Yadda ake aikin ceto mutane daga ɓarnar harin Isra'ila
Hotunan da muka samu daga kamfanonin dillancin labarai na nuna yadda ma'aikatan agaji ke ta ƙoƙarin zaƙulo mutane daga ɓaraguzai a Beirut bayan harin Isra'ila.
Harin ya lalata wasu gidaje a tsakiyar birnin.
Wakilin BBC a Beirut ya ce suna ganin mutane na dudduba ɓaraguzai a cikin duhu da zimmar ceto waɗanda gini ya danne.
Zuwa yanzu mutum 18 ne suka mutu tare da raunata wasu kusan 100, a cewar hukumomin Lebanon.