Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Asabar 18/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Asabar 18/04/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. An gargaɗi 'yan jarida kan walaƙanta baƙinsu - NBC

    Hukumar kula da harkokin watsa labarai ta Najeriya ta gargaɗi masu watsa labarai da su guji cin zarafin baƙinsu yayin gudanar da shirye-shiryensu ko kuma amfani da shafukansu ta hanyar da ba ta dace ba, in da suke karya dokakin aikin, yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

    Cikin wata sanarwa, hukumar ta nuna yadda ake samun ƙaruwar karya dokar aikin jarida wanda hakan ya ci karo da ka'idojin yaɗa labarai wadda aka sabunta kashi na shida wadda ta hada da harkokin yau da gobe da na shirye-shiryen siyasa.

    Ta nuna damuwa kan yadda kafafen yaɗa labarai ke sauka doron abubuwan da aka sansu akai na wayar da kan al'umma da kwarewa da yin labarai sahihai, NBC ta ce za ta ɗauki hukunci kan duk wanda ya karya dokar hukumar.

    Tace dole abi a hankali yayin da ake tunkarar zaɓen 2027, a ba da bayanan da za su ƙarafafawa mutane gwiwa su kuma tabbatar da kwanciyar hanakali da haɗiin kai tsakanin al'umma.

  2. An kashe sojan Faransa a Lebanon

    Faransa ta ce an kashe sojanta ɗaya da ke aikin kiyaye zaman lafiya a Lebanon, yayin da aka ka jikkata wasu uku.

    Shugaban ƙasar, Emmanuel Macron ya ce akwai alamun ƙungiyar Hezbollah ce ke da alhakin harin, sai dai ƙungiyar ta musanta zargin.

    Mista Macron ya ce an yi wa motar da sojojin ke ciki ne kwanton ɓauna, a lokacin da suke kan hanyar zuwa wani yanki.

    A wani labarin na daban, sa'o'i 36 bayan fara aiwatar da yarjejeniyat tsagaita wuta, Isra'ila ta ce ta kashe mutane da dama da ta bayyana a matsayin waɗanda take zargi da kasancewa mayaƙa, yayin da suka kusanci wurin da Isra'ila ta iyakance.

  3. Wani mutum ya buɗe wa mutane wuta a Ukraine tare da kashe mutum biyar

    Magajin garin birnin Kyiv ya ce an kashe mutum biyar, yayin da wasu dama suka jikkata, bayan da wani mutum ya buɗe wa mutane wuta a babban birnin ƙasar ta Ukraine.

    An yi harbin ne a kan wani titi a gundumar Holosiivskyi da ke kudu maso yammacin birnin.

    Bayanai sun ce cikin waɗanda suka jikkata a harin har da ƙaramin yaro.

    Vitaly Klitschko ya ce yanzu haka maharin na cikin wani babban kantin sayar da kayyaki, kuma rahotonni na cewa har yanzu ana jin ƙarar harbin.

    Ƴansanda na ƙoƙarin kama mutumin tare da tsare shi.

  4. Ba za mu yarda Iran ta tursasa mana yin abin da ba mu ga dama ba - Trump

    Yanzu kuma bari mu kawo muku wasu bayanai daga ofishin shugaban Amurka na Oval.

    Inda Shugaba Trump ya yi wani taƙaitaccen jawabi game da Iran kafin ya amsa tambayoyin manema labarai.

    Ya ce akwai tattaunawa mai kyau da Iran ke yi, ya kuma bayyana Iran a matsayin ''wadda ba ta sauya daga halayen da aka santa da su ba cikin shekara 47''.

    Shugaba Trump ya ce shugabannin Iran na son rufe mashigin Hormuz, amma Amurka ba za ta bari ''su tursasa mata yin abin da ba mu ga dama ba''.

    Ya ƙara da cewa Amurka na ɗaukar tsauraran matakai.

    Shugaban na Amurka ya ce nan ''daga yanzu zuwa maraice za a samu wasu bayanai'' kan Iran, sai dai bai amsa kowace tambaya game da yaƙin ba.

    Iran dai ta sanar da sake rufe mashigar Hormuz saboda zargin Amurka da ci gaba da toshe mata tasoshin ruwanta.

  5. Ba na son yin gardama da Trump kan yaƙin Iran - Fafaroma

    Fafaroma Leo ya ce ba shi da burin yin gardama da shugaban Amurka, Donald Trump game da yain Iran.

