Mu kwana lafiya
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi na Ranar Sallah.
Muna fatan za ku kasance da mu gobe da safe domin samun wasu sababbin rahotonnin.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 30 ga watan Maris 2025
Isiyaku Muhammed da Umar Mikail
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi na Ranar Sallah.
Muna fatan za ku kasance da mu gobe da safe domin samun wasu sababbin rahotonnin.

Asalin hoton, Reuters
Jama'a a Burkina Faso sun ce an kashe gomman sojoji da sauran jami'an tsaron sa-kai a wani hari da mayaƙa masu iƙirarin jihadi suka kai.
Sun ce mayaƙan ƙungiyar JNIM mai alaƙa da ƙungiyar al-Qaeda sun ƙwace iko da garin Diapaga a ranar Juma'a.
Rahotanni sun ce mayaƙan sun fatattaki wani barikin soji, inda suka kashe mutum 52.
Har yanzu hukumomi a Burkina Faso ba su ce komai ba kan lamarin, amma tun bayan ƙwace mulki a 2022, gwamnatin sojin ƙasar ke fama da matsalar hare-haren 'yanbindiga.

Asalin hoton, Reuters
Shugaba Trump na Amurka ya shaida wa kafafen yaɗa labaran ƙasar cewa yana fushi da takwaransa na Rasha, Vladmir Putin, saboda matsayarsa game da matakan sulhu da Ukraine.
Wakilin BBC ya ce kafar talabijin ta NBC ta ce a wata hira ta minti 10 da ta yi da Trump ta waya, shugaban ya shaida masu cewa yana fushi da yadda Putin ya soki salon mulkin Shugaba Zelensky na Ukraine, duk da cewa shi da kansa ya taɓa kiran Zelensky mai mulkin kama-karya a baya.
NBC ta ce Shugaba Trump ya sha alwashin ƙaƙaba sababbin haraji a kan ƙasashen da ke sayen mai daga Rasha, idan har aka gaza cimma tsagaita wuta tsakanin Ukraine da Rasha.
Mista Trump ya kuma bayyana shirinsa na ganawa da Putin nan gaba a makon nan.

Asalin hoton, Facebook/Sanusi II Dynasty
Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kano ta ce ta kama mutum ɗaya bisa zargin kashe wani jami'in tsaron sa-kai a filin Idi.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce wani matashi mai shekara 20 ne ya daɓa wa jami'in wuƙa yayin da yake aikin kare tawagar Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II bayan sallar Idi a yau Lahadi.
Kazalika, an ji wa wani jami'in sa-kai ɗin rauni kuma yana jinya a asibitin Murtala Muhammad da ke ƙwaryar birnin Kanon.
"Rundunar ta fara bincike kan lamarin, har ma ta gayyaci Shamakin Kano Alhaji Wada Isyaku domin amsa tambayoyi," a cewar sanarwar da DSP Abdullahi Kiyawa ya fitar.
A ranar Juma'a ne rundunar 'yansandan ta sanar da hana gudanar da hawan sallah a jihar, yayin da Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero ke ci gaba da bayyana kansu a matsayin sarakunan Kano.

Asalin hoton, EPA
Rundunar sojin Myanmar na ci gaba da kai hare-hare ta sama da ta ƙasa babu ƙaƙƙautawa a yankunan da girgizar ƙasa ta ɗaiɗaita.
An jefa bamabamai a yankin Sagaing da kuma kusa da jihar Karenni, inda aka raunata mutum ɗaya, a cewar wata majiya.
Kamar yadda muka dinga kawo rahotonni, Sagaing na cikin wuraren da suka fi shan wahalar girgizar ƙasar.

Asalin hoton, Reuters
Ƙungiyar Hamas ta ce tana goyon bayan komawa yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza, ta amfani da shawarar da masu shiga tsakanin suka bayar wadda za ta kai ga sakin ƙarin fursunonin Isra'ila biyar da kuma tsagaita wuta a Gaza tsawon kwana 50.
Babban jami'in Hamas da baya zaune a Gaza, Khalil al-Hayyam, ya ce ƙungiyar ta amince da ƙudirin da masu shiga tsakani daga Masar da kuma Qatar suka gabatar.
Ofishin firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ma ya ce ya karɓi tayin, amma ya gabatar da nasa tayin ''wanda ya ci karo da wanda masu shiga tsakanin suka gabatar masa, a ƙarƙashin jagorancin Amurka.''
Ƙarin bayani - https://trib.al/9WdeMvc

Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya dakatar da ayyukan ƴan sa-kai da aka fi sani da vigilante a faɗin jihar baki ɗaya.
Haka kuma gwamnan ya dakatar da kwamandan askarawan tsaron jihar, Friday Ibadin.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Umar Musa Ikhilor ya fitar, inda ya ce gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne bayan samun rahoton farko-farko na kisan matafiya ƴan arewa a yankin Uromi da ke jihar.
Ya ce "ƴan sa-kan da suka kashe matafiya a ranar 27 ga watan Maris ba su da rajista da hukumar askarawan tsaron jihar Edo. Aika-aikar da suka yi ba al'adar mutanen Edo ba ce, kuma gwamnatin Okpebholo ba za ta aminta ba.
"Ana cigaba da gudanar da bincike, kuma tuni an kama mutum 14, sanna ana farautar sauran," kamar yadda sanarwar, wadda tashar Channels ta ruwaito ta nuna.

