun yi amfani da harsasai da hayaƙi mai sa hawaye don tarwatsa masu zanga-zangar da suka fito tituna, bayan rikicin da ya faru jiya Laraba, ranar da aka fara kaɗa kuri’a.
Zanga-zangar ta barke ne saboda tsare wasu manyan shugabannin jam’iyyar adawa da hana su shiga zaɓen shugaban ƙasa, da kuma zargin danniya ga masu sukar gwamnati kuma suna neman a yi gyara a tsarijn zaɓe.
Rahotanni Reauters sun nuna cewa zanga-zangar ta faru a wurare da dama ciki har da Mbagala, Gongo la Mboto da Kiluvya.
Ofishin jakadanci Amurka a ƙasar Tanzaniya ya gargaɗi Amurkawan da ke ƙasar da su ƙara yin taka tsantsan sanadiyyar halin da ake ciki bayan zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar jiya.
Gargadin da ofishin jakadancin ya yi na cewa Amurkawa su ƙaurace wa wuraren da ake zanga-zanga da duk wani taron al'umma, su kasa kunne domin jin abin da ke faruwa a kafafen yaɗa labarai tare da yin taka tsantsan sosai a unguwannin da suke zama.
Wannan ya biyo bayan jerin zanga-zanga da ake samu a ƙasar tun bayan kammala jefa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasar na jiya Laraba.
Hukumomi sun ƙaƙaba dokar hana fita a wasu birane sannan an katse sadarwar intanet.

Asalin hoton, Presidency NG
Majalisar dokokin Najeriya ta amince da bukatar shugaban ƙasa, Bola Tinubu, na karɓo bashin dala biliyan 2.347 daga kasuwannin hada-haɗar kuɗi ta duniya domin cike giɓin kasafin kuɗin 2025 da kuma sake biyan takardun lamuni na Eurobonds da ke ƙarewa.
Tinubu ya bayyana cewa bashin zai kasance bisa tanade-tanaden dokar kula da bashi ta 2003, wadda ke buƙatar amincewar majalisa kafin ɗaukar sabon bashi ko sake biyan tsoffin bashi.
Shugaban ƙasa ya ce za a samo kuɗin ne ta hanyar kayan aikin kuɗi kamar Eurobonds da haɗin bashi daga bankuna, ko wasu hanyoyin wucin gadi dangane da yanayin kasuwa.

Asalin hoton, Getty Images
Ana sa ran zanga-zangar adawa da gwamnati za ta ci gaba a yau a kasar Tanzaniya, bayan tashin hankalin da ya ɓarke da katsewar intanet a jiya yayin gudanar da zaɓen shugaban ƙasar.
Hukumomin ƙasar sun umarci ma’aikatan gwamnatin da sauran mutane da su zauna a gida saboda tsananin tashin hankali yayin da ƙungiyoyin kare hakkin dan Adam ke kira da a kwantar da hankali bayan rahotannin mutuwa da jikkata da aka samu.
Dokar hana fita da aka saka da daddare a Dar es Salaam ba ta hana tashin hankali ba.
Masu zanga-zangar suna neman a yi gyara a tsarin zaɓe, inda arangama tsakaninsu da ‘yan sanda ta rikiɗe zuwa rikici.
Majiyoyi daga Asibitin Kasa na Muhimbili sun shaida wa BBC cewa suna karɓar mutane da dama da suka jikkata sakamakon tarzomar.
Kungiyar Amnesty International ta tabbatar da mutuwar farar hula daya da jami’in ɗansanda daya, tare da kiran a gudanar da bincike mai zaman kansa kan yadda ‘yan sanda suka mayar da martani.
Har yanzu intanet ɗin ƙasar a katse yake yayin da ake sa ran Shugaba Samia Suluhu Hassan za ta sake samun wa’adin mulki na biyu bayan an hana ‘yan adawa da dama tsayawa takara.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ya bai wa ma’aikatar tsaron ƙasar umarnin fara gwajin makaman nukiliya, kamar yadda sauran kasashe ke gudanar da irin wadannan gwaje-gwaje.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Trump ya ce za a fara gwajin nan da nan ba tare da ɓata lokaci ba.
Amurka dai ta yi gwajin makamin nukiliyarta na ƙarshe a shekarar 1992, kuma har yanzu ba a bayyana ainihin abin da Trump ke nufi da wannan umarni ba.
A kwanakin baya-bayan nan, ƙasar Rasha ta sanar da kammala gwajin sabbin makamanta na nukiliya, lamarin da ke ƙara haifar da fargabar sabuwar takaddama tsakanin manyan ƙasashen duniya masu karfin makaman nukiliya.

Asalin hoton, Getty Images
Firaiministan Jamaica, Andrew Holness, ya ce guguwar Melissa ta yi mummunar barna a wasu ɓangarori na ƙasar inda ta lalata garin Black River gaba daya.
Mr Holness ya shaida wa BBC cewa, gwamnatinsa na duba irin ɓarnar da kuma aikin dawo da hasken lantarki dama sadarwa a yanzu.
Firaiministan ya ce suna gyara hanyoyin da za su samu su kai wasu al'ummomin da wannan iftila'in ya shafa inda zasu kai musu kayan agaji kamar abinci da basu wuraren zama na wucin gadi da kuma magunguna.
Wata ƙididdiga da aka yi akan irin asarar da guguwar ta haddasa ta nuna cewa akalla kashi 40 cikin 100 na tattalin arzikin da kasar ke samu a shekara ya salwanta.