    Yayin da yake zantawa da manema labarai a cikin jirginsa bayan tashi daga Kamaru zuwa Angola, Fafaroma Leo ya ce wasu labaran da ake yaɗawa game da ziyarsa a Afirka ba gaskiya ba ne.

    Ya buƙaci ƙarin fayyace cewa kalamansa da ya ce duniya ta ''shiga hannun azzalumai'' ba da Donald Trump yake ba.

    Shugaban na Amurka ya soke shi a matsayin wanda ya gaza wajen magance laifuka.

  6. Ƴansanda sun kuɓutar da wasu daga cikin ɗaliban da aka sace a Benue

    Rundunar ƴansandan Najeriya ta tabbatar da kuɓutar da mafi yawa daga cikin mutane 14 da aka sace a jihar Beneu.

    Kakakin rundunar ƴansandan jihar, Udeme Edet ne ya bayyana hakan, sai dai bayar da adadin mutanen da aka kuɓutar ɗin ba.

    Ya ce an kuɓutar da mutanen ne a wani samamen jami'an tsaro.

    A ranar Alhamis ne aka bayar da rahoton sace mutanen ciki har da ɗaliban da suka tafi rubuta jarrabawar JAMB.

    Harin na iya zama na farko da aka sace ɗalibai a wannan shekara a ƙasar.

  7. Labarai da dumi-dumi, An sake kai wa wani jirgin ruwa hari a kusa da Oman - UKMTO

    Cibiyar kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta Birtaniya, UKMTO ta ce wani hari da ba a san wanda ya kai shi ba ya faɗa kan wani jirgin ruwa a arewa maso gabashin Tekun Omna.

    UKMTO ta ce harin ya faɗa kan jirgin ruwa, lamarin da ya haifar da ɓarna ga jirgin.

    Hukumomin na bincike kan harin, kamar yadda UKMTO ta bayyana.

  8. Fafaroma Leo ya kammala ziyararsa a Kamaru

    Fafaroma Leo ya kamala ziyarsa ta kwanaki huɗu da ya kai Jamhuriyar Kamaru.

    Jagoran ɗariƙar Katolikn ya kammalar ziyarar ne da wani taro a sansanin sojojin sama na ƙasar da ɗaruruwan mutane suka halarta ciki har da shugaban ƙasar, Paul Biya.

    Fafaroman ya umarci Kiristoci da taimakon juna, sannan ya baya wa coci-cocin ƙasar kan ƙoƙarin da suke yi da kuma aiki da matasa.

    “Ƴan'uwan maza da mata ina yi muku bankwana da juna'', kamar yadda ya bayayna wa dandazon mutane da suka halarci taron a aranar Asabar.

    Ya kuma nuna godiyarsa kan lokacin da ya ɗauka tare da al'ummar Kamarun a tsawon kwanaki huɗun da ya yi a ƙasar.

    A tsawon kwana huɗun, ya ziyarci manyan biranen ƙasar, ciki har da Bamenda da ke yankin renon Ingilishi mai fama da ƴantawaye.

    Haka ya ziyarci birnin Doula, inda ya yi kira ga matasan ƙasar su kauce wa rikici da tozarci.

    Yayain a yake kammala ziyarar tasa a Kamaru, Fafaroma Leo ya kama hanyar Angola, wadda ita ce ƙasa ta uku cikin ƙasashen Afirka da yake ziyara a bana.

  9. Kakakin majalisar dokokin Iran ya zargi Trump da jirkita gaskiya

    kakakin majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf - da ya jagorancin tawagar wakilan ƙasar zuwa tattaunawa da Amurka a baya-bayan nan a Pakistan - ya zargi Trump da yin wasu iƙirari ''bakwai cikin sa'a ɗaya, wanda kuma ya ce dukkansu ƙarya ne''.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Ghalibaf ya ce ''ba su yi nasara a wannan yaƙin ba, kuma ba inda za su je a tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin da irin waɗannan ƙarairayi.''

    Game da mashigar Hormuz, Ghalibaf ya ce ''in dai Amurka ta ci gaba da toshe tasoshin ruwan Iran, mashigar Hormuz ba za ta kasance a buɗe ba''.

    Ya kuma jaddada kalaman da kakakin harkokin wajen ƙasar, Esmail Baghaei, wanda ya ce ''Ko mashigar ta kasance a buɗe ko a rufe, za a cimma dokokin gudanar da ita ne a zahiri ba a shafukan sada zumunta ba''.