Asalin hoton, Nigerian Presidency

Asalin hoton, Nigerian Presidency

Asalin hoton, Nigerian Presidency

Asalin hoton, Nigerian Presidency

Asalin hoton, Amnesty International
Ƙungiyar Amnesty International mai fafatikar kare haƙƙin ɗan'adam ta ce dole binciken da za a yi, ya zama sanadiyar hukunta waɗanda suke da hannu a kisa tare da ƙona matafiya ƴan arewa da aka yi a garin Uromi da ke jihar Edo.
Shugaban ƙungiyar a Najeriya, Isa Sanusi ne ya bayyana haka, inda, "dole hukumomin Najeriya su tabbatar an gudanar da bincike a bayyane, sannan kuma binciken ya zama silar adalci ga waɗanda aka kashe da iyalansu. Ya kamata a riƙa bayya yadda binciken ke gudana tun daga farko har zuwa lokacin yanke hukunci."
Amnesty ta ce abin da ya faru Uromi na nuna yadda ake ƙara samun ƙungiyar ƴan sa-kai na garuruwan da suke kusa da manyan hanyoyi suke tare hanyoyin suna aikata ba daidai ba.
"Yadda aka daɗe ana irin waɗannan kashe-kashen na nuna akwai gazawar gwamnati wajen kare rayukan al'ummarta."
Isa Sanusi ya ƙara da cewa Amnesty ta yi Allah wadai da kisan, sannan ya sake nanata kiransu ga gwamnatin Najeriya da ta ɗauki matakin da ya dace.

Asalin hoton, Getty Images
A Najeriya, iyalan mahardacin Alkur'anin nan da ƴanbindiga suka sace a jihar Katsina tare da mahaifinsa sun ce sun kuɓuta daga hannun masu garkuwa da su.
Kimanin mako biyu da suka wuce ne dai aka sace Alaramma Abdulsalam Rabi’u Faskari, wanda ya zama gwarzon gasar karatun Alƙur’ani mai girma ta ƙasa da aka yi a jihar Kebbi tare da mahaifinsa da ƴanuwansa bayan gwamna jiharsa ta Katsina ya karrama shi.
Malam Rabiu Zakariya Faskari, shi ne mahaifinsa da aka sace su tare a yankin Faskari, ya bayyana wa BBC cewa sun tsira ne ba tare da biyan kuɗin fansa ba.
Ya ce asali a Katsina ne ƴanbindiga suke riƙe da su, sai ƙasurgumin ɗanbindiga, Yellow ya zo daga Zamfara, ya "ƙwace mu da ƙarfin tsaiya daga inda muke. Sai da ya musu dukan tsiya kafin ya tafi da mu," in ji shi.
Ya ce an yi ciniki, amma ɗanbindigar ya ƙi amicewa. "Haka muka cigaba da zama muna addu'a, sannan ana yi mana addu'a. Sai ranar Juma'a kawai aka zo aka ce mana mu fito mu tafi. Yaransa suka ɗauko mu suka tsallako da mu dajin Munhaye suka kawo wani gari suka ajiye mu. Daga garin sai da muka yi tafiya ta awa huɗu."
Ya ce da suka hau babur ne shi ne ɗan acaɓa ke faɗa musu an kashe shugaban dabar mai suna Yellow, "ashe shi ya sa yaransa suka sake mu muka tafi."

