Abu 10 da ake son Musulmi su yi ranar Idin ƙaramar Sallah
Abu 10 da ake son Musulmi su yi ranar Idin ƙaramar Sallah
Sheikh Nuru Khalid, Malamin addinin Muslunci a Abuja ya lissafa abubuwa 10 da ya kamata Musulmi su yi ranar Idin karamar sallah, kamar haka:
- Farawa da cin abinci kafin fita sallar
- Nuna godiya ga Allah ubangiji ta hanyar kyautata ko sabunta abinci domin iyali su ci so koshi kafin fita sallar Idi.
- Tabbatar da cewa an fitar da Zakkar Fidda-kai idan ba a fitar ba kafin ranar Idi.
- Yin wankan Idi wanda ba shi da maraba da sauran wankan tsarki a addinin Musulunci.
- Sanya sababbin tufafi ko kuma masu tsafta sannan a sanya turare.
- A tafi zuwa masallacin Idi da dukkan iyali - yara da manya, maza da mata har ma da masu jinin al'ada.
- Yawan ambaton Allah a fili yayin da aka kama hanyar zuwa masallacin Idi har zuwa lokacin da liman zai isa filin idi.
- Ana son bayan idar da sallah a saurari huduba daga liman.
- Sunna ce sauya hanya - wato mutum ya bi ta wata hanyar daban daga wadda aka tafi masallaci saboda al'ummar duniya su shaida cewa Musulmi suna yin biki.
- Bayan saukowa daga masallaci sai kuma a sada zumunci da kuma gudanar da bukukuwan Idi amma ba tare da wuce iyaka ba.