    "Amfani da kafofin yaɗa labarai da sauya tunanin mutane sun zama wasu muhimman ɓangare na yaƙi, kuma ƙasar Iran ba za ta tasirantu da waɗannan dabaru ba,'' kamar yadda Ghalibaf ya bayyana a shafinsa na X.

  10. Sabon jagoran addinin Iran ya sake fitar da saƙo

    Kafofin yaɗa labaran Iran sun wallafa wata rubutacciyar wasiƙa da suka ce sabon jagoran addinin ƙasar, Mojtaba Khamenei ne ya aika da ita.

    Cikin wasiƙar da aka aika a yau da ake gudanar da bikin Ranar Soji ta Iran, jagodan addainin bai ambaci manyan abubuwa biyu da jami'an Iran ke tattaunawa a kan a baya-bayan nan ba, wato batun mashigar Hormuz da yarjejeniyar dakatar da yaƙi da Amurka.

    A wani ɓangare na wasiƙar Mojtaba Khamenei ya gargaɗi waɗanda ya kira ''maƙiya'' cewa sojojin Iran a shirye suke wajen sanya su ''ɗanɗanar ɗacin rashin nasara'', sai dai bai yi ƙarin haske game da hakan ba.

    A baya ma jagoran addinin yakan fitar da irin waɗannan rubutattun saƙonni.

    Tun bayan da aka naɗa shi jagoran addinin Iran a farkon watan Maris, Mojtaba Khamenei bai bayyana a bainar jama'a ba.

  11. 'Iran ta buɗe wa wani jirgi wuta a mashigar Hormuz'

    Cibiyar kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta Birtaniya (UKMTO) ta ce dakarun juyin juya halin Iran sun buɗe wa wani jirgin dako wuta a mashigar Hormuz.

    Lamarin ya faru ne kimanin mil 23 daga arewa maso gabashin Oman.

    Cibiyar UKMTO ta ce ma'aikatan jirgin sun samu kuɓuta daga harin.

    A wani labarin na daban, wasu jiragen ruwan ƴan kasuwa biyu sun ce an kai musu hari yayin da suka yi yunƙurin wucewa ta mashigar, kamar yadda wasu majiyoyi uku suka shaida wa kamfanin dillancin labari an Reuters.

    Ɗazu ne dai rundunar sojin Iran ta sanar sake rufe mashigar Hormuz kwana guda bayan buɗe ta, saboda zargin Amurka da ci gaba da rufe tasoshin ruwan ƙasar.

  12. 'Iran ta fara buɗe sararin samaniyarta'

    Kamfanin dillancin labaran Iran na IRNA, ya bayar da rahoton cewa ƙasar ta fara buɗe sararin samaniyarta ga jiragen daga wasu ƙasashe.

    Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta ƙasar ta bayar da sanarwar cewa an buɗe sararin samaniyar ƙasar da wasu filayen jiragen saman ƙasar da misalin ƙarfe 7:00 na safe agogon ƙasar, kuma sannu a hankali za a ci gaba da jigilar jirage.

    Tuni dai aka buɗe hanyoyin jiragen sama a wasu sassan gabashin ƙasar ga jirage da ke jigila tsakanin ƙasashe.

    Sararin samaniyar Iran ta kasance a rufe tun bayan fara hare-haren Amurka da Isra'ila kan ƙasar a ranar 28 ga watan Fabrairu.

  13. Sojojin Amurka sun hana jirage 21 shiga tasoshin ruwan Iran tun bayan fara rufe su

    Kamar yadda muke kawo muku rahoto a baya cewa, Shugaban Amurka, Donald Trump ya dage cewa matakin rufe tasoshin ruwan Iran zai ci gaba har sai bayan cimma yarjejeniyar dindindin ta kawo ƙarshen yaƙin Iran.

    rundunar sojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya ta ce rufe tasoshin ruwan da aka fara a ranar litinin, 13 ga watan Afrilu, ta tilasta wa jiragen ruwa 21 juyawa tare da komawa cikin Iran, bayan da aka hana su shiga tasoshin jiragen ruwan da ke cikin teku.

  14. Ƙasarmu ta shiga wani sabon babi bayan tsagaita wuta - Shugaban Lebanon

    Shugaban Lebanon ya bayyana cewa ƙasarsa na shiga wani sabon mataki, domin mayar da tsagaita wuta ta wucin gadi tsakaninta da Isra'ila zuwa ta dindindin.