Asalin hoton, Tinubu X
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana jin daɗi da godiyarsa ga ƴan Najeriya bisa addu'o'in da suka yi masa na cika shekara 73 a duniya.
Tinubu ya bayyana haka a taron buɗa-baki na musamman da ya jagoranta a fadar gwamnatin ƙasar a daren Asabar domin murnar zagayowar ranar haihuwarsa, kamar yadda mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya bayyana a wata sanarwa.
Da yake jawabi kan fafatukar da ya sha kan zaɓensa na shekarar 2023, Tinubu ya ce sai da ya kusa haƙura da takarar baki ɗaya saboda ƙalubale.
"Waɗanda suke kusa da ni sai suka fara tunanin ba zan kai ga gaci ba. Wani daga cikinsu ya taɓa samuna, ya ce min yana neman naira dubu 50 ne zai saya wa wani kawunmu abinci. Ya ce min saboda ni babu tsabar kuɗi a gari, mutane suna ta wahalar neman tsabar kuɗi. Kuma kawunmu ɗin attajiri ne, amma ko naira 10,000 babu a hannunsa.
"Da na miƙa masa tsabar kuɗin naira 50,000, sai ya kalle ni ya ce min da wahala in samu nasara, ni kuma na ce masa zan samu nasara."
Tinubu ya ce a lokacin ne jikinsa ya yi sanyi har ya fara tunanin ajiye takarar, "amma sai Aminu Masari ya ƙarfafa min gwiwa, ya ce ba matsala, kada in juya baya," in ji shi.
Tinubu ya ƙara da cewa ya karɓi ƙasar ne a daidai lokacin da take fama da matsin tattalin arziki, "shi ya sa na yanke shawarar ɗaukar matakai masu tsauri tun a farko a mulki, ciki har cire tallafin man fetur wanda ba ya cikin asalin jawabin da zan yi."

Asalin hoton, Reuters
Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce matsanancin ƙarancin magunguna a ƙasar Myanmar na kawo cikas ga ƙoƙarin ceto masu sauran numfashi daga girgizar ƙasar da ta afka wa ƙasar ranar Juma’a.
Ta ce mutanen da ke yankin da girgizar ta fi yin ta'adi suna cikin mawuyacin hali - yayin da asibitoci suka cika maƙil.
Gwamnatin sojin ƙasar ta ce aƙalla mutum 1,700 aka tabbatar sun mutu, sannan ana sa ran adadin zai ƙaru saboda akwai sama da mutum 300 da ba a gansu ba.
Wakilin BBC ya ce an fara isar da kayan agaji da ake matuƙar buƙata, amma yaƙin basasar da ake ci gaba da yi a ƙasar na kawo tsaiko.
Gwamnatin masu rajin kare dimokuraɗiyya ta buƙaci mayaƙanta su dakatar da kai hari kan dakarun gwamnatin soji musamman a yankin da bala'in ya shafa.

Asalin hoton, FB/Multiple
Ƙungiyar dattawan arewa ta magantu kan kisan matafiya ƴan yankin arewa da aka yi a garin Uromi da ke jihar Edo, inda ta ce yankin arewa ya daɗe yana haƙuri da cin kashin da ake yi masa, amma kuma an kusa ƙure su.
Ƙungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakinta, Farfesa Abubakar Jika Jiddere ya fitar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Sanarwar ta ce, "dattawan arewa sun damu matuƙa da kisan dabbanci da rashin tausayi da aka yi wasu mafarauta ƴan arewa da suke hanyarsu ta komawa gida arewa domin bikin sallah. Muna Allah wadai da wannan aika-aikar.
"Mun daɗe muna haƙuri da irin wannan cin kashin da ake mana a kudancin Najeriya. Dole a kawo ƙarshensa haka," in ji shi.
Ya ƙara da cewa dole a kama waɗanda suka aikata laifin, sannan a musu hukunci a bayyane.
"Sannan dole a biya diyyar waɗanda aka kashe kamar yadda yake a addinance, sannan dole gwamnatin Edo ta fito ta bayar da haƙuri.
Dattawan sun kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta Edo ta cika waɗannan buƙatun nan da kwana da 14, "idan kuma ba a ga wani mataki ba zuwa lokacin, dattawan arewa za su yi amfani da duk matakan da suka dace wajen bin haƙƙin ƴaƴanta da aka kashe."

Asalin hoton, AFP
Shugaban riƙo na Syria Ahmed al-Sharaa ya sanar da kafa sabuwar gwamnati - wanda shi ne sabon mataki na baya-bayan da ya ɗauka tun bayan faɗuwar gwamnatin Assad.
Sabuwar gwamnatin ta ƙunshi ministoci daga ɓangarorin ƙabilu tsiraru da addinai na Syria.
Akwai mace mabiya addinin kirista - Hind Kabawat -- da za ta jagoranci ma'aikatar harkokin jin daɗi da walwalar jama'a.
Shugaban Syria Ahmed Al Sharaa ya sanar da kafa gwamnati tare da alƙawalin haɗa kan al'ummar Syria.
Babban ƙalubalen da ke gaban gwamnatinsa shi ne aikin sake gina Syria bayan shafe sama da shekara goma ana yaƙi.
Sabon shugaban wanda tsohon ɗantawaye ne -- ya yi alƙawarin gudanar da zaɓe cikin shekara biyar.
Jama'a a yau take Sallah a Najeriya da Nijar da Saudiyya da wasu ƙasashen duniya.
Barkanmu da sake saduwa a wannan shafin namu na labaran kai-tsaye, inda ni Isiyaku Muhammed zan jagoranta zuwa wani lokaci.
Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta irin su X da Facebook da Instagram domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyon bukukuwan Sallah.
Ku kasance tare da mu.