    A jawabin da ya gabatar ta talabijin kwana guda bayan tsagaita wutar ta fara aiki, Joseph Aoun ya ce Lebanon ba za ta sake zama “ƴar amshin shatan kowa ba''.

    Mista Aoun ya ce ''burinmu a bayyana yake, kawo ƙarshen mamayar Isra'ila, da kuma janyewarta daga yankunanmu, da ba wa mutane damar komawa gidajensu don zaunawa lafiya kamar kowa''.

    Ya ƙara da alƙawarin cewa rundunar sojin Lebanon za ta karɓe iko da yankunan kudancin ƙasar da zarar Isra’ila ta janye dakarunta.

    Tun da farko, shugaba Trump ya ce ya haramta wa Isra'ila sake kai hari Lebanon, sai dai bayanai na cewa tun daga lokacin ta kashe mutum guda, sakamakon wani harin jirgi maras matuƙi da ta kai.

  15. Ina ce mashigar Hormuz, kuma me ya sa take muhimmanci?

    Tun bayan da Iran ta sanar da sake rufe mashigar Hormuz ƙasa da sa'o'i 24 bayan buɗe shi, sakamakon yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran ɗin, mutane na ta tambayar ina ne mashigar, kuma ma ya sa take da matuƙar muhimmanci.

    Duk da cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yana samun nasara sosai a yaƙin, wani abu da ake ganin tamkar ya tsaya masa a wuya shi ne batun datse mashigar ta Hormuz.

    Trump ya sha nanata cewa zai tura sojojin ruwan Amurka, sannan ya nemi taimakon wasu ƙasashen domin tabbatar da cewa an buɗe mashigar domin a ci gaba da tafiyar da ɗanyen mai

    Kusan kashi biyar na ɗanyen man da ake amfani da shi a duniya yana bi ta mashigar ne mai girman kilomita 40.

  16. Iran ta musanta iƙirarin Trump na mayar da uranium ɗinta Amurka

    Iran ta musanta kalaman shugaban Amurka, Donald Trump cewa ƙasar za ta yi aiki da Amurkar don gano sinadarinta na Uranium da kuma mayar da shi Amurka.

    Wani jami'in Iran mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ya ce ba a ma taɓa kawo batun a tattaunawar da ake yi ba.

    A ranar Juma'a ne Trump ya yi iƙirarin cewa Amurka za ta yi aiki da Iran don gano duka sinadarin uranium na ƙasar domin tattara shi da kuma mayar da shi Amurka.

  17. Iran ta sake rufe mashigar Hormuz saboda toshe tasoshin ruwanta da Amurka ke yi

    Rundunar sojin Iran ta ce ta sake rufe mashigar Hormuz saboda ci gaba da toshe tasoshin ruwanta da Amurka ke ci gaba da yi, kamar yadda kafofinyada labaran kasar ta Iran ta rawaito.

    Kamfanin dillancin labaran Fars da ke da alaka da dakarun juyin juya halin ƙasar, da kamfanin dillancin labarai na Iran Students da kuma kafar yada labarai ta kasar IRIB, sun rawaito wata sanarwa daga rundunar ta IRGC na cewa mashigin ruwan zai koma "irin yadda yake a baya", inda dakarun sojin za su ci gaba da tsare mashigar.

    A baya mun ga wasu jiragen ruwa na jigilar kaya zuwa hanyar ruwan - amma babu tabbas ko jiragen ruwan soji sun bi ta mashigar ba.

    Sanarwar da sojojin ta fitar ta zargi Amurka da "fashin teku", tana mai cewa "abin da ake rufe mashigar da Amurka ke yi" ya kai fashin teku.

    Tun d afarko Iran ta yi barazanar janye matakin da ta ɗauka na buɗe mashigar ga jiragen ruwa, matuƙar Amurka ba ta kawo ƙarshen takunkumin hana jiragenta wucewa da ta sanya a tekun gabas ta tsakiya ba.

    Sai dai Shugaba Donald Trump ya dage cewa matakin zai ci gaba da kasancewa har sai an cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya, yana gargaɗin cewa watakila ba zai sake tsawaita tsagaita wutar da ake ciki ba idan ta kare ranar Laraba.

  18. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hantsi.

    Abdullahi bello diginza ke muku lale maraba a daidai wannan lokaci, domin kawo muku halin da duniyar ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.